Hamas ta saki Isra'ilawa 12, Isra'ila ta sako Falasɗinawa 30
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Rahoto kai-tsaye
A'isha Babangida, Ahmad Tijjani Bawage and Umar Mikail
Ƴan Isra'ila da aka saki sun haɗu da ƴan uwansu
Mun samu wasu sabbin hotunan ƴan Isra'ila 11 da Hamas ta saki a daren jiya bayan sake haɗuwa da ƴan uwansu.
Cikin mutanen da Hamas ɗin ta saki akwai yara takwas, mata mai shekara 18 da kuma wasu uwaye biyu.
Dukkansu sun fito ne daga kibbutz - Nir Oz, wanda ya kasance ɗaya daga cikin yankin da ya fuskanci kisan kiyashi a harin ranar 7 ga watan Oktoba da Hamas ta kai.
Ana ci gaba da rike da dukkan iyayen yaran da aka saki a Gaza.
Zuwa yanzu, akwai mutum 74 da aka saki daga Gaza, cikin 240 da aka yi imanin cewa Hamas da wasu mayaka Falasɗinawa sun yi garkuwa da su.
Asalin hoton, Israel Defense Forces
Bayanan hoto, Sahar Kalderon, mai shekaru 16, na daga cikin waɗanda aka sako tare da ɗan uwanta Erez mai shekaru 12
Asalin hoton, Israel Defense Forces
Bayanan hoto, An kuma saki wasu 'yan uwa matasa da suka haɗa da Yaakov mai shekaru 16, da Yagil - ɗan shekara 13.
Asalin hoton, Israel Defense Forces
Bayanan hoto, Eitan Yahalomi mai shekaru 12, tare da mahaifiyarsa Batshema a daren jiya
An fara shari'ar matar tsohon shugaban kasar Zambia
Asalin hoton, Getty Images
An fara shari'ar matar tsohon shugaban kasar Zambia Esther Lungu, matar tsohon shugaban kasa Edgar Lungu a birnin Lusaka.
Ana tuhumar ta ne da laifin satar motoci uku, da satar wani kadarori a Lusaka da kuma mallakar dala 400,000 da ake zargin ta samu ne ta aikata laifi.
Ana tuhumar ta ne tare da wasu ‘yan sanda biyu.
Wani shaida ya shaida wa kotu a ranar Litinin cewa Lungu ta ƙwace motarta da karfin tsiya da takardar mallakar gidanta da kuma motoci biyu na ‘yarta.
Ta kara da cewa jami'an 'yan sandan da ake zargi sun tilasta musu sanya hannu kan takardun kadarorin ga Lungu.
Lungu da wadanda ake tuhumarsu tare sun musanta aikata ba daidai ba lokacin da aka kama su kan laifukan da ake zarginsu da aikatawa a watan Satumba.
Zambia ta yi watsi da wasu shafukan batsa da ke cikin litattafan koyar da dalibai
Hakainde Hichilema: Yadda zaben sabon shugaban kasar Zambia ya karfafa gwuiwar 'yan adawar Afirka
Ana bincike don gano ko kirkirarriyar basira ce ta rubuta jawabin Shugaban Afirka ta Kudu
Fadar shugaban ƙasar Afrika ta Kudu na bincike gano ko kirkirarriyar basira ce ta rubuta wani ɓangare na jawabin shugaba Cyril Ramaphosa wanda ya yi a makon da ya gabata, kamar yadda kafofin yaɗa labaran ƙasar suka ruwaito.
Hakan ya biyo bayan iƙirari a shafukan sada zumunta cewa wani ɓangare na jawabin shugaban ƙasar da ya yi a wurin taro kan ilimi, cewa ba masu rubuta masa jawabi ne suka yi ba.
Mai magana da yawun shugaban ƙasar, Vincent Magwenya, ya musanta iƙirarin, inda ya ce ba sa amfani da kirkirarriyar basira wajen rubutu musamman ma irin waɗannan jawabai.
Ya ce sashen kula da ilimi na ofishin shugaban ƙasar ne ya rubuta wani ɓangare na jawabin, inda ya ƙara da cewa suna bicike don gano daga inda jawabin ya fito.
"Ba za mu lamunci amfani da kirkirarriyar basira ba wajen rubuta jawabai, kuma za a ɗauki mataki idan aka tabbatar da gaskiyar wannan iƙirari," in ji Mista Magwenya.
Masana na ganin Ƙirƙirarriyar basira ta AI ka iya kawo ƙarshen ɗan Adam
Ko China za ta iya kere Amurka a fagen ƙirƙirarriyar basira ta AI?
Wani riƙaƙƙen ɗan daba ya miƙa kansa ga ƴan sandan Kano
Asalin hoton, Abdullahi Haruna Kiyawa/Facebook
Hantar Daba, ɗaya daga cikin riƙaƙƙun ‘yan daba a jihar Kano, ya miƙa kansa ga rundunar ‘yan sandan jihar.
A cewar 'yan sandan, Hantar Daba yana da yara 'yan daba kimanin 100 a karkashinsa, kuma ya yi alkawarin shawo kansu su ma su kai kansu don ajiye makamai tare da rungumar turbar zaman lafiya.
A baya dai, ƴan sandan sun sanya tukwicin naira dubu ɗari biyar a kan wasu ‘yan daba uku, ciki har da Hantar Daba.
Wannan mataki dai na daga cikin kudurin rundunar ‘yan sandan na dakile ayyukan ‘yan daba a faɗin jihar.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ƴan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a yau Talata.
Sanarwar ta ce "Hantar Daba, tare da rakiyar mahaifiyarsa da ’yan uwa, ya nuna nadamar abin da ya aikata a baya tare da nuna aniyarsa ta shiga shirin gwamnatin jihar na afuwa."
"Mika wuyan ya zo ne bayan wani sauyin tunani da aka samu yayin wani taro na baya-bayan nan a filin wasa na Sani Abacha a ranar 17 ga Oktoba, 2023."
Tuni dai Abba Burakita da Chile Maidoki, sauran ƴan daban biyu da aka saka tukuici a kansu suka miƙa wuya ga ƴan sandan jihar.
Yanzu haka, Hantar Daba yana hannun ‘yan sanda, kuma ana tantance al'amuran tsaro da suka shafe shi.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Mohammed Usaini Gumel, ya yaba wa ƙoƙarin al’umma, ya kuma buƙaci duk wanda ke da korafi kan Hantar Daba da ya fito.
Ya kuma ja hankalin jama’a da su kai rahoton duk wani abu da ake zargi na rashin tsaro ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko kuma ta hanyar lambobin tuntuɓar gaggawa da kafofin watsa labarai na intanet.
Me ya sa 'yan daban Kano ke zubar da makamai da rungumar zaman lafiya?
'Dalilin da ya sa muke taro 'yan daba wasa a Kano'
Nijar ta soke dokar hana fasa-kwaurin 'yan ci-rani
Asalin hoton, Reuters
Sojojin da suka yi juyin mulki a jamhuriyar Nijar sun soke dokar hana fasa-kwaurin 'yan ci-rani a ƙasar, da ta shafe tsawon shekara takwas.
Dokar ta bai wa hukumomi damar ɗaukar mataki a kan masu safarar ƴan ci-rani ta yankin babbar hamadar Nijar zuwa Libya kafin su dangana da Turai.
Amma an hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum - wanda ya yi aiki da Tarayyar Turai don dakile kwararar mutane ta Tekun Bahar Rum - daga kan mulki a watan Yuli.
Tuni dai Janar Abdourahmane Tchiani ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban ƙasa.
Gwamnatin soji da ke mulki ta sanar da soke dokar ne a wata sanarwa da ta fitar, inda ta ce dokar ba ta yi la'akari da muradun Nijar da 'yan ƙasar ba.
Haka kuma ta ce za a saki duk waɗanda aka samu da laifi a karkashin dokar ta 2015.
Matakin dai wata manuniya ce cewa gwamnatin mulkin soji a Yamai, babban birnin ƙasar na shirin tabbatar da ikonta kan 'yancin cin gashin kan ƙasar, duk da matsin lamba daga ƙasashen duniya.
Bayan juyin mulkin da aka yi, Tarayyar Turai ta dakatar da duk wasu ayyukan haɗin gwiwar tsaro da ƙasar da ke Afirka ta Yamma.
Babban jami'in harkokin waje na EU, Josep Borrell, ya bi sawun Amurka da Faransa a watan Yuli ta hanyar kin amincewa da Janar Tchiani a matsayin shugaba.
Ya kuma ce za a dakatar da tallafin kuɗi da ake bai wa Nijar, har sai baba-ta-gani.
Kawo yanzu dai ba a bayyana yadda ƙungiyar ta Turai za ta mayar da martani ga abin da ke zama babbar illa ga dabarunta na dakile kwararar ƴan ci-rani daga Afirka ba.
A shekara ta 2015, masu neman mafaka da ƴan ci-rani sama da miliyan daya ne suka yi ƙoƙarin shiga Turai, lamarin da ya sa Nijar ta matsa kaimi wajen zartar da dokar da aka soke yanzu.
An samuwar raguwa sakamakon haka - amma masu fataucin sun koka da aiwatar da ita a cikin shekarun da suka biyo baya.
A yanzu dai akwai fargabar cewa ƙungiyoyin masu safarar mutane na iya ganin soke dokar a matsayin wata dama ta sake tura ƴan ci-rani zuwa ƙasashen da ke kan iyaka da Nijar kamar Libya ko Aljeriya domin tafiya Turai.
Abin da ya hana sulhu tsakanin Ecowas da Nijar - Tuggar
Kawuna sun rabu kan korar da sojojin Nijar ke wa ƙasashen duniya
Ɗaliban da suka karanci fannin likitanci a jami'o'in waje sun faɗi jarrabawa
Asalin hoton, Getty Images
Kimanin dalibai 433 a cikin 836 da suka karantai fannin likitanci a jami'o'in ƙasashen waje sun faɗi jarrabawar samun lasisi da cibiyar yi wa likitoci rijista a Najeriya (MDCN) ta shirya.
An gudanar da jarrabawar ne a asibitin koyarwa na Aminu Kano (AKTH) tsakanin 22 zuwa 23 ga watan Nuwamban 2023, ta hanyar kwamfuta.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa sakamako ya nuna cewa mafi yawan daliban da suka kammala karatun likitancin ba su ci jarrabawar ba.
Dalibai 403 ne kawai suka samu nasara a jarrabawar.
'Likitoci' 400 sun fadi jarrabawa a Nigeria
Abin da ya sa likitocin Najeriya suke neman aiki a kasashen waje
Abin da ya hana sulhu tsakanin Ecowas da Nijar - Tuggar
Ana ci gaba da farautar fursunonin Saliyo da suka tsere
Asalin hoton, AFP
Ƴan sanda a Saliyo sun ce suna ci gaba da farautar mutanen da ke da hannu a abin da gwamnati ta bayyana da far wa dimokraɗiyya.
Wasu ‘yan bindiga ne suka kai hari a kan wata ma’ajiyar makamai da gidajen yari da dama a Freetown, lamarin da ya kai ga tserewar kusan fursunoni 2,000.
Gwamnatin ƙasar ta sanar da bayar da tukuicin dala 2,000 ga duk wanda ya ba da bayanai kan waɗanda suka aikata laifukan, wadanda har yanzu ba su kai ga ganowa ba, da kuma dala 1,000 ga duk wanda ya ba da bayanai a kan fursunonin da suka tsere.
Har yanzu akwai dokar hana fitar dare a duk faɗin Saliyo.
Hare-haren sun yi sanadin mutuwar mutum ashirin, 13 daga cikinsu ma'aikatan gwamnati ne.
Saliyo: 'Yadda na tsira a gobarar tankar mai amma kuma rayuwata ta tarwatse'
Sakamakon zaɓen shugaban ƙasar Saliyo na 2023
An ga hayaƙi na tashi a birnin Gaza
Asalin hoton, AFP TV
An ga hayaki yana tashi sama a birnin Gaza a safiyar yau, Talata.
Rahotanni sun nuna cewa wataƙila wasu ƙungiyoyin Falasdinawa sun yi luguden wuta kan sojojin Isra'ila - ba tare da sanin cewa an tsawaita dakatar da buɗe wuta ba.
An amince da tsawaita dakatar da buɗe wuta na sa'o'i 48 a jiya, Litinin.
Ana sakin fursunonin Falasdinawa uku a matsayin musaya ga kowane daya daga cikin ƴan Isra'ila da aka yi garkuwa da su a Gaza.
Hamas: Su wane ne shugabanninta da suka fi fice?
'Ayyukan Isra'ila ka iya jefa Gabas ta Tsakiya cikin haɗari'
Tinubu ya sake naɗa Mele Kyari shugaban kamfanin NNPC
Asalin hoton, nnpc
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sake naɗa Mele Kyari a matsayin shugaban Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL).
Ya kuma naɗa Pius Akinyelure a matsayin Shugaban Hukumar gudanarwa na kamfanin.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Ajuri Ngelale, ya fitar a ranar Litinin, ta ce su biyun na cikin sabbin shugabanni gudanarwa na NNPC.
Nadin nasu, wanda ya yi daidai da sashe na 59 (2) na dokar kula da harkokin man fetur ta 2021, za ta fara aiki daga ranar 1 ga watan Disamba, 2023, in ji shi.
Baya ga Kyari da Akinyelure, Tinubu ya kuma naɗa Alhaji Umar Isa Ajiya – Babban Jami’in harkokin kuɗi na kamfanin.
Sannan sanarwar ta kuma ce shugaban ya amince da nadin manyan sakatarori biyu na ma’aikatar kudi ta tarayya da ma’aikatar albarkatun man fetur.
Mele Kyari: Moriyar da 'yan Arewa za su ci daga dokar mai ta PIB
Kamfanin NNPC ya ƙara farashin man fetur a Najeriya
Hotunan yadda jama'a suka tarbi Falasɗinawa 33 da aka sako
Fursunonin Falasdinawan 33 da aka sako a daren jiya an kai su wani shingen bincike na Isra'ila da ke kusa da Ramallah a yankin Yamma da Gaɓar Kogin Jordan. Jama'a ne suka tarbe su.
Sakinsu na nufin an sako Falasdinawa 150 - mata da samari maza - daga gidajen yarin Isra'ila tun ranar Juma'a a wani bangare na tsagaita wuta.
An zabo su ne daga cikin ainihin sunayen Falasdinawa 300 da Isra'ila ta tattara - akasarin waɗanda aka tsare a gidan yari yayin da suke jiran shari'a.
Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun ce adadin Falasdinawa da ake tsare da su a gidajen yarin Isra'ila ba tare da tuhumar su ba ya ƙaru ba tun bayan harin ranar 7 ga Oktoba.
Ga hotunan yadda jama'a suka tarbe su.
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Ƴan Najeriya sun kashe N2.6tn wajen sayen katin waya da data a cikin watanni tara
Asalin hoton, other
Masu amfani da layukan sadarwa a Najeriya sun kashe kusan naira tiriliyan 2.6 wajen siyan katin waya da na data a cikin watanni tara na farkon shekarar 2023, kamar yadda kamfanonin sadarwa na MTN Nigeria da Airtel Africa suka fitar.
Hakan ya nuna an samu karuwar kashi 32.57 cikin 100 daga naira tiriliyan 1.95 da aka samu a shekarar 2022.
A ɓangaren kamfanin sadarwa na Airtel, ya ce abubuwan da ke haifar da wannan shi ne ƙaruwar masu siyan data da kuma faɗuwar darajar naira
A cikin watanni tara na farkon shekarar 2022, Airtel ya samu dala biliyan 1.41 daga siyan katin waya da kuma data wanda lokacin da aka canza shi akan farashin N461 kan dalar Amurka ɗaya da aka samu a lokacin, ya kai naira biliyan 647.71.
A daidai wannan lokacin na 2023, kuɗaɗen shiga da waɗannan kamfanonin biyu suka samu a ɓangaren siyan katin waya da data sun kai dala biliyan 1.29 wanda lokacin da aka canza shi akan farashin naira 777 kan dala ɗaya ya kai naira tiriliyan 1.003.
A ɓangaren MTN, ƙaruwar masu siyan katin waya da data ne ke ƙara haɓaka da kuma kawowa kamfanin ci gaba.
Kuɗaɗen siyan data sun ƙaru da kashi 36.36 cikin 100 duk shekara, yayin da kuɗaɗen katin waya ya ƙaru da kashi 10.64 cikin 100, wanda ke nuna ƙaruwar amfani da Intanet a faɗin ƙasar.
Yadda matasa ke rayuwa babu wayar sadarwa da intanet a Kaduna
Abin da za ku yi idan aka toshe layin wayarku bayan kun hada katin SIM ɗinku da na NIN
An saki ƴan Isra'ila 11 da Falasɗinawa 33 yayin da aka tsawaita buɗe wuta
An saki Falasdinawa 33 da ake tsare da su a gidajen kason Isra'ila da tsakar daren jiya, yayin kuma da tun da fari Hamas ta saki Isra'ilawa 11 da suka haɗa da 'yan asalin Jamus da Argentina da Faransa.
Shugaban jam'iyyar Palestinian National Initiative, a yamma da Gabar kogin Jordan, Moustapha Barghoti yace dakatar da buɗe wuta ce kadai abinda ya dace.
Ya ce a halin yanzu kofa a bude ta ke ta cimma tsagaita wuta baki daya, wannan shi ne abin da duniya baki daya ke so.
Bayan wannan ya kamata a sako dukkan Isra'ilawan da ake tsare da su da Falasdinawa, wannan shi zai kawo zaman lafiya.
Abin da ya kamata ku sani kan yarjejeniyar Isra'ila da Hamas
Al-Shifa: Abin da muka sani game da farmakin da Isra'ila ta kai babban asibitin Gaza
Yaƙin Isra'ila - Gaza: An shiga rana ta biyar ta yarjejeniyar tsagaita wuta
Asalin hoton, Reuters
An shiga rana ta biyar da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas, bayan Qatar da ke shiga tsakani ta sanar da tsawaita wa'adin da sa'o'i 48, domin samun damar musayar ƙarin fursunoni tsakanin bangarorin biyu.
Ofishin Firaiministan Isra'ila ya ce an ba su sunayen Isra'ilawa 10 da Hamas za ta saka a yau Talata, wanda ta yi garkuwa da su ranar 7 ga watan Oktoba.
Shugaban hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya, Volker Turk ya yi maraba da wannan labari inda ya ce yana fatan wannan tsagaita wuta zai sanya mutane su koma cikin hankalinsu, da fahimtar tashin hankali da amfani da karfin soji ba za su magance matsalar ba.
Ita ma Isra'ila ta bada sunayaen Falasdinawa mata 50 da ka iya samun 'yanci kafin karewar wa'adin a ranar Alhamis.
Yadda ake fafata yaƙin Isra'ila da Gaza a shafukan sada zumunta kamar TikTok
Wane ne Yahya Sinwar shugaban Hamas na Gaza?
Assalamu Alaikum
Masu bibiyar mu barkan mu da hantsin Talata.
Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa tare da Aisha Babangida.
Ku kasance da mu domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da kuma sauran sassan duniya.