Za a shiga mummunan bala'i a Gaza idan ba ku ɗauki mataki ba - Guterres

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, A'isha Babangida and Umar Mikail

  1. Nijar na ci gaba da fama da matsalar tashin farashin kayan masarufi

    Al'ummar jamhuriyar Nijar na ci gaba da fama da matsalar tashin farashin kayayyakin masarufi, musammam ma na abinci.

    Nijar dai na fama da karancin abinci, tun bayan matakin da ƙungiyar ECOWAS ta dauka na rufe iyakokin ƙasar sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi.

    Baya ga tashin farashin abinci da kuma ƙarancin sa a kasuwanni, kuɗin ƙasar kansu na wahalar samu duk saboda takunkuman da ƙungiyar ECOWAS ta kakaba wa ƙasar wanda ta dalilin hakan magidanta ke kokawa suna neman taimako.

    Daga Yamai, ga rahoton da Tchima Illa Issoufou ta haɗa.

    Bayanan sautiLatsa hoton lasifika domin sauraron rahoton
  2. Wasu sassa na garin Tudun Biri inda jirgin sojoji ya yi ɓarin wuta ranar Lahadi

    Ga hotunan wasu sassa na garin Tudun Biri inda jirgin saman sojin Najeriya ya yi luguden wuta kan fararen hula a ranar Lahadi, 3 ga watan Disamban 2023 bisa kuskure.

    Gomman mutane ne ake fargabar sun rasa rayukansu bayan harin bam din kan gungun masu Mauludi.

    Majalisar Dattawan Najeriya dai ta lashi takobin gudanar da bincike kan harin da ya janyo mutuwar mutane da dama a jihar Kaduna.

    ...
    ...
    ...
    ...
    ...
    ...
    ...
    Bayanan hoto, Nan mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna ce, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe lokacin da ta kai ziyara garin Tundin Biri domin miƙa ta'aziyya kan iftila'in harin jirgin soji da ya rutsa da fararen hula, tare da ita akwai manyan jami'an gwamnati.
    • 'Dole a hukunta wadanda suka kai hari ta sama a jihar Kaduna'
    • Hare-haren jiragen yaƙin Najeriya bisa kuskure takwas a kan fararen hula
  3. WHO ta nemi ƙasashe su ƙara haraji kan barasa da lemukan zaƙi

    Lemuka da barasa

    Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta saki wata sabuwar kididdiga da ke nuna ƙarancin harajin da ake sakawa a duniya kan barasa da lemukan zaki.

    Bincike ya nuna akasarin ƙasashe ba sa amfani da haraji domin inganta lafiyar al'umma.

    WHO ta kuma saki wani littai ƙunshe da bayanai kan harajin barasa.

    A duniya, fiye da mutum miliyan biyu da rabi ne ke mutuwa sakamakon shan giya kowace shekara kuma sama da mutum miiyan takwas sakamakon rashin cin abinci mai inganta lafiya, saka haraji kan barasa da lemukan zaƙi zai rage yawan mace-macen da ake samu ta wannan ɓangare.

    Rabin ƙasashen da ke saka haraji kan lemukan zaƙi suna sa haraji kan ruwa wanda WHO ba ta ba da shawarar haka ba.

    Wani bincike da aka yi a 2017 ya nuna harajin da ke ƙara farashin barasa da kashi 50 cikin 100 zai rage mace-macen mutum miliyan 21 tare da samar da kuɗin shiga na dala triliyan 17.

    Wannan ya yi dai-dai da jumullar kuɗaɗen shiga na ƙasashe takwas mafiya ƙarfin tattalin arziki a shekara ɗaya.

    Hukumar lafiya ta duniya ta ba da shawarar a saka haraji kan dukkanin lemukan zaƙi da kuma barasa.

    • Dubai ta soke harajin barasa domin jan hankalin baki
    • Mene ne ciwon suga da alamominsa?
  4. Isra'ila ta soke bizar babbar jami'ar Majalisar Dinkin Duniya

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, ...

    Ministan harkokin wajen Isra'ila Eli Cohen ya ce za a soke takardar izinin zama na Lynn Hastings - jami'ar kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a yankin Falasɗinawa - saboda abin da Cohen ya ce na ƙin yin magana kan Hamas.

    Da yake zargin Majalisar Dinkin Duniya da "son kai", Cohen ya rubuta a cikin wani sakon da ya wallafa a kan shafin sada zumunta na X, in da yace,

    "Wacce ba ta la'anci Hamas ba kan mummunan kisan kiyashin da ta yi wa Isra'ilawa 1,200 da sace jarirai da tsofaffi da kuma mummunan ayyukan cin zarafi da zalunci kuma fyade, da yin amfani da mazauna Gaza a matsayin garkuwar ɗan adam, amma kuma ta la'anci Isra'ila, ƙasa mai mulkin demokraɗiyya da ke kare 'yan ƙasa, ba za ta iya aiki a Majalisar Dinkin Duniya ba kuma ba za ta iya shiga Isra'ila ba!"

    Isra'ila ta ci gaba da sukar Majalisar Dinkin Duniya kan martanin da ta mayar kan harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba.

    Hastings ta kasance mai sukar hare-haren da Isra'ila ke kai wa a Gaza kuma ta jagoranci kiraye-kirayen kara kai agajin jin kai a Gaza.

    A ranar Litinin, wata sanarwa da Hastings ta fitar ta ce: "Sharuɗɗan da ake buƙata don isar da kayan agaji ga al'ummar Gaza ba su wanzu ba, idan har zai yiwu, wani yanayi mai bala'i da munnin gaske na gab da afkuwa, wanda ayyukan jin kai ba za su iya mayar da martani ba."

    Ta ce rashin tsaftataccen ruwan sha da tsaftar muhalli da rashin abinci mai gina jiki ga mutane “ka’idan za su haifar da annoba da kuma bala’in lafiyar jama’a”.

    • Wanne irin taimako mutanen Gaza ke buƙata?
    • Halin da aka shiga a Gaza ranar da aka katse hanyoyin sadarwa
  5. Akwai buƙatar haɗin kai a arewa don kawo ƙarshen matsalar rashin tsaron

    Wasu dattawan arewacin Najeriya na nuna damuwa game da matsalar da suka bayyana a matsayin rashin haɗin kai da jagoranci a tsakanin magabatan yankin, wadda suka ce na cikin dalilan da suka sa ba a shawo kan matslar tsaro da ke addabar yankin ba.

    Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa daya daga cikin dattawan arewa na tofa albarkacin bakinsa ne game da iftila`in bom din da ya fada kan wata al`umma a jihar Kaduna, wanda ya yi sanadin asarar rayukan jama`a masu yawa.

    A tattaunawarsa da BBC, tsohon gwamnan ya ce matukar dattawan arewa ba su haɗa kai don magance matsalar tsaro a yankin baki ɗaya ba, to da wuya a daina ganin masifu na auka wa al`umma.

    Bayanan sautiLatsa hoton lasifika domin sauraron tattaunawar
  6. 'Yan Afirka ta Kudu da aka kwashe daga Gaza sun koma gida

    ...

    Asalin hoton, Clayson Monyela/X

    Wasu 'yan Afirka ta Kudu 19 da suka makale a Gaza tun bayan barkewar yakin Hamas da Isra'ila a watan Oktoba sun koma gida lafiya.

    Sun isa filin tashi da saukar jiragen sama na OR Tambo na birnin Johannesburg da yammacin ranar Talata, a cikin wani jirgin da ya taso daga birnin Alkahira na ƙasar Masar.

    Da farko dai an kwashe su zuwa birnin Alkahira ta mashigar Rafah, bayan samun amincewar hukumomin Isra'ila.

    Zane Dangor, babban darektan ma'aikatar harkokin wajen Afirka ta Kudu, ya ce hukumar za ta yi kokarin kwashe 'yan kasar da har yanzu ke Gaza cikin koshin lafiya, amma bai bayyana adadin wadanda suka makale a can ba.

    • Hamas: Su wane ne shugabanninta da suka fi fice?
    • Mutanen da ƙungiyar Hamas ke garkuwa da su tsawon shekaru
  7. Biden da Trump sun yi wa juna shaguɓe

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Joe Biden na Amurka ya ce ƙoƙarin da Donald Trump ke yi na yunkurin komawa Fadar White House na daga cikin abin da ya karfafa sake tsayawarsa neman wa'adin mulki karo na biyu.

    Da ya ke jawabi a gangamin tara kudin kamfe, Biden ya ce bai kamata su bar Donald Trump ya yi nasara ba.

    Wanna ne karon farko da joe Biden ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takarar shugaban Ƙasa a karo na biyu.

    Don haka kai tsaye kan burin tsohon shugaban, ya ce idan Trump ba zai sake tsayawa takarar ba shi ma baya tunanin zai tsaya.

    An tambayi Biden ko zai ci gaba da tsayawa takarar idan Trump ya janye, sai shugaban Amurkar mai shekaru 81 ya ce ba zai tsaya takara ba.

    • Zaɓen 2020: Biden da Trump na zaryar ƙarshe kafin zaɓen Talata
    • Ko ya za ta kaya tsakanin Trump da Biden?
  8. Halin da mutane ke ciki yayin da yaƙin Gaza ya shiga mataki mafi sarƙaƙiya, Rushdi Abu Alouf daga Istanbul

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Yayin da yaƙi tsakanin Isra'ila da Gaza ya shiga wata na uku, tankokin yaƙin Isra'ila na ci gaba da nausawa Khan Younis, mahaifar babban kwamandan ƙungiyar Hamas, Mohammed Dief da jagoran ƙungiyar Yahya Sinwar wanda Isra'ila ke ganin shi ya kitsa harin ranar 7 ga watan Oktoba.

    Yaƙi a arewacin Gaza ya mayar da hankali kan Jabalia da Zaytoun da Shejaiya da Al-Daraj da Al-Tuffah da ke maƙwabtaka da Gaza.

    Yaƙin dai ya shiga wani muhimmin mataki mai sarƙaƙiya yayin da tankoki ke tunkarar manyan cibiyoyin Hamas (Khan Yunis da Jabalia da Shuja'iya).

    Mutane da dama na ganin Hamas ta fi ƙarfin soji a wuraren kuma za ta fi iya tunkarar sojojin Isra'ila a inda ta fi ƙarfi.

    Dubban farar hula na ci gaba da zama a waɗan nan wuraren kuma akwai yiwuwar a samu mutuwar ƙarin farar hula.

    Neven Hassan, wata uwa mai ƴaƴa biyar, sun faɗa mani cewa: "Muna cin abinci sau ɗaya a rana - akasari ɗan ƙarain biredi da waken gwangwani.

    "Na kasa samo wa jariri na ɗan wata shida madara, duka ƴaƴana da ɗana ba su da lafiya, suna shan ruwa mara tsabta kuma mun kasa samun bargo don rage sanyi."

    Ta ce sanyin da ake ya ƙara jefa su cikin wani yanayi yayin da galibin al'umma ke zaune cikin tantuna kuma ba su da isassun kayan sanyi.

    • Takaddamar Isra'ila da shugaban MDD saboda kalamansa kan harin Hamas
    • WHO ta ce ayyuka sun tsaya cak a babban asibitin Gaza
  9. Matsalar ƙarancin abinci na ƙara ta'azzara a Gaza – MDD

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Hukumar samar da abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce dawowar yaƙi a Gaza ya ƙara ta'azzara matsalar ƙarancin abinci a yankin inda ta nemi a tsagaita buɗe wuta.

    Hukumar ta ce lokacin da aka dakatar da yaƙin na mako ɗaya, ta samu kai wa ga mutum 250,000 kafin ƙarshen yarjejeniyar ranar Juma'a.

    Sai dai ta ce a yanzu rarraba kayan agaji yana neman gagara sannan ci gaba da yaƙin na jefa rayukan masu aikin ceto cikin garari.

    WFP ta jaddada cewa ma'aikatan agaji na buƙatar samun hanyar isa ga mabuƙata a Gaza.

    "WFP ta yi kira a dakatar a yaƙin tare da neman shugabanni su yi aii cikin gaggawa domin samar da maslaha da za ta kawo ƙarshen halin tasku da mutane ke fuskanta sanadiyyar yaƙin," kamar yadda ta bayyana a wata sanarwa.

    • Isra'ila-Gaza: Me ya sa wannan yaƙi ya zama daban da sauran
    • ‘Lokacin da za mu mutu babu wanda zai sani': Labarai daga Gaza
  10. Netanyahu ya ƙalubalanci masu sukar yadda Isra'ila ke amfani da ƙarfi a Gaza

    ...

    Asalin hoton, EPA

    Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya maida martani kan wadanda ya ce su na ƙoƙarin matsawa sojin kasarsa lamba kan matakan da suke dauka a Gaza.

    Ya ce hanyar da ya dace ita ce amfani da karfi wajen murkushe Hamas.

    Wannan na zuwa ne bayan Jami'an gwamnatin Amurka suka fara bayyana rashin gamsuwa kan matakan da Isra'ila ke ɗauka a yaƙin ta da Hamas.

    Tun da fari Sojojin Isra'ila sun fara shirin ƙaddamar da yaƙi ta kasa a Khan Younis.

    Sojojin Isra'ila sun sanar da isa tsakiyar Khan Younus, wannan ne wurin da Sojin Isra'ila sukai amanna mambobin Hamas ke fakewa.

    Rahotanni sun ambato Netanyahu ya shaidawa 'yan uwan wadanda suke hannun Hamas cewa abu ne mai matukar wuya a kubutar da su ahalin da ake ci.

    • Rikicin Isra'ila da Gaza: Mene ne asalin sa?
    • Rayuwa a Gaza: 'Babu wurin fakewa a ruwan makamai masu linzami'
  11. Mali da Nijar za su kawo ƙarshen yarjejeniyar haraji da Faransa

    Gwamnonin sojan Mali da Nijar sun bayyana shirin kawo ƙarshen yarjejeniyar harajin da suka shafe shekaru da dama suna yi da Faransa cikin watanni uku masu zuwa.

    A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da mahukuntan ƙasashen biyu suka fitar sun bayyana cewa, sun kawo karshen yarjejeniyar harajin ne saboda yadda Faransa ke ci gaba da nuna kyama ga kasashensu da kuma rashin daidaiton wadannan yarjejeniyoyin da ke haifar da asarar kuɗaɗen shiga ga kasar Mali da Nijar”, kamar ​​kamfanin dillancin labaran AFP ya ruwaito.

    Yarjejeniyar haraji ta Mali da Faransa ta kasance tun shekarar 1972, yayin da Nijar ta ƙulla yarjejeniya da kasar Turai tun shekara ta 1965.

    An ƙirƙiri dukkan yarjejeniyoyin biyu don hana haraji ninki biyu da sauƙaƙe haɗin gwiwa a cikin lamuran kuɗi.

    Matakin dai ya biyo bayan irin wannan mataki da gwamnatin mulkin sojan Burkina Faso ta dauka a farkon wannan shekarar.

    Wannan dai shi ne mataki na baya-bayan nan a jerin matakan da gwamnatocin sojan kasashen uku suka dauka na yanke hulda da Faransa, wadda ke da karfin ikonsu, tun bayan da suka karbi mulki a juyin mulkin baya-bayan nan.

    • Me sojojin mulkin Nijar ke nema daga ƙawayensu?
    • Shin wane tasiri janyewar dakarun Faransa za ta yi ga Nijar?
  12. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar mu a wannan shafi na kai tsaye, BBC hausa, barkan mu da safiyar Laraba

    Nabila Mukhtar Uba da Aisha Babangida ne za su kasance da ku domin kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Kuma za ku iya tafka muhawara a shafukan sada zumuntarmu domin samun ƙarin labarai.

    Sai ku biyo mu.