Ƴan ƙwadago da ke yajin aiki sun garkame majalisar Najeriya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Haruna Kakangi, Mukhtar Adamu Bawa and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Za a janye ƴan sandan da ke bai wa manyan jami'an gwamnati tsaro a Najeriya

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Najeriya na shirin janye jami'an 'yan sanda masu bai wa manyan jami'an gwamnati tsaro bisa umarnin shugaban kasa, kamar yadda karamar ministar harkokin 'yan sanda, Hajia Imaan Sulaiman-Ibrahim ta sanar.

    Ta bayyana irin kalubalen da rundunar ‘yan sandan ke fuskanta sakamakon rashin kula da su na tsawon shekaru, wanda ke kawo mata cikas wajen sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya dora mata.

    A ci gaba da kokarin da shugaban kasa ya yi na ganin an farfado da aikin ‘yan sanda mai inganci, Sulaiman-Ibrahim ta jaddada buƙatar ‘yan sanda su daidaita tare da inganta ayyukansu.

    Ta bukaci cikakken nazari kan cibiyoyin horarwa don dacewa da tsarin aiwatar da doka na zamani da ka'idojin ƙasashen duniya.

    Ta yi wannan jawabi ne a wani taron kwana biyu da ‘yan sanda suka gudanar a Abuja.

    Ta ce ma'aikatar tana da muhimman a wajen "haɓaka da aiwatar da ingantaccen rahoton sake fasalin 'yan sanda da kuma yin gyaran fuska ga aikin 'yan sanda, tare da aiwatar da umarnin shugaban ƙasa kan janye jami'an 'yan sanda daga ayyukan tsaron ƴan siyasa don haɓaka dabarun aikin ɗan sanda na al'umma".

    Wadannan tsare-tsare na da nufin kawo sauyi da inganta harkokin tsaron cikin gida a Najeriya.

    • Matsalar tsaro: Ana so a fara sanya wa 'yan sandan Najeriya kyamara don naɗar ayyukansu
    • Yadda 'yan sandan Najeriya suka kama manyan masu satar mutane 34
  2. Bellingham da Colwill ba za su buga wa Ingila wasa ba

  3. Hotunan yadda Falasɗinawa ke rayuwa a tantuna a kudancin Gaza

    A kudancin Gaza, birnin Khan Younis, yanayin sanyi mai tsanani na kutso kai wanda zai iya jefa kimanin Falasɗinawa miliyan 1.6 cikin mummunan yanayi, waɗanda Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta ke gudun hijira sakamakon rikicin Isra'ila da Hamas da ya raba su da matsugunansu.

    Mutane da dama da suka hada da wakilin BBC na Gaza Rushdi Abualouf, sun samu kansu suna rayuwa ne a tantuna inda aka tilasta wa da dama kwana a ƙasa.

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    ...

    Asalin hoton, Reuters

  4. An binne gawa 179 a harabar asibitin Gaza

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Daraktan babban asibitin Gaza ya ce mutane 179 da suka haɗa da jarirai ne aka binne a wani ƙaton kabari da ke harabar asibitin.

    Mohammad Abu Salmiyah ya ce majinyatan sun mutu ne bayan da kayan aikin asibiti masu muhimmanci suka gaza sakamakon katsewar wutar lantarki.

    Ya ce jarirai bakwai da majinyata ashirin da tara na cikin waɗanda aka binne.

    Salmiyah ya ce yanzu haka gawarwaki na cika asibitin sannan kuma babu wutar lantarki a dakin ajiyar gawa.

    An bayar da rahoton tashin bama-bamai a kusa da kuma tankokin Isra'ila sun yi cunkoso a kofar asibitin.

    • Sabon harin Isra'ila ya kashe fararen hula fiye da 30 a Gaza
    • Rikicin Isra'ila da Gaza: Mene ne asalin sa?
  5. Ƴan adawar Madagascar sun yi kira da a kaurace wa zaɓen ƙasar

    ...

    Asalin hoton, EPA

    Gamayyar jam'iyyun adawa na ƙasar Madagascar, mai suna Collectif de Dix, mai kunshe da jam'iyyu 10, sun buƘaci masu kada kuri'a da su kaurace wa zaben shugaban kasar da za a yi ranar Alhamis.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin siyasa ke kara ƙazancewa.

    Ƴan takara 10 daga cikin 13 da ke neman shugabancin kasar sun nemi a yi wa kotun ƙoli da hukumar zabe garambawul, bisa zargin rashin cancantar shugaba mai ci Andry Rajoelina.

    Dalilin hakan shi ne saboda samun takardar zama dan kasar Faransa da ya yi a shekara ta 2014.

    Rajoelina ya yi watsi da zargin, yayin da shugaban majalisar ya bukaci a dakatar da zaɓe.

    An dai tarwatsa zanga-zangar magoya bayan 'yan adawa ta hanyar kame da watsa musu hayaƙi mai sa hawaye.

    Rajoelina ya bukaci ƴan kasar da su yi watsi da kiran kaurace wa zaɓen shugaban ƙasar, tare da jaddada manufofin gwamnatinsa na ci gaba.

    Tarayyar Turai da Amurka sun nuna matuƙar damuwa, kuma shugaban kotun tsarin mulkin ya yi kira da a kwantar da hankula, tare da bayar da shawarar yanke hukunci ta hanyar zaɓe.

    Zaben na buƙatar dan takara ya samu sama da rabin kuri'u, idan ba haka ba kuma, za a je zagaye na biyu a ranar 20 ga watan Disamba.

    • Dalilan neman kirkiro hukumar hukunta laifukan zaɓe a Najeriya
    • Yadda minista ya yi iyon sa'a 12 bayan jirgin samansa ya fada cikin teku
  6. An yi afuwa ga ɗan ƙasar Rasha da aka samu da laifin kisan kai

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    An yi wa ɗaya daga cikin mutanen da aka samu da laifin kisan ƴar jaridar ƙasar Rasha, Anna Politkovskaya a shekara ta 2006, Sergei Khadzhikurbanov, afuwa bayan ya shafe tsawon lokaci tare da kammala aikin soja na watanni shida a Ukraine, a cewar lauyansa.

    Khadzhikurbanov, wanda tsohon jami'in ƴan sanda ne a Rasha, an yanke masa hukuncin ɗaurin shekara 20 a 2014, a matsayin ɗaya daga cikin mutane biyar da aka samu da laifin kisan ƴar jaridar.

    An harbe Politkovskaya, wadda ta shahara kan rahoton binciken da take yi kan ayyukan da Rasha ta yi a Chechnya, an harbe ta ne a gidanta.

    Afuwar ta biyo bayan ɗaukar fursunoni ne da ma'aikatar tsaron Rasha ta yi a Ukraine, inda ta karbe ragamar kungiyar mayaƙan Wagner.

    • Hukuncin kisa da aka yanke wa ɗan sandan Najeriya na tayar da ƙura
    • Za a sake gurfanar da faston da ake zargi da sa mabiyansa azumin mutuwa
  7. David Cameron ya koma majalisar ministoci bayan shekara bakwai

    ...

    Tsohon firaministan Birtaniya, David Cameron ya koma majalisar ministocin ƙasar bayan shekaru bakwai, inda ya maye gurbin James Cleverly yayin da ya gana da firaminista mai ci Rishi Sunak.

    Cameron ya kuma gana da wata tawagar da aka yi wa kwaskwarima bayan wani gagarumin garambawul na gwamnati.

    Komawar tsohon firaministan babu zato ba tsammani ta zo ne bayan korar Suella Braverman saboda sukar da ta yi wa 'yan sandan Birtaniyya.

    Firaministan ya yi maraba da sabbin ministoci da masu dawowa.

    • Dogarin David Cameron ya manta bindiga a bandakin jirgi
  8. Yajin aikin ƙungiyoyin ƙwadago haramtacce ne - Tinubu

    ...

    Asalin hoton, Bola Tinubu

    Gwamnatin Najeriya ta bayyana rashin jin dadin ta game da matakin da kungiyoyin kwadagon Najeriya NLC da TUC suka dauka na fara yajin aikin a fadin kasar, duk da umarnin da kotun ma'aikata ta bayar na kada su yi yajin aiki.

    A cikin wata sanarwa da ta fitar, gwamnatin ta bayyana matakin a matsayin wata alama ta girman kai da ƙoƙarin shafa wa gwamnati kashin kaji.

    Sanarwar wadda ta samu sa hannun mai taimaka wa shugaba Tinubu kan yaɗa labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga ta ce "yajin aikin fatali ne da umarnin kotu da tozarta ɓangaren shari'a."

    Ta ƙara da cewa "Bai kamata ƙungiyoyin biyu su hukunta ƙasar baki daya ba kan wani lamari na ƙashin kai da ya shafi shugaban ƙwadagon, Joe Ajaero, wanda aka kai wa hari a Owerri"

    Gwamnati ta jaddada kudirinta na gudanar da bincike kan harin da aka kai wa shugaban ƙungiyar Ajaero, inda ta ce babban sufeton ‘yan sanda ya bayar da umarnin a gudanar da bincike, kuma an canja kwamishinan ‘yan sandan jihar Imo.

    Gwamnatin ta kuma jaddada cewa, yajin aikin, wanda ya bijirewa umarnin kotu, na nuni da rashin mutunta bangaren shari’a, kuma ya saɓawa ka’idojin kungiyar kwadago a tarihi.

    • Zanga-zangar da 'yan ƙwadago suka yi a sassan Najeriya
    • Ƙarin ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya sun ci alwashi shiga yajin aiki
  9. Isra'ila ta tabbatar da mutuwar wata budurwa da Hamas ta yi garkuwa da ita

    ...

    Asalin hoton, IDF

    Rundunar sojin Isra'ila ta tabbatar da mutuwar wata ƴar Isra'ila mai shekaru 19 da Hamas ta yi garkuwa da ita a ranar 7 ga watan Oktoba.

    An kwatanta matsayin Noa Mariciano a matsayin tamkar sojojin da suka mutu a lokacin kare ƙasa.

    Ba a yi bayani kan musabbabin mutuwar ba, amma rundunar sojin Isra'ila ta ce an sanar da danginta.

    Wani faifan bidiyo da aka yaɗa a intanet a daren jiya ya nuna Marciano inda ta bayyana kanta kuma ta ce ta shafe kwanaki hudu tana tsare.

    • Mutanen da ƙungiyar Hamas ke garkuwa da su tsawon shekaru
    • Kalli jariran Falasɗinawa da ake fargabar za su rasu idan lantarki ta katse a Gaza
  10. 'An sake buɗe hanyar "Salah al-Din" don ficewa zuwa kudancin Gaza'

    ...

    Asalin hoton, ...

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta sake yin kira ga Falasɗinawa da ke arewacin Gaza da su fice zuwa kudu ta hanyar "Salah al-Din" da aka kebe.

    An fara bude hanyar kwashe mutanen ne a ranar 5 ga Nuwamba.

    Dakarun tsaron Isra'ila dai sun shafe makonni suna gaya wa jama'a da su koma kudancin kasar, domin kaucewa fadan da ya fi kamari a arewacin kasar.

    Dangane da sanarwar da aka fitar na baya-bayan nan cewa Isra'ila za ta aiwatar da tsaikon soji na tsawon sa'o'i hudu a kowace rana, rundunar ta shawarci mazauna yankin da su "yi amfani" da wadannan dama a wasu unguwanni don isa hanyar da aka kebe don komawa kudancin ƙasar.

    Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa kimanin mutane 200,000 sun riga sun yi amfani da hanyar Salah al-Din don ƙaura zuwa kudancin Gaza.

    Dubban daruruwan mutane, wadanda ko dai ba sa so ko kuma ba za su iya zuwa kudu ba, sun kasance a arewa.

    • Hamas: Su wane ne shugabanninta da suka fi fice?
    • ‘Lokacin da za mu mutu babu wanda zai sani': Labarai daga Gaza
  11. Tinubu ya gaji ƙasar da tattalin arziƙinta ya durƙushe - Ribadu

    ...

    Asalin hoton, Nuhu Ribadu /Facebook

    Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya ce shugaban Najierya Tinubu ya gaji gwamnati wadda ta talauce, sa'ilin da yake magana kan matsalar kudin da ƙasar ke fama da ita.

    Ribadu, wanda ya amince cewar akwai matsaloli a ɓangaren kuɗi na ƙasar, ya ce duk da waɗannan kalubalen, gwamnatin tarayya ta himmatu wajen tabbatar da ingantaccen tsarin kula da tsaro a kasar.

    Ribadu ya faɗi hakan ne a taron shekara-shekara na shugaban sashen tattara bayanan sirri na 2023 a Abuja, mai taken “Yin amfani da diflomasiya na tsaro da ingantaccen haɗin kan yanki don Inganta tsaron ƙasa,”.

    Ribadu ya jaddada sadaukarwar gwamnati ga tsaron ƙasa.

    Taron ya samu halartar manyan baƙi da suka hada da ministan tsaro, Abubakar Badaru, da babban sakatare Ibrahim Kana, da babban hafsan soji, tare da wasu hafsoshin tsaro.

    • Me Tinubu zai yi da bashin kusan dala biliyan takwas da zai karbo?
    • Me 'yan Najeriya ke cewa game da janye haramcin bizar Dubai?
  12. An gano gawarwakin baƙin haure 16 a gaɓar tekun Mauritaniya

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Hukumomin ƙasar Mauritaniya sun ba da rahoton gano gawarwaki 16 da ake kyautata zaton bakin haure ne a gabar tekun arewacin Lagouera.

    Hakan ya biyo bayan gano gawarwaki 13 da aka samu a cikin kwale-kwale a makon da ya gabata a kusa da birnin Nouadhibou.

    Al'amarin na baya-bayan nan dai ya faru ne sakamakon kwale-kwalen nasu ya ci karo da wasu duwatsu.

    A cikin 'yan kwanakin nan, an samu ƙaruwar yawan mutanen da ke tashi daga makwabciyarta Senegal, da ke yunƙurin isa tsibirin Canary na kasar Spain.

    Tun daga watan Janairu, sama da mutum 23,000 ne suka isa tsibirin Canary na kasar Spain ta jirgin ruwa.

    • ‘Yadda muka maƙale a tsakiyar teku bayan man jirgi ya ƙare’
    • La Palma: Aman wuta ya laƙume gidaje sama da 200 a Spain
  13. Sabbin bayanai a rikicin Isra'ila da Hamas

    Ga sabbin abubuwan da suka faru a rikicin Gaza da Isra'ila.

    • Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce babban asibitin birnin Gaza, Al-Shifa, “ya zama tamkar maƙabarta”, gawarwakin da ke ciki da wajen ginin na ruɓewa.
    • An yi ta gwabza faɗa a kusa da asibitin a ‘yan kwanakin nan, kuma tankokin yaƙi sun kewaye wurin, kamar yadda wata majiya ta shaida wa BBC a Gaza.
    • Sojojin Isra'ila sun sha zargin Hamas da cewa suna da wata cibiyar bayar da umarni a karkashin asibitin Al-Shifa - cibiyar da Hamas dai sun musanta hakan.
    • Akwai damuwa ta musamman kan rayuwar jarira bakwaini da kuma sauran jariran da aka haifa a daidai lokaci, katsewar wutar lantarki ya sa ma’aikatan asibitin ba su iya amfani da kayan aiki irin su kwalaban saka jarire.
    • Dakarun tsaron Isra'ila sun ce suna kan aiwatar da aikin jigilar kwalaben saka jarire zuwa Gaza - amma ba ta bayyana ko za su je asibitin Al-Shifa ba.
    • Kakakin Majalisar Dinkin Duniya ya kuma ce masu ciwon koda 45 da ke buƙatar wankin ƙoda a wurin ba za a iya kula da su ba yadda ya kamata saboda rashin wutar lantarki.
    • Shugaban Amurka Joe Biden ya ce "dole ne Isra'ila ta kare asibitocin Gaza"
  14. Ƴan ƙwadago sun fara yajin aiki a Najeriya

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Manyan ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya, NLC da TUC sun buƙaci mambobinsu da su daina aiki daga ranar Talata, yayin da suke shiga yajin aikin na sai-baba-ta-gani a fadin ƙasar duk kuwa da umarnin da kotu ta bayar na hana su yin hakan.

    Ƙungiyoyin dai na matsa wa shugaban ƙasar Bola Tinubu ne ya dawo da tallafin man fetur din da aka kwashe shekaru ana amfani da shi a baya, wanda ke sanya farashin man fetur yin rahusa.

    Amma gwamnatin ta ce tana la’akari da tabarbarewar tattalin arziƙin ƙasar, tare da shirin karkatar da kudadenta wajen gudanar da ayyukan jin kai.

    Ƙungiyoyin dai na son gwamnati ta ƙara mafi karancin albashin ma'aikata zuwa akalla dalar Amurka 120 daga kusan dala 36, tare da sauya wasu manufofinta na tattalin arziki da ba su yi wa talakawa daɗi ba.

    Shugaban TUC, Festus Osifo ya bayyana cewa yajin aikin zai ci gaba da tafiya har sai an samu kyakkyawan martani daga gwamnati a dukkan matakai.

    Wannan matakin dai ya biyo bayan umarnin dakatar da yajin aikin da wata kotu da ke Abuja ta bayar a baya-bayan nan, koda yake har yanzu babu tabbas kan tsawon lokacin da yajin aikin zai gudana.

    Amma ana sa ran zai shafi manyan ayyuka kamar asibitoci da tashoshin jirgin kasa, da makarantu a ƙasar mafi girman tattalin arzikin Afirka.

    Kungiyoyin dai sun yi barazanar shiga yajin aikin akalla sau uku tun bayan da Tinubu ya hau kan karagar mulki a watan Mayu, amma sai aka yi gaggawar dakatar da su bayan ganawar da suka yi da shugaban, lamarin da ya sanya ayar tambaya kan yanke hukuncin nasu.

    Ana kuma kallon yajin aikin na ranar Talata a matsayin nuna adawa da harin da aka kai wa shugaban ƙwadagon, Joe Ajaero a jihar Imo a makon da ya gabata.

    • Abu bakwai da gwamnatin Najeriya ta cimma da 'yan ƙwadago
    • An fara yajin aikin sai baba ta gani a Najeriya
  15. Yau ne zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasan Laberiya

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    A yau ne za a yi zagaye na biyu na zaɓen shugaban kasa a Laberiya.

    Shugaba mai ci George Weah na neman wa'adin mulki na biyu, inda ake ganin fafatawar za tai zafi tsakaninsa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Joseph Boakai.

    Wakiliyar BBC ta ce shugaba George Weah da abokin takararsa Joseph Buakai mai shekara 71 na kankankan a lokacin zaɓen mai cike da matuƙar zafi a watan da ya gabata.

    Amma babu wanda ya sami kuri'u kashi 50 a zaben tsakanin ƴan takarar biyu.

    Weah na da matuƙar farin jini a kasar ta fuskar kasancewa fitaccen tsohon dan wasan kwallon kafa, lamarin da ya kai shi ga nasara a zaben shekarar 2017.

    • George Weah na neman ƙarin lokaci duk da fitintinun da ke damun Liberia
    • George Weah ya kori macizai a ofishinsa
  16. Sojojin Isra'ila sun zargi Hamas da jefa Isra'ilawa cikin halin ɗimuwa

    Sojojin Isra'ila sun zargi Hamas da jefa Isra'ilawa cikin halin dimuwa da tsananin damuwa, bayan sun ga bidiyon da Hamas ta nuna na wata matashiya 'yar shekara 19 da ke cikin waɗanda ta yi garkuwar da su ranar 7 ga watan Oktoba.

    A bidiyon an nuna Noa Marciano na karanta wani saƙo, daga nan kuma sai suka haska jikinta tamkar gawa, wadda Hamas ta ce hare-hare ta sama da isra'ila ta kai ne ya hallakata.

    Daniel Hagari shi ne mai magana da yawun sojin Isra'ila ya kare matakin kai hare-haren da suke yi kusa da asibitico yana mai cewa akwai gidan kasa karkashin asibitin inda Hamas ke bada umarnin kai hari.

    Babu tabbaci daga sojin Isra'ila kan ko Marciano ta mutu ko ta na raye.

    • Abotar Bayahude da Bafalasɗine ta kawo zaman lafiya Gaza
    • Sojojin Isra’ila sun amince su kwashe jarirai daga babban asibitin Gaza
  17. Amurka da Birtaniya sun ce dole Isra'ila ta kare asibitocin Gaza

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙasashen Amurka da Birtaniya sun ƙara yin kira ga Isra'ila ta kare asibitoci da farar hula a daidai lokacin da ta ke gwabza yaƙi ta ƙasa a Gaza.

    Shugaba Biden ya shaida wa 'yan jarida a fadar shugaban ƙasar Amurka, ya na fatan za a samu sassauci a asibitin Al-Shifa, wanda shi ne mafi girma a Gaza da sojin Isra'ila suka yi wa kawanya.

    Shi ma Firaiministan Birtaniya Rishi Sunak, ya ce fararen hula na mutuwa a kowanne minti.

    Ya ƙara da cewa ya kamata a dauki duk matakin da ya dace domin kare farar hula da ba su aikata komai ba, ciki har da kare asibitoci, da daina tsattsauran hukunci a Gaɓar Yamma da kogin Jordan.

    Sunak ya kuma jaddada batun barin agaji ya shiga Gaza. Sai dai dukkan shugabannin biyu ba su yi kira kan Isra'ila ta dakatar da buɗe wuta ba.

    • Asibitocin da yakin Isra'ila da Hamas ya ritsa da su a Gaza
    • 'Na rasa kusan duk ƴan'uwana a rikicin Isra'ila da Gaza'
  18. Assalamu alaikum

    Maraba da sake haɗuwa a shafin labaran BBC Hausa, wanda zai kawo rahotonni kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa daga sassan duniya.

    Aisha Babangida ce ke fatan kasancewa da ku.