Isra'ila ta ce an kashe sojojinta 10 a Gaza

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba and A'isha Babangida

  1. Isra'ila ta ce an kashe sojojinta 10 a Gaza

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Sojojin Isra'ila sun ce an kashe sojoji 10 a faɗan da aka gwabza a arewacin Gaza a jiya wanda ya zama rana mafi muni ga sojojin tun bayan fara kai farmaki ta kasa kan Hamas.

    Tara daga cikin waɗanda aka kashe - ciki har da kwamandan bataliyar da Kanar - sun kasance suna fafatawa a Shejaiya, da ke gabashin birnin Gaza.

    An bayyana cewa sun fada cikin wani harin kwantan bauna da hadin gwiwa.

    Ya zuwa yanzu dai an kashe sojoji 115.

    A kan shafin zumunta na X, Benny Gantz, memba na Majalisar Yakin Isra'ila, wanda kuma tsohon babban hafsan soji ne, ya rubuta cewa yaƙin ya janyo yanayi mai raɗaɗi da wahala".

    A shafukan sada zumunta, wasu 'yan Isra'ila na nuna shakku kan ko ƙaruwar fadan kasa na da nasaba da matsin lambar da Amurka ke yi na rage yawan hare-hare ta sama.

    • Wane ne Yahya Sinwar shugaban Hamas na Gaza?
    • Wane irin ciwon ciki ne yake turnuƙe sojojin Isra'ila da suka je yaƙi Gaza?
  2. Abin da ya faru a yaƙin Isra'ila da Hamas a yau

    • Sojojin Isra'ila sun ce sun kai hare-hare sama da 250 a Zirin Gaza a ranar da ta gabata.
    • Jami'an Hamas sun ce an kashe aƘalla mutUM 50 a Gaza.
    • Sojojin Isra'ila 9 da suka hada da kwamandan bataliyar, sun mutu a wani lamari da ya faru a Gaza ranar Talata, kamar yadda dakarun sojin Isra'ila suka tabbatar.
    • Wata 'yar Falasɗinawa ta shaida wa BBC cewa ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi da daddare ya kara tsananta mata da 'yan uwanta yayin da suke mafaka a Deir al-Balah.
    • A wani wuri kuma, Isra'ila na kallon a keɓanceta a fannin diflomasiyya bayan da babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya amince da kudurin da ba shi da tushe balle makama da ke bukatar tsagaita bude wuta a Gaza.
    • Shugaban Amurka Joe Biden ya yi kakkausar suka kan shugabancin Isra'ila
    • Biden ya alakanta asarar goyon bayan ƙasashen duniya da abin da ya kira harin bama-bamai da Isra'ila ke kai wa Gaza.
  3. Masu zanga-zanga a Isra'ila na son a ƙara kaimi wajen sako mutanen da Hamas ta sace

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Mutane da dama ne suka taru a wajen majalisar Knesset (majalisar dokokin Isra'ila) a birnin Ƙudus a daren jiya da safiyar yau, domin yin kira da a sako sauran mutanen da Hamas ke garkuwa da su a Gaza.

    Duk da ruwan sama da aka tafka da guguwar dare, 'yan uwan ​​waɗanda aka yi garkuwa da su da sauran jama'a sun yi tattaki don neman gwamnati ta yi aiki don ganin an dawo da su Isra'ila.

    Kimanin mutum 240 ne Hamas ta kai gidan yari a ranar 7 ga watan Oktoba, 78 daga cikinsu an sako su a wani bangare na yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Isra'ila da Hamas suka yi na kwanaki shida a watan Nuwamba.

    An kuma sake wasu mutum 27 da aka yi garkuwa da su a wani ɓangare na tattaunawar Hamas da wasu gwamnatoci.

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

  4. Sudan na gab da faɗa wa ƙangin yunwa – MDD

    Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargaɗi cewa Sudan na gab da faɗawa ƙangin yunwa - mafi ƙololuwar matsalar abinci.

    An taƙaita hanyoyin isa ga mutanen da ke cikin matsananciyar bukatar abinci tun bayan ɓarkewar yaƙi a watan Afrilu tsakanin ɓangarori biyu na sojojin ƙasar da ke rikici da juna.

    Gargaɗin na zuwa ne yayin da mutumin da ke iƙirarin shugabantar Sudan, wanda ke jagorantar ɗaya daga cikin ɓangarorin da ke rikici da juna, ya yi alƙawarin ci gaba da yaƙi har sai ya yi galaba.

    Sudan na fuskantar matakin yunwa mafi ƙololuwa a lokacin noma, a cewar wani nazari da Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi.

    Amma mutanen da ke fuskantar matsalar rashin abinci ya ninka idan aka kwatanta da lokacin noman a bara.

    Dama Sudan tana fuskantar matsalar karancin abinci kafin ɓarkewar yaki a watan Afrilu.

    Taɓarɓarewar yanayin tsaro a kasar ya sa samun shiga sassa daban daban na ƙasar ya zama abu mai matuƙar wahala.

    • Zaɓi mai tsauri da masu shiga tsakani ke da shi a rikicin Sudan
    • Ana fama da yunwa a Sudan Ta Kudu
  5. Sojojin Kamaru sun kuɓutar da ɗaliban da aka yi garkuwa da su

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Hukumomi a Kamaru sun ce an kuɓutar da wasu ɗalibai maza takwas da ake zargin ƴan aware ne suka sace su daga wata makaranta a yankin Arewa maso Yammacin ƙasar da yaƙi ya ɗaiɗaita.

    Abdoullahi Aliou, wani jami’in ƙaramar hukumar, ya ce ƴan bindigar sun kai farmaki makarantar da ke unguwar Esu a ranar Talatar da ta gabata inda suka “gallazawa” daliban kafin su yi awon gaba da su.

    An ƙona ajujuwa biyu da ofisoshin shugaban makarantar yayin harin.

    An kuma yi garkuwa da wasu jami’an makarantar, ciki har da mataimakin shugaban makarantar.

    Ɗalibai da dama da suka samu raunuka suna jinya a asibiti.

    "Dalibai takwas da aka yi garkuwa da su duk an sako su ne bayan shiga tsakani da jami'an tsaro suka yi," in ji Aliou, ba tare da bayar da cikakken bayani kan inda mataimakin shugaban makarantar da wani jami'in makarantar suke ba.

    Ya zuwa yanzu babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin harin na ranar Talata.

    Sama da yara 700,000 ne ke zaman gida bayan rufe makarantu da dama tun bayan ɓarkewar rikici a shekarar 2017, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

    Kimanin mutum 6,000 ne aka kashe tare da raba dubunnan mutane da muhallansu a rikicin, in ji Kungiyar International Crisis Group da ke bincike kan tashe-tashen hankula a ƙasashen duniya.

    • An ceto mutane 30 da aka yi garkuwa da su a jihar Bauchi
    • An kama wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a Taraba
  6. 'Ƴan majalisar da suka sauya sheƙa a Rivers sun rasa kujerunsu'

    Harabar Majalisar dokokin Rivers
    Bayanan hoto, Harabar Majalisar dokokin Rivers

    Shugaban ɗaya ɓangaren majalisar dokokin Rivers, Edison Ehie ya ayyana kujerun ƴan majalisa 27 da a baya-bayan nan suka fice daga jam'iyyar PDP zuwa APC a matsayin na waɗanda babu kowa a kai.

    An ɗauki wannan matakin ne da safiyar yau Laraba yayin zaman majalisar da Ehie ya jagoranta inda hakan ya zo daidai lokacin da ake rushe ginin majalisar dokokin.

    Lamarin ya faru ne sakamakon sauya sheƙar da mambobin 27 suka yi ƙarƙashin jagorancin Martin Amaewhule, wanda shi ne shugaban ɗaya ɓangaren majalisar da ke goyon bayan tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike.

    Majalisar dokokin jihar mai mambobi 32 ta tsunduma cikin rikicin shugabanci tun watan Oktoba inda ɓangarorin biyu da ke rikici da juna ke fafutukar ƙwace ikon majalisar.

    Wata babbar kotu a Patakwal a baya-bayan nan kuma ta tabbatar da Ehie a matsayin halastaccen shugaban majalisar.

    Kotun ta kuma hana magoya bayan Wike daga shiga harabar majalisar har sai an gama gyara majalisar da gwamnatin jihar ta ba da umarni.

    • Zaɓen Najeriya 2023: Sakamakon zaɓen gwamnoni na dukkanin jihohin Najeriya
    • Ƙuri'un da ba za a iya bayaninsu ba a zaɓen Najeriya mai cike da taƙaddama
  7. Al Sisi na kan gaba a zaɓen Masar da ake ƙirgawa

    Zaɓe a Masar

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, A ranar 18 ga watan Disamba ne ake sa ran sanar da sakamakon zaɓen a hukumance

    Hukumar zaɓe a Masar tana ci gaba da ƙirga ƙuri'u bayan kammala zaɓen shugaban ƙasa.

    An soma zaɓe ranar Lahadi inda aka kammala jefa ƙuri'a da ƙarfe 9 na dare agogon ƙasar inda mutum fiye da miliyan 67 suka yi rajistar zaɓen.

    Shugaban ƙasar mai ci Abdul Fattah al-Sisi na neman wa'adi na uku.

    Duk da cewa akwai ƴan takara uku da ke fafatawa a zaɓen, akasarin al'ummar Masar na ganin Mr Sisi ne zai lashe zaɓen cikin sauƙi.

    Sakamakon farko na zaɓen da aka fitar ba a hukumance ba ya nuna Mr Sisi ne ke kan gaba.

    Ana sa ran sanar da wanda ya yi nasara a zaɓen ranar 18 ga watan Disamba.

    • An fara zaben shugaban kasa a Masar
    • An gano birni mai shekara 3,000 da 'ya yi ɓatan dabo' a Masar
  8. Victor Osimhen: Daga ɗan talla kan titi a Lagos zuwa 'sabon sarki a Afirka'

  9. Isra'ila ta fara rasa goyon bayan duniya saboda Gaza – Biden

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Amurka, Joe Biden ya yi wata kakkausar suka kan shugabancin Isra'ila inda ya alaƙanta rasa goyon bayan da ƙasar ta yi da abin da ya kira luguden wuta ba ji ba gani a Gaza.

    Ya yi waɗan nan kalamai ne a wani taron kafa asusu da aka yi ranar Talata.

    "Tsaron Isra'ila na iya jingina da Amurka amma a yanzu haka, tana da fiye da Amurka. Tana da Tarayyar Turai, tana da Turai, tana da galibin ƙasashen duniya,' kamar yadda ya faɗa a Washington.

    "Amma sun fara rasa goyon baya saboda hare-haren bom da ke faruwa," in ji shi.

    • Biden na fuskantar ƙarin bijirewa a cikin gida kan yaƙin Isra'ila a Gaza
    • An fara cire rai kan yiwuwar sake tsagaita wuta a Gaza
  10. Tsohon Shugaban Saliyo na da hannu a yunƙurin juyin mulki – Ƴan sanda

    Ernest Bai Koroma

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomin tsaro a Saliyo sun ayyana tsohon shugaban ƙasar Ernest Bai Koroma a matsayin wanda ke da hannu a binciken da ake yi game da juyin mulkin da aka yi watan da ya gabata.

    Mr Koroma, wanda tun ranar Asabar aka ba da shi beli, yana ƙarƙashin dokar ɗaurin talala.

    Babban spetan ƴan sandan ƙasar, William Fayia Sellu ya ce Mr Koroma ba ya hannun ƴan sanda yayin da ƴan sandan ke ba shi duk girmamawar da yake buƙata.

    "Hakan ba wai yana nufin ya fi ƙarfin doka bane," in ji Mr Sellu.

    Ya bayyana cewa mutum 80 da ake zargi suna hannun yan sanda kuma daga cikinsu akwai jami'an tsaro da ke aiki a yanzu da waɗanda aka kora da waɗanda suka bar aiki da farar hula da kuma wani jami'i ma'aikacin gidan yari.

    An bayyana ƴar Koroma, Dankay Koroma cikin sauran mutum 54 da ake zargi a matsayin wadda ake nema ruwa a jallo, cikin jerin sunayen da ƴan sanda suka sake saki ranar Talata yayin da ake ci gaba da bincike.

    Gwamnati ta yi alƙawarin ba da tagomashi ga duk wanda ya taimaka da wani bayani da zai kai ga kama waɗanda ake zargin da a yanzu ake neman su ruwa a jallo.

    A makon da ya gabata ne Mr Koroma ya ce zai ƙyale doka ta yi aikinta.

    Ƙungiyar Ecowas ta amince da tura sojoji zuwa ƙasar ta Saliyo.

    • Ƙasashen da aka samu dawowar juyin mulki baya-bayan nan a Afirka
    • An kama masu yunkurin juyin mulki a Ghana
  11. Ƴan bindiga sun sace ƴan Koriya ta Kudu, sun kashe sojoji a Rivers

    Sojojin Najeriya

    Asalin hoton, AFP

    Wasu ƴan bindiga a Rivers da ke Kudancin Najeriya sun far wa wani jerin gwanon motocin wani kamfanin mai a jihar inda suka yi garkuwa da ma'aikatan kamfanin biyu ƴan Koriya ta Kudu tare da kashe sojoji huɗu.

    An kai wa tawagar hari ne ranar Talata kan titin East West da ke jihar.

    Ma'aikatan ƴan Koriya suna daga cikin ma'aikatan kamfanin Daewoo - da sojojin Najeriya suke yi musu rakiya zuwa wajen aiki.

    An ba da rahoton kisan direbobi biyu yayin harin.

    Rundunar sojin Najeriya tuni ta tabbatar da kisan sojojin da kuma sace baƙin.

    Cikin wata sanarwa, kakakin rundunar sojin, Manjo Jonah Danjuma,ya ce sojoji suna gudanar da bincike domin gano ma'aikatan da aka sace.

    Rundunar sojin ta ɗora alhakin harin kan wasu da take zargin ƴan bindiga ne amma zuwa yanzu, babu wanda ya ɗauki nauyin kai harin.

    Batun garkuwa da mutane matsala ce da ta zama ruwan dare a sassan Najeriya.

    • 'Rashin haɗin kan gwamnatoci dama ce ga 'yan bindiga'
    • ' Muna fama da karuwar hare-haren 'yan bindiga a yankinmu'
  12. Assalamu Alaykum

    Masu bibiyarmu, barkanmu da warhaka. A wannan shafi na Kai Tsaye da BBC Hausa ke tafiyar da shi, za mu rika bayyana muku irin wainar da ake toyawa a Najeriya da Nijar da sauran sassan duniya.

    Nabeela Mukhtar Uba da Aisha Babangida ne ke fatan kasancewa da ku.

    Da fatan za ku biyo mu domin karanta labaran da za mu wallafa muku daga yanzu har zuwa lokacin da za mu rufe wannan shafin.