Za a shiga mummunan bala'i a Gaza idan ba ku ɗauki mataki ba - Guterres

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, A'isha Babangida and Umar Mikail

  1. Asuba ta gari

    Nan za mu rufe wannan shafi na labarai kai-tsaye, wanda ya kawo rahotonni daga sassan duniya.

    Mu haɗu da ku gobe da safe don samun wasu sababbin rahotonnin.

    Umar Mikail ne ke cewa mu zama lafiya.

  2. Sakataren MDD ya yi gargaɗin faɗawa bala'i a Gaza cikin wasiƙarsa ga Kwamatin Tsaro

    Har yanzu dai game da wasiƙar da Babban Sakataren MDD António Guterres ya rubuta, inda ya nemi a gaggauta tsagaita wuta a yaƙin da Isra'ila ke yi da Hamas a Zirin Gaza.

    Ya yi amfani da ayar doka ta 99 ta MDD, wadda ta ba shi damar jawo hankalin Kwamatin Tsaro kan "duk wani batu da yake ganin zai iya barazana ga zaman lafiyar duniya da tsaro".

    "Yayin da ake fuskantar shiga bala'in rasa agaji a Gaza, ina neman Kwamatin ya taimaka wajen kauce wa aukuwar bala'i, kuma ya nemi a tsagaita wuta don kai agaji," in ji shi ciki wani saƙo da ya walafa a dandalin X.

    Ya ce wannan ne karon farko da ya yi hakan tun da ya zama sakatare janar a 2017.

    Cikin wasiƙar da ya rubuta wa shugaban Kwamatin Tsaron, Guterres ya nanata cewa yanayin na ƙara ƙazancewa cikin sauri, ta yadda ba za a iya gyara wa Falasɗinawa komai ba daga baya da kuma tsaron yankin.

  3. Harin Kaduna: Dole ne Najeriya ta sake duba dokokin kai hari - MDD

    Najeriya

    Asalin hoton, NAF

    Bayan harin da ya kashe mutum 85 tare da raunata wasu da dama a garin Tudun Biri na jihar Kaduna, Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta nemi rundunar sojin Najeriya ta sake duba dokokinta na yaƙi da matsalar tsaro.

    Wani jirgi maras matuƙi na runduar sojin ƙasa ta Najeriya ne ya jefa wa mutanen bam suna tsaka da bukukuwan Mauliidi a yankin ƙaramar hukumar Igabi ranar Lahadi.

    Shugaban sashen yaɗa labarai na ofishin kare haƙƙin ɗan'adam na MDD, Seif Magango, ya yi tir da harin yana mai cewa shi ne na baya-bayan nan daga cikin aƙalla huɗu da suka kashe fararen hula tun 2017.

    "Duk da cewa gwamnati ta ce kuskure ne, muna kira gare su da su yi duk mai yiwuwa wajen kare rayukan fararen hula da dukiyoyinsu a nan gaba," a cewar Magango cikin wata sanarwa.

    "Dole ne su sake duba dokokin kai hari da kuma tsarin aiki don tabbatar da cewa ba a sake maimaita irin wannan ba."

    • Hare-haren jiragen yaƙin Najeriya bisa kuskure takwas a kan fararen hula
  4. Sakataren MDD Guterres ya nemi kwamitin sulhu ya dakatar da yaƙi a Gaza

    Guterres

    Asalin hoton, Reuters

    Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya (MDD), Antonio Guterres, ya rubuta wasiƙa ga kwamitin tsaro na majalisar, inda ya nemi ƴan kwamitin su taimaka don kauce wa mummunar annoba a Gaza.

    Ya ƙara jaddada buƙatar tsagaita wuta saboda yadda lamarin ke ƙara ƙazancewa a Gazar, da kuma neman wanzar da zaman lafiya a yankin.

    Wakilin BBC ya ce "wannan ne karon farko da Antonio Guterres ke ɗaukar irin wannan mataki tun bayan zamansa sakatare janar na MDD a 2017.

    Mista Guterres ya ce alhakin ƙasashen duniya ne su shiga tsakani don kawo ƙarshen yaƙin.

  5. Manyan mutanen da suka yi magana kan jefa wa fararen hula bam a Kaduna

  6. Amurka ta tuhumi sojojin Rasha huɗu da laifukan yaƙi

    Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka ta tuhumi sojojin Rasha huɗu da aikata laifukan yaƙi kan zargin "sacewa da kuma azabtar da ɗan ƙasarta mazaunin Ukraine," a cewar hukumomi.

    Masu shigar da ƙara a Amurka sun ce mutumin na zaune ne a Ukraine tun 2021 kuma bai shiga yaƙin ƙasar da Rasha ba.

    An riƙe shi tsawon kwana 10 a watan Afrilun 2022, kuma an yi zargin cewa an yi ta dukansa da gwada yadda za a kashe shi.

    Wannan ne karon farko da Amurka ta tuhumi wani a ƙarƙashin dokar yaƙi.

    Da yake ba da sanarwar tuhumar a ranar Laraba, Antoni Janar Merrick Garland ya ce wannan "muhimmin mataki ne na hukunta yaƙin da ya saɓa wa doka a Ukraine".

  7. Al Jazeera ta ce Isra'ila ta kashe dangin wakilinta 22 a Gaza

    Kafar talabijin ta Al Jazeera ta ce hare-haren Isra'ila sun kashe 'yan uwan wakilinta 22 a Zirin Gaza.

    Cikin wata sanarwa, gidan talabijin ɗin na Qatar ya bayyana "ta'aziyyarsa da jimami" ga Momin Alshrafi, da iyalansa da kuma abokan aikinsa.

    Ya ce an kashe dangin Alshrafi ne a yau Laraba a sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia da ke arewacin Gaza, ciki har da mahaifiyarsa, da mahaifinsa, da kuma 'yan uwansa uku.

    "Haka nan, an kashe yara da yawa a dangin Alshrafi yayin harin," in ji rahoton da Al Jazeera ta wallafa.

    Kafar talabijin ɗin ta ce "ya kamata a hukunta Isra'ila saboda cin zalin da take aikatawa kan 'yan jarida da kuma fararen hular Falasɗinawa a Gaza".

  8. Ana matsa wa Isra'ila lamba don ta kare fararen hula a Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Isra'ila na ci gaba da shan matsin lamba don ta kare rayukan fararen hular Falasɗinawa yayin da take farautar mayaƙan Hamas a Zirin Gaza.

    Babbar ƙawarta, Amurka, ta ce lallai ta kiyaye kada ta maimaita ɓarna a kudancin zirin irin wadda ta yi a arewaci, inda ta rusa unguwanni, ta kashe dubban mutane, sannan wasu dubban suka shiga gudun hijira.

    Rundunar sojin Israilar kan ce tana saita hare-harenta kuma ta ɗauki matakin sanar da mazauna yankunan. Amma kuma hare-haren sun ƙara ta'azzara halin da Falasɗinawan ke ciki a Gaza.

    Asibitoci sun cika maƙil da marasa lafiya, da yawansu yara ne, kuma likitoci na aiki ne da ɗan abin da suke da shi.

    Yayin da ake ƙara tilasta wa mutane guduwa daga muhallansu, ana ƙara tura su ƙananan wurare da ke arewaci.

  9. Jirgin dakon kaya na 200 maƙare da makamai ya sauka a Isra'ila

    ...

    Asalin hoton, Israel Ministry of Defence

    Rundunar tsaro ta Isra'ila ta ce ta karɓi jirgin dakon kaya na 200 maƙare da makaman yaƙi na soji.

    Wata sanarwa da rundunar ta fitar na cewa sama da tan 10,000 na kayan yaƙi ne Isra'ila ta karɓa tun bayan ɓarkewar faɗa tsakaninta da Hamas.

    Cikin kayan akwai motoci masu sulke da makamai da kayan bincike da na kiwon lafiya da kuma alburusai.

    Amurka ce babbar ƙasar da ke samar wa Isra'ila da makamai, inda take kashe dalar Amurka biliyan uku a kowace shekara domin tallafin harkar tsaro ga Isra'ila.

  10. Shugaba Putin ya isa Saudiyya domin tattaunawa da Bn Salman

    Shugaban Rasha, Vladmir Putin ya isa Saudiyya inda zai tattauna da yarima Mohammed Bin Salman, bayan wata ƴar taƙaitacciyar ziyara da ya kai a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

    Ziyarar tasa na zuwa ne gabanin haduwar da zai yi da shugaban ƙasar Iran, Ibrahim Ra'isi a Moscow ranar Alhamis.

    Wannan dai wani yunƙuri ne na shugaba Putin domin nuna cewa Rasha ba ta zama saniyar ware ba a tsakanin ƙasashen duniya.

    Tun bayan da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta bayar da sammacin kama shi, Putin ya kai ziyara ne kawai a ƙasashen da ba su amince da dokokin kotun ba.

  11. Abu biyar game da Liliana Mohammed, Baturiyar da ta sauke Ƙur'ani a Kano

  12. Shugaba Putin na Rasha na kan hanya zuwa Saudiyya

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Rasha, Vladimir Putin na kan hanyarsa zuwa Saudiyya daga Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa bayan ganawa da firaministan ƙasar, Zayed Al Nahyan.

    Ana sa ran shugaban na Rasha zai gana da yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman.

    Jirgin da ke ɗauke da Putin ya shiga sararin samaniyar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa tare da rakiyar wasu jiragen yaƙin ƙasar ta Rasha.

    Mr Putin ya bayyana Sheikh Zayed a matsayin 'amini' inda ya bayyana cewa dangantakar da ke tsakanin Rasha da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta yi matuƙar ƙarfi.

    Hakan na zuwa ne yayin da ake gudanar da taro kan sauyin yanayi a birnin Dubai.

  13. Abinda ya kamata ku sani kan wasan Man United da Chelsea

  14. Najeriya da Kuwait sun ƙulla yarjejeniyar fara zirga-zirgar jiragen sama

    ...

    Asalin hoton, Festus Keyamo/X

    Gwamnatin Najeriya ta cimma yarjejeniya da ƙasar Kuwait don fara zirga-zirgar jiragen sama kai tsaye tsakanin ƙasashen biyu.

    Ministan sufurin jiragen sama da raya sararin samaniya, Festus Keyamo ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

    Mista Keyamo ya ce ya rattaɓa hannu a madadin gwamnatin Najeriya don cimma yarjejeniyar jigilar jiragen sama tsakanin ƙasashe biyu, don bayar da dama ga kamfanonin jiragen sama da aka keɓe don gudanar da zirga-zirgar jiragen sama na kasuwanci, wanda ya shafi jigilar fasinjoji da kaya.

    A cewar Keyamo, an rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a taron tattaunawa kan harkokin sufurin jiragen sama na ƙasashen duniya (ICAN) da hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta ƙasashen duniya (ICAO) ta shirya a birnin Riyadh na ƙasar Saudiyya.

    “Wannan zai bunƙasa harkokin kasuwanci da yawon bude ido da tattalin arziki tsakanin kasashen biyu. Ni da tawagata za mu ci gaba da tattaunawa kan hanyoyi daban-daban tare da ƙasashe daban-daban da ke nan don halartar wannan taron na ICAO na shekara-shekara har zuwa karshen mako, '' in ji Keyamo

    ...

    Asalin hoton, Festus Keyamo/X

    Bayanan hoto, Festus Keyamo da wakilin Kuwait a lokacin ƙulla yarjejeniyar
    ...

    Asalin hoton, Festus Keyamo/X

    Bayanan hoto, An cimma yarjejeniyar ne lokacin babban taron tattaunawa kan harkokin sufurin jiragen sama na ƙasashen duniya (ICAN)
    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  15. Pope golan Newcastle zai yi jinyar wata hutu

  16. Sojojin Isra'ila sun kai farmakin ramuwar gayya kan ƙasar Labanon

    Sojojin Isra'ila na kai hare-hare kan wurare a Lebanon, da suka hada da tankunan yaki da manyan bindigogi, yayin da jiragenta kuma suka kai farmaki kan wani abin da ta bayyana a matsayin cibiyar ba da umarnin soji da kayayyakin aikin soji na Hezbollah.

    Dakarun sojojin Isra'ila sun ce suna mayar da martani ne kan hare-haren da ƙasar Lebanon ta kai mata a arewacin Isra'ila.

    Tun lokacin da aka fara yaƙin, Hezbollah - ƙungiyar da Iran ke marawa baya wacce ke da karfin soji da siyasa a Lebanon - ta sha kai hare-hare kan wuraren Isra'ila daga kan iyaka.

  17. Hotunan yadda firaministan Nijar ya gana da shugaban ƙasar Chadi

    Fraministan jumhuriyar Nijar Ali Mahamane Lamine Zeine ya gana da shugaban kasar Chadi janar Mahamat Idriss Deby Itno ,yau a Jamena.

    Ga wasu hotuna da ke nuna yadda suka gana.

    ...

    Asalin hoton, Media Niger

    ...

    Asalin hoton, Media Niger

    ...

    Asalin hoton, Media Niger

    ...

    Asalin hoton, Media Niger

  18. Ƙasar Saliyo ta kama wani mai gadin tsohon shugaban ƙasar kan juyin mulkin da bai yi nasara ba

    ...

    Asalin hoton, EPA

    Hukumomi a Saliyo sun kama wani mai tsaron tsohon shugaban kasar Ernest Bai Koroma, bisa alaka da juyin mulkin da bai yi nasara ba a watan Nuwamba.

    Ministan yaɗa labarai na Saliyo Chernor Bah ya bayyana a ranar Talata cewa, an kama Amadu Koita, tsohon soja ne tare da wasu jami’an ‘yan sanda biyu da ke dauke da shi.

    Ya ƙara da cewa Koita "yana kan gaba a jerin wadanda ake nema ruwa a jallo".

    A ranar 26 ga Nuwamba, 'yan bindiga sun kutsa cikin rumbun ajiye makamai da gidajen yari da dama a babban birnin Freetown, inda suka sako fursunoni kusan 2,000.

    Aƙalla mutane 19 da suka haɗa da sojoji 13 ne suka mutu a rikicin a cewar rundunar.

    Kamen da aka yi wa Koita da abokansa ya kawo adadin wadanda aka kama bisa yunkurin juyin mulkin zuwa 60.

    A ranar Litinin din da ta gabata ne gwamnatin kasar ta sanar da kama mutane 57 da suka hada da sojoji 37 da farar hula 10 da wasu sojoji hudu da aka kora da jami’an ‘yan sanda biyar da kuma wani dan sanda mai ritaya.

  19. A cikin hotuna: Ana ci gaba da gwabza fada a kudancin zirin Gaza

    Sojojin Isra'ila na ci gaba da tunkarar tsakiyar Khan Younis, birni mafi girma a kudancin Gaza, yayin da sojojin suka yi imanin cewa wasu daga cikin shugabannin Hamas na boye a can.

    Ga wasu sabbin hotuna daga Zirin Gaza a yau.

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Wannan motar sojojin Isra'ila ne a kusa da kan iyaka da Zirin Gaza a safiyar yau
    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Khan Younis da ke kudancin Gaza ya fuskanci mummunan tashin bama-bamai daga hare-haren da Isra'ila ta kai a 'yan kwanakin nan
    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, An ga hayaki mai yawa na tashi a Gaza da safiyar yau
    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutum 600,000 ne ke karkashin umarnin kwashe mutane a kudancin Gaza, kusan rabin waɗanda tuni aka tilasta musu barin gidajensu.
  20. Sojojin Isra'ila sun ce sun gano ɗaya daga cikin rumbun makaman Hamas mafi girma

    ...

    Asalin hoton, @AvichayAdraee/X

    Dakarun sojin Isra'ila sun ce sun gano ɗaya daga cikin rumbun makaman Hamas mafi girma a arewacin Zirin Gaza wanda ya kunshi daruruwan rokoki da gurneti da jirage marasa matuka da kuma abubuwan fashewa.

    Kakakin IDF na kafofin yaɗa labaran Larabci, Avichay Adraee, ya ce an gano makaman ne a kusa da wani asibiti da wata makaranta.

    Dakarun sun yi iƙirarin cewa sun gano daruruwan makamai masu linzami da na'urorin harba makamai masu linzami da bama-bamai da dama da gurneti, da kuma motoci marasa matuka.

    “Dakarun sun kama dukkan makaman, wasu kuma an tayar da su a cikin filin, yayin da wasu kuma aka tura su domin bin diddigin binciken da aka gudanar.

    Ya ce "an gano kayayyakin ayyukan ta'addancin ne a kusa da gine-ginen fararen abin da ke nuna "ƙarin shaidar kungiyar ta'addanci ta Hamas na yin amfani da mazauna Zirin Gaza a matsayin garkuwar mutane".