Babban hafsan sojin Najeriya ya nemi afuwar al'ummar Tudun Biri

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai daga sassan duniya daban-daban, musamman dai Najeriya da makwabta.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Nabeela Mukhtar Uba and Umar Mikail

  1. Sojojin Isra'ila sun kashe mutum ɗaya a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan

    Ma'aikatar lafiya ta Falasɗinawa ta sanar da cewa sojojin Isra'ila sun kashe wani Bafalasdine guda daya tare da jikkata wasu hudu a wani samame da suka kai cikin dare a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan. .

    Ɗaya daga cikin waɗanda suka jikkata yana cikin mawuyacin hali", in ji ma'aikatar.

    A cikin kwanaki bakwai da suka gabata, an kashe aƙalla Falasdinawa takwas a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan ciki har da yara biyu.

    Bisa ƙididdigar da Majalisar Dinkin Duniya ta yi, an kashe Falasɗinawa 246 da suka hada da yara 65 a Gaɓar Yamma da Kogin Jordantun ranar 7 ga watan Oktoba.

    Wannan adadi bai hada da ‘yan uwan ​​Falasɗinawa biyu da aka kashe a harin da aka kai kan fararen hula a wata tashar bas a makon jiya.

    • Daruruwan mutane na ci gaba da ficewa daga asibitin Al-Shifa na Gaza
    • 'Na rasa kusan duk ƴan'uwana a rikicin Isra'ila da Gaza'
  2. Tinubu ya ba da umarnin yin bincike kan harin bom a Kaduna

    Bola Ahmad Tinubu

    Asalin hoton, FACEBOOK/BOLA TINUBU

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmad Tinubu ya ba da umarnin a gudanar da cikakken bincike kan harin bom da rundunar sojin ƙasar ta ce ta kai bisa 'kuskure' a jihar Kaduna.

    Shugaban ya bayyana haka ne yayin miƙa saƙon ta'aziyya ga al'ummar jihar Kaduna da kuma alhini ga mutanen da suka ji rauni sakamakon lamarin da ya faru a ƙauyen Tudun Biri a ƙaramar hukumar Igabi.

    Cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan kafafen yaɗa labarai, Ajuri Ngelale ya fitar, Shugaban Najeriyar ya ce abin takaici ne inda kuma ya bayyana jimami kan asarar rayukan da aka yi.

    Shugaban Najeriyar ya kuma buƙaci mutane su kwantar da hankalinsu yayin da hukumomi ke nazari a kan lamarin.

    Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin a bai wa mutanen da suka jikkata kulawa sosai a asibiti tare da addu'ar Allah ya ji ƙan waɗanda suka rasu.

    • 'Dole a hukunta wadanda suka kai hari ta sama a jihar Kaduna'
    • Harin jirgin sama a Kaduna: 'An kashe ƴan'uwana 34'
  3. 'Hamas na cin zarafin matan da take garkuwa da su'

    ...

    Asalin hoton, EPA

    Ma'aikatar cikin gidan Amurka ta ce yarjejeniyar tsagaita wuta ta mako guda da aka cimma tsakanin Isra'ila da Hamas, ta wargaje saboda Hamas ta ƙi sakin matan da ta yi garkuwa da su, saboda ba ta son su tona asirin cin zarafinsu ta hanyar lalata da aka yi.

    Mai magana da yawun ma'aikatar, Matthew Miller, ya shaidawa 'yan jarida a Amurka ba ta da wani dalili na yin shakku kan rahotannin fyaden da ake zargin Hamas da aikatawa.

    Wata mai rajin kare haƙƙin matan Isra'ila ta ce daman Hamas ta yi shirin cin zarafin matan a ranar 7 ga watan Oktoba da ta fara ƙaddamar da hari kan Isra'ila.

    Ƴan sanda sun samu mata babu sutura a jikinsu, wasu an yi musu fyade, sun kuma ce sun samu bayanan ne daga wadanda suka kubuta a baya-bayan nan.

    • Wane ne Yahya Sinwar shugaban Hamas na Gaza?
    • Yadda ake fafata yaƙin Isra'ila da Gaza a shafukan sada zumunta kamar TikTok
  4. Isra'ila ta musanta bai wa WHO umarnin ficewa daga Kudancin Gaza

    ...

    Isra'ilata musanta ikirarin shugaban Hukumar lafiya ta duniya, cewa ta bai wa ma'aikatanWHO awa 24 su janye kai kayan asibiti da magunguna a wurin da suke ajiyewake kudancin GAZA.

    Shugaban Hukumar Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus ne ya wallafa sakon ashafin hukumar na X.

    Sojin Isra'ila dai sun sanar da mutane da jami'an lafiya na cikin gida, da na MDD su kaucewa inda suke kai hare-hare;

    Shi kuwa wakilin BBC cewa ya yi mutane sun rasa inda za su nufa, ba su da tabbacin zuwa arewaci ko kudanci, kowa a kidime ya ke.

    Mr Ghebreyesus ya ce ya yi kira ga Isra'ila ta janye umarnin, amma Isra'ila ta musanta bai wa ma'aikatan WHO umarnin kwashe kayan aikinsu daga wurin.

    • Halin da yaran Gaza ke ciki: An raunata su kuma an kashe iyayensu
    • Iyakar Lebanon: Dakarun Ireland da ke sa ido kan boyayyen rikicin Isra'ila
  5. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar mu a wannan shafi na kai tsaye, BBC hausa, barkan mu da safiyar Talata.

    Aisha Babangida da Nabila Mukhtar Uba ne za su kasance da ku domin kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Kuma za ku iya tafka muhawara a shafukan sada zumuntarmu domin samun ƙarin labarai.

    Sai ku biyo mu.