Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba and Haruna Kakangi

  1. Malamai kusan 4,000 sun faɗi jarabawar ƙwarewa a Najeriya

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar yi wa Malaman Makaranta Rijista ta Najeriya (TRCN) ta bayyana cewa kimanin malaman makaranta dubu uku da dari tara da sittin da uku ne suka faɗi jarrabawar da ke nuna ƙwarewa da suka zana a watan Nuwamban wannan shekara ta 2023.

    Hukumar ta ce malamai dubu goma sha biyar da dari bakwai da hamsin da uku ne suka zauna jarabawar, daga ciki dubu goma da dari shida da talatin da shida suka samu nasara, yayin da dubu uku da dari tara da sittin da uku suka fadi.

    Wannan lamari ya sa masana a ɓangaren ilmi a Najeriya yin tsokaci game da batun.

    Masana irin su Dakta Aliyu Umar Tilde, tsohon kwamishinan ilimi na jihar Bauchi, ya ce jarabawa ce mai kyau saboda "da yawa daga cikin malamai, ana samu suma kansu suna buƙatar karatu."

    Ya ba da misali da jihar Kaduna inda a kwanakin baya, aka yi wa malamai jarabawa kuma da yawan su suka faɗi.

    "Sanin cewa akwai rauni wajen horar da malaman shi ne ya sa dole a samar da jarabawa kafin a ba da lasisi", kamar yadda masanin ya ce.

    Ya ce a baya, ba a irin wannan jarabawa ta tantance ƙwarewar malami saboda karatu a lokacin yana da ƙarfi a makarantu "amma daga baya da makarantu suka yi yawa, har da na jeka na yi ka, akwai kuma yaudara da shaidar karatu ta bogi, wannan shi ne ya tilasta cewa ya kamata a jarraba ka kafin a tabbatar." in ji Dakta Tilde.

    Ya bayyana cewa akwai buƙatar a yi gyara sosai a ɓangaren ilimi na Najeriya idan ana son tsarin karatu ya koma irin na shekarun baya, lalacewar gwamnati shi ne ya haifar da lalacewar ilimin, a cewarsa.

    Masanin ya ce sai an samu gyara ta ɓangaren gwamnati da su kansu malaman sannan al'amura za su daidaita a tsarin ilimin ƙasar.

  2. Mutum 250,000 sun tserewa rikicin Sudan – MDD

    ..

    Asalin hoton, AFP

    Hukumar da ke kula da ƴan ci-rani ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce aƙalla mutum dubu 250 ne suka tserewa rikici a Sudan yayin da dakarun ƙungiyar RSF suka doshi kudancin Khartoum, babban birnin Sudan.

    Dubban mutane ne suka rasa muhallansu inda suka nemi mafaka a Wad Madani don tserewa faɗan da ake a babban birnin ƙasar.

    Wad Madani na ƙarkashin ikon sojojin ƙasar waɗanda suka fatattaki dakarun RSF.

    Rundunar sojin Sudan ta zargi Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da goyon bayan ƙungiyar RSF, wadda ta ce tana aikata kisan kiyashi a yankunan da ta kwace, zargin da Hadaddiyar Daular Larabawan ta musanta.

  3. Mutum fiye da 100 sun mutu sakamakon girgizar ƙasa mafi muni a China

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Mahukunta a China sun ce gine gine sun rushe sosai, sannan wutar lantarki ta ɗauke bayan girgizar kasar da ta afkawa lardin Gansu da ke arewa maso yammacin China.

    Ga abubuwan da muka sani game da ibtila'in kawo yanzu:

    • Aƙalla mutum 118 ne suka mutu a girgizar ƙasar da ƙarfinta ya kai maki 6.2 a ma'auni a daren Litinin.
    • Masu aikin ceto suna hanzarin nemo waɗanda suka rayu sai dai matsanancin sanyin da ake yi na nufin suna da ƙarancin lokacin gudanar da aikin ceton.
    • Shugaban tawagar masu aikin ceton a Gansu ya faɗa wa BBC cewa yanayin sanyin da ake yana da wuyar jurewa kuma masu aikin ceto daga wasu sassan ƙasar da suke ba da gudummawa za su fuskanci wahalar jure wa yanayin.
    • Girgizar kasar ta gansu ita ce mafi muni da ta afku a China cikin shekara 10 bayan girgizar da ta afku a 2010 wadda ta kashe kusan mutum 3000.

    Wakiliyar BBC ta ce wasu bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda mutane ke gujewa gidajen da suke girgiza, kuma yawancin inda abin ya shafa yanayinsu ya canja.

    Wani bincike na Amurka ya ce girgizar ƙasar ta faru ne cikin dare. Kafar yaɗa labaran China ta ce tuni aka tura jami'an ceto da masu kashe gobara wuraren da girgizar ta afkawa.

  4. Ricikin Rivers: Abu takwas game da yarjejeniyar Wike da Fubara

    ..

    Asalin hoton, RIVERS STATE GOVERNMENT PRESS

    Bayan shafe tsawon makwanni da fara zaman doya da manja tsakanin gwamnan jihar Rivers Siminilinayi Fubura da wanda ya gada Nyesom Wike, kawo yanzu za a iya cewa an sasanta su.

    Yayin wani zama na shiga tsakani da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya jagoranta a fadarsa, ɓangarorin biyu sun sanya hannu kan wata takardar yarjejeniya da suka rattaba hannu a kai.

    Ga abin da yarjejeniyar ta ƙunsa:

    1. Gwamna Siminalayi Fubara zai janye dukkan wata ƙara da ya shigar wadda ta shafi rikicin daga gaban kotu nan take.

    2. Shi ma ɓangaren Wike zai janye dukkan wani yunƙuri na tsige gwamnan nan take.

    3. Ɓangarorin sun amince da shugabancin Martin Amaewhule a matsayin Kakakin majalisar dokokin jihar Rivers da sauya sheƙar da wasu ƴan majalisar 27 suka yi daga Jam'iyyar PDP zuwa APC.

    4. Gwamna Fubara zai tsame kansa daga shiga harkokin majalisar ta hanyar dakatar da biyansu kuɗaɗensu da sauran haƙƙoƙinsu da a baya ya dakatar bayan ɓarkewar rikicin.

    5. Bai wa ƴan majalisar damar zama a duk inda suke so ba tare da katsalandan ba daga ɓangaren zartaswar jihar ba da a baya ta rushe wani sashe na ɓangaren majalisar bisa uzurin da ta bayar na cewa ginin ya yi kan hanya.

    6. Mayar da dukkan kwamishinonin da suka ajiye aiki sakamakon rikicin kan muƙamansu ba tare da ɓata lokaci ba.

    7. Gwamna Fubara zai sake gabatar da kasafin kuɗi a gaban halastacciyar majalisar dokokin jihar domin amincewa.

    8. Fasa duk wani yunƙuri na cire shugabannin ƙananan hukumomin jihar daga ɓangaren gwmanati.

  5. Aƙalla mutum 20 aka kashe a Rafah – Hamas

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Ma'aikatar lafiya ta Hamas da ke Gaza ta ce luguden wutar da aka shafe dare Isra'ila na yi a Rafah da ke Kudancin Gaza ya halaka aƙalla mutum 20.

    A cewar jami'an Gaza, hare-haren Isra'ila sun shafi gine-gine guda uku.

    Dubban ƴan Gaza na samun mafaka a Rafah da ke iyakar Masar ta kudancin Zirin Gaza yayin da sojojin Isra'ila suka umarci farar hula su fice zuwa kudanci inda yaƙi ya ƙazanta a Khan Younis.

  6. Da fatan mun wayi gari lafiya!

    Kamar kullum, a wannan shafi na Kai Tsaye, za mu riƙa kawo muku labarai da rahotannin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta da ma sauran sassan duniya.

    Sunana Nabeela Mukhtar Uba kuma ina tare da abokin aiki, Haruna Ibrahim Kakangi. Sai ku ci gaba da kasancewa tare da mu a wannan shafi da ma shafukanmu na shafukan sada zumunta domin sanin abubuwan da ke faruwa a duniya.