Kotun Ƙoli za ta saurari ƙarar zaɓen gwamnan Kano ranar Alhamis

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, Haruna Kakangi and Umar Mikail

  1. Sai da safe

    Mun zo ƙarshen rahotonni a wannan shafi na kai-tsaye.

    Ku tara gobe da safe don samun wasu sababbi.

    Sai da safenku.

  2. Wike da Fubara sun sasanta rikicin jihar Rivers bayan ganawa da Tinubu

    Wike da Fubara

    Asalin hoton, Rivers State Governemnt

    Bayan shafe makonni suna tafka rikicin siyasa a jihar Rivers da ke kudancin Najeriya, mahukuntan jihar sun cimma matsaya bayan ganawa da Shugaba Bola Tinubu a Abuja.

    Tinubu ya gana ne da Gwamna Siminalayi Fubara da wanda ya gada kuma Ministan Abuja Nyesom Wike a asirce. A ganawar, akwai kuma tsohon gwamnan jihar, Peter Odil da wasu sarakuna.

    Bayan ganawar da aka yi ranar Litinin, duka ɓangarorin biyu suka amince cewa dukkan ƙorafin da Gwamna Fubara ya shigar a gaban kotu za a janye su nan take.

    Shi ma ɓangaren Wike ya amince cewa za su dakatar da dukkan yunƙurin tsige Fuabara da suka fara yi a majalisar dokoki.

    Wike da Fubara da Kakakin Majlisar Dokokin Rivers Amaewhule, waɗanda su ne jagoroin rikicin, duka sun saka hannu kan takardar yarjejeniyar.

    Kazalika, ɓangarorin sun amince su goya wa Martin Amaewhule baya a matsayin kakakin majalisar - wanda da ma shi ne gwamnan ke mara wa baya - ba Edison Ehie ba.

    • Abu biyar da ke da ɗaure kai a rikicin siyasar Rivers
  3. RSF ta ƙwace sansanin sojojin Sudan

    RSF

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Wani mayaƙin RSF lokacin da suka kai hari wani sansanin sojin Sudan a watan Yuni

    Mazauna birnin Wad Madani na ƙasar Sudan sun ce dakarun Rapid Support Forces (RSF) sun kai hari a wani asibiti tare da ƙwace wani sansanin sojoji.

    Yankin na ɗauke da dubban ɗaruruwan fararen hula da suka yi gudun hijira zuwa arewacin ƙasar daga Khartoum, babban birnin kasar.

    Dallia Abdelmoniem, wacce a halin yanzu take birnin Alkahira amma tana da iyali a Wad Madani, ta shaida wa shirin BBC Newsday abin da ya faru a sansanin sojojin.

    "Wuri ne da sojoji suka mamaye kuma kasancewar RSF ta iya kutsawa sansanin sojojin abin tashin hankali ne," in ji ta.

    "Hakan na nufin cewa RSF suna da ƙwarin gwiwa kan iyawarsu, kuma cewa yakin yana ƙara ƙamari. Kuma wannan wuri ne da ke da tsaro ga 'yan gudun hijira da suka tsere daga Khartoum. Ba ƙaramin tashin hankali ba ne ga fararen hulan da ke wurin saboda yanzu ba su da wurin zuwa''.

    Ƙasashen duniya sun nuna damuwar cewa yakin - wanda ya fara a watan Afrilu - yana ƙara ta'azzara.

    A karshen mako, Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta yi kira ga RSF da ta dakatar da kutsen da take yi a a Wad Madani.

    Sudan
  4. Kwamatin Tsaro na MDD zai kaɗa ƙuri'a kan ƙudirin tsagaita wuta a Gaza ranar Talata

    MDD

    Asalin hoton, Reuters

    Kwamatin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ya ɗage ƙuri'ar da ya yi niyyar kaɗawa kan ƙudirin da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta gabatar da ke kiran "tsagaita wuta nan take" zuwa gobe.

    An tsara za a jefa ƙuri'ar ce a yammacin yau Litinin amma kuma an shafe yinin yau ɗin ana tafka siyasar difilomasiyya kan ƙudirin.

    An ce Amurka na son rage kaifin kalaman da ke cikin kundin ƙudirin, wanda a yadda yake a yanzu yana buƙatar Isra'ila da Hamas su bari a shiga da kayan agaji Gaza ta sama da ƙasa da kuma ruwa.

    Haka nan, ƙudirin ya nemi a saki mutanen da Hamas ke garkuwa da su nan take ba tare da sharaɗi ba, kuma ya jaddada goyon baya kan kafa ƙasa biyu.

    Gwamnatin Amurka, ɗaya daga cikin ƙasashe biyar masu kujerar-na-ƙi, ta ƙi amincewa da ƙudirin da ya nemi a "tsagaita wuta don kai kayan agaji" a Gaza da aka kaɗa wa ƙuri'a a baya.

  5. Kenya ta ƙulla gagarumar yarjejeniyar tattalin arziki da Turai

    ..

    Asalin hoton, William Ruto/X

    Kenya da Tarayyar Turai sun ƙulla wata muhimmiyar yarjejeniyar tattalin arziki da za ta bai wa ƙasar ta gabashin Afirka dama mara iyaka ta zaɓar kayayyakin da za ta shigar zuwa Turai.

    Shugaban Kenya, William Ruto da Shugabar majalisar Tarayyar Turai, Ursula Von Der Leyen su halarci taron rattaba hannu kan yarjejeniyar da aka yi a Nairobi, babban birnin Kenya.

    Shugaba Ruto ya ce da wannan yarjejeniya, babban burinsu shi ne buɗe kafar samun kuɗaɗe ga al'umma - manoma da mata da masu aikin sufuri da sauran ma'aikata da ke ba da gudummawa ta fuskoki da dama bai wa mutane damar samun kuɗi.

    Akwai buƙatar ita ma Kenya ta buɗe kasuwanninta ga kayayyakin turai.

    Dole ne majalisar dokokin Turai da Kenya su amince da yarjejeniyar kafin ta soma aiki.

  6. An kashe Falasɗinawa 19,453 zuwa yanzu - Ma'aikatar lafiyar Gaza

    Ma'aikatar lafiyar Gaza ƙarƙashin Hamas ta ce an kashe Falasɗinawa 19,453 tun bayan ɓarkewar yaƙi tsakanin Isra'ila da Hamas.

    Mutum 151 ne suka mutu sakamakon hare-haren Isr'aila a Gaza cikin kwana ɗaya da ya wuce, in ji ma'aikatar.

    Cikin wata sanarwa, ta ƙara da cewa adadin ya ƙunshi mutanen da aka kashe ne a harin Isra'ila kan sansanin Jabalia.

    An raunata sama da mutum 52,000 tun daga ranar 7 ga watan Oktoba, a cewarta.

  7. Bitar rukunin farko zuwa na hudu a gasar Kofin Ƙasashen Afirka ta 2023

  8. Za a gudanar da zaɓukan cike gurbi a watan Fabarairu – Inec

    ..

    Asalin hoton, @inecnigeria/X

    Hukumar zaɓe a Najeriya, Inec, ta ce tana duba yiwuwar gudanar da zaɓukan cike gurbi da kuma sake zaɓuka a wasu wuraren ranar 1 ga watan Fabarairu domin cike guraben da ake da su a majalisun dokoki na jiha da na tarayya.

    Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka a wani taro da shugabannin jam'iyyu gabanin zaɓukan.

    Yakubu ya ce a ƙarshen shari'oi kotuna sun umarci Inec ta gudanar da zaɓen cike gurbi a mazaɓu 34 na jihohi, da kuma tarayya da suka haɗa da ɗaya a majalisar dattawa, sai mazaɓun tarayya 11, da mazaɓun jihohi 22.

    ..

    Asalin hoton, @inecnigeria/X

    Shugaban Inec ya ce hukumar za ta gudanar da zaɓukan ne sakamakon gurbin da aka samu sanadin ajiye aiki ko kuma mutuwa.

    Ya ƙara da cewa za a saki jadawalin zaɓen da kuma ranar da za a yi a ƙarshen taron da shugabannin jam'iyyu.

  9. Fafaroma ya ce limaman Katolika na iya yi wa ma'auratan jinsi ɗaya addu'a

    Paparoma

    Asalin hoton, Getty Images

    Fafaroma Francis ya ce limaman coci za su fara sa albarka kan ma'auratan jinsi ɗaya, a wani gagarumin cigaba ga masu fafutukar auren jinsi a Cocin Roman Katolika.

    Shugaban na ɗarikar Katolika ya ce ya kamata a bar limamai su albarkaci ma'auratan jinsi ɗaya a wasu lokuta.

    Sai dai fadar ta Vatican ta ce bai kamata albarkar ta kasance cikin al'adun coci na yau da kullun ba, ko kuma ta shafi zama da farka ko bukukuwan aure ba.

    Ya kara da cewa ana ci gaba da daukar aure a matsayin tsakanin mace da namiji.

    Paparoma Francis ya amince da wata takarda da fadar Vatican ta fitar inda ta sanar da sauyin a ranar Litinin.

    A ɗariƙar Katolika, saka albarka ko kuma "blessing" a Turance na nufin yi addu'a, wadda fasto ko malamin coci kan yi don nema ma'aurata alhairai daga Allah, ko kuma sauran mutanen da ake yi wa addu'ar.

    Fadar ta Vatican ta ce ya kamata ya zama alamar cewa "Allah yana maraba da kowa", amma takardar ta ce dole ne limaman coci su duba lamuran ɗaya bayan ɗaya.

    Da yake gabatar da takardar, Cardinal Víctor Manuel Fernández, shugaban cocin, ya ce sabuwar sanarwar ta ci gaba “daidai da koyarwar Cocin kan batun aure”.

    Cardinal Fernández ya jaddada cewa sabon matakin bai tabbatar da amincewar cocin kan ma'auratan jinsi ɗaya ba.

    Sanarwar na nuni ga sassauci kan auren jinsi ɗaya daga ɓangaren Cocin, kodayake ba ya nufin cewa cocin ta sauya matsayi.

  10. Kotun Ƙoli za ta saurari ƙarar zaɓen gwamnan Kano ranar Alhamis

    Abba Kabir Yusuf da Nasiru Gawuna

    Kotun Ƙolin Najeriya ta sanya ranar Alhamis, 21 ga watan Disamba domin sauraron ƙarar da aka shigar kan zaɓen gwamnan jihar Kano.

    Gwamna Kabir Abba Yusuf na jam'iyyar NNPP na kalubalantar hukuncin kotun daukaka ƙara da ta tabbatar da hukuncin kotun sauraran ƙararrakin zaɓe da ta soke nasararsa tare da bayyana Nasiru Gawuna na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar na ranar 11 ga Maris.

    Lauyan Gwamna Yusuf, Barista Bashir Tudun Wazirci, ya tabbatar wa BBC cewa an ba su sanarwar fara sauraron ƙarar a matsayinsu na tawagar lauyoyin da ke wakiltar gwamnan da jam’iyyarsa.

    Wannan ne karon farko da kotun za ta fara zama, inda za ta fara jin bahasi, yayin da har yanzu akwai muhimman takardun da ba a kai wa kotun ba.

    "Har yanzu akwai takardun da muka [NNPP] ba su [APC] da ba su dawo mana da martani ba tukunna, kuma mu ma muna da damar sake yin martani idan suka dawo da su," in ji Bashir Tudun Wazirci.

    Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukuncin cewa Gwamna Yusuf ba dan jam’iyyar NNPP ba ne a lokacin da ya tsaya takarar gwamna.

    Amma tabbataccen kwafin hukuncin, wanda ya bayyana kwanaki kaɗan bayan zaman kotun, ya kunshi bayanai masu karo da juna game da hukuncin da ya janyo ce-ce-ku-ce.

    Duka ɓangarorin biyu dai sun yi iƙirarin cewa hukuncin ya tabbatar da nasarar da suka samu a zaben.

    Sai dai jam'iyyar NNPP ta shigar da ƙara a gaban kotun ƙoli, inda take ƙalubalantar hukuncin kotun daukaka ƙara da ta tabbatar da hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaben gwamna.

  11. Abdel Fattah al-Sisi ya lashe zaɓen shugaban Masar karo na uku

    al-Sisi

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi ya lashe zaɓe a karo na uku bayan ya yi nasarar cinye kashi 90 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa makon da ya gabata, in ji hukumar zaɓen ƙasar.

    'Yan takara uku ne suka fafata da shi a zaɓen, amma babu wanda ake ganin zai iya yi masa wani ƙalubale.

    Mista Sisi ya zama shugaban ƙasa a 2014 - bayan ya lashe kashi 97 na ƙuri'un. Ya ƙara yin nasara da irin wannan adadin a 2018.

    Wannan nasara na nufin zai ci gaba da mulki har zuwa 2029, lokacin da kundin tsarin mulki zai hana shi sake yin takara.

  12. Farar hula da dama sun mutu a yaƙin Isra'ila da Gaza – Sunak

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Firaministan Birtaniya, Rishi Sunak ya ce "farar hula da dama sun rasa rayukansu" a yaƙin da ake tsakanin Isra'ila da Hamas inda ya ce "babu wanda yake son ganin wannan yaƙin ya ci gaba".

    Da yake magana da ƴan jarida a Scotland, Sunak ya sake jaddada cewa yayin da Isra'ila ke da ikon kare kanta sakamakon hare-haren ranar 7 ga watan Oktoba, dole ne ta yi hakan bisa tsarin doka.

    A makon da ya gabata, gwamnatin Birtaniya ta ƙara ƙaimi a kiraye-kirayen tsagaita wuta a Gaza.

    Sunak ya ce gwamnatinsa ta yi ta kira a cimma yarjejeniya "inda har aka saki wasu da aka yi garkuwa da su, Hamas ta daina harba rokoki zuwa Isra'ila kuma muna ci gaba da kai kayan agaji zuwa Gaza".

  13. Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da nasarar Fintiri

    AHMADU UMARU FINTIRI

    Asalin hoton, AHMADU UMARU FINTIRI

    Kotun ƙoli da ke zama a Abuja ta tabbatar da nasarar gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri na jam'iyyar PDP a zaɓen gwamnan jihar na 2023, tare da yin watsi da ɗaukaka ƙarar A'ishatu Binani ta jam'iyyar APC.

    A hukuncin da kotun ta yanke a yau Litinin, alƙalan kotun sun kuma buƙaci ƴar takarar ta APC, A'ishatu Binani ta biya Fintiri da jam'iyyar PDP kudi naira 500,000.

    Kotun ƙolin ta yi alla-wadai da matakin kwamishinan zaɓen jihar ta Adamawa, Hudu Ari, na sanar da sakamakon zaɓe gabanin kammala ƙidayar ƙuri'a.

    Wannan hukunci ya gaskata hukuncin kotun sauraron ƙorafin zaɓe ta jihar ta Adamawa, wadda ta yi watsi da ƙorafin sanata Binani, saboda ta gaza gabatar da shaidun da za su gamsar da kotun cewa an yi aringizon ƙuri'u a lokacin zaɓen.

    • Fintiri ya ci zaɓen gwamnan Adamawa
    • Binani ta nemi kotu ta hana INEC 'soke nasararta ta zama gwamna'
  14. Yadda za a kara a zagayen ƴan 16 a gasar Europa

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Feyenoord v Roma

    Lens v Freiburg

    Benfica v Toulouse

    Galatasaray v Sparta Prague

    AC Milan v Rennes

    Young Boys v Sorting Lisbon

    Sporting Braga v Qarabag

    Shakhtar Donetsk v Marseille

  15. Yadda za a kara a zagayen ƴan 16 a gasar zakarun Turai ta Champions League

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Manchester City masu riƙe da kofin za su kara da ƙungiyar Copenhagen a zagayen ƴan 16, yayin da Arsenal za ta kara Porto.

    Ga yadda karawar za ta kasance:

    • Porto v Arsenal
    • Napoli v Barcelona
    • Paris St-Germain v Real Sociedad
    • Inter Milan v Atletico Madrid
    • PSV Eindhoven v Borussia Dortmund
    • Lazio v Bayern Munich
    • Copenhagen v Manchester City
    • RB Leipzig v Real Madrid
  16. Manyan ƙawayen Isra'ila sun nemi a tsagaita wuta a Gaza

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙawayen Isra'ila uku - Jamus da Birtaniya da Faransa sun bi sahun kiraye-kirayen da ake a duniya na neman a kawo ƙarshen yaƙin da ake a Gaza.

    Sakataren harkokin wajen Birtaniya David Cameron ya bi sahun ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock don kiran a tsagaita buɗe wuta a yaƙin Isra'ila da Hamas - amma sai idan zai ɗore.

    Cameron da Baerbock sun yi wani rubutu na haɗin gwiwa da aka wallafa a jaridar Sunday Times ta Birtaniya cewa "ƙudirinmu ba wai kwao ƙarshen yaƙin yau bane. Dole ya zama zaman lafiya ya ɗore tsawon kwanaki da shekaru."

    Birtaniya da Jamus a makon da ya gabata sun janye jiki daga shawarar da aka cimma a Majalisar Ɗinkin Duniya wadda ƙasashe 153 suka goyi baya don a gaggauta kawo ƙarshen yaƙi a Gaza.

    Ministar harkokin wajen Faransa Catherine Colonna ta ce "ana kashe farar hula da dama".

    • Matan da ke haihuwa ana tsaka da yaƙi a Gaza
    • Wace ce Hamas, mene ne ke faruwa a Isra'ila, da sauran tambayoyi
  17. Abu huɗu da suka kamata ku sani kan zazzaɓin Dengue da ya ɓulla a Najeriya

  18. Mutum takwas sun mutu bayan fashewar ma'ajiyar mai a Guinea

    Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ba da rahoton kisan mutum takwas a fashewar rumbun mai a Conakry, babban birnin Guinea.

    AFP ya ambato wani jami'i a asibiti na cewa "an kawo mutum takwas da suka ƙone zuwa asibitin Ignace Deen,"

    Tun farko kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa wani jami'in ɗan sanda ya ce mutum takwas sun mutu.

  19. An rufe makarantu a Guinea bayan fashewar rumbin mai

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Hukumomin soji a Guinea sun ba da umarnin rufe dukkan makarantu da ke Conakry, babban birnin ƙasar sakamakon fashewar da aka samu a wata ma'ajiyar mai da safiyar yau Litinin.

    Fashewar babbar ma'ajiyar mai ta kamfanin mai na Guinea a yankin Kaloum ta haddasa gobara lamarin da ya janyo mazauna yankin tserewa.

    Ba a samu asarar rai ba sai dai wani babban jami'in ɗan sanda ya faɗa wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa akalla mutum takwas aka kashe, 84 kuma suka jikkata sanadiyyar lamarin.

    Sojojin da ke mulki a ƙasar sun ba da umarnin a rufe dukkanin makarantun gwamnati da na masu zaman kansu tare da kira kan ma'aikata su zauna a gida.

    Sojojin sun kuma ce a rufe dukkan gidajen ban da masu ayyukan gaggawa da ke yankin.

    Kawo yanzu, ba a bayyana abin da ya janyo gobarar ba kamar yadda hukumomi suka ce kuma tasirin gobarar na iya shafar jama'a.

    Gwamnati ta buƙaci mutane a yankin su kauce daga wajen da abin ya faru inda kuma ta ba da tabbacin kashe wutar da kuma daƙile girman ɓarnar da take iya haddasawa.

  20. Gwamnatinmu za ta yi wa Musulmi da Kirista adalci - Uba Sani

    ...

    Asalin hoton, X/Uba Sani

    Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani ya bai wa al'ummar musulmi da kirista da ke jihar tabbacin cewa gwamnatinsu za ta yi wa kowa adalci.

    Sanata Uba Sani ya bayyana hakan lokacin da ya halarci taron waƙoƙin kirsimeti da ƙungiyar kiristoci ta Najeriya CAN ta shirya a cocin Ecwa, reshen Kaduna.

    An shirya taron domin rera waƙe-waƙen yabo da yin addu'oi domin samun zaman lafiya da haɗin kai a jihar Kaduna.

    A jawabinsa, shugaban ƙungiyar CAN reshen jihar Kaduna, Rev Dr John Joseph Hayab ya yaba wa gwamnatin Kaduna saboda yadda ta maido da yadda da kuma yadda take sa kowa cikin tsarin tafiyar da shugabancinta.

    Gwamna Uba Sani ya ƙara da cewa "za su yi duk mai yiwuwa domin ganin an samu ci gaba a kowane ɓangare na jihar Kaduna musamman yankunan karkara."

    Ya kuma ce cikin ƴan kwanaki masu zuwa, gwamnatinsu za ta fara ayyukan shimfiɗa tituna a wasu kananan hukumomi da ke kudancin jihar kamar yadda suka yi a arewacin jihar.

    • Harin sojoji a Kaduna: 'An ƙona mana yara an ƙona mana mazaje'
    • Ba na kamun ƙafa don Tinubu ya naɗa ni shugaban ma'aikata-El-Rufai