Rufewa
Da haka muke bankwana da ku a wannan shafi da ke kawo labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya. A kasance damu gobe Lahadi da yardar Allah.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najieriya da sauran sassan duniya.
Abdullahi Bello Diginza
Da haka muke bankwana da ku a wannan shafi da ke kawo labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya. A kasance damu gobe Lahadi da yardar Allah.
Jami'an tsaro a kasar Mali sun ce sun daƙile wasu hare-hare biyu da ake zargin mayaƙa masu kishin Islama na Alƙa'ida da kai wa.
Sai dai mayaƙan sun yi zargin cewa sun halaka sojoji da dama sannan sun ƙwace iko da wani sansanin soja da ke lardin Timbuktu.
Sojojin Mali dai sun daɗe suna yaƙi da mayaƙa masu ikirarin jihadi da kuma mayaƙan 'yan aware a yankin.
Masu ikirarin jihadi na kokari soma amfani da sansanonin sojin samar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya wadanda suka fice daga ƙasar kafin dakarun Mali su umurce su su bar sansanonin.

Asalin hoton, MURI/AJAKA
Kotun shigar da korafin zaɓe ta Tribunal da ke zamanta a Lakoja ta amince da bukatar ɗan takarar gwamna, Murtala Ajaka na SDP na a ba su damar binciken kayayyaki da takardun zaɓen da aka gudanar a ranar 11 ga watan Nuwamba.
Mai shari'a Yusuf Ado Birnin-Kudu da ya bada wannan umarni, ya umarci hukumar zaɓe ta INEC ta bada wannan dama a cikin sa'o'i 24.
Wannan umarni na zuwa ne bayan da lauyan masu korafi ya ce duk wani kokarinsu na samun damar nazartar kayayyakin zaɓen a Abuja da Lakoja ya gaggara.
Sai dai Mai shari'a Birnin-Kudu ya ce dole ne a bada wannan dama bisa tanadi na dokokin zaɓe da aka yiwa gyaran fuska a 2023.
Hukumar zaɓe ta INEC dai ta bayyana Ahmed Usman-Ododo a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Kogin.
Ododo ya samu ƙuri’a 446,237, inda ya doke mai biye masa, Muritala Ajaka na jam’iyyar SDP, wanda ya samu ƙuri’u 259,052.
Dino Melaye na PDP ne ya zo na uku, inda ya samu ƙuri’u 46,362.
Ma'aikatar harkokin wajen Qatar ta tabbatar da cewa Hamas ta saki yara takwas da yara biyar cikin 'yan Isra'ila 13 da ta saka a yau Asabar.
Sannan ta ce za a sake sakin wasu 'yan kasashen ketare bakwai.

Asalin hoton, EPA
Ɗan kwallon Manchester City, Erling Haaland ya kafa tarihi a matsayin ɗan kwallon da ya zura kwallo 50 cikin wasanni kaɗan a gasar Firimiya ta Ingila.
Ɗan wasan ya ci kwallon ne a wasansu da Liverpool. A yanzu ya ci kwallo 50 cikin wasa 48.
A wasan da aka buga a filin Etihad an tashi wasa kunnen doki wato 1-1.
A baya, tsohon ɗan kwallon Manchester United da New Castle, Andy Cole ne ke riƙe da kanbum inda ya ci kwallo 50 cikin wasa 65.
Wani babban jami'in Falasdinawa ya ce an daidaita a tattaunawar Qatar kan rikicin da ya biyo bayan zargin Isra'ila na karya dokokin tsagaita wuta da musayar fursunoni.
A cikin daren wannan rana ake saran a miƙawa ƙngiyar agaji ta Red Cross fursunonin Isra'ila.
'Yan Isra'ila 13 ake saran a saka.

Asalin hoton, Reuters
Dubban masu goyon-bayan Falasdinawa sun gudanar da zanga-zanga a birnin Landan, inda suka karaɗe yankin Park Lane har zuwa ginin majalisa da ke Westminster.
Masu zanga-zangar na kira ne da a tsagaita wuta a Gaza. Galibinsu riƙe da tutar Falasdinu suna ta ambatar a 'yanta Falasdinawa.
'Yan sanda sun yi kawanya a duk inda masu zanga-zangar ke ratsawa tare da gargaɗin cewa ba za su lamunci nuna goyon-baya ga Hamas ko kiyayya ga wani addini ba.
An dai kama mutane biyu cikin masu zanga-zangar da ake zargi da goyon-bayan ƙungiyar da aka haramta da kuma wasu hudu da ake cewa sun yi kokarin ingiza rikici.
Kungiyar Hamas ta zargi Isra'ila da karya dokokin yarjejeniyar da aka cimma kan musayar fursunoni.
Hamas ta ce wannan na daya daga cikin dalilan da suka sa ta jinkirta sakin 'yan Isra'ilar da take garkuwa da su a yau Asabar.
Sauran dalilan sun kuma haɗa da jinkirin shigar da kayan agaji arewacin Gaza.
Ma'aikatar tsaron Isra'ila taƙi cewa uffan a kan batun.
Gwamnonin Arewa maso gabshin Najeriya na taro a birnin Yola na Adamawa inda suke tattaunawa kan hanyoyin shawo kan matsalolin da suka addabi yankinsu.
Taron da ake gudanarwa a gidan gwamnatin Adamawa ya samu halartar gwamnonin shida na yankin Arewa maso gabashin Najeriya.
A wajen taron, Gwamna Babagana Umara Zulum na Borno, ya jadadda muhimmancin haɗin-kai domin warware duk matsalolin da ke jefa yankin cikin wani yanayi.
Gwamnonin sun sha alwashi bijiro da hanyoyin aiki tare domin shawo kan matsalolin tsaro da talauci da cigaban yankunansu.
Zulum ya kuma buƙaci gwamnatin tarayya ta taimaka wa yankinsu domin shawo kan manyan matsalolinsu kamar su rashin hanyoyi, samar da layukan dogo da ruwan sha.
Ofishin Firaministan Isra'ila ya fitar da hotunan rukunin farko da 'yan ƙasar da Hamas ta saki a ranar Juma'a, an kai mutanen asibiti domin a duba lafiyarsu.

Asalin hoton, IDF

Asalin hoton, IDF

Asalin hoton, IDF

Asalin hoton, IDF

Asalin hoton, IDF
Masar ta ce tana ganin ''alamun tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta ta wucin gadi da aka cimma tsakanin Isra'ila da Hamas'' zuwa kwana guda ko biyu.
Shugaban hukumar 'yan sandan ciki ta ƙasar, Diaa Rashwan, ya ce jami'ai na tattaunawa da wakilan ɓangarorin domin cimma yarjejeniyar tsawaita wa'adin wucin-gadi na kwanaki huɗu da aka cimma tun da farko.
sun ƙara da cewa hakan na nufin ''za a saki ƙarin mutanen da ake garkuwa da su a Gaza tare da sakin Falasɗinawa masu yawa daga gidajen yarin Isra'ila''.
"Masar ta samu kyakkyawan labari daga duka ɓangarorin biyu, game da wannan batu," in ji Rashwan.

Asalin hoton, AFP
Shugaban ƙasar Madagascar Andry Rajoelina ya samu nasarar wa'adi na uku a zaɓen da 'yan ƙasar da dama suka ƙaurace wa.
Ya lashe zaɓen da kashi 59% na ƙuri'un da aka kaɗa, inda ya doke babban abokin hamayyarsa tsohon hamɓararren shugaban ƙasar Marc Ravalomanana.
Kashi 46 ne na masu kaɗa ƙuri'a suka fito zaɓen da ake gani a matsayin wanda ya fuskanci ƙaracin fitowar masu zaɓe a tarihin ƙasar.
Ana ganin hakan na da alaƙa da kiran ƙaurace wa zaɓen da 'yan takarar adawa 10 suka yi.
Sun kuma janye takarar tasu ne saboda fargabar da suke da ita kan sahihancin zaɓen, da kuma nuna rashin amincewa da takarar shugaba Rajoelina a karo na uku, musamman game da sahihancin takarar tasa kasancewar suna zarginsa da mallakar takardar shaidar zama ɗan faransa.
To sai dai kotun tsarin mulkin ƙasar ta yi watsi da ƙararsu ta hana Mista Rajoelina tsayawa takarar.
Shugaba Rajoelina dai ya musanta zargin nasu, yana cewa bi-ta-da-ƙullin siyasa ne kawai.
A yanzu kotun tsarin mulkin ƙasar na da kwana tara domin tabbatar da sakamakon da hukumar zaɓen ta ayyana ranar Asabar.

Asalin hoton, .
Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun kai hari garin Yangtu da ke yankin karamar hukumar Takum a jihar Taraba, inda suka kashe mutum 10.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar, SP Usman Abdullahi ya tabbatar wa BBC faruwar lamarin, da ya ce ya auku a ranar Juma'a da maraice.
Ya ƙara da cewa rundunarsu tare da haɗin gwiwar sauran jami'an tsaro sun tura ƙarin jami'ai zuwa yankin domin farauto 'yan bindigar, tare da kwantar wa jama'a hankali.
Rahotonni sun ce tun da farko maharan sun tare hanyar Takum zuwa Ussa, inda suka riƙa kashe mutane.
A baya-bayan nan jihar Taraba ta kasance cikin jihohin da ke fama da hare-haren 'yan bindiga masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

Asalin hoton, Tinubu/X
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya daidaita rikicin siyasar jihar Ondo da aka kwashe watanni ana fama da ita bangaren gwamnan jihar Rotimi Akeredolu da mataimakin gwamnan Lucky Aiyedatiwa.
Cikin wata sanarwar da mai magana da yawun shugaba Tinubun, Ajuri Ngelale, ya fitar ranar Asabar, ya ce an cimma hakan ne bayan kwashe lokaci mai tsawo ana tattaunawa tsakanin bangarorin biyu da 'yan majalisar jihar da bangaren jam'iyyar APC na jihar, da kuma shugaban kasar ranar Juma'a a fadarsa da ke Abuja.
Sanarwar ta ce shugaba Tinubu ya shawarci duka bangarorin da su manta da duka abubuwan da suka faru, domin zaman lafiyar jihar da gudanar da ayyukan ci gaba.

Asalin hoton, X/Nigerian Presidency
Sasancin ya tabbatar da cewa Akeredolu zai ci gaba da zama a matsayin gwamna, yayin Aiyedatiwa zai ci gaba da kasancewa a matsayin mataimaki.
A baya-bayan nan dai an samu rashin jituwa tsakanin majalisar dokokin jihar da mataimakin gwamnan bayan da majalisar ta zarge shi aikata wasu laifuka ciki har da rashin biyayya ga gwamnan jihar.
Lamarin da ya kai har da barazanar tsigewa, inda ya garzaya wata babbar kotu a Abuja wadda ta dakatar da 'yan majalisar daga yunkurin.

Asalin hoton, Hostages and Missing families forum
Wata kungiya a Thailand da ke rajin sako mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su, ta wallafa hotunan 'yan kasar tare da dan Philippines guda da Hamas ta saki ranar Juma'a.
Kungiyar da ke fafutikar sako mutanen ta ce za ta ci gaba da gwagwarmaya tare da tuntubar ofisoshin jakadun kasashen waje har sai an tabbatar da sakin duka mutanen da Hamas din ke garkuwa da su.
A ranar Juma'a ne dai gwamnatin Thailand ta sanar da sakin mutanen a wani bangare na wata yarjejeniya da Qatar ta jagoranta.