Masana sun gano abin da ke sa masu juna biyu laulayi

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba and Abdullahi Bello Diginza

  1. 'Isra'ila ba za ta amince da maslahar ƙasa biyu ba'

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Jakadiyar Isra'ila a Birtaniya ta ce ƙasarsu ba za ta amince da maslahar samar da ƙasashe biyu ba idan yaƙin Gaza ya kawo ƙarshe.

    Da aka tambaye ta game da yiwuwar Falasɗinawa su samu tasu ƙasar, Tzipi Hotovely ya faɗa wa Sky News cewa ba zai yiwu ba.

    Tsarin ƙasashe biyu shi ne samar da ƙasar Falasɗinu kusa da Isra'ila zai bai wa al'ummar ƙasashen dama ta yin zaman lafiya. Tsarin ya samu goyon bayan Amurka da sauran ƙawayen Isra'ila.

    Amurka da wasu ƙasashen yamma na goyon bayan tsarin.

    Da aka tambaye shi yadda za a samu zaman lafiya a yankin ba tare da tsarin samar da ƙasashe biyu ba, Hotovely ta ce "ya kamata duniya ta san cewa Falasɗinawa kwata-kwata ba sa son zama kusa da Isra'ila".

  2. Hare-haren Uganda sun halaka ɗaruruwan mayaƙan ADF – Museveni

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Uganda ya ce sojojin ƙasar sun kashe mayaƙan ƙungiyar ADF kusan 200 a jamhuriyar demokradiyyar Congo, yayin da suke ci gaba da fatattakar mayaƙan.

    "Muna ta kai hare-hare ta sama kan mayaƙan a Congo," in ji Shugaba Yoweri Museveni a shafinsa na X da a baya ake kira Tuwita.

    Ya ƙara da cewa kusan su 200 aka kashe a hare-haren da aka kai ranar 16 ga watan Satumba.

    An ci gaba da kai hare-hare kan mayaƙan tun lokacin kamar yadda Mr Museveni ya bayyana, sai dai bai yi ƙarin bayani ba.

    Kakakin rundunar sojin Uganda Felix Kulayigye ya faɗa wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa shugaban ƙasar yana magana ne a kan mayaƙan na ADF.

    A 2021 Uganda da Congo suka kaddamar da harin haɗin gwiwa kan ADF a gabashin Congo, amma ƙungiyar tana ci gaba da kai hari a kasashen biyu.

    A watan Oktoba ne aka kashe wani ɗan Birtaniya da wata ƴar Afirka ta mutu da suka je shaƙatawar amarci kumaƙungiyar ta ɗauki nauyin kai harin.

    A watan Yunin, an kashe mutum 42 har da ɗalibai 37 a wani hari da aka kai kan wata makarantar sakandare a yammacin Uganda- harin da shi ma aka alaƙanta shi da mayaƙan ADF.

  3. A mayar da sunan madugun ƴan hamayyar Senegal cikin rajistar zaɓe – Kotu

    Ousmane Sonko

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Ousmane Sonko

    Wata kotu a Senegal ta ba da umarnin a mayar da sunan tsararren jagoran ƴan hamayya na ƙasar, Ousmane Sonko cikin rajistar zaɓe.

    Hukuncin ya ba shi damar ya tsaya takarar shugaban ƙasa a watan Fabrairun shekara mai zuwa.

    An shafe kusan shekara biyu Mr Sonko yana fuskantar tuhume-tuhume da dama kan ɓata suna da fyaɗe - abubuwan da ya musanta aikata su.

    An kama shi a watan Yuli saboda gurɓata matasa lamarin da ya aka cire sunansa daga ƴan takara.

    Ya sha bayyana cewa matakin yunƙuri ne na hana shi neman takarar shugaban ƙasa.

    Wani lauyan gwamnati ya ce za su ɗaukaka ƙara game da hukuncin kotun.

  4. Me ake ciki a yaƙin Isra'ila da Hamas?

    .

    Asalin hoton, EPA

    Ana ci gaba da yaƙi tsakanin sojojin Isra'ila da ƙungiyar Hamas. Ga bayanin abuuwan da suka faru a baya-bayan nan:

    • Jakadiyar Isra'ila ga Amurka ta ce ƙasar ba za ta amince da tsarin ƙasashe biyu idan aka daina yaƙi a Gaza. "Falasɗinawa kwata-kwata ba sa son samun ƙasa kusa da Isra'ila," kamar yadda Tzipi Hotovely ta shaida wa Sky News. Tsarin ƙasashe biyu shi ne samar da ƙasar Falasɗinu kusa da Isra'ila zai bai wa al'ummar ƙasashen dama ta yin zaman lafiya. Tsarin ya samu goyon bayan Amurka da sauran ƙawayen Isra'ila.
    • Mai bai wa Fadar White House shawara kan sha'anin tsaro, Jake Sullivan yana kan hanyarsa ta zuwa Isra'ila inda zai tattauna da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu. Ma'aikatar lafiya a Gaza da ke ƙarkashin Hamas ta ce mutum 18,600 aka kashe a yankin tun soma yaƙin.
    • Ma'aikatar lafiya ta ce kimanin mutum 19 aka kashe da safiyar yau a Gaza sakamakon hare-haren Isra'ila ta sama.
    • Sannan a Gabar Yamma da Kogin Jordan, sojojin Isra'ila a Jenin sun ci gaba da kai samame kwana uku jere - Falasɗinawa 11 aka kashe, wasu da dama sun jikkata.
  5. Abin da ke sa masu juna biyu yin laulayi mai tsanani

    .

    Asalin hoton, SUSIE VERRILL

    Masu bincike sun ce sun gano dalilan da ya sa wasu mata ke yin rashin lafiya mai tsanani a lokacin da suke da juna biyu.

    Masanan sun ce hakan na faruwa ne sakamakon wasu sinadaran ƙwayoyin halitta guda goma sha biyar da jarirai ke samarwa a cikin mahaifa, wanda ka iya haifar da rashin lafiya ga uwa.

    Masanan da suka fito daga Birtaniya da Amurka da Srilanka sun ce binciken zai taimaka wajen magance matsalar ta hanyar da ta dace.

    Wakiliyar BBC ta ce masu binciken sun ce mataki na gaba shi ne fara aiki kan maganin da zai warkar da rashin lafiyar.

  6. Kalli mummunan halin da masu cutar kansa ke ciki a Gaza saboda yaƙi

    Bayanan bidiyo, Kalli mummunan halin da masu cutar kansa ke ciki a Gaza saboda yaƙi

    Islam Abu Rakaa, mazaunin Gaza na fama da cutar kansar maƙogwaro, sai dai yanzu ba ya iya samun magani saboda yaƙi ya yi sandin lalata asibitoci masu yawa a yankin.

    Ala tilas asibitoci ke rufewa sanadiyyar ruwan bama-bamai da Isra'ila ke yi a Gaza.

  7. Amurka ta gindaya sharaɗin mayar da alaƙarta da Nijar

    Amurka ta ce a shirye ta ke ta dawo da alaƙar da ke tsakanin ta da Nijar idan har gwamnatin mulkin sojin ƙasar ta amince da mayar da mulki ga farar hula cikin ƙanƙanin lokaci.

    Jami'ar ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Molly Phee ce ta bayyana hakan a yayin wata ziyara da ta kai birnin Yamai, inda ta ce dole ne shugabannin mulkin sojin su bayyana ranar da za su mayar da ƙasar bisa turbar dimokradiyya.

    Ta ce Amurka ta damu matuƙa kan yadda dangataka ta yi tsami tsakanin Nijar da wasu ƙasashe maƙwabta.

    Sojojin mulkin Nijar din dai sun ce za su mayar da mulki ga farar hula cikin shekaru uku.

  8. 'Gwamnatin Tinubu ba ta da hannu a rikicin siyasar Rivers'

    .

    Asalin hoton, KANO STATE GOCT/FACEBOOK

    Bayanan hoto, Shugaban Najeriya, Bola Tinubu

    Ministan yaɗa labarai a Najeriya, Idris Malagi ya ce gwamnatin tarayya ba ta da hannu a rikicin siyasar da ake yi a jihar Rivers.

    Ministan ya yi magana ne a gidan Talabijin na Channels yau Alhamis inda ya ce kasancewar wasu da ke cikin rikicin na cikin majalisar ministocin Shugaba Bola Tinubu, hakan ba wai yana nufin gwamnatin APC ce ta kitsa halin da ake ciki ba a jihar.

    "Ban gano wata shaida da zan iya cewa gwamnatin tarayya ce take ingiza rikici a jihar Rivers ba," in ji ministan.

    Ya ƙara da cewa abu ne mai sauki a yaɗa jita-jita saboda wasu da ke cikin rikicin mutane ne da suke da kusanci da gwamnati".

    Malagi ya bayyana cewa akwai rikicin siyasa a wasu jihohin kamar Ondo kuma Shugaban ya sa baki aka warware rikicin da ya shafi ƴan jam'iyya daya.

  9. Majalisar wakilan Amurka ta kaɗa kuri'ar amincewa da binciken tsige Biden

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Shugaba Joe Biden

    Ƴan majalisar wakilai na jam'iyyar Republican sun kaɗa ƙuri'ar amincewa da kafa kwamitin binciken tsige shugaba Biden.

    Hakan na zuwa watanni uku bayan da ƴan Republican suka soma binciken Biden din, in da suka zargi iyalansa da cin hanci da rashawa a lokacin da yake mataimakin shugaban ƙasa.

    Wakilin BBC ya ce mista Biden ya musanta dukkan zarge-zargen kuma cikin sanarwar da ya fitar bayan kaɗa kuri'ar ya kira matakin da marar tushe kuma bita da ƙullin siyasa.

    A karkashin dokar Amurka, ana iya tsige shugaban ƙasa daga muƙaminsa ba tare da wani tsarin zaɓe ba, idan Majalisar Dattijai ta same shi da laifin "cin amanar kasa, ko cin hanci ko wasu munanan laifuka."

    Binciken tsigewa shi ne matakin farko na tsarin da zai kai ga ci gaba da tsige shi a Majalisar, kuma idan aka yi nasara, za a yi shari’a a Majalisar Dattawa.

  10. An kashe ƴan jarida 17 da ke ba da rahoto kan yaƙin Gaza

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, An kashe ɗan jarida Issam Abdallah a wani hari da aka kai kan iyakar Isra'ila da Lebanon a watan Oktoba

    A farkon watan nan na Disamba ne, ƙungiyoyin kare haƙƙin bil adama suka ce ya kamata a yi bincike kan Isra'ila saboda zargin tafka laifukan yaƙi game da kisan wani ɗan jarida a Lebanon cikin watan Oktoba.

    Ɗan jaridar, Issam Abdallah, na Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya mutu ne sakamakon luguden wutar da aka yi a kan iyakar Isra'ila da Lebanon.

    Wasu mutum shida kuma sun ji rauni.

    Ƙungiyar Amnesty da ta Human Rights Watch ta ce binciken da aka yi ya nuna akwai alamun an harbi ɗan jaridar ne.

    Isra'ila dai ta musanta kai wa ƴan jarida hari.

  11. Harin Isra'ila ya halaka Falasɗinawa 19, Yolande Knell daga Jerusalem

    .

    Asalin hoton, FRANCESCO TOSTO/BBC

    Ma'aikatar lafiya a Gaza wadda ke ƙarƙashin Hamas ta ce hare-haren da Isra'ila ta kai ta sama da saiyar yau Alhamis ya kashe mutum 19.

    Akwai alamun samun rashin jituwa a tsakanin Isra'ila da babbar ƙawarta - Amurka gabanin isar mai bai wa Fadar White House shawara kan sha'anin tsaro, Jake Sullivan.

    A wannan makon, Shugaba Joe Biden ya zargi Isra'ila da jefa bama-bamai kan Gaza ba-ji-ba-gani lamarin da ya ce ya rasa ƙasar ta fara rasa goyon bayan duniya.

    Gabanin ziyarar tasa, an rawaito Sullivan na cewa zai tattauna game da kawo ƙarshen yaƙin tare da neman shugabannin Isra'ila su sauya salo.

    Da yake mayar da martani kan kiraye-kirayen dakatar da yaƙin, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya faɗa wa sojoji a Gaza cewa "za mu ci gaba har sai mun murƙushe Hamas...babu ain da zai dakatar da mu."

  12. Barka da hantsi!

    Masu bibiyarmu, barkanmu da warhaka. Da fatan za ku kasance tare da mu a wannan shafin Kai Tsaye na BBC Hausa.

    Za mu rika kawo muku rahotanni da labaran da suka shafi Najeriya da Nijar da sauran sassan duniya.

    Nabeela Mukhtar Uba ce za ta kasance tare da ku.

    Za kuma ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin karanta ƙarin labarai da kuma kallon bidiyo.