Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, Haruna Kakangi and Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Masu bin mu a wannan shafi nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

    Sai kuma gobe idan allah ya kai mu za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    A madadin sauran abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Kansila ya jefa bam a taron ƙaramar hukuma

    Ukraine Council meeting

    Asalin hoton, FACEBOOK

    Bayanan hoto, An haska zaman majalisar kai tsaye a shafin Facebook lokacin da lamarin ya faru

    'Yan sanda a Ukraine sun ce wani kansilan ƙauye a yammacin ƙasar ya jefa gurneti a cikin ɗakin da majalisar ƙaramar hukumar ke zama, tare da raunata mutum 26.

    Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Juma'a, a shelkwatar ƙaramar hukumar Keretsky ta jihar Transcarpathian da ke yammacin ƙasar.

    Kawo yanzu 'yan sanda ba su ce komai ba kan manufar harin, wanda mutum shida suka samu munanan raunuka.

    A lokacin da abin ya faru ana tsaka da haska zaman majalisar kai-tsaye a shafin Facebook

    Kansilolin na tsaka da zazzafar muhawara kan kasafin kuɗin ƙaramar hukumar na shekarar 2024, tare da kuɗin da ƙaramar hukuma ta kashe a wannan shekara da kuɗaɗen garaɓasar da shugaban kansilolin zai samu.

    Kimanin sa'a ɗaya da rabi kafin fara zaman, an hasko ɗaya daga cikin kansilolin na magana da ƙarfi, inda yake nuna adawa da kasafin kuɗin, daga nan sai ya fice daga zauren, tare da wani mutum.

  3. An samo jaririn da mahaukaciyar guguwa ta yi gaba da shi a kan bishiya

    Tennessee baby

    Asalin hoton, CAITLYN MOORE/GOFUNDME

    An gano wani jariri ɗan wata huɗu da ransa "cikin ƙudurar Allah" kamar yadda iyayensa suka ce bayan wata mahaukaciyar guguwa ta yi awon gaba da shi a jihar Tennessee.

    Ma'aurata sun ce wata mummunar mahaukaciyar guguwa a ranar Asabar ce ta kacaccala gidansu, inda ta ɗauki wani kwandon da ake shimfiɗe jaririn a ciki.

    Ya dai tsallake rijiya da baya inda aka gano shi a kan wata bishiya da ta karye bayan an lafta ruwan sama.

    Jaririn da ɗan'uwansa mai shekara ɗaya da mahaifansu sun ji ƙwarzanen ciwuka ne kawai.

    A lokacin da mahaukaciyar guguwar ta tunkari Tennessee, mahaifiyar jaririn mai shekara 22, Sydney Moore, ta ce guguwar ta yage rufin gidan da suke ciki.

    "Harshen guguwar sai ya sauko kuma ya zari kwandon da jaririna yake ciki," Sydney Moore ta faɗa wa tashar talbijin ta yankin. "Shi ne na farko da ta ɗauka ta yi sama."

    Saurayinta - wanda shi ne mahaifin yaron - ya daka tsalle don kare kwandon da jariri Lord yake ciki, sai dai shi ma ya guguwar ta yi wuf ta yi awon gaba da shi.

    Bayanan bidiyo, An riƙa ganin fashewar abubuwa da curin wuta a lokacin da guguwar take ketawa ta Tennessee

    Bayan guguwar ta lafa ne, sai Sydney Moore da saurayinta suka fara neman Lord.

    Sun yi ta nema a cikin ruwan saman da ake yi a lokacin, inda suka gano jaririn a raye cikin abin da Sydney ta ce "ya yi kama da wani ɗan ƙaramin gado a kan bishiyar".

  4. Babban kamfanin fiton kaya ya dakatar da aiki a tekun Maliya

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Babban kamfanin fiton kayayyaki na ƙasar Denmark, Maersk ya ce zai dakatar da duka ayyukansa a tekun Maliya.

    Matakin na zuwa ne bayan yawaitar hare-hare kan jigaren fiton kaya da 'yan tawayen Houshi da ke Yemen, waɗanda ke samun goyon bayan ƙasar Iran.

    Ƙungiyar ta bayyana goyon bayanta ga Hamas, tare da cewa tana kai hare-haren ne kan jiragen ruwan da ke kan hanyar zuwa Isra'ila.

    Tekun Maliya ya kasance ɗaya daga cikin manyan hanyoyin jigilar man fetur da jiragen ruwa a duniya.

    "Hare-haren baya-bayan nan kan jiragen fiton kaya a yankin ya zama abin tayar da hankali, tare da haifar da babbar fargaba kan tsaro da kariyar masu safara da jiragen ruwa,'' kamar yadda kamfanin ya wallafa a wata sanarwa da aike wa da BBC.

  5. Sojojin Isra'ila sun ce sun kashe 'yan ƙasar uku da Hamas ke garkuwa da su

    .

    Asalin hoton, Hostage and Missing Families Forum

    Sojojin Isra'ila sun ce sun kashe uku daga cikin 'yan ƙasarta da Hamas ke garkuwa da su a Gaza, bayan da suka yi tsammanin cewa mayaƙan Hamas ne.

    Mai magana da yawun rundunar sojin Isra'ilar Daniel Hagari, ya ce an kashe mutanen ne a garin Shejaiya da ke arewacin Gaza.

    Mista Hagari ya ce rundunar sojin Isra'ila ta ɗauki alhakin abin da ya faru, ta kuma ƙaddamar da bincike kan lamarin.

    Ya ƙara da cewa tuni aka mayar da gawarwakin mutanen - waɗanda aka kama a garin Kibbutz Nir Am da ke Isra'ila.

    Fiye da mutum 100 ne har yanzu Hamas ke garkuwa da su a Gaza, bayan kama su a harin ranar 7 ga watan Oktoba

    "Babban burinmu shi ne gano inda mutanen suke tare da maido su Isra'ila," in ji Mista Hagari.

  6. An sako ɗaliban Jami'ar Dutsin Ma da 'yan fashin daji suka sace

    ..

    Asalin hoton, others

    Rahotanni daga jihar Katsina, na cewa an sako ɗaliban Jami'ar Tarayya ta Dutsin Ma, bayan shafe sama da wata biyu a hannun 'yan fashin daji.

    Shugaban makarantar Farfesa Arma Ya'u Hamisu Bichi, ya shaida wa BBC cewa ya samu labarin sakin sakin ɗaliban daga ɗaya daga cikin mahaifan ɗaliban da misalin ƙarfe huɗu na yamma.

    Ya ƙara da cewa an saki duka ɗaliban huɗu da suka rage a hannun 'yan bindigar.

    A ranar Laraba 4 ga watan Oktoba ne, wasu 'yan bindiga suka auka gidan kwanan ɗaliban - dukkansu mata - da ke zaune a wajen jami'ar cikin unguwar Maryama Ajiri da tsakar dare.

    Sai dai daga baya 'yan bindigar sun saki guda ɗaya daga cikinsu.

    Hukumomi dai sun ce suna ci gaba da tuntuɓa da tattaunawa don ganin an sako ɗaliban ba tare da wani lahani ba.

    Lamarin ya faru ne ƙasa da mako biyu bayan sace wasu ɗalibai 'yan mata a Jami'ar Tarayya ta Gusau cikin jihar Zamfara mai maƙwabtaka.

    Duka jihohin biyu suna fama da rikicin 'yan fashin daji waɗanda ke kai hari kan garuruwa da ƙauyuka tare da sace mutane don yin garkuwa da su da zimmar neman kuɗin fansa.

    Shugaban Jami'ar ya shaida wa BBC cewa a iya sanin saninsa ba a biya diyya ba kafin a saki ɗaliban, sai dai ya gode wa mai bai wa shugaban ƙasa shawar kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu, da kwamishin 'yan sandan jihar Katsina da daraktan hukumar tsaro ta DSS da ke jihar da karin wasu mutane, bisa ƙoƙarin da ya ce ya yi har aka kai ga sakin ɗaliban.

  7. Turkiyya ta gina katangar kankare mai tsawon kilomita 170 tsakaninta da Iran

    ...

    Asalin hoton, @aa_persian

    Kafafin yaɗa labaran Turkiyya sun bayyana cewa ƙasar ta gina katangar tsaro mai tsawon kilomita 170, tsakaninta da Iran.

    A shekarun da suka gaba ne aka soma gina katangar daga lardin Van da ke gabashin ƙasar, kusa da kan iyakar ƙasar da Iran.

    An tsara cewa katangar kankaren za ta kai nisan kilomita 295 da za a gina tsakanin Turkiyya da Iran.

    Dalilin gina katangar shi ne don magance ''tuɗaɗar masu neman mafaka ba bisa ƙa'ida ba''.

    Kamfanin dillancin labaran Turkiyya Anatolia ya ce sojojin Turkiyya na kula da kan iyakar da sabbin fasahohin tsaro ciki har da jirage marasa matuƙa.

  8. Gwamnonin arewa sun bayar da naira miliyan 180 ga dangin mutanen Tudun Biri

    .

    Kungiyar gwamnonin arewacin Najeriya ta bayar da tallafin naira miliyan 180 ga dagin mutanen da harin Tudun Biri ya rutsa da su.

    A taron da ƙungiyar da gudanar karon farko tun bayan kafa sabuwar gwamnati

    Ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahya, ta bayyana haka ne a lokacin taron da ta gabatar a gidan gwamnatin jihar Kaduna.

    Gwamnonin sun kuma buƙaci a gabatar da cikakken bincike domin gano waɗanda ke da hannu a lamarin.

    A farkon wannan wata ne dai wani jirgin sojin Najeriya maras matuƙi ya kai hari kan wasu fararen hula masu maulidi a ƙauyen Tudun Biri da ke ƙaramar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

    Lamarin da ya yi sandanin kisan aƙalla mutum 85 tare da jikkata wasu da dama.

    Haka kuma gwamnonin sun jaddada ƙudurinsu na haɗin kai tsakaninsu don magance matsalar tsaro da inganta zaman lafiya da tattalin arzikin yankin, da magance matsalar rashin aikin yi, da matsalar shaye-shaye tsakanin matasa a yankin arewacin ƙasar.

    .
  9. Aikinmu kare mutane ne ba kashe 'yan ƙasa ba - Babban hafsan tsaron Najeriya

    Bayanan bidiyo, Babban hafsan sojojin Najeriya
  10. Tsohon shugaban Zambiya ya garzaya kotu don ƙalubalantar janye masa hakkoki

    ..

    Asalin hoton, AFP

    Tsohon shugaban Zambiya, Edgar Lungu, ya garzaya kotu don ƙalubalantar dakatar masa da haƙƙoƙin aiki da ake biyansa.

    A watan da ya gabata ne aka janye wa Mista Lungu haƙƙoƙin da doka ta tanadar masa, bayan matakin da ya ɗauka na komawa harkokin siyasar ƙasar.

    Rahotonni sun ce an rufe masa ofishi, tare da janye jami'an tsaro da ababen hawan da gwamnati ta ba shi a baya.

    Cikin takardar shigar da ƙarar da wata kafar yaɗa labarai mai zaman kanta a ƙasar, 'News Diggers' ta gani, Mista Lungu ya bayyana matakin da gwamnatin ƙasar ta ɗauka a matsayin take hakkinsa.

    Mista Lungu ya kuma ce abin da ya sa shi mamaki shi ne, wannan mataki, bai shafi sauran tsoffin manyan jami'an gwamnatin ba.

    To sai dai babban Antoni Janar na ƙasar Mulilo Kabesha ya yi watsi da ƙorafin mista Lungu, yana mai cewa ci gaba da ba shi haƙƙinsa alhalin yana cikin harkokin siyasar ƙasar ya saɓa wa dokar ƙasar, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta Diomond TV a ƙasar ta ruwaito.

  11. A ɗauki matakan tabbatar da amincin mata da 'yan mata a Najeriya - Unicef

    ..

    Asalin hoton, unicef

    Najeriya ta bi sahun ƙasashen duniya wajen gudanar da bikin gangamin yaƙi da zin zarafi mai nasaba da jinsi,da ƙungiyar Unicef ke jagoranta.

    Gangamin na bana- mai taken ''zuba kuɗaɗe don yaƙi da cin zarafin mata da 'yan mata'' - ya jaddada ƙudurin gwamnati na magance duka nau'ikan cin zarafin mata da ƙananan yara.

    Taron na bana - wanda aka kwashe kwanaki 16 ana gudanarwa ya ƙarfafa wa mutane gwiwa wajen bayyana ƙudurinsu don magance matsalar cin zarafin mata da 'yan mata ta hanyar musayar matakan da ake ɗauka don magance matsalar a faɗin duniya.

    Haka kuma gangamin ya kuma buƙaci gwamnatoci da hukumomin duniya da su bayyana irin jarin da suke zuba wa don magance matsalar cin zarafin jinsi.

    Cikin wata sanarwar ta Unifef ta fitar bayan taron, ta ce nau'ikan cin zarafin jinsi da ake aikatawa a Najeriya sun haɗar da fyaɗe da cin zarafin matan aure, da aikata lalata da auren wuri da kaciyar 'ya'ya mata da sauran abubuwa, lamarin da ke tasiri ga matan ta fuskar tunani da zamantakewa da tattalin arzikinsu.

    Sanarwar ta ce gwamnatin Najeriya ƙarƙashin ma'aikatar lafiya da ma'aikatar harkokin mata, sun haɗa hannu da hukumar Unicef da sauran masu ruwa da tsaki wajen wayar da kan al'umma wajen magance matsalolin da suka jiɓanci cin zarafin mata.

    Wakiliyar Unicef a Najeriya, Cristian Munduate ta ce ''a hukumarmu mun fahimci cewa magance matsalar cin zarafin mata da 'yan mata ba abu ne da ke buƙatar gaggawa ba, babbar buƙatarmu ita ce aiki da gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki don magance matsalar tun daga tushe. A yanzu lokacin ɗaukar mataki ya yi, domin tabbatar da cewa mata da 'yan mata sun rayu cikin aminci da karimci da girmamawa tare da 'yanci''.

  12. Isra'ila ta sa ladan dala 400,000 ga wanda ya ba da bayanin maɓoyar shugaban Hamas

    ..

    Asalin hoton, EPA

    Rundunar sojin Isra'ila ta watsa wasu takardu a faɗin Zirin Gaza ɗauke da sanarwar biyan tukwici ga duk wanda ya bayar da bayanai kan maɓoyar shugabannin Hamas.

    Sun yi alƙawarin biyan dala 400,000 ga duk wanda ya sanar da inda shugaban ƙungiyar Yahya Sinwar na Zirin Gaza yake, da kuma dala 300,000 a kan ɗan'uwansa Muhammad Sinwar.

    Akwai kuma wasu ƙananan tukwici da sojin Isra'ila suka yi alƙawarin biya a kan sauran manyan ƙusoshin Hamas.

    Takardun dai na ɗauke da lambobin wayar salula da kuma tabbacin rufe asirin wanda ya bankaɗo maɓoyar waɗanda sojin Isra'ilan ke nema ruwa-a-jallo.

  13. An sayar da rigunan da Messi ya sa a Gasar Kofin Duniya fam miliyan 6.1

  14. Sojoji sun kashe ƴan bindiga tare da kuɓutar da mutum shida a Sokoto

    ..

    Asalin hoton, @HQNigerianArmy/X

    Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe wasu 'yan bindiga tare da kuɓutar da wasu mutane da suke garkuwa da su a jihar Sokoto.

    Cikin wani saƙo da rundunar sojin ƙasar ta wallafa a shafinta na X, ta ce cikin wani hari da dakarunta na Hadarin Daji suka ƙaddamar a ƙauyen Bauni da dajin Bauni a jihar ranar 14 ga watan Disamba, inda sojojin suka shafe sa'o'i masu yawa suna musayar wuta da 'yan bindigar.

    Sanarwar ta ce bayan da sojojin suka matsa wa 'yan bindigar, sai suka tsere tare da barin maɓoyarsu, lamarin da ya sa sojojin suka samu nasarar kuɓutar da mutum shida da suke garkuwa da su.

    ''Sai dai kafin tserewar 'yan bindigar, sojojin sun kashe uku daga cikinsu, tare da gano makamai'', in ji sanarwar.

    Makaman da aka gano sun haɗar da bindiga ƙirar AK-47 biyu da kuttun adana alburusai 19, da alburusai, da bindigogin toka biyu d babura, da na'urorin oba-oba da sauran kayayyaki

    Sanarwar ta ce sojojin sun lalata maɓoyar 'yan bindigar tare da babuwarn da suka gano nan take.

  15. Tawagar Spain ta mata ta zama ta ɗaya a jerin ƙasashen da Fifa ta fitar

  16. Hotunan Kudancin Gaza yayin da Isra'ila ke ci gaba da luguden wuta a yankin

    Isra'ila ta ci gaba da yin luguden wuta a Gaza inda hare-haren suka shafi yankunan Khan Younis da Rafah.

    Ga wasu hotuna da ke nuna ɓarnar da aka yi a yankin.

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Yadda gine-gine a kudancin Gaza suka ruguje bayan hare-haren Isra'ila
    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, A Rafah, wani Bafalasɗine na tafiya cikin ɓuraguzan wani gida da harin ya shafa
    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Masu jimami a Rafah, zaune a jana'izar Falasɗinawan da aka kashe a yaƙin
    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Jiragen sama masu saukar ungulu mallakin sojojin Isra'ila na shawagi ta sama a iyakar Isra'ila da Gaza
  17. An samu hauhawar farashin kaya mafi muni a Najeriya cikin shekara 20

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar ƙididdiga ta Najeriya ta ce hauhawar farashin kayayyaki ta yi tashi mafi muni da ɓata taɓa yi ba cikin shekara 20 - kashi 28.2 cikin 100 a watan Nuwamba.

    A rahoton da hukumar ta fitar yau Juma'a, ta ce hauhawar farashin ta ƙaru zuwa kashi 28.20 saɓanin watan Oktoba da ya ke kashi 27.33.

    Hukumar ta ce "tashin farashin kayan masarufi na shekara zuwa shekara ya faru ne sakamakon ƙaruwar farashin biredi da dankali da doya da kifi da nama da kayan itatuwa da gahawa da shayi da kuma cocoa,"

    A wata bayan wata kuma, hauhawar kayan masarufi a Nuwamba ya kai kashi 2.42 cikin 100, ya ƙaru da kashi 0.51 idan aka kwatanta da yadda yake a Oktoban 2023 da yake kashi 1.93 cikin 100.

  18. Bayanin abubuwan da suka faru a baya-bayan nan a yaƙin Isra'ila da Hamas

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ga bayani kan abubuwan da suka faru a baya-bayan nan a yaƙin da Isra'ila take yi da Gaza:

    • An gano gawawwakin ƴan Isra'ila uku har da sojojin ƙasar biyu, Nik Nik Beizer da Ron Scherman da Hamas ta yi garkuwa da su ranar 7 ga watan Oktoba.
    • Lamarin ya faru bayan da aka gano gawar Elia Toledano da Hamas ta yi garkuwa da shi daga wani biki na Supernova ranar 7 ga watan Oktoba.
    • Mai bai wa Fadar White House shawara kan sha'anin tsaro, Jake Sullivan zai gana da shugaban Falasɗinu Mahmoud Abbas a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan nan gaba a yau.
    • Da yake magana da safiyar yau, Sullivan ya ce Amurka na son ganin sakamakon ƙudirin Isra'ila domin kare mutuwar farar hula a Gaza amma ya ƙara da cewa "Amurka na tare da Isra'ila"
    • A gefe guda kuma, wani harin makami mai linzami da aka kai daga wani yankin Yemen da ke ƙarƙashin mayaƙan Houthi ya shafi wani jirgin ruwa na dakon kaya a tekun Bahar maliya. Ƴan kungiyar Houthi da ke samun goyon bayan Iran sun ce za su kai wa duk wani jirgin ruwan da zai shiga Isra'ila hari.
    • An ci gaba da yin luguden wuta a Gaza inda aka samu rahoton mutuwar mutane da jikkatar wasu har da yara a kudancin yankin.
    • Sojojin Isra'ila sun ce sun murƙushe wani sansanin ƙungiyar Hamas a arewacin Gaza.
  19. Ƙarin kwamishinonin jihar Rivers sun ajiye aiki

    ..

    Wasu kwamishinonin Rivers shida sun sake ajiye aiki yayin da rikicin siyasa ke daɗa ƙamari a jihar.

    Kwamishinan sufuri na jihar, Dr Jacobson B Nbina da kwamishinan ilimi, Farfesa Prince Chinedu da kwamishinar gidaje, Gift Worlu na daga cikin kwamishinonin da suka miƙa takardar ajiye aikinsu a baya-bayan nan.

    Kwamishinan shari'a Prof Zacchaeus Adangor shi ne jami'i na farko da ya sanar da ajiye aikinsa.

    Kwamishinan ayyuka a takardar ajiye aikin, ya ce ya ɗauki matakin ne bayan dogon nazarin da ya yi. Ya miƙa godiyarsa ga gwamnan tare da yi masa fatan alheri.

    Sai dai kwamishinan kuɗi,Isaac Kamalu, a nasa ɓangaren bai faɗi dalilinsa na ajiye aiki ba.

    A ɓangarenta, kwamishinar kula da walwalar al'umma ta yi wa gwamnatin ta Siminalayi Fubara fatan alheri inda ita ma ta ce ta ɗauki matakin ne bisa raɗin kanta da kuma wasu dalilai da suka buƙaci hakan.

  20. Sojojin Isra'ila sun tarwatsa hedikwatar Hamas a arewacin Gaza

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kama tare da lalata babbar bataiyalar soji ta Hamas da ke Shejaiya a gundumar gabashin birnin Gaza.

    Kakakin rundunar Avichay Adraee ya wallafa a shafin X cewa an murƙushe mayaƙan Hamas a yankin sakamakon hare-haren da aka kai ta sama da tankokin yaƙi da kuma wasu injiniyoyi da suka lalata hanyar ƙarƙashin ƙasa da ke wajen.

    Rundunar sojin Isra'ilar ta kuma tarwatsa wasu rukunin gidaje a farkon makon nan, sojojin Isra'ila tara aka kashe a yankin.

    IDF ta ƙara da cewa ta kai hari kan gine-ginen mayaƙan a birnin Khan Younis.

    Ta kuma yi iƙirarin lalata wani wurin ajiyar makamai na ƙungiyar da kuma tarin motoci da aka gano da ta ce an yi amfani da su ne a hare-haren ranar 7 ga watan Oktoba.