Ana ci gaba da gwabza faɗa a Gaza da Gaɓar Yamma da Kogin Jordan
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Rahoto kai-tsaye
Nabeela Mukhtar Uba and A'isha Babangida
Abubuwan da suka faru a Isra'ila da Gaza kawo yanzu a yau
Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare a Gaza, inda ta fi mayar da hankali kan Khan Younis a kudancin kasar.
An kuma gwabza fada a Rafah kusa da kan iyakar Masar, inda dubban Falasɗinawa da suka rasa matsugunansu suka nemi mafaka.
A halin da ake ciki kuma a Jenin da ke Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da ke ƙarƙashin mamaya, an kashe mutum hudu a wani abin da shaidun gani da ido suka bayyana a matsayin wani harin da jirgi mara matuki ya kai.
Har yanzu dai sojojin Isra'ila na ci gaba da gudanar da ayyukansu a Zirin Gaza, kuma BBC ta ga wasu katapila masu sulke na sintiri.
Matsin lamba na ƙasashen duniya yana ƙaruwa game da rikicin jin ƙai, kuma Amurka ta sake yin kira ga Isra'ila da ta ƙara yin kokarin kare fararen hula a Gaza.
Bayan haka, ana sa ran babban taron Majalisar Dinkin Duniya zai kada kuri'a kan wani kuduri na neman tsagaita bude wuta a Gaza.
Shahararriyar mawaƙiya, Zahara Bulelwa ta Afirka ta Kudu ta rasu
Asalin hoton, AFP
Mawaƙiyar afro pop ta Afirka ta Kudu, Bulelwa Mkutukana, da aka fi sani da suna Zahara, wadda ta lashe kyautukan yabo da dama, ta rasu.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ministan al'adu na ƙasar ya fitar.
Rahotanni sun ce mawaƙiyar ta jima a asibiti tana jinya, inda ta yi fama da ciwon hanta, sannan gwamnati ta riƙa tallafa wa iyalanta na tsawon lokaci, a cewar ministan al'adu Zizi Kodwa.
Mawakiyar ta samu shahara ne a shekarar 2011 bayan ta fitar da kundin waƙoƙinta mai suna 'Loliwe', da ya samu karbuwa a fadin Afirka.
A shekarar 2019, Zahara ta bayyana yadda take fama da matsalar yawan shan barasa.
A watan da ya gabata ƴan'uwanta suka bayyana cewa an kwantar da ita a asibiti, inda suka buƙaci al'ummar ƙasar su sanya ta cikin addu'a.
Ta rasu ne a daren Litinin a wani asibiti da ke birnin Johannesburg tana da shekara 36 da haihuwa.
Mece ce cutar anthrax kuma ta yaya take kisa?
Sojojin Isra'ila sun kai hari a asibitin Kamal Adwan da ke arewacin Zirin Gaza
Asalin hoton, Getty Images
Ashraf Ghadra, kakakin ma'aikatar lafiya ta Gaza da ƙungiyar Hamas ke iko da shi, ya bayar da rahoton cewa, a faɗan da ake ci gaba da yi a arewacin Gaza, sojojin Isra'ila sun kai hari a asibitin Kamal Adwan.
A cewar Ghadra, sojojin Isra'ila sun tara maza da suka haɗa da ma'aikatan lafiya a harabar asibitin.
Asibitin, wanda aka yi wa kawanya tun makon da ya gabata, shi ne wurin kiwon lafiya na karshe da ke aiki a arewacin Gaza.
Ghadra, a wani sakon da ya aike ta wayar tarho, ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya, da hukumar lafiya ta duniya, da kungiyar agaji ta Red Cross da su ɗauki matakin gaggawa don ceto rayukan marasa lafiya a asibitin.
Ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya OCHA ya bayar da rahoton cewa, an kashe mata biyu a harin da aka kai a sashen mata na asibitin.
A halin yanzu, majinyata 65, ciki har da yara 12, suna cikin sashin kulawar gaggawa, kuma jarirai shida suna cikin sashin kula da jarirai.
OCHA ta bayyana cewa kusan mutane dubu uku da suka rasa matsugunansu na makale a asibitin, suna jiran ruwa da abinci.
Asibitocin da yakin Isra'ila da Hamas ya ritsa da su a Gaza
Abin da muka sani game da farmakin da Isra'ila ta kai babban asibitin Gaza
Giwaye 100 sun mutu a Zimbabwe
Asalin hoton, Getty Images
Karancin ruwan sama yayi sanadin mutuwar akalla giwaye 100 a babban gandun-daji na zimbabwe, Hwange.
Rahotanni sun ce giwayen sun mutu ne bayan rijiyoyin da suke shan ruwa daga gare su sun ƙafe. Ana fargabar cewa wasu ƙarin giwayen da yawa za su mutu.
Cikin wata sanarwa a watan Disamba, Asusun kula da walwalar dabbobi na duniya (IFAW) ya yi gargaɗin cewa "giwaye da sauran namun daji za su shiga cikin matsala idan damina ba ta faɗi da wuri ba".
Asusun na IFAW ya ce an samu jinkirin faɗuwar damina a Zimbabwe da mako biyar saboda yanayin tunkuɗowar zafi daga teku na El Nino.
Aƙalla giwaye 45,000 ne ke rayuwa a gandun daji na Hwange da ke ƙasar ta Zimbabwe.
Majalisar Ɗinkin Duniya za ta kaɗa kuri'a kan tsagaita wuta nan take a Gaza
A yau ne babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya zai kaɗa kuri’a kan tsagaita wuta nan take a Gaza, kwanaki bayan da Amurka ta ƙi amincewa da wani kuduri makamancin haka da kwamitin sulhu ya gabatar.
Ƙungiyar kasashen Larabawa 20 da ƙungiyar haɗin kan ƙasashen musulmi ne suka gabatar da daftarin da aka gabatar a halin yanzu.
Babu wata ƙasa da ke da kujeran na-ƙi a zauren Majalisar mai wakilai 193.
Sai dai kuma, ba kamar a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ba, shawarwarin babban zauren majalisar ba wajibi ba ne a yi amfani da su duk da dai hakan na nufin ra'ayin mafi rinjaye a duniya
Tun lokacin da aka fara yaƙin, kwamitin sulhun ya gaza sau shida wajen zartar da kudurin neman tsagaita buɗe wuta saboda rashin jituwa tsakanin mambobinsa 15.
Yadda Hamas ta haɗa dakarun da suka kai wa Isra'ila harin 7 ga Oktoba
Wane ne Yahya Sinwar shugaban Hamas na Gaza?
CBN ya dakatar da karɓar kuɗi ga masu ajiya sama da 500,000
Asalin hoton, CBN/FACEBOOK
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya dakatar da karbar kuɗi daga masu ajiye kuɗi a asusunsu na banki, waɗanda suka kai sama da naira 500,000, daga yanzu har zuwa ranar 30 ga Afrilu, 2024.
Babban Bankin ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin mai dauke da sa hannun mukaddashin daraktan sanya ido kan harkokin bankuna, Adetona Adedeji.
A shekara ta 2019, babban bankin ya bayyana cewa zai fara cire wa masu mu'ammala da banki kuɗi a lokacin da za su cire ko ajiye kuɗi a banki a wani bangare na kokarinsa na rage amfani da tsabar kuɗi.
A baya, babban bankin ya umarci bankuna su riƙa karbar kashi biyar bisa dari na kudaden da za a cire da kuma kashi uku cikin dari na kuɗaɗen da za a ajiye sama da naira miliyan uku.
Sai dai, a cikin sabon umarnin da ya bayar, babban bankin ya ce, ya kamata bankunan su karbi dukkan kudaden da jama’a ke ajiyewa a banki ba tare da wani caji ba.
'Yan Najeriya na kumfar baki a kan 'ɓacewar sabbin takardun naira'
Umarnin kotun kolin Najeriya a kan batun shari'ar daina amfani da tsoffin kudi ya jefa mutane cikin rudani
Za mu ci gaba da fafata yaƙi ko za mu mutu - al-Burhan
Asalin hoton, Reuters
Shugaban ƙasar Sudan kuma shugaban rundunar sojojin kasar, Laftanar Janar Abdel Fattah al-Burhan ya ce sojoji za su ci gaba da yaƙar dakarun RSF "har sai sun su sami nasara ko da za su mutu ne", a cewar kafar yaɗa labaran ƙasar.
Janar Burhan ya bayyana haka ne a lokacin da ya ziyarci sansanin sojoji a garin Shendi da ke arewacin jihar Kogin Nile.
Matakin nasa na zuwa ne kwanaki biyu kacal bayan da kungiyar Igad ta Gabashin Afirka ta sanar da samun alkawurra daga rundunonin soji da kuma RSF domin tattaunawa cikin gaggawa tare da cimma matsaya kan dakatar da yaƙin da ake yi.
Sai dai majalisar da sojoji ke jagoranta ta musanta ikirarin amincewa da tsagaita bude wuta da tattaunawa da RSF.
Rikicin Sudan: Shugabanni sun ɗauki aniyar kawo ƙarshen rikici
Me za a yi da gawawwakin mutanen da aka kashe a Khartoum?
Hotunan bayan harin da Isra'ila ta kai a Khan Younis
Waɗannan hotuna daga Khan Younis, wani birni da ke kudancin Zirin Gaza, sun nuna sakamakon harin bam da Isra'ila ta kai.
A cikin makon da ya gabata, Isra'ila ta mayar da hankali wajen kai hare-hare a kudancin Gaza.
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, An ga hayaƙi na tashi a Gaza, kamar yadda aka gani daga kudancin Isra'ila
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Falasɗinawa na kallon tarkacen wuraren da Isra'ila ta kai hari kan gidaje
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Wani Bafalasdine na kallon ɓarnar da harin Isra'ila ya yi
Alƙalin wasa ya sha naushi daga shugaban wata ƙungiyar ƙwallon ƙafa a Turkiyya
Asalin hoton, Getty Images
Jami'ai a Turkiyya sun ce suna ɗaukar mataki na magance duk wata matsala a ɓangaren wasannin kwallon ƙafa ta hanyar dakatar da dukkan wasu wasanni a ƙasar.
Hakan ya biyo bayan naushi da aka yi wa ɗaya daga cikin manyan alƙalan wasan ƙasar bayan wasan da aka yi a jiya Litinin.
Halil Umut Meler, ya sha naushi daga shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafar ƙasar ta MKE Ankaraguju, bayan sun faɗi a wasan da aka yi a gasar Super Lig Clash.
Kazalika magoya bayan ƙungiyar ma sun daki alkalin wasan wanda aka garzaya da shi asibiti don yi masa magani.
Wakilin BBC ya ce abin da ya faru a daren Litinin ya janyo tashin hankali wanda ya haɗa da 'yan wasa da 'yan kallo a inda aka kama mutane da dama a filin wasan.
Shugaban ƙasar Recep Tayyip Erdogan na daga cikin wadanda suka yi alawadai da abin da aka yi.
Wane ne Messin Turkiyya da Real Madrid ke nema
Fifa za ta kara daukar tsauraran matakai a kan Rubiales
Hotunan yadda Isra'ila ta harba atileri zuwa Gaza
Sojojin Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare a Zirin Gaza
Ga wasu hotunan da ke nuna yadda sojojin Isra'ila suka harba atileri zuwa Gaza
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Sojojin Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare a Zirin Gaza
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Rundunar sojin Isra'ila ta yi luguden wuta kan Gaza kusa da kan iyaka a kudancin Isra'ila
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Sojoji sun harba atileri a daren biyar na bikin Hanukkah na Yahudawa.
Ana ci gaba da gwabza faɗa a Gaza da Gaɓar Yamma da Kogin Jordan
Asalin hoton, Reuters
A cikin 'yan sa'o'i da suka gabata mun sami rahotannin ci gaba da kai hare-haren bama-bamai da fada a Gaza, da kuma hare-hare a Gaɓr Yamma da Kogin Jordan.
A kudancin Gaza, Isra'ila na kai hare-hare ta sama kan birnin Rafah, a cewar kamfanin dillancin labaran Falasɗinawa Wafa
A Khan Younis, inda dubban ɗaruruwan mutanen Gaza suka nemi mafaka, tankunan Isra'ila sun yi ta tahowa zuwa tsakiyar birnin.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, mayaƙan masu iƙirarin jihadi sun tarwatsa wani gida a Khan Younis inda sojojin Isra'ila ke neman wani hanyar ƙarƙashin ƙasa. A cikin sa'o'i na karshe rundunar ta ce sojojinta da dama sun samu munanan raunuka a kudancin Gaza.
Har ila yau Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare a yankunan arewacin yankin, inda sojojin suka ce sun kewaye yankunan karshe na Hamas a Jabaliya da Shejaiya.
Kafofin yaɗa labaran Falasɗinawa sun kuma bayar da rahoton samame tare da kame a wasu garuruwan da ke Gaɓar yamma da Kogin Jordan cikin dare.
Hotunan da cibiyar yaɗa labaran Falasɗinawa ta wallafa ya nuna yadda sojojin Isra'ila ke kutsawa cikin sansanin 'yan gudun hijira na Jenin da ke Gaɓr Yamma da Kogin Jordan da ke ƙarƙashin mamaye.
Akwai kuma rahotannin wasu hare-hare a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, kamar garuruwan Silwad da Nablus.
An kama aƙalla mutum goma, ciki har da wani yaro ɗan shekara 12 a Silwad, inji rahoton Wafa.
Kafofin yaɗa labaran Majalisar Dinkin Duniya da na Isra’ila sun ce ƙungiyoyin Falasdinawa na ci gaba da harba makaman roka a Isra’ila.
Rikicin kama-wuri-zauna ya haddasa fargaba a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan
'Ina takaicin yadda na gaza ceto rayuwar yaran da ke mutuwa a Gaza'
An kashe mutum huɗu a wani harin da jiragen yaƙin Jenin suka kai
Hotunan bidiyo
daga cikin tsohon birnin Jenin, a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye, sun nuna gawarwaki da
dama kwance a ƙasa, wasu mutane kalilan ne suka taru a
kusa da su.
Shaidu sun ce an kai harin ne da jiragen yaƙi mara matuki .
Asibitoci a Jenin
sun tabbatar da mutuwar mutum huɗu, kuma ana tunanin aƙalla ɗaya ya samu munanan raunuka.
Sojojin Isra'ila
kuma suna aiki a cikin sansanin Jenin - mazauna masu ɗaukar hotuna daga cikin gidajensu sun yada bidiyon yadda sojoji ke tafiya
cikin tsanaki a kan tituna sanye da kayan yaƙi da makamansu.
Sojojin Israila sun fara janye farmaki kan Falasdinawa a Jenin
Ina ne sansanin Jenin, kuma me ya sa rikici ke ta'azzara a yankin?
'Isra'ila za ta yi duk mai yiwuwa wajen kare rayukan fararen hula a Gaza'
Asalin hoton, Reuters
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka ya ce Isra'ila zata yi duk mai yiwuwa wajen kare rayukan fararen hular falasɗinawa a Gaza.
Nathaniel Tek, ya ce akwai buƙatar a rinka ƙyale mutane na matsawa daga wajen da ake yaƙin, kodayake ya ce alhakin Hamas ne ma ta tabbatar da kare fararen hular.
Rahotanni sun ce an kashe mutane fiye da dubu 18 a Gaza, tun bayan da Hamas ta ƙaddamar da hari a kudancin Isra'ila a watan Oktoban da ya gabata.
A yanzu haka Falasɗinawa na mutuwa saboda sanyi da yunwa, yayinda al'amura kuma ke kara cabewa.
Nan gaba a yau ne babban zauren majalisar dinkin duniya zai kada kuri'a a kan batun gaggauta tsagaita wuta.
An fara cire rai kan yiwuwar sake tsagaita wuta a Gaza
BBC ta ga bidiyon yadda aka yi wa Falasɗinawa tsirara a Gaza
Assalamu alaikum
Masu bin mu a wannan shafi barkanmu da safiyar Talata.
Aisha Babangida ke fatan kasancewa da ku domin kawo muku labaran wasu abubuwan da ke faruwa a faɗin duniya.
Kada ku manta da tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta.