Ga wannan...

Asalin hoton, Reuters
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
A'isha Babangida, Ahmad Tijjani Bawage and Umar Mikail

Asalin hoton, Reuters
Nan za mu rufe wannan shafi da ya yi ta kawo rahotonni tun daga hantsin Talata.
Sai kuma gobe Laraba - ta bawa ranar samu - inda zamu zo da wasu sababbin rahotonnin.
Umar Mikail ne ya kasance da ku daga maraice zuwa yanzu.
Mu zama lafiya.

Asalin hoton, Reuters
Fafaroma Francis ya soke zuwa Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa don halartar taron sauyin yanayi na MDD bayan likitoci sun ba shi shawara.
A baya an shirya yadda jagoran ɗriƙar Katolika mai shekara 86 zai bi sawun shugabannin kasashen duniya a taron na COP 28 wanda za a fara ranar Juma'a.
Fadar Vatican ta fitar da sanarwa cewa Fafaroma na fama da mura da cutukan numfashi.

Asalin hoton, Reuters
Ƙasar Ƙatar da ke shiga tsakanin Hamas da Isra'ila, ta tabbatar da cewa Falasɗinawa 30 Isra'ila za ta sako daga gidajen yarinta a daren nan.
Za a sako su ne bisa musayar Isra'ilawa 12 da Hamas ta yi garkuwa da su a Gaza tun ranar 7 ga watan Oktoba.
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Ƙatar, Majed al-Ansari, ya wallafa ɗazun nan cewa: "Ƙarin bayani: Falasɗinawa da Isra'ila za ta sako sun ƙunshi yara 15 da mata 15."

Asalin hoton, Reuters
Ministan tsaro na Isra'ila mai tsattsauran ra'ayi, Ben-Gvir, ya yi gargaɗin cewa dakatar da yaƙi a Zirin Gaza na nufin rushewar majalisar yaƙi da Firaminista Benjamin Netanyahu ke jagoranta.
Saƙon da ministan ya wallafa a dandalin X ya yi kama da gargaɗi ga Mista Netanyahu, wanda da ma yake ta shan suka tun bayan harin Hamas na ranar 7 ga watan Oktoba.
Harin ne ya sa 'yan adawa suka shiga gwamnatin, har ma suka kafa majalisar da ake yi wa laƙabi da "war cabinet" - wato majalisar ministoci ta lokacin yaƙi.
'Yan awannin da suka wuce, Ben-Gvir ya wallafa wani saƙon da ke kira ga Netanyahu ya ƙyale sojojin Isra'ila su koma filin yaƙi a Gaza don su "kawar da Hamas" bayan yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwana huɗu da aka tsawaita da kwana biyu.
Wata sanarwa da ta fito daga rundunar sojin Isra'ila ta tabbatar da sakin ƙarin mutum 12 da ake garkuwa da su a Gaza, inda yanzu haka suka bar yankin.
Sanarwar ta ce: "Ɗazu-ɗazun nan, jami'an ƙungiyar Red Cross suka karɓi wasu mutum 12 da ake garkuwa da su tare da mayar da su Masar. Yanzu haka motocin da ke ɗauke da mutanen da aka saki na kan hanyarsu zuwa inda za su haɗu da sojojinmu a Kerem Shalom. Jami'an tsaro za su tantance mutanen da aka sakin."

Asalin hoton, IDF
Rundunar sojin Isra'ila ta tabbatar da mutuwar ƙarin sojojinta uku, waɗanda harin Hamas na ranar 7 ga watan Oktoba ya rutsa da su.
A baya dai an ayyana sojojin a matsayin waɗanda suka ɓata.
A wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar, ta ce sojojin da aka kashen su ne kofur Tomer Yaakov mai shekara 20, da kofur Kirill Brodsky mai shekara 19, da kuma kofur Shaked Dahan.
Sanarwar dai ba ta yi ƙarin bayani kan yadda aka kashe sojojin uku ba, sai dai kawai ta ce "ƙungiyar ƴan ta'adda ce ta sace su" sannan ta kashe su a ranar 7 ga watan Oktoba.
Haka nan rundunar ta ce an yi musu ƙarin girma bayan mutuwar tasu.

Asalin hoton, STATE HOUSE
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu zai bar ƙasar a ranar Laraba zuwa birnin Dubai na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa domin halartar taron sauyin yanayi na COP28.
Wata sanarwa da ta fito daga hannun mai taimaka wa shugaban ƙasar kan hulɗa da jama'a, Ajuri Ngelale, a yau Talata, ta ce Tinubu zai gabatar da jawabi a taron wanda zai gudana tsakanin ranakun 1 da 2 ga watan Disamba.
Bayanin da shugaba Tinubu zai gabatar lokacin taron zai mayar da hankali ne kan matsayar Najeriya game da sauyin yanayi, musamman abin da ya shafi amfani da makamashi maras gurɓata muhalli da kuma samar da kuɗi kan ayyukan daƙile ɗumamar yanayi.
Ana sa ran kuma shugaban na Najeriya zai yi amfani da damar wajen neman ƙasashen da suka ci gaba da su ƙara tallafa wa ƙasashe masu tasowa wajen yaƙi da sauyin yanayi.
Haka nan Tinubu zai yi amfani da lokacin taron wajen ganawa da masu ruwa da tsaki da nufin janyo ra'ayinsu wajen zuba jari domin samar da aikin yi a Najeriya.

Asalin hoton, @ARG_1880
Gwamnatin Taliban a Afghanistan ta ce mai taimaka wa firaministan ƙasar kan tattalin arziƙi, Abdul Ghani Baradar, ya ƙaddamar da rijiyoyin haƙar man fetur takwas a yankin arewacin ƙasar.
A lokacin bikin ƙaddamarwar, Ghani ya ce za a gina makeken asibiti da madatsar ruwa da kuma kwalta a yankin haƙar man fetur ɗin na Amu Darya.
Bayanin da gwamnati ta fitar ya ce ƙaddamar da rijiyoyinn zai ƙara yawan ɗanyen man fetur da Afghanistan ke haƙowa a kowace rana zuwa cubic mita 800 a kowace rana, yayin da nan gaba ake sa ran ƙaddamar da wasu ƙarin rijiyoyin guda 10.
Yanzu haka dai injiniyoyi 350 da sauran ma'aikata 550 ne ke aiki a filin haƙar ɗanyen man fetur ɗin na Amu Darya.
A kwanakin nan ne Afghanistan ta fara aikin neman rijiyoyin ɗanyen mai a arewacin Afghanistan tare da haɗin gwiwar wani kamfanin ƙasar China mai suna 'Afchin'.

Asalin hoton, @ARG_1880

Wata babbar kotun tarayya da ke zaman ta a Abuja, ta ɗage shari'ar da ake yi wa tsohon gwamnan babban bankin ƙasar (CBN) zuwa watan Janairun shekara ta 2023, yayin da zai ci gaba da zama a gidan yari har sai ya cika ƙa'idar belinsa ta kuɗi naira miliyan 300.
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) ce ta gurfanar da Emefiele bisa zargin sa da laifuka shida, ciki har da zargin badaƙala da kuɗi naira biliyan 1.6.
Sai dai tsohon gwamnan babban bankin ya musanta zargin.
Yanzu kotun ta ayyana 18 ga watan Janairun 2024 domin sake zama kan shari'ar.
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ne ya dakatar da Emefiele daga muƙaminsa a ranar 9 ga watan Yuli bayan "wani bincike da ake yi da kuma shirin sake fasalin ɓangaren kuɗi na ƙasar.

Asalin hoton, Getty Images
Yayin da aka shiga kwana na biyar bayan tsagaita wuta a Gaza, ƙungiyoyin bayar da agaji na duniya sun ce ana ci gaba da aikin kai ɗauki - kuma sun ce akwai buƙatar tsagaita wutar ta ci gaba da aiki domin tallafa wa al'umma.
Mun ɗauko muku hotunan halin da ake ciki yau a wasu unguwannin Gaza:

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Gwamnatin Indiya ta tabbatar da cewa an ceto mahaƙa 41 da suka maƙale a ramin haƙar ma'adanai na Uttarakhand da ke ƙasar har tsawon kwana 17.
Wata sanarwa da gwamnati ta fitar na cewa "wannan labari ne mai faranta rai ga ɗaukacin ƙasa."
Mutanen waɗanda akasarinsu matasa ne masu kimanin shekara 20 an fito da su ne cikin ƙoshin lafiya.
Sai dai an garzaya da su zuwa wata asibiti da ke kusa domin samun kulawa.
A bayanin da ya wallafa ta shafinsa na manhajar X, firmanistan Indiya, Narendra Modi ya jinjina wa wadanda suka ceto mahaƙan.
Ya ce "nasarar ceto wadannan ƴan'uwa namu a Uttarkashi ta jefa kowa cikin hali na farin ciki."
Tun ranar 12 ga watan Nuwamba ne mahaƙan suka maƙale a ƙarƙashin ƙasa bayan wani ɓangare na ƙofar shiga ramin haƙar ma'adanan ya rufta sanadiyyar zabtarewar ƙasa.
Hotunan wasu daga cikin mahaƙan da aka ceto:



Majalisar zartarwar Najeriya ta amince wa gwamnatin ƙasar ta karɓi rancen dala biliyan ɗaya don cike giɓin kasafin kuɗin kasar na badi.
Bankin raya ƙasashen Afirka ne zai ba da rancen, wanda za a biya a cikin shekara ashirin da biyar.
A gobe ne ake sa ran shugaban kasar, Bola Ahmed Tinubu zai gabatar da kudurin kasafin kuɗin ga majalisar dokoki don neman amincewar `yan majalisar.
Farfesa Muhammad Muntaka Usman, masanin tattalin arziki a jami`ar Ahmadu Bello da ke Zaria bayyana wa wakilin BBC, Ibrahim Isa yadda yake kallon rancen da yadda zai shafi rayuwar `yan Najeriya:
Wata kotu a Kenya ta dauki harajin gidaje kashi 1.5 cikin 100 da gwamnatin kasar ta sanya, wanda aka gabatar a matsayin wani ɓangare na dokar kudi a watan Yuli, a matsayin ba ya cikin tsarin dokar ƙasar.
Alkalan kotun uku sun yanke hukuncin cewa harajin ba shi da cikakken tsarin doka kuma an dauke shi rashin hankali.
Ƙaddamar da harajin gidaje tare da wasu haraji, ya haifar da zanga-zangar tsadar rayuwa.
Gwamnati ta bukaci a dage shari'ar na tsawon kwanaki 45 yayin da ta yanke hukunci kan mataki na gaba.

Asalin hoton, Subair Enitan
An ga bidiyon wata daliba 'yar Najeriya da ta kuduri aniyar kafa sabon tarihi a fannin yin awanni tana wanki da hannu a jejjeme bayan ta kammala.
Bidiyon Subair Enitan ya karade shafukan sada zumunta, inda aka gan ta kwance male-male a kan gado tana hutawa, bayan abin da ta ce a ranar Litinin, kwashe sa'a 58 tana ta wanki, sannan ta rika nuna wa kawayenta hannuwanta da suka kode, suka yi fari fat, sannan duk sun yi tattara.
Zuwa yanzu masu kula da kundin bajinta na Guinness World, ba su ce uffan a kan yunkurin Subair Enitan ba, kamar yadda ta fada wa kafofin labarai a ranar Litinin:
Yunwar shiga kundin bajinta na duniya, ta karade Najeriya a watannin baya-bayan nan.
Shahararriyar mai girki Hilda Baci ce ta fara wannan salo, inda ta yi ta girki tsawon sa'a 93 babu kakkautawa, sai dai bayan wata biyar, an samu wani gwanin girki dan kasar Ireland, Alan Fisher da ya ture ta daga kan matsayin, lokacin da ya yi girki na fiye da awa 119.
A baya-bayan nan ma, wata 'yar Najeriya da ake kira Helen Williams ta kafa wani sabon tarihi wajen yin karin gashi da hannu mafi tsawo - da ya kai mita 351.28.

Asalin hoton, AFP
Mutane 11 sun mutu a wani lamari da ya faru a wata mahakar platinum da ke kasar Afirka ta Kudu, a cewar kamfanin hakar ma'adinai na Implats.
Hatsarin ya faru ne ranar Litinin da yamma a Impala Rustenburg da ke lardin Arewa maso Yamma.
Mai magana da yawun kamfanin Johan Theron ya shaida wa BBC cewa mutane 86 ne lamarin ya shafa kuma 11 daga cikinsu sun mutu.
Wasu daga cikin mutanen da abin ya shafa sun samu munanan raunuka.
Kakakin ya ƙara da cewa an kammala aikin ceto kuma an fara gudanar da bincike kan lamarin.
Wannan ne lokacin da jirgin da zai yi tafiyar tsallaka tekun Atalantika, ya tashi a karon farko, daga filin jirgin sama na Heathrow da ke London, kuma yana amfani ne da man 'ya'yan itatuwa.
Kamfanonin jiragen sama na ganin tashin jirgi a matsayin wani gwaji da ke nuna cewa hanyar amfani da man tsirrai don jiragen sama, abu ne mai yiwuwa - sai dai rashin samun isasshen man da ake bukata na iya zama wani kalubale.
Ana iya sarrafa man da ake kira man jiragen sama mai dorewa wato da Ingilishi (sustainable aviation fuels) daga hanyoyi iri daban-daban ciki har da amfanin gona da sharar gida da kuma man girki.
Shi dai wannan jirgin sama, wanda Boeing ne kirar 787, an cika shi da tan 50 na man tsirrai. An yi amfani da nau'i guda biyu ne, kashi 88, an samo ne daga maikon da aka tatso daga shara, sai kuma ragowar daga masarar da ake sarrafawa a Amurka.

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Malawi ta sanar da shirin tura ƙarin matasa 5,000 aiki a gonakin Isra'ila, duk da sukar da ake yi na tura mutuma 221 a karshen makon jiya.
Ministan yada labaran Malawi, Moses Kunkuyu ya shaida wa shirin BBC Newsday a ranar Talata cewa, "Wasu ('yan Malawi) sun shafe fiye da shekara biyar suna can, kuma muna da nufin karawa a kan wadannan alkaluma."
Ministan ya kare matakin da ake suka, inda ya ce yana cikin shirye-shiryen gwamnati na samar da ayyukan yi ga matasa a ciki da wajen kasar.
Kunkuyu ya kara da cewa, "An kwashe shekaru da dama ana yin hakan a kasar Malawi, kuma muna fitar da matasa zuwa kasashen Afirka da ma wajen Afirka."
Jagoran ‘yan adawa a kasar, Kondwani Nankhumwa a ranar Litinin ya caccaki gwamnatin Malawi yayin wata hira da BBC Newsday, inda ya zarge ta da jefa ‘yan Malawi cikin hatsari, ta hanyar tura su kasar da ke cikin yaƙi.
Sai dai minista Kunkuyu, ya ce Isra'ila ta tabbatar wa Malawi cewa 'yan kasar za su yi aiki a yankunan da fadan bai shafa ba.
'Yan Malawin za su maye gurbin wasu ma'aikatan gona na kasashen waje fiye da 10,000 da suka bar Isra'ila saboda yakin.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi gargadin cewa mace-macen da za a iya samu daga mutanen da ke fama da cutukan da ba a iya yi musu magani ba a Gaza, sai ta zarce ta wadanda suka mutu sanadin luguden bama-bamai.
Wani bin diddigi da Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi a cibiyoyin tsugunnar da 'yan gudun hijira na hukumar kula da masu gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, ya gano cutukan gudawa da larurorin numfashi a tsakanin kananan yara da jarirai, kuma babu wata kulawar lafiya da suke samu.
Mutanen da ke fama da kwantattun cutuka kamar daji ko kansa da ciwon zuciya da ciwon suga su ma, ba sa samun wani magani.
A lokaci guda kuma, wani ayarin Unicef a arewacin Gaza ya yi gargadi game da annobar raunukan yaki da mutane suka ji, ga kananan yara ana iya gani da "munanan raunuka" suna kwance a filayen ajiyar motoci ko a dandalin shakatawa.
Hukumomin ba da agaji sun nanata cewa bai kamata a yi ko tunanin ci gaba da fada ba, inda suka sake yin kira a tsagaita wuta na dindindin.