Mu kwana lafiya
Masu bibiyarmu a wannan shafi, ƙarshen rahotonnin ke nan.
Kuna iya duba rahotonnin da muka kawo muku a yau Laraba idan kuka yi ƙasan shafin.
Mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
A'isha Babangida and Abdullahi Bello Diginza
Masu bibiyarmu a wannan shafi, ƙarshen rahotonnin ke nan.
Kuna iya duba rahotonnin da muka kawo muku a yau Laraba idan kuka yi ƙasan shafin.
Mu kwana lafiya.
Ana ci gaba da musayar fursunoni tsakanin Isra'ila da Hamas a kwana na shida a jere bayan tsagaita wuta.
Ko wannan yarjejeniya zai ci gaba - wadda ba ta samu wata tangarɗa sosai ba - har gaba da wannan dare abu ne da babu tabbas a kansa.
Duka Hamas da Isra'ila sun nuna alamun tsawaita tsagaita wutar amma dai babu wata yarjejeniya da aka sanar zuwa yanzu, har ma jami'an Isra'ila na cewa suna ci gaba da shirin komawa fagen daga.
Benny Gantz, ɗaya daga cikin jami'an majalisar yaƙi ta Isra'ila, ya ce hakan zai iya faruwa a kowane lokaci kuma za su faɗaɗa hare-haren a faɗin Gaza.
A cewarsa babu wani gidan ɓuya. Wannan ya yi kama da gargaɗi ga mazauna unguwannin Khan Younis da Rafah da su fice daga gidajensu kafin ci gaba da yaƙin.
Gwamnatin Isra'ila ta bayar da umarnin gudanar da wani tsari, wanda da alama za a iya ci gaba da zaman lafiya har zuwa ƙarshen mako matuƙar dai Hamas za ta ci gaba da sako mutanen da ke hannunta.
Hakan zai bayar da damar sakin yara 100, da iyaye mata da kuma mata tsofaffi.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ci alwashi cigaba da gwabza yaki da Hamas a Gaza da zarar an kammala sakin ragowar mutanen da aka yi garkuwa da su.
Ya kara da cewar Isra'ila ba za ta dakatar da yaki ba har sai ta kakkabe kungiyar Hamas gaba daya.
Wadannan jawabai na zuwa ne jim kadan bayan Hamas ta sanar da mutuwar Kfir Bibas, wani jariri mai wata 10, tare da mahaifiyarsa da dan'uwansa mai shekaru 4 dukkansu 'yan Isra'ila.
A nata bangaren, Hamas ta bayyana cewa iyalan sun rasa rayukansu sakamakon luguden wutar sojojin Isra'ila, batun da sojin Isra'ilan suka ce suna bincike don tabbatar da sahihancinsa.
Ana sa ran sanar da musayar karin fursinonin Falasdinawa nan gaba kadan.
Gwamnatin jihar Kano ta sanar da cewa za ta fara kwashe masu larurar tabin hankali daga titunan jihar.
Matakin na zuwa ne ya yin da korafe-korafe suka yi yawa cewa irin wadannan mutane suna bararamba a tituna tare da fuskantar barazanar cin zarafi ga kuma yanayin sanyi na kara kunno kai.
Ofishin maitaimakawa gwamnan Kano kan harkokin marasa galihu da tallafawa masu karamin karfi ne ya sanar da matakin gwamnatin Kanon na kwashe masu tabin hankalin daga kwararo.
Fauziyya D. Sulaiman itace mai taimakawa gwamnan ta musamnan, ta ce aikin kwashe masu larurar dabin hankalin zai fi mayar da hankali ne kan wadanda suke yawo tsirara da masu duka.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce mutum biyu daga cikin mutanen da ake garkuwa da su a Gaza waɗanda aka saki yanzu haka sun shiga ƙasar ta Isra'ila.
Rundunar ta ce mutanen biyu ƙari ne a kan jerin mutanen da aka sa ran za a sake su a yau Laraba.
Tun farko Hamas ta ce ta miƙa mata biyu waɗanda ke da shaidar zama a Rasha ga jami'an ƙungiyar Red Cross.
Sanarwar rundunar ta IDF ta ce "Bayan jami'an lafiya sun yi wa waɗanda aka sakin dubawa da gaggawa, sojoji za su kuma raka su zuwa asibiti."
Yayin da ake fargaba game da ko za a tsawaita wa'adin tsagaita wuta a Gaza, wani magidanci mai ƴaƴa biyar ya koma gidansa, wanda hare-haren Isra'ila suka yi raga-raga da shi a Gaza.
Wael Qudeih ya ce ya koma ne domin ganin abin da ya rage a gidan nasa.
Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare kan Gaza ne bayan wani hari da mayaƙan Hamas suka kai a Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 1,200 tare da garkuwa da wasu 200.
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya sake jaddada matsayarsa kan cewa ƙasarsa ba za ta tsagaita wuta na dindindin ba, kuma dakarun ƙasar za su ci gaba da fafatawa "har ƙarshe."
Kamar yadda BBC ke ruwaitowa, masu shiga tsakani na ƙasashen Masar da Qatar na ci gaba da ƙoƙarin ganin an tsawaita tsagauta wuta.
Sai dai a cikin wata sanarwa da ya fitar, Netanyahu ya ce "Tun daga farkon wannan yaƙi na bayyana ƙudurori uku: kawar da Hamas, dawo da dukkanin mutanenmu da ake yin garkuwa da su tare kuma da tabbatar da cewa Gaza bai sake zamewa barazana ga Isra'ila ba. Har yanzu waɗannan ƙudurori na nan daram."
Ya ce sakin gomman mutanen da ake garkuwa da su "babban ci gaba ne."
"To amma a kwanakin nan na ji wasu na tambayar: Bayan kammala wannan mataki na dawo da waɗanda ake garkuwa da su, ko Isra'ila za ta ci gaba da yaƙin? Amsar ita ce e."
"Babu abin da zai hana mu komawa yaƙi har sai mun kai ƙarshe. Wannan ce manufata. Kuma majalisar sojin na goyon bayan hakan. Gwamnati tana goyon bayan haka."
Har yanzu akwai mutum 161 da Hamas ke riƙe da su a Zirin Gaza, kamar yadda mai magana da yawun gwamnatin Isra'ila Eylon Levy ya bayyana.
Adadin ya ƙunshi 'yan Isra'ila 146 da 'yan ƙasar waje 15, cikinsu akwai maza 126 da mata 35.
Mista Levy ya ce har yanzu akwai yara huɗu masu shekaru ƙasa da 18 a hannun Hamas, da kuma 10 masu shekaru 75 ko fiye.
Ya ce babu tabbas game da yawan sojojiin da ke hannun Hamas ɗin.
"Muna son dawo da dukkan mutanen gida, mun duƙufa kan hakan, babu wanda za mu bari," a cewar Levy yayin wani taron manema labarai.
Ya ƙara da cewa "matuƙar dai akwai abin da Hamas za ta bayar" Isra'ila za ta duba yiwuwar tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta don tabbatar da sakin ƙarin mutanen.
Tuni muka shiga kwana na shida kuma na ƙarshe a yarjejeniyar tsagaita wutar tsakanin Hamas da Isra'ila, amma akwai fatan cewa za a iya tsawaita ta.
Magoya bayan jam'iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano su na ci gaba da gudanar da zanga-zangar lumana kan abin da suka kira ƙoƙarin murɗe musu zaben gwamnan jihar.
Wannan na zuwa ne bayan da kotun ɗaukaka ƙara ta soke zaben gwamna Abba Kabir Yusuf.
A waje daya kuma rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayar da umarnin kama wani jami’inta da ake zargi da bude wuta kan wasu matasa unguwar Kurna abin da yayi sanadin mutuwar mutum guda lamarin da ya janyo matasan suka gudanar da zanga-zanga
Ga rahoton Zahraddeen Lawan daga Kano.
Hukumar Kula da Gidajen Yarin Najeriya ta ce ta yi wa fursunoni 1,137 rajista domin shiga jarrabawar kammala makarantar sakandare ta ƙasa (NECO) a jihar Enugu.
Hukumar ta ce ta yi wa' ɗaurarrun rajistar ne cikin shekara 12 da suka gabata.
Jaridar Punch a Nariya, ta ruwaito Kwanturolan gidan yarin Enugu, Nicholas Obiako na bayyana cewa a halin yanzu fursunoni 124 ne ke zana jarabawar NECO da ke gudana a cibiyar rubuta jarrabawar a jihar ta bana a jihar.
Ya kara da cewa ''ci gaban karatun fursunonin ya fara ne tun daga azuzuwan firamare da sakandare zuwa ingantaccen ilimin manya, yana inganta dogaro da kai da kare lafiyar jama'a bayan zamansu a gidan yari''.
Bugu da kari, ana ba da horon sana'o'i a fannoni kamar ɗinki, aikin ƙarfe, da na katako, wanda ke ba da gudummawa ga gyare-gyaren halayen fursunonin domin sake shiga cikin jama'a.
Hukumomin ba da agaji na ci gaba da yin amfani da damar da aka yi na tsagaita bude wuta na kai agajin abinci da ruwan sha ga Falasdinawa.
Kamar yadda aka ruwaito a baya, akwai kimanin mutane miliyan 1.7 da suka rasa matsugunansu a cikin Gaza - da yawa daga cikinsu sun koma kudancin Gaza sakamakon mummunan rikici tsakanin Isra'ila da Hamas.
Waɗannan hotunan sun nuna yadda hukumar ba da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya UNRWA take raba buhunan garin fulawa da ruwan sha a Khan Younis da ke kudancin yankin.
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken yana birnin Brussels a yau, kuma ya gana da taron ministocin harkokin wajen Nato.
Ya ce Amurka na son ganin an tsawaita dakatar da faɗa tsakanin Isra'ila da Gaza, kuma tana kokarin cimma wannan manufar "kowace rana".
"Tsawaita dakatar da buɗe wuta yana nufin ƙarin waɗanda aka yi garkuwa da su za su dawo gida, ƙarin taimako gaggawa zai kasance a cikin Gaza.
"A bayyane yake, wannan wani abu ne da muke so. Na yi imani kuma abu ne da Isra'ila ke so," kamar yadda ya shaida wa taron.
Ma'aikatar lafiya ta Falasɗinawa ta bayar da rahoton cewa wasu yara biyu sun mutu sakamakon harbin da sojojin Isra'ila suka yi a garin Jenin da ke Yamma da Gabar Kogin Jordan.
Sojojin Isra'ila sun kai wani gagarumin farmakin soji a can a yau Talata da yamma.
Majalisar dokokin Kenya ta haramta wa mambobinta sanya wata nau'in rigar kwat da ake kira Kaunda suit, wadda ta samo sunanta daga sunan tsohon shugaban ƙasar Zambia, marigayi Kenneth Kaunda.
Shugaban majalisar ya ce ba a maraba da kwat din da kuma wasu kaya na gargajiyar al'ummar Afirka a zauren majalisar, kasancewar sun ci karo da dokar sanya kaya ta majalisar.
Ya kuma jaddada aikin dokar a kan ƴan majalisa mata, wadda ta ƙunshi haramcin sanya gajerun siket da riguna bulawus marasa hannu.
Dandazon matasa sun gudanar da wata zanga-zanga a unguwar Kurna da ke tsakiyar birnin Kano, inda suka toshe babban titin zuwa Katsina tun da safiyar yau domin nuna fushinsu a kan harbin wasu matasa.
Suna zargin ƴan sanda da harbin matasan ne, wanda ya yi sanadin mutuwar daya daga ciki, karin wasu biyu kuma sun samu raunuka har ma an kwantar da su don yin jinya a asibiti.
A baya-bayan nan, ana fama da tunzuri saboda shari'ar zaben gwamnan jihar.
Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce tuni an kama dan sandan da ake zargi da yin harbin na ranar Talata, wanda ya kai ga matasan gudanar da zanga-zanga a wayewar gari.
A ciki wata sanarwa da ta fitar, rundunar ta ce dan sandan mai mulkamin sufeto ya yi harbi kan kungiyoyin matasan da ke rikici da juna ne inda ya raunata biyu, daya kuma ya riga mu gidan gaskiya.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Mohammed Usaini Gumel, ya ba da umarnin gudanar da bincike kan lamarin.
A cewar sanarwar tuni aka kama sufeton, kuma a halin yanzu yana tsare a hannun ‘yan sanda.
Wani ɗan jam'iyyar adawa a Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo, ya ce an kashe wani mai fafutuka a taho mu gamar da 'yan siyasa suka yi a gabashin ƙasar.
Ganau sun ce tashin hankalin ya barke ne lokacin gangamin yaƙin neman zaben shugaban kasa a yankin Maniema, inda Moise Katumbi, ke neman kujera a zaɓen da za a yi a watan gobe.
Katumbi da jam'iyyarsa ta Republic , sun zargi magoya bayan gwamnatin shugaba Felix Tshisekedi, da kai musu harin.
Tun da fari ƙungiyar Tarayyar Turai ta ce tawagar masu sa ido kan zaɓen da aka tura ƙasar a baya , sun gagara zuwa wasu sassan ƙasar saboda matsalar tsaro. Lamarin da ya dauki lokaci kan sa ido a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisu.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta yi duk abin da ya kamata don magance matsalolin da suka daɗe suna ci wa fannin ilimi tuwo a ƙwarya.
Yayin da yake jawabi a lokacin gabatar da kasafin kuɗin ƙasar, shugaba Tinubu ya ce ''za a yi hakan ne ta hanyar aiwatar da wani tsari mai ɗorewa na tallafin karatu, ciki har da tsarin bashin karatu na ɗalibai da aka tsara zai fara aiki nan da Janairu 2024."
Makarantun Najeriya dai na fama da matsaloli masu tarin yawa, ciki har da yajin aikin malamai da ƙarin kuɗin makaranta.