Hamas ta yi barazanar ƙin sakin mutanen da take garkuwa da su

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba and A'isha Babangida

  1. Za a binciki masu yaɗa jita-jitar mutuwar mataimakin shugaban Tanzania

    Philip Mpango

    Asalin hoton, TANZANIAN STATE HOUSE/X

    Hukumomi a Tanzania sun fara gudanar da bincike kan masu amfani da shafukan sada zumunta da ake zargi da yaɗa labaran ƙarya game da lafiyar mataimakin shugaban ƙasar, Philip Mpango.

    An ga Mista Mpango ranar Lahadi bayan da ya shafe wata ɗaya ba a ji ɗuriyarsa ba, lamarin da ya kawo ƙarshen jita-jitar da ake yaɗawa cewa ya mutu.

    Ministan yaɗa labaran ƙasar Nape Nnauye ya ba da umarnin yin bincike kan waɗanda suka yaɗa jita-jitar.

    Mr Mpango ya ce bai ji daɗin labaran ƙaryar ba da aka riƙa yaɗawa a kafafen sada zumunta.

    Rabon da a ga mataimakin shugaban ƙasar a bainar jama'a tun 31 ga watan Oktoba lokavin da yake wakiltar shugaba Samia Suluhu assan a wani taron shugabanni daga ƙungiyar raya ƙasashen Kudancin Afirka.

    Rashin ganinsa a bainar jama'a ya janyo damuwa inda Firaminista Kassim Majaliwa a baya ya gargaɗi jama'a kan yaɗa jita-jita.

  2. 'Yan sandan Bauchi na bincike kan magidancin da ake zargi da yi wa matarsa fashi da taɓarya

    Police item

    Asalin hoton, Nigeria Police Force Bauchi State Command/Facebook

    Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi sun ce suna ci gaba da bincike kan zargin wani magidanci da yunƙurin kashe matarsa lokacin da ya je yi mata fashi a gidansu na aure, tare da gabatar da taɓarya da hijabin da suka ce, da su ne aka aikata laifin.

    Kwamishinan 'yan sandan Bauchi, CP Auwal Musa Mohammed ya ba da umarnin cewa a mayar da maganar zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar don bankaɗo hakikanin abin da ya faru tsakanin magidancin da ake zargi da mai dakinsa.

    Wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan Bauchi, SP Ahmed Mohammed Wakil ya fitar a ƙarshen mako ta ce tuni jami'ansu suka kama magidancin mai shekara 35 da haihuwa.

    Sanarwar ta ce ana zargin magidancin wanda muka sakaya sunansa da kai wa matarsa farmaki da haddasa mugun rauni da yunƙurin aikata laifin da ya yi daidai da kisan kai.

    Ahmed Wakil ya ce a ranar Asabar 2 ga watan Disamba ne suka samu rahoton faruwar wannan lamari, inda suka garzaya wurin da abin ya faru tare da ɗaukan matar da aka yi wa fashi zuwa asibitin ƙwararru na jihar Bauchi.

    'Yan sanda sun ce binciken farko-farko sun bayyana cewa, mutumin da ake zargi ba tare da yawan turjiya ba, ya amsa cewa ya aikata abin da ake zarginsa da shi.

    "A jawabinsa, wanda ake zargi ya ankarar da matarsa bisa ƙarya cewa 'yan fashi sun shiga gidansu, kuma cikin hanzari ya shiga ɗakinta ya ce ta rufe fuskarta da hijabi.

    "Daga nan sai ya fito daga ɗakin, ya rufe fuskarsa da hijabi, tare da ɗaukan tabarya sannan ya koma dakin, inda ya fara buga wa matar tabaryar," in ji sanarwar 'yan sanda.

    'Yan sanda sun ce wanda ake zargi ya ƙara shaida musu cewa ya yi niyyar halaka matar tasa tare da ɗauke talbijin dinta don sayarwa ya ƙara jarin shagonsa.

    SP Ahmed Wakil ya ce za su gurfanar da magidancin da ake zargi a gaban kotu da zarar sun kammala bincike.

    Bauchi Police CP

    Asalin hoton, Bauchi state police command/Facebook

    Bayanan hoto, Tuni dai kwamishinan 'yan sandan Bauchi CP Auwal Musa Mohammed ya ba da umarnin a mayar da maganar zuwa sashen binciken manyan laifuka
    • Ana tuhumar mutum takwas da laifin tayar da gobarar da ta kashe 'yan ci-rani a Mexico
    • Matar da ta 'mutu' ta farfaɗo lokacin jana'izarta
  3. Kashin ƙarshe na sojin Faransa za su fice daga Nijar kafin ƙarshen Disamba

    Sojojin Faransa

    Asalin hoton, GETTY IMAGES

    Gwamnatin sojoji da ke mulki a Nijar ta ce sojojin Faransa 180 ne kaɗai suka rage a ƙasar zuwa 10 ga watan Disamba.

    Ta ce sojojin Faransan za su fice daga ƙasar kafin ƙarshen watan nan, kamar yadda gidan Talabijin ɗin ƙasar Tele Sahel ya ruaito.

    A wata sanarwa, sojojin sun ce nan da 22 ga watan Disamba, duk wani sojin Faransa da kayan aikinsu za su bar Nijar".

    Faransa ta soma janye sojojinta 1,400 daga Nijar a watan Oktoba bayan da sojojin da ke mulki suka umarce su da ficewa daga ƙasar wadda Faransa ta raina.

    A baya, Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya ce sojojin ƙasarsa za su fice daga Nijar "nan da ƙarshen shekara".

    Sojojin da suka koma Chadi an aike su zuwa Nijar a wani ɓangare na yaƙi da ƴan bindiga a sassan yankin Sahel.

    Sojojin da ke mulki a Nijar ɗin sun yi iƙirarin cewa aikin sojojin na Faransa ba shi da wani tasiri.

    • Me ya sa Faransa ke da sansanonin soji a Afrika?
    • Yaƙi ba mafita ba ne ga Nijar a rikicinta da su Ecowas - Masana
  4. Cutar Anthrax ta ɓarke a ƙasashen Afirka biyar

    ...

    Asalin hoton, Thinkstock

    Ƙasashe biyar a gabashi da kudancin Afirka na fama da ɓarkewar cutar anthrax, in ji hukumar lafiya ta duniya WHO a yankin Afirka.

    Sama da mutane 1100 ne ake zargin sun kamu da cutar kuma mutane 20 ne suka muta a Kenya da Malawi da Uganda da Zambia da kuma Zimbabwe - tun farkon wannan shekara.

    Ƙasar Zambia dai na fuskantar bullar cutar mafi girma tun shekara ta 2011, inda larduna 9 daga cikin 10 nata suka kamu da cutar.

    Yayin da cutar ke yaɗuwa a cikin dabbobi a Malawi, ƙasar ta ba da rahoton bullar cutar ta farko da aka taɓa samu a bana.

    Dakta Matshidiso Moeti, darektan hukumar ta WHO a Afirka ta ce tana tallafawa wajen ƙoƙarin yaƙi da ɓarkewar cutar a faɗin ƙasar.

    Ta kara da cewa "Don kawo karshen wadannan barkewar dole ne mu karya tsarin kamuwa da cuta ta hanyar fara rigakafin cutar a dabbobi," in ji ta.

    A cewar masana kiwon lafiya, ana iya haifar da ɓarkewar cutar ta hanyar abubuwa da yawa, da suka haɗa da girgizar yanayi da ƙarancin abinci da rashin fahimta da kamuwa da cutar ta hanyar kula da naman dabbobin da suka kamu da cutar.

    • Mece ce cutar Anthrax kuma ta yaya ake kamuwa da ita?
    • Shin takunkumin kariya zai hana yaduwar kwayoyin cuta?
  5. Sojojin Isra'ila fiye da 100 sun mutu tun soma kai farmaki ta ƙasa

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Sama da sojojin Isra'ila 100 ne suka mutu tun soma kai hare-hare ta ƙasa a Gaza.

    Uku cikin mutane huɗu da aka sanar da mutuwarsu, an kashe sune a Kudancin Gaza kamar yadda rundunar sojin Isra'ila ta bayyana.

    Rundunar sojin ta wallafa snayen sojoji 430 da aka kashe tun soma yaƙin ranar 7 ga watan Oktoba.

    Daga cikin adadin, an kashe sojoji 101 tun bayan da sojojin Isra'ilar suka afka Gaza ta ƙasa ranar 27 ga watan Oktoba, wanda kuma tun lokacin ake ta gwabza yaƙi, sai dai an samu lafawar yaƙin lokacin da aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta tsawon mako ɗaya da ta zo ƙarshe ranar 1 ga watan disamba.

    • Iyakar Lebanon: Dakarun Ireland da ke sa ido kan boyayyen rikicin Isra'ila
    • Wane ne Yahya Sinwar shugaban Hamas na Gaza?
  6. Ɗauke wutar lantarki a Kenya ya fusata al'ummar ƙasar

    Kenya

    Asalin hoton, AFP

    Al'ummar Kenya na neman ƙarin bayani bayan da ƙasar ta faɗa cikin duhu ranar Lahadi.

    Wannan ne karo na uku da aka samu ɗaukewar hasken wutar lantarki a faɗin ƙasar cikin wata huɗu da ya gabata.

    Rashin wutar ya janyo tsaiko a babbar tashar jirgin sama a Nairobi, babban birnin ƙasar.

    Galibin ƴan Kenya sun soki gwamnati tare da nuna fushi game da lamarin da ke ci gaba da faruwa.

    Sai dai zuwa safiyar yau Litinin, an samu dawowar hasken wutar lantarki a wasu yankunan Kenya sai dai wasu sassan Nairobi har yanzu ba su ga haske ba.

    Hukumar samar da wutar lantarkin a Kenya ta ce suna aiki kai da fata domin gyara wutar a yakunan da har yanzu ba su da wuta,"

    • Nijar ta shiga matsalar lantarki bayan katsewa daga Najeriya
    • Najeriya: Yadda rashin lantarki ke kassara harkokin kasuwanci a fadin ƙasar
  7. Yadda tituna suka zama kufai yayin da Falasɗinawa ke yajin aiki

    Ƙungiyoyin Falasɗinawa sun yi kira a shiga yajin aiki a duniya domin nuna goyon baya ga al'umar Gaza.

    Ga wasu hotuna daga Gaɓar Yamma da Kogin Jordan yayin da wasu mutane suka shiga yajin aikin.

    An empty street in Ramallah in the occupied West Bank

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Yadda ƙafa ta ɗauke a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan
    A man walks through an otherwise empty street in Nablus in the West Bank

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Wani mutum na tattaki a gefen titi a Nablus da ke Gaɓar Yamma da Kogin Jordan
    A closed shop front in Hebron

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Wani shago ke nan an kulle shi da kwaɗo a Hebron
  8. Ƴan majalisar dokokin Rivers 27 sun fice daga PDP

    Siminalayi Fubara da Nyesom Wike

    Asalin hoton, RIVERS STATE GOVERNMENT PRESS

    Ƴan majalisar dokokin jihar Rivers 27 cikin su 32 sun fice daga Jam'iyyar PDP mai mulki a jihar zuwa APC.

    Ƴan majalisar dokokin sun sanar da matsayarsu ne a wani taro da suka yi yau Litinin.

    An kuma ga wani bidiyo da yake yawo a shafukan sada zumunta inda yan majalisar ke ɗauke da tutar APC.

    Sun ce babban dalilin da ya sa suka sauya sheƙa shi ne rarrabuwar kan da aka samu a jam'iyyar PDP.

    Lamarin dai ya ƙara zafafa rikici tsakanin gwamnan jihar, Siminalayi Fubara da ƴan majalisar dokokin da ke yi wa tsohon gwamna Nyeson Wike mubaya'a.

    • 'Umurnin da PDP ta bayar zai iya sake tsunduma jam'iyyar cikin rikici'
    • Ƙuri'un da ba za a iya bayaninsu ba a zaɓen Najeriya mai cike da taƙaddama
  9. Shugaba Tinubu na kan hanyar zuwa Maiduguri

    Shugaba Bola Tinubu

    Asalin hoton, PBATMediaCentre/X

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu yana kan hanyar zuwa jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin ƙasar domin halartar taron shekara-shekara na rundunar sojin ƙasar.

    Wannan ce ziyara ta farko da ya kai yankin tun hawansa karagar mulki.

    Cikin sanarwar da daraktan yaɗa labarai na rundunar sojin Najeriya, Brigediya Janar Onyema Nwachukwu ya fitar, Shugaba Tinubu ne babban baƙo na musamman a taron.

    A cewar sanarwar, bikin buɗe taron zai ƙunshi jawabi ga sojojin da ke aiki ƙarƙashin rundunar Haɗin Kai inda kuma zai yi rangadi kan asibitin sojoji a Maiduguri da kuma iza tubalin ginin hedikwatar shiyya ta bakwai.

    • Dambarwar kasafin kuɗin Najeriya da mayar da Emefiele gidan yari
    • Me Tinubu zai yi da bashin kusan dala biliyan takwas da zai karbo?
  10. Hamas ta yi barazanar ƙin sakin mutanen da ta yi garkuwa da su

    Ƙungiyar Hamas ta yi gargaɗin cewa babu wani da take garkuwa da shi da zai bar Gaza da ransa har sai an biya buƙatunmu.

    Kakakin Hamas, Abu Obeida ne ya bayyana haka cikin wani saƙon murya da aka wallafa ranar Lahadi ta shafin Telegramt.

    Ana i gaba da matsa wa Hamas lamba game da fiye da mutum 38 da har yanzu suke hannunta da wasu ƙungiyoyin masu riƙe da makamai.

    Isra'ila ta sha yin alƙawarin yin duk bai yiwuwa na kuɓutar da sauran mutanen da ke hannun Hamas.

    Mutum 110 aka saki a jumulla sai dai yarjejeniyar dakatar da yaƙi ta mako ɗaya wadda a ƙarƙashinta aka saki gommai ta zo ƙarshe kuma tun lokacin Isra'ila ta ci gaba da luguden wuta a Gaza.

    • An fara cire rai kan yiwuwar sake tsagaita wuta a Gaza
    • Halin da yaran Gaza ke ciki: An raunata su kuma an kashe iyayensu
  11. Martanin ƴan Nijar game da matakin ECOWAS kan ƙasar

    Bayanan sautiDanna alamar lasifikar domin sauraron rahoton

    Al'ummar jamhuriyar Nijar sun soma martani kan matakin Ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma, Ecowas na jaddada takunkuman da ta sanya wa ƙasar sakamakon juyin mulkin sojoji.

    Yayin da wasu ke ganin yanzu kallo ya koma kan sojojin da ke rike da mulki don ganin ko za su cika sharuɗan da aka gindaya musu, wasu kuwa na ganin cewa amincewar Ecowas na gindaya sharuɗan ga shugabannin sojin wani ci gaba ne a kokarin warware rikicin.

    Ga ƙarin bayani cikin rahoton Tchima Illa Issoufou.

    • Abin da ya hana sulhu tsakanin Ecowas da Nijar - Tuggar
    • Me taron ECOWAS zai mayar da hankali a kai a Abuja?
  12. Kotun ƙolin Indiya za ta yanke hukunci kan kawo ƙarshen cin gashin kan yankin Kashmir

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Kotun ƙolin Indiya za ta yanke hukunci kan ƙarar da ke ƙalubalantar matakin gwamnatin ƙasar na shekaru huɗu da suka gabata kan kawo ƙarshen cin gashin kan yankin Kashmir.

    An tsaurara matakan tsaro a yankin gabanin sauraron koken.

    Kashmir shi ne kaɗai yankin da ya kasance musulmi sun fi rinjaye a Indiya, kuma kafin shekaru huɗu da suka wuce yankin na da damar samar da kundin tsarin mulki da yin dokokisa.

    An dai haramtawa Indiyawa daga wajen Kashmir sayen duk wasu abubuwa a yankin.

    A shekarar 2019, gwamnatin jam'iyyar BJP a Indiya ta ƙwace wannan damar tana mai cewa dole ne a haɗe yankin na Kashmir da Indiya.

    Yunƙurin da 'yan siyasa a Kashmir din suka ce ya saba ƙa'ida.

    • Uttar Pradesh: Musulman Indiya na fargabar hare-haren kiyayya
    • Me ke faruwa a Kashmir kuma me ya sa aka damu da yankin?
  13. Netanyahu ya buƙaci mayaƙan Hamas su miƙa wuya

    Benjamin Netanyahu

    Firaministan Isra’ila ya ce gomman mayaƙan Hamas sun ajiye makamansu tare da miƙa wuya.

    Cikin wata sanarwa da aka fitar a jiya Lahadi, Benjamin Netanyahu ya ce “ana ci gaba da yaƙin gadan-gadan” sannan samun galaba a kansu zai ɗauki ɗan lokaci amma ya bayyana cewa “ƙarshen Hamas ya zo”.

    A cewarsa, ina faɗa wa mayaƙan Hamas: ta faru ta ƙare. Kar ku sadaukar da ranku ga [Jagoran Hamas Yahya] Sinwar. Ku miƙa wuya – yanzu,” in ji shi.

    • Yadda Hamas ta haɗa dakarun da suka kai wa Isra'ila harin 7 ga Oktoba
    • Wane irin ciwon ciki ne yake turnuƙe sojojin Isra'ila da suka je yaƙi Gaza?
  14. Barkanmu da safiya!

    Masu bibiyarmu a wannan shafi na kai tsaye, barkanmu da safiyar ranar Litinin.

    Daga yanzu har zuwa lokacin da muka saba rufe wannan fage, za mu yi ta kawo muku rahotannin abubuwan da ke wakana a Najeriya da Nijar da sauran sassan duniya.

    Nabeela Mukhtar Uba tare da abokiyar aiki Aisha Babangida ne za su kasance tare da ku kafin mu miƙa ragama ga sauran abokan aikinmu