Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Sai mun ga abin da ya ture wa buzu naɗi a Gaza - Netanyahu

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida and Abdullahi Bello Diginza

  1. Majalisa za ta mara wa Tinubu baya don inganta Najeriya - Tajudeen

    Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya Honorable Tajuden Abbas ya ce majalisar dokokin ƙasar za ta mara wa shugaban ƙasar baya wajen aiwatar da tsare-tsaren da za su inganta ƙasar.

    Yayin da yake gabatar da jawabin godiya a taron kasafin kuɗin ƙasar da shugaba Tinubu ya gabatar wa majalisar, kakakin majalisar ya ce majalisar dokokin ƙasar a shirye take wajen mara wa shugaban ƙasar baya don aiwatar da ayyukan da za su amfani ƙasar

    ''Musamman tsare-tsaren da za su inganta tattalin arzikin ƙasarmu tare da magance fatara da talauci tsakanin al'umma", in ji shi.

  2. Kotun Koli ta yanke hukuncin ci gaba da amfani da tsoffi da sabbin takardun kuɗin Najeriya

    Kotun Kolin Najeriya ta bayar da umarnin a ci gaba da amfani da tsoffin takardun kudi na Naira 200, da 500 da kuma 1000 tare da sabbin da aka sauyawa fasali.

    Kotun ta yanke wannan hukuncin ne yau yayin da ta yi Nazari kan wata bukata da gwamnatin tarayyar kasar ta gabatar ma ta.

    Kotun kolin dai ta yanke hukuncin cewa duka sabbin da tsoffin takardun kudin za su ci gaba da zama kudi har gwamnatin tarayyar kasar ta shirya ma canja tsoffin bayan tattaunawa da dukkan masu ruwa a lamarin.

    Haka na nufin wannan hukuncin ya shafe wanda kotun ta yanke a farko shekarar nan cewa za a ci gaba da amfani da tsoffin kudin har zuwa ranar 31 ga watan gobe na Disamba.

    Kotun dai ta yanke hukunci ne kan wata bukata da gwamnatin kasar Ta shigar gabanta ta hannun babban lauyan gwamnati Leteef Fagbemi a makon jiya, inda ta nemi kotun da ta soke hukuncin nata na baya cewa tsoffin kudin za su daina aiki daga ranar 31 ga wata Disamba.

    A cikin hujjojin da ta gabatar, gwamnatin ta yi wa kotun bayanin cewa idan kotun ta ki amincewa da wannan bukatar, to kasar na cikin kasadar sake fadawa cikin wata sabuwar matsalar karanci kudi da ci bayan tattalin arziki irin wadanda aka gani a watanni ukun farko na wannan shekarar lokacin da babban bankin ya yi canjin sabbin kudi.

    Babban lauyan gwamnatin ya shaidawa kotun cewa ya kamata a tsawaita wa’adin tsoffin kudi ta yi la’akari da yadda tuni wasu ‘yan kasar suka fara taskace duka sabbi da tsoffin kudin ganin wa’adin nata na 31 ga watan Disamba na karatowa.

    Kimanin Makonni biyu da suka wuce ne dai Babban Bankin Kasar ya sanar da cewa tsoffin takardun Naira 200 da 500 da kuma 1000 za su ci gaba da zama kudin har illa masha Allahu; abin hukuncin kotun kolin ya kara tabbatarwa a yau.

    • CBN ya ce a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudi
    • Ya za a yi da tsofaffin kuɗin Najeriya da aka sauya?
  3. 'Za mu rage hauhawar farashi da kashi 21 a 2024'

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta yi duk abin da ya kamata domin rage hauhawar farashin kayayyaki da kashi 21 cikin 100 a shekarar mai zuwa.

    Yayin da yake gabatar da kasafin kuɗin ƙasar, shugaba Tinubu ya ce hakan zai taimaka wajen farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar.

    Najeriya dai na fama da hauhawar farashin kayayyaki musamman bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin Tinubu ta yi ranar 29 ga watan Mayu.

    • Mece ce hauhawar farashi, kuma me ya jawo tsadar kayayyaki a duniya?
    • Ba mu yarda da kayan tallafi a hannun gwamnoni ba - Ƴan ƙwadago
  4. Ya kamata 'yan majalisa su tsefe kasafin kuɗi yadda ya kamata - Tinubu

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce akwai buƙatar 'yan majalisar dokokin ƙasar su riƙa tsefe kasafin kuɗin ƙasar kafin su amince da shi.

    Tinubu ya ce hakan zai bayar da dama ga gwamnati wajen cika alƙawuran da ta ɗaukar wa 'yan ƙasar a lokacin yaƙin neman zaɓe.

    Shugaban na wannan jawabi ne a gaban majalisar dokokin ƙasar lokacin da yake gabatar mata da kasafin kuɗin ƙasar na shekarar 2024

  5. A soke wasu ma'aikatu da cibiyoyin gwamnati - Akpabio

    Shugaban Majalisar dattawan Najeriya Sanata Godswill Akpabio ya buƙaci gwamnatin tarayyata ta soke wasu ma'aikatun gwamnati, sannan ta yi garambawul a wasu, ta yadda za a samu ingantuwar aiki.

    Yayin da yake jawabi jim-kadan kafin shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin 2024 a zauren majalisar, Sanata Akpabio ya ce hakan zai tabbatar da an gudanar da ayyukan gwamnati yadda ya kamata.

    Shugaban Majalisar dattawan ya shawarci gwamnati ta duba hanyoyin rage basukan da ta gada daga tsahuwar gwamnati.

    Sanata Akpabio ya kuma bayyana cewa majalisa za ta bai wa ɓangaren zartarwa haɗin kai domin aiwatar da kasafin kuɗin yadda ya dace.

    • Akpabio da Tajuddeen sun zama shugabannin majalisa ta goma a Najeriya
    • Kotun daukaka kara ta kori Goodswill Akpabio a matsayin dan takarar sanata na APC
  6. An tuhumi wata fursunar Falasɗinawa da aka sako da "yunƙurin kai hari da almakashi"

    A jiya ne aka sako fursunonin Falasdinawa 30 daga gidajen yarin Isra’ila a karkashin yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka ƙulla.

    Budour Hassan, na kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International, ya yi magana a shirin gidan rediyon BBC a yau, inda ya mayar da hankali kan wata fursuna da aka sako mai suna Nurhan.

    An zargi Nurhan, ƴar shekara 15 da yunƙurin kai hari da almakashi inda sojojin Isra'ila suka harbe ta tare da raunata ta, wanda ya yi sanadiyar mutuwar ƴar uwarta.

    An yanke wa Nurhan hukuncin zaman gidan yari na shekara 13 da rabi,

    Hassan ya bayyana hukuncin daurin a matsayin "ba a yi daidai ba,"

    Bayan an sallame ta, aikin farko da Nurhan ta yi shi ne ziyartar kabarin ƴar uwarta

  7. Labarai da dumi-dumi, Tinubu ya isa majalisa don gabatar da kasafin kuɗin 2024

    Shugaban Najeriya ya isa zauren majalisar dokokin ƙasar domin gabatar da kasafin kudinsa na farko a matsayin shugaban kasar.

    Haɗakar majalisar dattawa da ta wakilai ne shugaba Tinubun zai gabatar wa kasafin kuɗin.

    An dai ƙiyasta cewa kasafin zai ci naira tiriliyan 27, kuma sai gwamnati ta nemi rance dala biliyan daya don cike gibin.

    Shugaban ya samu rakiyar mataimakin shugaban ƙasar Kashim Shettima, da sakataren gwamnatin tarayya Sanata Gorge Akume, da shugaban ma'aikatar fadar shugaban ƙasa Femi Gbajabiamila da shugaban jam'iyyar APC na ƙasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje da wasu gwamnonin jihohi da ministoci da manyan jami'an gwamnati a lokacin gabatar da kasafin.

    • Me Tinubu zai yi da bashin kusan dala biliyan takwas da zai karbo?
    • Abin da 'yan Najeriya ke cewa kan kasafin kudin 2022 na Buhari
  8. Jirgin sojin Amurka ɗauke da mutum takwas ya faɗi a Japan

    Jirgin sojin Amurka ɗauke da mutum takwas ya faɗi a tsibirin Yakushima da ke Japan

    Jami'an gadin tekun Japan sun shaida wa BBC cewa jami'an ceto sun samu wani fasinja ''da ba ya numfashi''

    Kafofin yaɗa labaran Japan sun ambato jami'ai na cewa an ga tarkacen jirgin a kusa da tsibirin Yakushima.

    Kafar yaɗa labaran NHK ta Japan ta ce jirgin mai lamba CV-22 na koƙarin sauka ne a filin jirgin Yakushima yayin da ɗaya daga cikin injinansa ya kama da wuta.

    Bayanai sun ce jirgin ya taso ne daga sansanin soji da ke Iwakuni a yankin Yamaguchi, inda yake kan hanyarsa ta zuwa sansanin soji na Kadena a yankin Okinawa.

    kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato sakataren majalisar zartarwar Japan, Hirokazu Matsuno na cewa jirgin ya ɓace ne daga kan hanyarsa da misalin ƙarfe 2:40 na rana agogon ƙasar.

    A watan Agustan da ya gabata ma, wani jirgin sojin na Amurka ya yi hatsari a arewacin Ostiraliya yayin wani atisaye, lamarin da ya yi sanadin mutuwar sojojin Amurka uku daga cikin mutum 23 da ke cikin jirgin.

    • Hatsarin jirgin Nepal: 'Direban jirgin bai bayar da rahoton komai ba kafin hatsarin'
    • Mutumin da ya makale a tayar jirgin sama daga Afirka ta Kudu zuwa Holland ya isa lami lafiya
  9. Sanatocin arewacin Najeriya na ƙara matsa wa Tinubu lamba don buɗe iyakar Nijar

    Kungiyar Sanatocin Arewacin Najeriya ta gudanar da wani taro ranar Talata domin tattauna batun rufe iyakar ƙasar da jamhuriyar Nijar, da janye wutar lantarki, sakamakon juyin mulkin da sojojin ƙasar suka yi.

    Sanatocin sun buƙaci Najeriya wadda ke jagorancin ƙungiyar ECOWAS ta buɗe iyakokinta da ta rufe da Nijar, a kuma mayar musu da wutar lantarki, saboda a cewarsu lamarin talakawa ke shafa.

    Ga ƙarin bayanin da Sanata Lawal Adamu Usman, (Mr Laa) na jihar Kaduna, ya yi wa BBC.

  10. Tinubu ya nemi amincewar majalisa don karɓo ƙarin bashin $8.8bn

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya rubuta wa majalisun dokokin ƙasar biyu takardar neman amincewarsu don karɓo ƙarin bashin dala biliyan 8.6 da kuma euro miliyan 100, kimanin naira tiriliyan 7.1.

    Domin gudanar da manyan ayyuka a ɓangarorin wutar lantarki da gina tituna da samar da ruwan sha da gina layin dogo da kuma ɓangaren lafiya.

    Haka kuma shugaba Tinubu ya aike da ƙwarya-ƙwaryar kasafin birnin Abuja zuwa ga majalisar domin neman amincewarta.

    A yau ne kuma shugaban ƙasar zai gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2024 ga haɗin gwiwar majalisun dokokin biyu, bayan da majalisar zartarwar ƙasar ta amince da kasafin wanda ya kai naira tiriliyan 27.5

    Wannan na zuwa ne bayan da majalisar ta sake nazarin tsarin kashe kuɗaɗen gwamnati na matsaicin lokaci, wanda aka yi ƙiyasin canjin dala a kan naira 700, tare da ƙiyasta gangar mai a kan dala 73.96.

    A ranar Litinin ne, ministan kasafin kuɗi da tsare-tsare na ƙasar, Sanata Atiku Bagudu ya shaida wa manema labarai cewa majalisar zartarwar ta sake nazarin tsarin kashe kuɗaɗen gwamnati na matsaicin lokaci da manufar harkokin kuɗi, inda ta amince da naira 750 a kan kowace dala, da kuma ƙiyasta gangar mai a kan dala 77.96.

    A shekarun baya-bayan nan dai Najeriya ta dogara da karɓo bashi daga ƙetare domin gudanar da wasu manyan ayyuka.

    A baya dai adadin kuɗin da ake in Najeriya bashi ya kai naira tiriliyan 87.3, kamar yadda ofishin kula da bashi na kasar ya bayyana.

    Lamarin da ke nuni da cewa adadin ka iya kai wa naira tiriliyan 94.

    Hakan na nufin bashin da ake bin ƙasar, ya ninka - kasafin kuɗin da shugaban ƙasar ke shirin gabatarwa a yau na naira tiriliyan 27.5 - fiye da sau uku.

    • Shugaba Tinubu zai gabatar da kasafin kudin badi na naira Tiriliyan 27.5
    • Abu uku da Tinubu zai mayar da hankali a matsayin Shugaban Ecowas
  11. Yau ce ranar Falasɗinawa ta Majalisar Dinkin Duniya

    Majalisar Dinkin Duniya ta ware kowacce ranar 29 ga watan Nuwamba da zummar nuna damuwa da halin da Falasɗinawa ke ciki da kuma aniyar samar musu da ƙasa mai cin gashin kanta.

    Dangane da wannan ranar BBC ta tattauna da Muhammad Qaddam Sidik, mai sharhi kan harkokin ƙasashen Larabawa, mazaunin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

    Qaddam Sidik ya jaddada tasirin wannan rana da ta zo a daidai da lokacin da ake fama da yaƙi tsakanin Hamas da Isra'ila.

  12. Faɗa tsakanin ƴan daba a Haiti ya raba mutane da muhallansu

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce fadan da kungiyoyi ke yi a Haiti ya watsu daga birnin Poeto-prince zuwa yankunan karkara, lamarin da ya janyo dubban mutane rasa muhallansu da koma baya wajen kai agajin kayan abinci.

    Kakakin hukumar kare haƙƙin ɗan adam ta Majalisar Dinkin Duniya Ravina Shamdasani ta ce lamarin ya munana.

    Ta ƙara da cewa rahoton da suka samu ya nuna ƙungiyoyin masu aikata muggan laifuka sun fara afkawa kauyukan abokan gabarsu. Su na afkawa mutane tare da cin zarafi ta hanyar lalata ga mata, ciki har da kananan yara.

    Shamdasani ta ƙara da cewa su na sacewa manoma amfanin gonarsu, da kwacen kudi da dabbobi, da lalata duk wani abun amfani.

    • Haiti : An bankaɗo wanda ya bada umarnin kisan shugaban ƙasar
    • Babban birnin da 'yan bindiga ke cin karensu babu babbaka a cikinsa
  13. Za mu yi bincike kan takardun hukuncin zaɓen gwamnan Kano - NJC

    Majalisar Koli Kan Harkokin Shari'a ta Najeriya (NJC) ta ce za ta gudanar da bincike kan batutuwan da suka shafi takardun hukuncin zaɓen gwamnan Kano da kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta yi.

    Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ambato wasu jami'an majalisar shari'ar ƙasar, na bayyana haka a lokacin da suka ziyarci ofishinta da ke Abuja.

    An dai samu ruɗani kan takardun hukuncin shari'ar da kotun ɗaukaka ƙarar ta yi ranar 17 ga watan Nuwamba a shari'a tsakanin gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, da Nasiru Yusuf Gawuna na APC.

    A hukuncin da kotun ta sanar ta soke zaɓen Abba Kabir na NNPP tare da tabbatar da Nasiru Yusuf Gawuna na APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris.

    To sai dai bayan fitar da takardun hukuncin, sai wani ɓangare na takardun ke nuna cewa Abba Kabir Yusuf na NNPP ne ya yi nasara a hukuncin, wanda mafi yawan bangarensa ke nuna cewa Nasiru Yusuf Gawuna ne ya yi nasara.

    Lamarin ya janyo ce-ce-ku-ce mai tarin yawa a ciki da wajen jihar, tare da jefa shakku a zukatan jama'a.

    To sai dai cikin wata sanarwar da magatakardar kotun ɗaukaka ƙarar, Umar Mohammed Bangari, ya fitar, ya ce ya amince da kuskure a cikin takardun hukuncin da kotun ta fitar, to amma ya jaddada sahihancin hukuncin.

    Majalisar shari'ar ta ce ta karɓi ƙorafe-ƙorafen da suka shafi shari'ar, inda ta alƙawarta duba lamarin kamar yadda dokoki suka tanada.

  14. 'Waɗanda cutuka za su kashe ka iya fin waɗanda aka kashe a yaƙin Isra'ila da Hamas'

    Wakilin asusun kula da yara na Majalisar UNICEF , ya ce ma'aikatan agaji a Gaza na cikin kaduwar ganin kananan yara na mutuwa saboda cutukan da ake dauka ta hanyar amfani da ruwa maras tsafta.

    Mai magana da yawun UNICEF, James Elder wanda ke cikin masu rarraba ruwan sha da magani da man fetur albarkacin tsagaita wutar da aka yi, ya ce abokan aikin shi na fargabar wadanda cutuka za su yi ajalinsu ka iya fin waɗanda aka kashe lokacin yaƙin.

    Ya shaidawa BBC cewa ana bukatar ƙarin agaji, hakan ba zai samu ba har sai an samu dorewar zaman lafiya.

    Elder ya ambato wani Bafalasɗine na bayyana yadda aka lalata musu rayuwa tamkar a mummunan mafarki, ga kuma fargabar nan da lokaci za a ci gaba da kai musu hare-hare.

    • Asibitocin da yakin Isra'ila da Hamas ya ritsa da su a Gaza
    • Rikicin Isra'ila da Gaza: Mene ne asalin sa?
  15. Akwai kyakkyawan fatan tsawaita dakatar da faɗa a Gaza

    Isra'ila ta sanar da karbar ƙarin sunayen waɗanda Hamas ke tsare da su da ake fatan za a sako a yau Laraba.

    Kakakin firaiministan Isra'ila Tal Heinrich, ta faɗ wa BBC cewa sun sanar da iyalan waɗanda aka bada sunayensun.

    Ta ƙara da cewa iyalan sauran waɗanda aka yi garkuwa da su na jiran tsammani, inda ta ce ana magana ne akan mutane 170 da ke hannun Hamas a Zirin Gaza.

    Wannan dai za su kasance kashi na shida da Hamas ta saka tun bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.

    Isra'ila dai ta amince a tsagaita wuta da karin kwana guda, inda Hamas za ta sako mutum 10 da ke hannunta, kuma akwai fatan tsawaita dakatar da faɗa a Gaza.

    • Asibitocin da yakin Isra'ila da Hamas ya ritsa da su a Gaza
    • Mene ne hatsarin shiga yaƙi ta kasa a Zirin Gaza?
  16. Rasha ta ce ta harba makamai masu linzami zuwa Ukraine

    Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce jirgin ruwa na yaki ya harba makamai masu linzami daga Baharul Aswad zuwa sansanin sojin Ukraine.

    Ma'aikatar ta sanar da hakan a shafinta na telegram, sun ce an harba makamai masu linzami samfurin Kalibr, kuma an yi nasara ya fada inda ake buƙata.

    Sai dai babu wata kafa mai zaman kan ta da ta tabbatar da ikirarin Rashar.

    Sai dai a daren Talata sojin ruwan Ukraine sun ce su na fuskantar barazana daga sojin ruwan Rasha, kuma sun ambato mamakami masu linzamin da Rashar ta bayyana.

    A bangare guda magajin birnin Moscow, ya ce sojin saman kasar sun yi nasarar kakkabo jirage marassa matuka da ke shawagi a sararin samaniyar Rasha, wanda ya yi ikirarin na Ukraine ne.

    • Harin Ukraine ya lalata jirgin yaƙin Rasha
    • Amurka ta bai wa Ukraine harsashi miliyan daya da ta kwace daga Iran
  17. Assalamu Alaikum

    Masu bibiyar mu barkan mu da hantsin Laraba.

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa tare da Aisha Babangida.

    Ku kasance da mu domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da kuma sauran sassan duniya.