Al'ummar Congo na zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisu
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Nabeela Mukhtar Uba, Haruna Kakangi and Ibrahim Yusuf Mohammed
Zaɓen Congo: An tarwatsa rumfunan zaɓe a Bunia
Asalin hoton, Charlie Omba
Rahotanni na cewa an tarwatsa wasu rumfunan zaɓe a cibiyar ilimi ta Higher Pedagogical Institute da ke ISP Bunia a Congo.
Kawo yanzu ba a san girman ɓarnar ba.
Lamarin ya faru ne yayin da wata tawaga ta mutanen da suka ɗaiɗaita waɗanda suka kasa zuwa ƙauyukansu na asali a yankin Djugu domin yin zaɓe suka so su bayyana rashin jin daɗinsu.
Zaɓen Congo: Yadda masu zaɓe suka kafa dogayen layuka domin jefa ƙuri'a
Bayanan hoto, Al'ummar Congo fiye da miliyan 40 da suka cancanci jefa ƙuri'a sun soma kafa layi domin kaɗa ƙuri'a a zaɓukan da ake yi yau Laraba.
Bayanan hoto, Al'ummar ƙasar ta Congo za su zaɓi sabon shugaban ƙasa daga ƴan takara 19 da suke fafatawa a zaɓen har da shugaba Mai ci Felix Tshisekedi.
Bayanan hoto, Hukumar zaɓen ƙasar CENI ta bai wa al'umma tabbaci cewa duk wanda ya yi rajista zai samu damar jefa ƙuri'arsa sai dai akwai fargabar rashin tsaro da ƙalubalen da ya jawo cikas wajen kai kayayyakin zaɓe zuwa wasu sassan ƙasar.
Bayanan hoto, Kazalika, yau ɗin ne al'ummar ƙasar za su zaɓi ƴan majalisar dokoki da za su wakilce su a mazaɓunsu.
An soma zaɓen shugaban ƙasa a Congo
Al'umma a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo sun soma kaɗa ƙuri'a yau Laraba a zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisar dokoki.
Masu kaɗa ƙuri'a sun fusata a Kinshasa, babban birnin ƙasar sakamakon rashin buɗe wasu rumfunan zaɓe a kan lokaci.
Hukumar zaɓe ta ƙasar Congo ta ce a shirye take ta gudanar da zaɓen duk da tarin ƙalubale musamman daga yankunan da ƴan tawaye ke damalmaya lamarin da ke hana yin zaɓe.
Shugaba Felix Tshisekedi zai fafata da yan takara 18 da ke neman kujerar ta shugaban ƙasa.
A karon farko, al'ummar Congo da ke zaune a kasashen ƙetare biyar har da Belgium da ta reni ƙasar - za su jefa ƙuria.
An samu koma-baya a ƙoƙarin neman dakatar da yaƙi a Gaza
Asalin hoton, EPA
An samu koma baya a ƙokarin da kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya ke wajen cimma yarjejeniyar samar da wani daftari da zai yi kiran a dakatar da yaƙi a Gaza.
Ƙuri'ar da aka yi niyyar kaɗawa a ranar Litinin, an ɗaga har zuwa yau Laraba.
Masu shiga tsakani na ƙoƙarin amincewa da buƙatun da Amurka ba za ta ƙi amincewa da su ba misali, wajen samar da kalmar da za ta maye batun tsagaita wuta da gaggauta dakatar da garkuwa zuwa bayar da damar rarraba kayan agajin da ake matuƙar buƙata.
Wakliyar BBC ta ce Amurka da Isra'ila ba sa goyon bayan tsagaita wuta, sannan kuma sun hau kujerar naƙi a kan matakin da kwamitin ya buƙata tun da farko.
Kotu Ƙolin Colorado ta haramta wa Trump tsayawa takara a 2024
Asalin hoton, REUTERS
Kotun ƙoli a jihar Colorado ta Amurka ta yanke hukuncin cewa tsohon Shugaban ƙasar Donald Trump bai cancanci tsayawa takara ba a jihar kuma ba zai iya fitowa a zaɓen fidda gwani na jam'iyyar Republican a shekara mai zuwa ba.
Kotun ta ce saboda abin da tsohon shugaban ya yi a ranar 6 ga Janairun 2021 - ranar da aka kai hari kan ginin majalisa - Capitol hill – da aka yi wa kallon yunƙurin tayar da zaune tsaye.
Ofishin yaƙin neman zaben Trump ya kira hukuncin kotun a matsayin abin da ya saɓawa dimokradiyya, sannan kuma ya ce zai ɗaukaka ƙara zuwa kotun ƙolin tarayya.
Za a jingine hukuncin har sai kotun tarayya ta yanke nata, to amma duk da haka jami'an zaɓe a Colorado sun ce akwai buƙatar a yi abin da ya dace kafin nan da 5 ga watan Janairun 2024.
Hukuncin bai hana Trump tsayawa takara ba a sauran jihohin Amurka.
Barka da hantsi!
Masu bibiyarmu a wannan kafa, assalamu alaikum. Da fatan mun wayi gari cikin ƙoshin lafiya.
Kamar koda yaushe, za mu wallafa muku labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da sassan duniya a wannan shafi na Kai Tsaye.
Nabeela Mukhtar Uba ce tare da ku a wannan lokaci. Za ku iya zuwa shafukanmu na sada zumunta domin karanta wasu labaran da ma kallon bidiyo.