Gwamnonin Arewa maso Gabashin Najeriya sun gudanar da taro a Yola

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najieriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Gwamnatin Najeriya za ta kaddamar da noman rani a kasar

    .

    Asalin hoton, X/Sen Abubakar Kyari

    Bayanan hoto, Ministan albarkatun noma na Najeriya

    Gwamnatin Najeriya za ta kaddamar da noman rani na wannan shekara a Hadejia da ke jihar Jigawa.

    Cikin wata sanarwa da ma'aikatar albarkatun noma da samar da abinci ta kasa, ta fitar ta ce mataki wani bangare ne na kokarin kawar da tsadar abinci a fadin kasar.

    A cikin watan Yuli ne shugaban kasar Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan samar da abinci a fadin Najeriya.

    Ministan harkokin noma da samar da abinci na kasar Sanata Abubakar Kyari ne zai jagoranci masu ruwa da tsaki zuwa garin Hadejia a jihar Jigawa domin kaddamar da aikin a ranar Asabar 25 ga watan Nuwamba, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

    Sanarwar ta ce za a bai wa manoma kayyakin aikin noma da suka kunshi iri da takin zamani da magungunan feshi a lokacin bikin.

    Tuni dai gwamnatin kasar ta ce ta yi rangwamen kayayyakin aikin noma da kashi 50

    Ana sa ran gudanar da noman ranin a duka jihohin kasar 36 da Abuja.

    Inda ake ra san shuka alkamar - da aka shigo da irinta daga Mexico - da shinkafa, da masara da dawa da waken suya da kuma rogo.

    Kamfanonin sarrafa fulawa hudu ne suka bayyana aniyarsu na sayen alkamar daga wajen manoman.

    Ministan albarkatun noman ya bayyana kaddamar da shirin da cewa wani gagarumin ci gaba, a yunkurin da gwamnatin kasar ke yi na burin inganta kasar.

    Ya kara da cewa samar da kayayyakin aikin noma da na'urorin zamani za su taimaka wajen habaka harkokin noma a fadin Najeriya.

  2. Hamas za ta saki mutum 14, yayin da Isra'ila za ta saki fursunoni 42

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Jami'an Israila sun ce a yau Hamas za ta saki Isra'ilawa 14 da take garkuwa da su, yayin da ita kuma za ta saki fursunonin Falasdinawa 42 da take tsare da su.

    Hakan na zuwa ne a rana ta biyu ta yarjejeniyar tsagaita wuta ta wucin-gadi dac Qatar ke jagoranta.

    Yarjejeniyar ta amince da sakin Falasdinawa uku a kan kowane dan Isra'ila guda da Hamas ke garkuwa da su.

  3. Ra'ayi Riga: Yadda jam'iyyun adawa ke zargin gwamnati APC da amfani da karfin shari’a wurin murkushesu

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
  4. Ana sa ran karin musayar fursunoni a yau

    .

    Asalin hoton, Ariel

    Isra'ila ta ce tana sa ran sakin karin mutum 13 daga cikin wadanda Hamas ke garkuwa da su a yau.

    Haka kuma ana sa ran ita ma Isra'ila ta saki karin Falasdinawa masu yawa da take tsare da su a gidajen yarinta.

    Sannan kuma, akwai manyan motoci makare da kayan agaji da ke jiran a tantance su a kan iyakar Rafah domin shiga Gaza.

    Duk da cewa yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Hamas da Isra'ila karkashin jagorancin Qatar domin kawo karshen yakin, rahotonni na cewa har yanzu akwai tsananin bukatar kayan tallafi a Gaza.

    Akwai rahotonnin karancin man fetur da abinci da ruwan sha da magunguna da kayan aiki.

    Kusan motocin agaji 200 ne suka shiga Gaza a ranar Juma'a, adadi mafi yawa tun ranar 26 ga watan Satumba.

  5. 'Ana tsananin bukatar kayan agaji a Gaza'

    Wani likitan asibitin Al-shifa da ke Gaza ya shaida wa BBC cewa halin da ake ciki a Gaza ya tabarbare, sakamakon tsananin bukatar tallafi.

    Hakan na zuwa ne bayan da a ranar Juma'a motocin agaji fiye da 150 sun shiga Gazar dauke da kayan agaji da man fetur.

    Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Dakta Tedro Adhanom Ghebreyesus, ya ce ana kai mutanen da ke fama da raunukan harbin bindiga daga arewaci zuwa kudancin Gaza domin samun kulawa.

    Dubban Falasdinawa da yakin ya sa suka gujewa muhallansu, sun yi amfani da dakatar da yakin domin komawa gidajensu, duk kuwa da gargadin Isra'ila na cewa yakin bai kare ba.

  6. Yarjejeniyar musayar fursunoni tsakanin Isra'ila da Hamas na ci gaba da aiki

    ,

    Asalin hoton, .

    Da alama yarjejeniyar wucin-gadi tsakanin Isra'ila da Hamas na ci gaba da aiki.

    Matakin da zai bayar da dama da kuma share fagen karin musayar fursunoni tsakanin bangarorin biyu a yau Asabar.

    Isra'ila ta ce Qatar - wadda ta shiga tsakani a yarjejeniyar - ta bayar da jerin sunayen 'yan Isra'ila 13 da nan gaba za a saki galibinsu kananan yara.

    Mutum 24 da aka saki ranar Juma'a, ana duba lafiyarsa a asibitocin Isra'ila, kuma Isra'ilar ta ce suna cikin koshin lafiya.

  7. Marabanku

    Masu bin shafin BBC Hausa barkanmu da safiyar wannan rana ta Asabar,

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin sanar da ku halin da duniyar ke ciki.

    Kuna kuma iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta.