Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, Haruna Kakangi and Abdullahi Bello Diginza

  1. Kotun Ecowas ta umarci sojoji su saki Bazoum nan take

    ..

    Asalin hoton, Facebook/Bazoum

    Kotun Ecowas ta umarci sojojin Nijar da su gaggauta sakin Mohammed Bazoum da suka tsare tun daga ranar 26 ga watan Yuli da suka hamɓarar da shi.

    Kotun ta nemi a gaggauta sakin sa ba tare da wani sharaɗi ba sannan a mayar da Bazoum kan kujerarsa, kamar yadda alƙalin kotun ya faɗa a ƙarar da aka saurara a Abuja, babban birnin Najeriya.

    A ranar Alhamis ne ƙungiyar ta Ecowas ta sanar da cikakkiyar dakatarwar da ta yi wa Nijar sanadiyyar juyin mulkin.

    A baya, wasu ƙasashe mambobin ƙungiyar sun yi watsi da hukuncin kotun ta Ecowas.

    "Mohamed Bazoum ne yake wakiltar Nijar ... kuma har yanzu shi ne shugaban Jamhuriyar," kamar yadda hukuncin kotun ya bayyana.

    "Akwai haƙƙoƙin da aka take." An tsare Bazoum a gidansa na shugaban ƙasa tare da mai ɗakinsa da ɗansu tun lokacin da aka tsige shi.

    A tsakiyar watan Satumba ne, hamɓararren shugaban ya nemi kotun ta Ecowas ta bayar da umarnin sakin shi tare da mayar da ƙasar kan turbar dimokraɗiyya.

  2. Kotun ƙoli ta ce dole Nnamdi Kanu ya fuskanci shari'a

  3. Kotun ƙolin Najeriya ta ce dole Nnamdi Kanu ya fuskanci shari'a

    .

    Asalin hoton, Nnamdi Kanu

    Kotun Ƙoli ta amince da buƙatar gwamnatin Najeriya da ke ƙalubalantar hukuncin kotun ɗaukaka ƙara na soke tuhume-tuhumen da ake yi wa Nnamdi Kanu, jagoran ƙungiyar Ipob mai neman ɓallewa daga Najeriya.

    Kotun Ƙolin ta ce dole ne Kanu ya fuskanci shari'a.

    A watan Oktoban bara ne, wata kotun ɗaukaka ƙara ta bayar da umarnin a saki Mista Kanu inda ta ce akwai kura-kurai a shari'ar.

    Sai dai gwamnati ta sake shigar da ƙara inda ta ce Kanu barazana ne ga tsaron Najeriya.

  4. Isra'ila na da ikon yaƙar Hamas - Jake Sullivan

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Mai ba da shawara kan harkokin tsaron Amurka, Jake Sullivan ya ce Amurka na son ganin sakamako game da ƙudirin Isra'ila na kare mutuwar farar hula a Gaza.

    Sullivan ya ce akwai batu na mutuntawa da ya kamata a bai wa Falasɗinawa a matsayinsu na mutane kuma ya ce ya aike wannan saƙo ga gwamnatin Isra'ila.

    Ya ƙara da cewa Hamas ta ci gaba da riƙe ƴan Isra'ila cikin mummunan yanayi kuma suna amfani da farar hula a matsayin kariya, suna fakewa da asibitoci da makarantu.

    Sullivan ya jaddada cewa Isra'ila tana da ikon ta yaƙi Hamas bisa dokokin ƙasa da ƙasa.

  5. An gano gawawwakin sojin Isra'ila biyu a Gaza

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Isra'ila ta ce an gano gawawwakin sojojinta biyu da aka yi garkuwa da su a Gaza.

    Rundunar sojin Isra'ila IDF ta ce ta gano gawarwakin sojin da Hamas ta yi garkuwa da su yayin da ta kai hari ranar 7 ga watan Oktoba a kudancin Isreal.

    Hakan na zuwa ne sa'o'i bayan da Isra'ila ta gano gawar Elia Toledano, wanda Hamas ta yi garkuwa da shi daga wurin bikin kalankuwa na Supernova.

    Nik Beizer mai shekara 19 yana bakin aiki ne a wani sansanin sojojin Isra'ila lokacin da aka kai wa wurin hari.

    An yi garkuwa da Ron Scherman shi ma ɗan shekara 19 yayin da yake aiki a hedikwatar ƴan sanda a Gaza.

    A wani saƙo da aka wallafa a shafin X, rundunar sojin ta ce "Muna jimami tare da iyalan mutanen kuma za mu ci gaba da mara musu baya."

    • Ana fama da bala'in rashin magunguna a Gaza, in ji likita
    • Mene ne tukwicin zaman lafiya a yaƙin Isra'ila da Hamas?
  6. Taliban na tura matan da aka ci zarafin su gidan yari – MDD

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce gwamnatin Taliban a Afghanistan na kulle matan da suka tsira daga cin zarafi a gidan yari tare da iƙirarin cewa tana yin haka ne domin kare su.

    Majalisar Ɗinkin Duniyar ta ce matakin na shafar lafiyar ƙwaƙwalwar matan.

    Rahoton ya ce babu sauran matsugunai na mata da gwamnati ke ɗaukar nauyinsu yayin da gwamnatin Taliban ke ganin babu buƙatar irin waɗan nan cibiyoyin.

    Wani shirin tallafa wa al'umma a Afghanistan na Majalisar Ɗinkin Duniy UNAMA, ya ce cin zarafin da ake yi wa mata da ƴan mata a Afghanistan yana da yawa tun kafin Taliban ta ƙwace gwamnati.

    Sai dai tun lokacin, irin waɗan nan matsalolin sun sake zama ruwan dare ganin tasirin tattalin arziki da kuma matsalolin jin ƙai da suka shafi ƙasar, kamar yadda UNAMA ta ce.

    An ci gaba da tsare mata a gidajensu abin da ke daɗa jefa su cikin haɗarin fuskantar cin zarafi daga abokan zamansu.

    Kafin Taliban ta ƙwace mulki a 2021, akwai cibiyoyin kare mata 23 da ke ƙarƙashin gwamnati a Afghanistan amma a yanzu babu waɗan nan cibiyoyin.

    Jami'an Taliban sun faɗa wa UNAMA cewa babu buƙatar cibiyoyin saboda matan suna tare da mazajensu ko ƴan uwansu maza.

  7. Yadda attajirai ke cutar da duniya

    Bayanan bidiyo, Yadda attajirai ke cutar da duniya

    Ko kun san cewa attajirai, masu dukiya, waɗanda su ne kashi 1% na al'ummar duniya sun fi talakawa, waɗanda su ne kashi 66% yin illa ga duniya?

    Suna yin haka ne ta hanyar rayuwarsu ta ƙasaita, inda suka amfani da jiragen sama da gina manyan gidaje da kuma shiga jiragen ruwa na shaƙatawa, waɗanda ke ƙara yawan sanadarin carbon mai gurɓata muhalli a doron ƙasa.

  8. Sojojin Isra'ila sun ci gaba da luguden wuta a kudancin Gaza

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Sojojin Isra'ila sun ci gaba da luguden wuta a biranen Gaza har da Khan Younis da Rafah duka a kudancin yankin.

    Jami'an lafiya a Falasɗinu sun ce an kashe mutum huɗu ciki har da yara biyu tare da jikkata wasu da dama a hari ta sama da Isra'ila ta kai kan wani gida a Khan Younis da safiyar yau Juma'a.

    Rahotanni kuma sun ce sauran Falasɗinawan da suka ji rauni an kai su asibitin Nasser a Gaza.

    Kamfanin dillancin labarai na Falasɗinu WAFA ya ce hare-hare ta sama da Isra'ila ta kai cikin dare sun halaka tare da jikkata mutane a Rafah. Rahotanni kuma na cewa hare-haren sun shafi wani gini kusa da asibitin Kuwaiti a birnin.

    Ana iya hango turnuƙukin hayaƙi a kudancin Gaza daga Isra'ila sai dai ba a san abin da ya haddasa hayaƙin ba.

    Akasarin ƴan Gaza sun tsere zuwa Rafah bayan da Isra'ila ta byƙace su da su fice daga wasu yankunan Khan Younis - inda dubban mutane suka koma daga arewacin Gaza tun farko-farkon yaƙin.

  9. Tsohon gwamnan Anambra ya mutu

    Tsohon gwamnan jihar Anambra, Dr Chukwuemeka Ezeife ya mutu.

    Wata sanarwa da Chief Rob Ezeife ya fitar a madadin iyalan marigayin ta ce tsohon gwamnan ya mutu ne a wani asibiti da ke Abuja.

    Ezeife ya riƙe muƙamin gwamna a jihar ta Anambra tsakanin Janairun 1992 zuwa Nuwamban 1993.

    Sanarwar ta ƙara da cewa marigayin ya taɓa zama Babban sakatare kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ne.

  10. Fifa ta amince rafari 30 ƴan Najeriya su yi alƙalanci a wasannin 2024

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya, Fifa ta amince rafari 30 ƴan Najeriya su yi alƙalanci a wasanni daban daban na duniya a shekara mai kamawa.

    Kakakin hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya, Ademola Olajire ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa jiya Alhamis.

    Ya cealƙalan wasan sun haɗa da Basheer Salisu da Ogabor Odey Joseph da Olufunmilayo Abigeal Alaba da Nuruddeen Abubakar da Abdulsalam Kasimu Abiola.

    Jami'an ƙwallon ƙafar Najeriya ba sa samun shiga wasannin duniya har da gasar Afcon da za a yi a Ivory Coast.

  11. Kotun Ƙoli za ta yanke hukunci kan buƙatar sakin Namdi Kanu

    .

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Nnamdi Kanu

    A yau ne Kotun Ƙolin Najeriya za ta yanke hukunci game da neman a saki jagoran ƙungiyar Ipob, Nnamdi Kanu.

    Kanu na neman a sake shi inda ya ce gwamnati ba ta da hurumin ci gaba da riƙe shi.

    A shekarar 2015 ne aka kama Mista Kanu amma ya tsere daga Najeriya a 2017 bayan an bayar da shi beli.

    Ya kasance a tsare tun 2021 lokacin da aka tasa ƙeyarsa daga Kenya domin fuskantar tuhume-tuhumen ta'addanci.

    A watan Oktoban bara ne, wata kotun ɗaukaka ƙara ta bayar da umarnin a saki Mista Kanu inda ta ce akwai kura-kurai a shari'ar.

    Sai dai gwamnati ta sake shigar da ƙara inda ta ce Kanu barazana ce ga tsaron Najeriya.

    Wasu shugabannin yankin kudu maso gabashin Najeriya sun nemi a saki Kanu.

  12. An samu raguwar hauhawar farashin kayayyaki a Ghana

    Hauhawar farashin kayayyaki a Ghana ta yi raguwar da bata taɓa yi ba cikin wata 19 inda a yanzu hauhawar farashin ta kai kashi 26.5 cikin 100 a watan Nuwamba saɓanin kashi 35.2 cikin 100 a watan da ya gabata.

    Hauhawar farashin kayayyakin ta yi tashi mafi muni a watan disambar bara.

    A watan Mayu, asusun ba da lamuni IMF ya amince da tallafin dala biliyan uku domin taimaka wa ƙasar da ke fama da taɓarɓarewar tattalin arziki mafi muni.

  13. 'Yara na cikin waɗanda suka mutu a luguden wutar da Isra'ila ta yi cikin dare', Yolande Knell daga Jerusalem

    Isra'ila ta shafe dare tana ci gaba da luguden wuta a Gaza inda rahotanni ke cewa yara suna cikin waɗanda harin ya ritsa da su a hare-haren na Khan Younis da Rafah da ke Kudancin yankin.

    A baya-bayan nan Amurka ta bayyana damuwa kan yawan farar hular da suke mutuwa da kuma matsalar jin ƙai sakamakon yaƙin.

    Mai bai wa Fadar White House shawara kan harkokin tsaro, Jake Sullivan ya ce an samu ci gaba a tattaunawarsa da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu game da rage ƙarfi a yaƙin.

    A yau kuma Sullivan zai gana da jami'ai daga Falasɗinawa a Gabar Yamma da kogin Jordan.

  14. Assalamu Alaykum!

    Barkanmu da safiya, da fatan mun wayi gari lafiya.

    Kamar kullum, wannan shafin na Kai Tsaye yana kawo muku labaran da suke faruwa a Najeriya da Nijar da kuma sassan duniya.

    Nabeela Mukhtar Uba ce za ta kasance da ku.

    Za ku iya zuwa shafukanmu na sada zumunta domin duba irin labaran da muke wallafawa a kai a kai.