An shiga rana ta ƙarshe ta yaƙin neman zaɓe a Congo

Asalin hoton, Reuters
A yau Litinin ne za a kammala yaƙin neman zaɓe a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo, kwana biyu kafin masu zaɓe su jefa ƙuri'a.
Rashin tsaro da batun lafiya da ilili na cikin manyan batutuwan da suka mamaye yaƙin neman zaɓe yayin da ƙasar ke shirin shiga zaɓe mai zafi.
Babu masaniya kan ko zaɓukan za su gudana a gabashi inda gomman ƴan bindiga ke cin karensu ba babbaka.
Gwamnati na amfani da jiragen sama na sojojin Congo da na Masar da dakarun wanzar da zaman lafiya na Monusco domin jigilar ragowar kayayyakin zaɓe, kamar yadda kakakin gwamnati Patrick Muyaya ya bayyana ranar Lahadi.
An tantance fiye da yan takara 12 har da Shugaba mai ci Felix Tshisekedi da Denis Mukwege mai lambar yabo ta Nobel da kuma fitaccen jagoran ƴan hamayya Moïse Katumbi a matsayin waɗanda za su fafata a zaɓen.
Ƙungiyar Human Rights Watch ta bayyana damuwa game da tashin hankali gabanin zaɓen.
Ƴan bindiga sun kashe ƴan takara biyu na kujerar majalisar dokoki yayin da suke neman ƙuri'u.





