Isra'ila ta ce an kashe sojojinta 10 a Gaza

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba and A'isha Babangida

  1. Sai da safenku

    Nan za mu ƙarƙare rahotonni a wannan shafi na labarai kai-tsaye na ranar Laraba.

    Sabo na nan tafe gobe Alhamis, wanda zai kawo wasu rahotonnin.

    Sai da safe.

  2. Duk tattaunawa kan makomar Gaza ba tare da mu ba mafarki ne kawai - Shugaban Hamas

    Ismail Haniyeh

    Asalin hoton, Reuters

    Ƙungiyar Hamas ta ce duk wani yunƙuri na tsara shugabancin Zirin Gaza ba tare da ita ba "molon-ka ne kawai".

    Mutumin da aka yi imanin shi ne shugaban ƙungiyar, Ismail Haniyeh, shi ne ya bayyana hakan cikin wani jawabi da ya yi ta kafar talabijin.

    "A shirye muke mu tattauna duk wani tsari da zai kawo ƙarshen mamayen Isra'ila da kuma ba da damar saita rayuwar Falasɗinawa a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da kuma Zirin Gaza," a cewar Haniyeh kamar yadda kamfanin labarai na Reuters ya fassara.

    A gefe guda kuma, Isra'ila ta haƙiƙance cewa ɗaya daga cikin manufar yaƙin da take yi a Gaza shi ne kawar da Hamas ɗin daga doron ƙasa.

    Ƙasashe da dama na kallon Hamas a matsayin ƙungiyar ta'addanci, cikinsu har da Amurka da Birtaniya.

  3. Sojojin Najeriya sun musanta zargin wani hafsa da sayen gida da kudin almundahana a Amurka

    General Lagbaja

    Asalin hoton, Nigerian Army Headquarters

    Rundunar sojin Najeriya ta ce ta lura cike da damuwa da kokarin wasu mutane na birkita tunanin jama'a da gangan, ta hanyar yunkurin shafa kashin kaji da jamhuru ga wani babban hafsanta, Manjo Janar Erema Akerejola kan zargin sayen gida a Amurka da kudaden almudahanar kwangila.

    Ta ce ba shakka, an sayi gidan da ake magana kansa a Amurka, amma bisa yarjejeniyar rancen gina gida da ake biya wata-wata, kuma har yanzu matar Manjo Janar Erema Akerejola wadda mazauniyar Amurka ce, tana ci gaba da biya.

    Rundunar sojin Najeriya a sanarwar da daraktan hulda da jama'anta Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya fitar, ta ce kokarin nuna cewa mai gidan asali ya/ta fito ne daga gidan talakawa, wani kokarin kunyata dukkan 'yan Najeriya ne masu aiki tukuru, wadanda suka tabuka wani abin kirki a rayuwa.

    Sanarwar ta ce muhimmin abu ne a lura cewa an nada Janar Erema Akerejola kan mukamin Babban Hafsan Tsara Dabarun Sufuri da Gyare-gyare na rundunar sojin Najeriya ne wata shida da ya wuce, gidan kuma da ake magana kansa, an mallake shi ne shekara 12 a baya.

    Ta kalubalanci mutumin da ya buga labarin a jaridar Sahara Reporters ta intanet da cewa bai iya gabatar da wata shaida ba, in ban da kalmomin wata majiya da bai iya bayyana sunanta ba, wadda ga alama a cewar rundunar sojojin Najeriya na cike da hauci, idan ma akwai ta a zahiri.

  4. EFCC na neman tsohon ministan lantarki na Najeriya ruwa a jallo

    Hukumar yaƙi da cin hanci a Najeriya (EFCC) ta bayyana cewa tana neman tsohon ministan makamashi da ƙarafa na kasar, Olu Agunloye, ruwa a jallo.

    EFCC na zargin sa ne da almundahanar dala biliyan shida na kwangilar wutar lantarki da aka bayar tun a gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo daga 1999 zuwa 2003.

    Rahotonni sun ce kwangilar ta shafi aikin tashar wuta ta Mambila da ke Gembu a jihar Taraba, wadda wani binciken BBC Hausa ya gano cewa ba a fara aikin ba shekara 40 da fara maganarsa.

    Tun da farko hukumar ta taɓa gayyatar Mista Agunloye a 2016, inda ta yi masa tambayoyi, sai dai ya sha musanta zarge-zargen.

    • Binciken BBC ya gano ba a fara aikin wutar Mambila ba shekara 40 da fara maganar aikin
    Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari rahoton Muhammad Annur:
  5. Kashim Shettima ya sake ganawa da 'yan fim da mawakan Najeriya

    Mataimakin shugaban Najeriya ya sake jaddada kudurin goyon bayan masana'antun fina-finai na Kannywood da Hollywood da ke kasar.

    Ya ce taron wanda shi ne na biyu a 'yan kwanakin nan na da nufin nanata kudurin gwamnatinsu na sake fasalin bangaren shirya fina-finai da wakoki zuwa kan gaba a kokarin baza komar tattalin arzikin Najeriya.

    Wata sanarwa da mataimakin shugaban kasar ya wallafa a shafinsa na X, ta don tabbatar da hakan, gwamnatinsu ta kara kasafin kudin ma'aikatar raya al'adu da harkokin nishadi daga naira biliyan 1.1 zuwa naira biliyan tara.

    Daga bangaren Kannywood, taron ya samu halartar jiga-jigan masana'antar kamar Ali Nuhu da Nuhu Abdullahi da kuma Mansura Isa.

    Kashim

    Asalin hoton, Kashim Shettima/X

    Kashim

    Asalin hoton, Kashim Shettima/X

    Kashim

    Asalin hoton, Kashim Shettima/X

    Kashim

    Asalin hoton, Kashim Shettima/X

  6. Majalisar Wakilan Amurka za ta kada kuri'ar amincewa da bincike don tsige Biden

    Biden

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yan majalisar wakilan Amurka na jam'iyyar Republican na ci gaba da yunkurin kada kuri'a don amincewa da kudurin bincike wanda zai kai ga tsige Shugaba Joe Biden.

    Nan gaba a Larabar nan ne, 'yan majalisar za su kada kuri'a a kan kudurin gudanar da bincike, wanda suka ce zai ba su karin iko na tattara shaida tursasa aiki da bukatun shari'a.

    Kwaimitoci guda uku na majalisar wakilan mai rinjayen 'yan jam'iyyar Republican na zargin aikata cin hanci da rashawa yayin mulkin Joe Biden na mataimakin shugaban kasa.

    Ya dai musanta aikata ba daidai ba, kuma har yanzu kwamitocin ba su fito da wata shaida ba.

  7. USAID da Gidauniyar Abdulsalam Rabi’u sun gyara cibiyoyin kula da masu tarin fuka a Najeriya

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar raya ƙasashe ta Amurka USAID da haɗin gwiwar gidauniyar AbdulSamad Rabi’u sun gyara cibiyoyi guda goma na kula da masu fama da tarin fuka a Najeriya.

    Cibiyoyin za su taimaka wajen gwaje-gwaje don gano mutanen da suka kamu da tarin da kuma hana yaɗuwarsa a sassan ƙasar.

    An raba aikin gyaran cibiyoyin kula da masu tarin fukar ne a sassan ƙasar, inda jihar Legas da Anambra da Oyo da kuma Rivers suka ci gajiya daga kudanci.

    Sauran jihohin da suka amfana sun haɗar da Kano da Bauchi da kuma Katsina.

    Waɗannan cibiyoyi sun samu gyara da kuma kayan aiki na zamani domin gudanar da gwaje-gwajen lafiya da kula da masu ɗauke da tarin fuka.

    Najeriya wadda ke matsayi na ɗaya a jerin ƙasashen da suka fi fama da bazuwar tarin fuka a Afirika, tana fuskantar manyan ƙalubale a fannin kula da lafiya, wanda kuma ke buƙatar kulawar gaggawa.

    Yanzu haka dai kusan kashi biyar na masu tarin fuka a duniya baki ɗaya, suna Najeriya.

    Aƙalla mutum dubu 98 ne cutar ke kashewa duke shekara a Najeriya.

    A shekarar 2022, hukumar tallafawa ƙasashe ta Amurkan ta samu tallafin dala dubu 500 daga gidauniyar AbdulSamad Rabi’u domin gudanar da ayyukan yaƙi da tarin fuka da dakile cin zarafin mata.

  8. Shugabar EU ta goyi bayan sa takunkumi ga 'yan kama-wuri-zauna 'masu tsaurin ra'ayi'

    EU chief

    Asalin hoton, EPA

    Yayin da Amurka da Birtaniya suka kakaba wa jami'an Hamas karin takunkumai, shugabar Hukumar Tarayyar Turai na kira a sanya wa 'yan kama-wuri-zauna "masu tsattsauran ra'ayi" takunkumai, wadanda ta ce su ne da alhakin kai hare-hare ga Falasdinawa a yankin Gabar Yamma da Kogin Jordan.

    Ursula von der Leyen ta ce: "Karuwar tarzoma daga 'yan kama-wuri-zauna masu tsattsauran ra'ayi, na haddasa tsananin wahalhalu ga Falasdinawa. Kuma hakan na yin zagon kasa ga yiwuwar samun dawwamammen zaman lafiya sannan yana iya rura wutar rashin kwanciyar hankali a yankin."

    Majalisar Dinkin Duniya da kasashe masu yawa na cewa duk matsugunnan 'yan Isra'ila a Gabar Yamma da Kogin Jordan haramtattu ne a karkashin dokokin kasashen duniya.

    Sai dai wannan batu ne da 'yan Isra'ila masu yawa, musamman wadanda ke zaune a irin wadannan matsugunai, cikin kakkausar murya suke musantawa.

    Karfafawa da fadada matsugunnan 'yan Isra'ila a Gabar Yamma, sun kasance wani muhimmin kuduri na gwamnatin Benjamin Netanyahu, kuma yana daya daga cikin batutuwa masu janyo ka-ce-na-ce tsakanin Isra'ila da Falasdinawa.

    A farkon wannan shekara, Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya soki lamirin harkokin gina matsugunan 'yan Isra'ila a Gabar Yamma wadda ke karkashin mamaya, inda ya bayyana lamarin da cewa ya zama wani kadangaren bakin tulu ga yunkurin samun zaman lafiya.

  9. Hamas ta yi tir da takunkuman da Amurka da Birtaniya suka saka mata

    Ƙungiyar 'yan gwagwarmaya ta Falasɗinawa Hamas ta yi tir da matakin gwamnatin Amurka da ta Birtaniya na saka wa wasu shugabanninta takunkumai.

    Cikin wata sanarwa a dandalin Telegram, ƙungiyar ta ce yunƙurin alama ce da ke nuna "hannunsu cikin hare-haren da Isra'ila ke kai wa mutanenmu".

    Amurka da Birtaniya sun saka ƙarin takunkumai kan mutanen da ke da alaƙa da Hamas a Turkiyya da wasu ƙasashe.

    Sashen baitul-malin Amurka ya faɗa cikin wata sanarwa cewa mutum takwas ne matakin na baya-bayan nan ya shafa. Ita ma Birtaniya ta ce ta saka wa ƙarin wasu bakwai.

    "Wannan matakin, bisa zarge-zarge marasa tushe da Isra'ila ta ingiza, ba zai dakatar da Hamas ba wajen kare haƙƙin Falasɗinawa," in ji Hamas.

  10. An kashe Falasɗinawa 18,608 a gaza zuwa yanzu - Ma'aikatar lafiya

    Ma'aikatar lafiya a Zirin Gaza da ke ƙarƙashin ikon Hamas ta ce adadin Falasɗinawa da hare-haren Isra'ila suka kashe zuwa yanzu sun kai 18,608.

    Ta ƙara da cewa an jikkata wasu 50,594 tun daga ranar 7 ga watan Oktoba.

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce sama da rabin mazauna Gaza na fama da yunwa saboda ƙarancin kayan agajin da ke shiga zirin.

  11. Jana'izar sojan Isra'ila da aka kashe a Gaza

    Kamar yadda muka kawo muku rahoto, dakarun sojin Isra'ila sun ce an kashe sojojin kasar goma a fagen daga cikin arewacin Gaza a jiya - abin da ya sanya ta zama rana mafi muni ga rundunar sojin tun da ta fara mamaye ta kasa.

    A cikinsu har da Laftanal Kanal Tomer Grinberg, wanda aka yi jana'izarsa yau a birnin Kudus.

    Israeli soldiers

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, An kashe Kanal Grinberg a Gaza ranar Talata
    Funeral in Israel

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, An gudanar da jana'izar Kanal Grinberg a makabartar sojoji ta Tsaunin Herzl da ke Kudus ranar Laraba
    Israeli minister

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Ministan Tsaron Isra'ila Yoav Gallant yana rarrashin matar marigayin kwamandan Laftanal Kanal Tomer Grinberg
  12. Labarai da dumi-dumi, Tinubu ya cire malaman jami'a daga tsarin albashi na IPPIS

    Bola Tinubu

    Asalin hoton, State House

    Majalisar zartarwa ta Najeriya ta cire malaman jami'a, da na kwalejojin ilimi da fasaha daga tsarin albashi na Integrated Personnel Payroll Information System (IPPIS).

    Ministan Ilimi Farfesa Tahir Mamman ya ce Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ne ya ba da umarnin yin hakan a zaman majalisar da ya jagoranta a yau Laraba.

    Ya ƙara da cewa hakan zai bai wa shugabannin cibiyoyin ilimin damar ɗaukar ma'aikata ba tare da sun nemi amincewar ofishin shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya ba.

    "A taƙaice, shugaban ƙasa da majalisar sun nuna damuwarsu ne kan yadda ake gudanar da jami'o'in, amma hakan ba shi da alaƙa da zaɓar wani tsarin biyan albashi ko kuma zargin rashin adalci," a cewar ministan kamar yadda kafofin yaɗa labaran Najeriya suka ruwaito shi yana faɗa jim kaɗan bayan kammala zaman a fadar shugaban ƙasa.

    Ƙungiyar malaman jami'a ta ASUU ta daɗe tana neman gwamnatin Najeriya ta cire su daga tsarin, wanda ya hana su gudanar da wasu ayyuka da kuma ƙayyade kuɗin da za su samu a matsayin albashi.

    Hakan na nufin yanzu jami'o'in da sauran kwalejoji za su dinga biyan malamansu albashi da kansu ba sai sun dogara da gwamnatin tarayya ba, in ji Ministan Yaɗa Labarai Muhammed Idris.

  13. Alluran riga-kafin yara sun ƙare a Gaza - Ma'aikatar lafiya

    Gaza

    Asalin hoton, EPA

    Ma'aikatar Lafiya a Gaza ta sanar da karewar riga-kafin cutukan yara, yayin da hukumomin MDD suka yi gargadin barkewar cutuka masu saurin yaduwa.

    Hukumomin lafiya a Gaza sun yi kira ga kasashen ketare su samar musu da karin riga-kafi cikin kankanin lokaci.

    Yakin da Hamas ke fafatwa da Gaza ya ɗaiɗaita kashi 80 na al'ummar Gaza, inda a halin yanzu mutane na rayuwa cikin cunkoson jama'a a wurare marasa tsafta.

    Alexandra Murdoch, Jami'ar Asusun Tallafawa Yara Kanana ta ce: "Muna kiran bangarorin da suke rikici da juna su tsagaita wauta, yara na cikin yanayi mai wahala a Gaza"

    Wani rahoto da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta fitar ya bayyana karuwar cutar numfashi da gudawa da cutukan fata yayin da ake ci gaba da yaki a arewaci da kudancin Gaza.

    Isra'ila ta kara da cewa ta yi nasarar kai hare-hare sama da 250 cikin sa'o'i 24.

  14. Isra'ila za ta ci gaba da yakar Hamas ko da goyon baya ko babu - Minista

    Idan muka sake komawa kan rikicin Gaza, ministan harkokin wajen Isra'ila ya yi jawabi bayan gagarumin goyon bayan Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya kan wani kuduri da ba lallai ne a yi aiki da shi ba da ke neman a tsagaita wuta a Gaza.

    Lamarin ya sanya ana ganin Isra'ila a matsayin wadda ke kara saniyar ware bayan Shugaban Amurka Joe Biden ya gabatar da suka mafi zafi ga shugabancin Isra'ila.

    Kai tsaye dai ya alakanta asarar goyon bayan kasashen duniya ga Isra'ila, da abin da ya kira luguden bama-bamai kan Falasdinawa ba-ji-ba-gani.

    Ministan harkokin wajen Isra'ila Eli Cohen ya mayar da martani, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ba da rahoton, inda ya dage a kan cewa:

  15. Kotu ta ɗaure wani ɗan Uganda shekara 105 saboda kisan kai

    Wata babbar kotu a Kampala babban birnin Uganda ta yanke wa wani matashi hukuncin ɗaurin shekara 105 bayan samun sa da laifin kashe mutane masu yawa

    An yanke wa Musa Musasizi, mai shekara 25 hukuncin ne ranar Laraba, bayan ya amsa laifin kashe mata uku ciki har da budurwarsa da wata yarinya ‘yar wata uku.

    Rahotanni sun bayyana cewa ya yi soyayya da matan kafin ya yi lalata da su kuma ya kashe su, sannan ya zubar da gawarwakinsu.

    Mai shari'a, Margaret Mutonyi, ta ce hukuncin ɗaurin ya zama dole, domin kare matasa mata ciki har da 'yar Musasizi 'yar shekara shida, kamar yadda tashar NTV mai zaman kanta ta ruwaito.

    An kama Musasizi ne a watan Maris na 2021 bisa zargin kashe mata biyar da wani jariri.

    An same shi da laifin kisan ɗaya daga cikin matan a watan Yulin bana, a lokacin, lauyansa ya nemi alƙali ya yi masa afuwa, yana mai cewa Musasizi, wanda ya girma a kan titi, ba samu cikakiyar tarbiyya ba.

  16. Gwamnan Ribas ya gabatar da kasafin kuɗi ga majalisar dokoki mai mambobi biyar

    Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya gabatar da kudurin kasafin kudi na naira biliyan 800 na shekarar 2024 ga ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas da ke zama a gidan gwamnati.

    Hakan ya faru ne a daidai lokacin da aka rusa ginin zauren majalisar dokokin jihar bisa umarnin gwamnati.

    Gwamnatin jihar dai ta ce matakin da ta ɗauka na rusawa da sake gina zauren majalisar dokokin jihar, sun zama tilas, sakamakon matsalolin da wasu sassan ginin suka fuskanta, sanadin fashewar wani abu da kuma tashin wata gobara a baya-bayan nan, lamarin da ya tilasta sabunta ginin don tabbatar da ingancinsa.

    Gwamnan ya gabatar da kasafin kuɗin ne a yau, Laraba yayin zaman majalisar da ya ƙunshi ‘yan majalisar biyar kawai masu biyayya gare shi.

    Idan dai za a iya tunawa, ‘yan majalisar 27 da ke biyayya ga ministan Abuja, babban birnin Najeriya kuma tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike ne suka fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC mai mulki.

    ‘Yan majalisar 27 ba su halarci taron ba lokacin da gwamnan ya gabatar da kasafin kuɗin.

    • Fankon kundin kasafin kuɗi Tinubu ya ba mu — Ƴan Majalisa
    • Abu biyar da ke da ɗaure kai a rikicin siyasar Rivers
  17. Sojojin Nijar sun sanya wa Faransa wa'adin janye dakarunta daga ƙasar

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Rundunar sojan Nijar ta ce sauran sojojin Faransa 157 da ke ƙasar za su kammala janyewarsu nan da ranar 22 ga watan Disamba.

    Dakarun da suka rage sun fito ne daga tawagogin da ke kula da kayan aiki daga farkon dakaru 1,346 da aka tura a yankin Sahel, in ji runudunar sojin a cikin wata sanarwa da ta fitar ta X.

    An dai samu takun saka tsakanin Faransa da Nijar biyo bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yuli ƙarƙashin jagorancin Janar Abdourahmane Tchiani wanda ya hamɓarar da zabaɓɓen shugaban ƙasar, Mohamed Bazoum.

    Bayan an ɗauki tsawon lokaci ana gwabzawa, Faransa ta fara janye sojojinta daga Nijar a cikin watan Oktoba, a daidai lokacin da gwamnatin mulkin sojan kasar ta buƙaci Faransawa da su fice, bisa zarginsu da yunkurin dawo da shugaba Bazoum da karfin tsiya.

    Gwamnatin mulkin sojan ta kuma ce tana shirin kawo karshen wasu yarjejeniyoyin soja da na tattalin arziki da aka cimma da Paris.

    Ana kallon Nijar a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashen yammacin duniya a yankin Sahel da keyaƙi da ta'addanci.

    Tasirin Faransa a Nijar na raguwa bayan juyin mulkin da aka yi a wasu ƙasashen da ta yi wa mulkin mallaka..

    • Kawuna sun rabu kan korar da sojojin Nijar ke wa ƙasashen duniya
    • Me ya sa har yanzu wasu ƙasashen Afirka ke maraba da sojojin Faransa?
  18. Amurka da Birtaniya sun saka wa jami'an Hamas ƙarin takunkumi

    Hukumar kula da Baitul-mali ta Amurka ta sanar a jiya Laraba cewa, Amurka da Burtaniya sun kakaba takunkumi kan jami'ai da masu kai ɗauki ga ƙungiyar Hamas ta Falasɗinawa.

    Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto ma'aikatar baitul-malin kasar ta ce takunkumin ya shafi mutane takwas ne waɗanda ke ci gaba da ajandar Hamas ta hanyar wakiltar muradun kungiyar a kasashen waje da kuma kula da kudadenta.

    • An nuna wa BBC hujjojin yadda mayaƙan Hamas suka yi wa matan Isra'ila fyaɗe
    • Wane ne Yahya Sinwar shugaban Hamas na Gaza?
  19. Yaƙin Ukraine: Mutane sun jikkata a harin makami mai linzami da aka kai a Kyiv

    ....

    Mutane da dama ne suka jikkata sakamakon wani harin makami mai linzami da aka kai a Kiev babban birnin ƙasar Ukraine cikin dare, kamar yadda hukumomi suka ce.

    Magajin garin Kyiv Vitali Klitschko ya ce mutum 53 ne suka jikkata a hare-haren da suka hada da yara shida.

    An bayar da rahoton cewa, harin ta lalata gine-ginen ajin renon yara da na asibiti, yayin da hukumomi suka ce an harbo makamai masu linzami na Rasha 10.

    Hare-haren sun faru ne bayan shugaban ƙasar Volodymyr Zelensky ya bar Amurka.

    Roƙon da ya yi na Majalisar Dokokin ta amince da ƙarin tallafin soji ga Ukraine bai samu ci gaba ba.

    Shugabannin Tarayyar Turai za su kuma tattauna batun ƙarin taimako ga Ukraine a ranar Alhamis, kuma shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta ce "dole ne mu baiwa Ukraine abin da ya kamata ya sa ta kasance mai ƙarfi a yau".

    Zelensky ya yi alkawarin mayar da martani ga harin na daren Laraba.

    "Rasha ta sake tabbatar da cewa ƙasa ce mai muni da ke harba makamai masu linzami da daddare, tana kokarin kai hari a wuraren zama, ajin renon yara, da wuraren makamashi a lokacin hunturu," in ji shugaban a kan shafin sada zumunta na X.

    • Jirgin Ukraine ya kai wa jirgin ruwan Rasha hari a Bahar Aswad
    • Amurka ta bai wa Ukraine harsashi miliyan daya da ta kwace daga Iran
  20. Abin da ya sa muka rushe ginin majalisar dokokin Ribas – Fubara

    .

    Asalin hoton, Others

    Bayanan hoto, Motocin rusa gine-gine yayin da suke ruguje ginin majalisar ranar Laraba

    Gwamnatin Ribas da ke Kudancin Najeriya ta sanar da matakin da ta ɗauka na rusawa da sake gina zauren majalisar dokokin jihar, sakamakon matsalolin da wasu ɓangarorin ginin suka fuskanta sanaiyyar fashewar wani abu da kuma tashin gobarar da ta faru a baya-bayan nan, lamarin da ya tilasta sabunta ginin don tabbatar da ingancinsa.

    Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Ribas, Joseph Johnson ne ya fitar da wannan sanarwa.

    “Bayan tantance ingancin ginin, masana sun shawarci gwamnati cewa ci gaba da amfani da ginin a halin da take ciki zai zama haɗari,” in ji shi.

    Johnson ya bayyana ƙoƙarin da gwamnati ke yi na gano matakan bin hanyoyin rage kashe kuɗi wajen gyara har sai sun amince da tsarin sabon ginin.

    Kafin lokacin, gwamnatin Ribas ta samar da madadin wurin da majalisar za ta gudanar da harkokinta har sai an sake gina majalisar.” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

    Sanarwar ta ce madadin wurin da aka samar don gudanar da harkokin majalisar na wucin gadi yana cikin fadar gwamnati.

    • Yadda Wike ya tayar da ƙura bayan naɗa shi ministan Abuja
    • Zaɓen Najeriya a Jihar Rivers: Jiha mai arzikin man fetur maras lantarki