Haka kuma ya ɗauki makamancin wannan mataki kan ministoci da jami'an gwamnatinsa a wani yunƙuri na rage kashe kuɗin gwamnati.
Matakin na zuwa ne sakamakon karyewar darajar kudin ƙasar, yayin da ƙasar ta samu bashi daga Asusun Bayar da Lamuni na Duniya IMF domin bunƙasa tattalin arzikinta.
Mista Chakwera, ya kuma umarci duka ministocinsa da yanzu haka ke ƙasashen waje da su koma cikin ƙasar.
An kuma rage alawus ɗin man fetur da ake bai wa manyan jami'an gwamnati da kashi 50.
Tattalin arzikin Malawi na cikin mawuyacin hali da ya haɗa da karancin man fetur da iskar gas, da kuma matsalar hauhawar farashin kayyaki.
An tarwatsa masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a Kaduna
Asalin hoton, Getty Images
"Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Rahotonni sun ce masu zanga-zangar sun fara tattaki ne daga kan babban titin Ahmadu Bello, inda suka ratsa ta titin Muhammadu Buhari a tsakiyar birnin Kaduna, kafin daga bisani 'yan sanda suka tsarwatsa su.
A tattaunawarsa da BBC, ɗaya daga cikin jagororin ƙungiyar IMN, Aliyu Umar Tirmidhi ya ce sun fito ne kawai domin nuna adawa da rikicin da ke faruwa a yankin Gaza.
Ya kuma ce a lokacin arangamar tasu da ƴan sanda an raunata mutane da dama, kuma "mutum ɗaya ya rasa ransa."
Tun bayan fara yaƙin Isra'ila da Hamas, an gudanar da irin waɗannan zanga-zanga na nuna goyon baya ga Falasɗinawa a manyan biranen duniya.
Shugaban adawar Isra'ila ya buƙaci Netanyahu ya sauka
Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock
Shugaban adawar Isra'ila, Yair Lapid ya yi kira ga Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da ya sauka daga muƙaminsa saboda gwamnatinsa ta kasa ɗaukar matakan da suka dace kan yaƙin Isra'ila da Hamas.
Lapid ya ce yana buƙatar samar da "gwamnatin da za ta sake gina ƙasar" ko da kuwa jam'iyyar Netanyahun ce za ta jagorance ta, amma dai yana son shi Netanyahun ya sauka.
Cikin wani saƙon X ta Lapid ya wallafa, ya ce sojojin Isra'ila da 'yan ƙasar sun nuna turjiya tun bayan harin 7 ga watan Oktoba da Hamas ta kai Isra'ila, to amma harin ya nuna gazawar gwamnatin ƙasar, musamman firaministan.
"Na ji wasu na cewa wannan ba shi ne lokacin da ya dace ba. Mun jira aƙalla kwanaki 40, don haka babu wani lokaci. Abin da muke buƙata yanzu shi ne gwamnati ta magance matsalar tsaro da tatalin arziki", in ji shi.
Lapid ba ya cikin majalisar lura da yaƙi da aka kafa bayan harin 7 ga watan Oktoba, saɓanin shugaban jam'iyyar masu matsakaicin ra'ayi Benny Gantz wanda ke cikin majalisar.
An sace matar hakimi a Kaduna
Asalin hoton, Getty Images
Wasu mahara da suka durfafi yankin yammacin ƙaramar hukumar Birnin Gwari sun shiga garin Kakangi inda suka sace mutum takwas, ciki har da matar tsohon hakimin garin.
Lamarin wanda ya faru a daren Laraba na zuwa ne bayan barazanar da ƴan fashin daji da ke addabar yankin suka umarci al'umma da su biya su miliyoyin kuɗaɗe dmoni tsira da hare-hare.
Ko a ranar Litinin, maharan sun far wa sojoji uku da aka ajiye domin tabbatar da tsaro a garin, inda suka harbi guda biyu daga cikin su yayin da ɗaya ya gudu a cikin mota mai sulke.
Yankin Birnin Gwari na daga cikin wuraren da suka yi ƙaurin suna kan matsalar ƴan fashin daji a Najeriya.
Hukumomi na cewa suna bakin ƙoƙarinsu, sai dai hare-haren na ci gaba da faruwa.
Wani mazaunin yankin ya ce a halin yanzu al'ummar yankin na rayuwa cikin fargaba da rashin tabbas, kuma mutanen da dama sun kasa girbe ɗan amfanin gona da suka noma.
Saudiyya ta yi bayani kan hana wasu ƴan Najeriya shiga ƙasarta
Asalin hoton, Reuters
Ofishin jakadancin Saudiyya a Najeriya ya yi ƙarin haske kan rahotonnin mayar da 'yan Najeriya 264 a lokacin da suka shiga ƙasar, yana mai cewa ba da wata manufa aka yi hakan ba.
A ranar Lahadi ne gwamnatin Saudiyya ta soke bizar wasu fasinjoji da jirgin Air Peace ya ɗauka a lokacin da suka sauka a ƙasar bayan tashin su daga Kano - abin da ya sa ƙasar ta buƙaci fasinjojin su koma Najeriya.
Cikin wata sanarwar da ofishin jakadancin Saudiyyar ya fitar ranar Laraba, ya ce "fasinjojin da aka hana shiga ƙasar, ba su cika sharuɗɗa da dokokin Saudiyya ba, saboda sun gabatar da bayanan da ba na gaskiya ba domin samun bizar da ba ita ya kamata a ba su ba, inda sai bayan sun isa Saudiyya ne aka gano hakan".
Sanarwar ta ƙara da cewa ''Ba 'yan Najeriya kaɗai aka yi wa hakan ba, har da na wasu ƙasashe".
Haka kuma ita ma ma'aikatar harkokin ƙasashen waje ta Najeriya cikin tata sanarwar da ta fitar ranar Talata, ta ce 'tana bincike game da lamarin, domin tabbatar da ko an saɓa wata ƙa'ida".
Mataimaki na musamman ga ministan harkokin wajen ƙasar, kan kafofin yaɗa labarai, ya ce ma'aikatar za ta tabbatar da irin wannan abu bai sake faruwa kan 'yan ƙasar ba a nan gaba.
Ofishin jakadancin na Saudiyya ya kuma fitar da gargaɗi ga mutanen kan su riƙa cika ƙa'ida wajen neman bizar shiga ƙasar.
''Haka kuma muna son jaddada muhimmancin bin ƙa'idoji da dokokin da saudiyya ta gindaya ga duka mutanen da ke da burin zuwa kasar", kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Daga ƙarshen ofishin ya buƙaci duka fasinjojin da ke muradin ziyartar ƙasar da su riƙa nazarin takardun bizarsu, domin dacewa da dokokin ƙasar kafin su fice daga ƙasashensu zuwa Saudiyya."
Bayanan hoto, Kefiritzak Franco (daga hagu) da Asif Master su ne biyu daga cikin sojoji Isra'ila da aka kashe a samamen da ake yi a Gaza
Rundunar sojin Isra'ila ta ce an kashe ƙarin sojojinta biyu, tun bayan samame ta ƙasa da dakarunta suka ƙaddamar a Gaza.
A yanzu, yawan sojojin Isra'ila da aka kashe a rikicin na Gaza ya kai 50.
Hukumar sojin ta Isra'ila ta ce Kefiritzak Franco (daga hagu) da Asif Master su ne sojojinta na baya-bayan nan da aka kashe.
'An kashe fararen hula a tsakiyar Gaza'
Asalin hoton, Getty Images
Kamfanin dillanacin labaran Falasɗinawa (wafa) ya ce wani hari ta sama da Isra'ila ta kai Laraba da daddare ya kashe kusan fararen hula 50 tare da jikkata gommai.
Wafa ya ce jirgin yaƙin Isra'ila ya kai hari wata unguwa da ake kira Sabra da ke tsakiyar Gaza, inda ya kai hari kan wani masallaci.
Kamfanin dillancin labaran ya ƙara da cewa harin ya yi sanadin mutuwar mutum uku a makarantar 'Malaysian school' da ke sansanin 'yan gudun hijira a Gaza, sannan wani ƙaramin yara ya mutu a wani harin na daban a birnin Khan Younis da ke Kudancin Gaza.
Sojojin Ira'ila ba su ce komai ba game da iƙirarin, amma ta ce hare-haren da ta kai ta sama sun lalata cibiyoyin Hamas. Sai dai BBC ba ta iya tantace sahihancin rahoton ba.
A ranar Litinin, ma'aikatar lafiyar Hamas ta ce mutum 11,240 ne aka kashe, ciki har da ƙananan yara 4,630, tun bayan da Hamas ta ƙaddamar da hare-hare zuwa Isra'ila
Isra'ila ta ce ta kai hari gidan jagoran harkokin siyasa na Hamas
Dakarun Isra'ila sun ce sun kai hari gidan ɗaya daga cikin manyan shugababbin ƙungiyar Hamas, Ismail Haniyeh, a Gaza.
Cikin wani saƙo da rundunar sojin Isra'ilar ta wallafa a shafinta na X, ta ce dakarunta sun yi amfani da jirgin yaƙi ranar Laraba da daddare wajen kai hari kan gidan shugaban harkokin siyasar ƙungiyar.
Sojojin sun yi iƙirarin cewa ''ana Amfani da gidan ne wajen kista hare-haren'' da kuma amfani da shi a matsayin "wurin taron taron manyan jami'an ƙungiyar''.
Sai dai BBC ba ta iya tabbatar da wannan iƙirarin na dakarun Isra'ila ba.
Isra'ila ta ce za ta gabatar da shaidar Hamas na amfani da asibitin Al-Shifa
Asalin hoton, Israel Defense Forces
Isra'ila ta yi alƙwarin gabatar da shaidar da ke tabbatar da zarginta na cewa akwai sashen da Hamas ke gudanar da ayyukanta a cibiyar lafiya mafi girma a Gaza.
Bayan samamen da sojojinta suka kai a ginin asibitin Al-Shifa a ranar Laraba, akwai rahotanni da ke cewa ta rusa wasu ɓangarori na asibitin.
Sai dai sojojin na Isra'ila har yanzu ba su gabatar da sahihan shaidu da ke nuna hanyar da Hamas ke bi wajen mafaka ko gudanar da ayyukanta a ƙarƙashin ginin asibitin ba.
Amma dai sun fitar da wani bidiyo da ba a tabbatar da sahihancinsa ba, da ke nuna makaman da Isra'ila ta ce a cikin asibiti ta gano su.
Wani jami'in Isra'ila ya ce sojojin ƙasarsa ba sa shiga asibiti haka kawai, sai da dalili kuma wannan na nuna ƙarara ana amfani da asibitin wajen sarrafawa da tara manyan makamai.
Hamas dai ta sha musanta waɗannan zarge-zarge.
Amurka da China sun amince da dawo da tattaunawar soji
Asalin hoton, Getty Images
Shugaba Biden ya bayyana tattaunawarsu ta San Francisco da shugaban China, Xi Jinping, a matsayin tsarariyar ganawar da ake saran ta kasance mafi alfannu a garesu.
A lokacin da yake jawabi a wajen wani taron- wanda Mista Xi bai halarta ba - Shugaba Biden ya ce ƙasashen biyu sun amince su dawo da tattaunawar ayyukan soji a matakin kololuwa.
Shugaban na Amurka ya ce musayar bayanai kai-tsaye ba tare da ɓoye-ɓoye ba na da muhimmanci wajen hana afkuwar matsaloli da rashin fahimtar juna tsakaninsu.
Mitsa Biden ya kuma shaida cewa sun amince a daƙile shigar da ƙwayar Fentanyl daga China zuwa Amurka.
Sannan kuma ƙasashen biyu za su yi aiki tare wajen rage barazanar amfani da ƙirƙirarriyar basira ta 'artificial intelligence' ko AI.
Mista Xi ya ce danganta tsakani China da Amurka na da matuƙar muhimmaci ga duniya.
Assalamu alaikum
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da wannan lokaci.
Ku ci gaba da kasancewa da mu domin kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Kuna kuma iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.