Mu kwana lafiya
Nan muka zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Mu kasance gobe da safe idan Allah ya kai mu don samun wasu sababbi.
Ahmad Tijjani Bawage da Mukhtar Bawa ke cewa sai da safenku.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
A'isha Babangida, Haruna Kakangi, Mukhtar Adamu Bawa and Ahmad Tijjani Bawage
Nan muka zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Mu kasance gobe da safe idan Allah ya kai mu don samun wasu sababbi.
Ahmad Tijjani Bawage da Mukhtar Bawa ke cewa sai da safenku.
An zargi wakilin Kevin McCarthy da cin zarafin wani ɗan jam'iyyar Republican yayin da majalisar dokokin Amurka ke shirin kaɗa kuri'a kan kudirin kashe kuɗi na gajeren lokaci.
Wakilin Tim Burchett daga ƙasar Tennessee da ba ta kusa da teku, ya ce tsohon kakakin majalisar ya “yi masa gula a baya yayin da yake tsaye a zauren majalisar.
"Shi mutum ne mai cin zarafi da dala miliyan 17 da cikakken bayani kan tsaro," in ji Mista Burchett, ɗan jam'iyyar Republican mai ra'ayin gurguzu.
Mista McCarthy ya shaida wa manema labarai cewa haɗa kashi da suka yi ya faru ne bisa tsausayi.
Ofishin Mista McCarthy bai mayar da buƙatar yin martani ba.

Asalin hoton, Getty Images
Babban Bankin Najeriya ya ce tsoffin takardun naira da aka sake wa fasali, za su ci gaba da zama halastattun kudi har bayan wa'adin farko da hukumomin kasar suka sanya na 31 ga watan Disamban 2023.
Ya ce an dauki matakin ne bisa dacewa da tsarin hada-hadar kudi na kasashen duniya da kuma hana sake maimaita abin da ya faru a baya.
Wata sanarwa da daraktan sadarwa na Babban Bankin, Isa AbdulMumin ya fitar, ta ce CBN yana aiki da hukumomin da ke da jibi don ganin an soke hukuncin kotu da ya ba da umarni kan karewar wa'adin takardun kudin.
Babban Bankin ya ce yana sanar da al'ummar kasar game da kudurinsa na kara wa'adin tsoffin takardun da ake sake na naira 200 da 500 da kuma 1000 har zuwa abin da hali ya yi.
Ya kuma umarci dukkan rassansa a fadin Najeriya su ci gaba da bayarwa da kuma karbar duk takardun kudin Najeriya, tsofaffi da kuma sababbin da ake sake fasalinsu.
Haka zalika ya yi kira ga al'ummar kasar su ma su ci gaba da karbar dukkan takardun tsoffi da sabbin naira don hada-hadar kudi ta yau da kullum.
A watan Oktoban 2022 ne, Babban Bankin Najeriyar ya bullo da tsarin sake fasalin takardar naira 200 da 500 da 1000, kuma ya ba da wa'adin dakatar da karbar tsoffin takardun da aka sauya, a matsayin halastattun kudi.
Sai dai takaddama ta ɓarke, inda wasu gwamnonin jihohi suka shigar da kara gaban kotu, wadda ta bai wa gwamnatin tarayya da babban bankin kasar rashin gaskiya, sannan ta umarci a ci gaba da amfani da tsoffin takardun nairar har zuwa karshen watan Disamban bana.

Asalin hoton, AFP
Sojojin Mali sun kwace iko da Kidal, wani muhimmin gari da ke arewacin ƙasar, wanda ƴan tawayen suka riƙe tsawon shekara goma.
Garin Kidal dai ya kasance muhimmiyar tunga, musamman ma ga ƴan tawayen Tuareg da suka kasance cikin tsakiyar rikicin siyasa da kuma rashin tsaro da aka ɗauki tsawon lokaci ana fama da shi.
Sojojin, waɗanda aka ruwaito cewa suna samun goyon baya daga sojojin hayar Rasha na Wagner, sun ɗauki tsawon kwanaki uku suna artabu da ƴan tawayen da nufin kwato garin.
Shugaban gwamnatin mulkin sojin ƙasar, Kanal Assimi Goita, ya ce ba su kammala aikinsu ba.
Ya wallafa wani sako a shafin X, inda yake cewa zimmarsa shi ne ganin dukkan suna iko da dukkan yankunan ƙasar.
Sojojin sun buƙaci fararen hula a garin Kidal da su kwantar da hankulansu.
Gwamnatin tarayya a Mali ta rasa iko da yawancin arewacin ƙasar sama da shekara goma da suka wuce bayan da ƴan tawayen Tuareg suka nemi a ba su ƙasarsu.
Ɓangaren tsaron ƙasar ya ƙara taɓarɓarewa ne da ayyukan masu iƙirarin jihadi.
Hakan ya janyo samun juyin mulki har guda uku tun 2012.
A yau Talata ne aka shafe wunin farko na yajin aikin da ƙungiyar ƙwadagon a Najeriya ta umarci ƴaƴanta su yi don nuna rashin amincewa da cin zarafin da take zargin an yi wa shugabanta a jihar Imo.
Sai dai rahotanni na nuna cewa yajin aikin bai samu karɓuwa ba a wasu sassan ƙasar, idan aka kwatanta da yajin aikin da ƙungiyar ta saba yi a baya.
Ku lasta ƙasa don sauraron rahoton Ibrahim Isa.

Asalin hoton, Dauda Lawal/Facebook
Gwamnatin Zamfara ta ayyana dokar ta-ɓaci a ɓangaren ilimi a faɗin jihar.
A wani jawabi da ya yi wa ƴan jihar ta kafofin watsa labarai a yau Talata, gwamna Dauda Lawal ya ce watsi da ɓangaren ilimi da aka yi a jihar yana shafar dukkan matakai, kama daga makarantun firamare har zuwa jami'o'i.
Ya ce tsarin ilimin jihar yana da muhalli mara kyau na koyo da rashin ingantattun malamai.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta ce ayyana dokar ta-ɓaci kan ɓangaren ilimi a jihar da gwamnan ya yi, na cikin alkawuran yaƙin neman zaɓensa na ganin kyautatuwar ilimi a faɗin jihar.
Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnatin jihar na da zimmar yin garanbawul ga ɓangaren ilimi, wanda ya durkushe gabaki ɗaya.
Wani karamin jirgi mai farfela ya yi saɓi zarce a kan titin da yake sauka cikin filin jirgin Texas, kafin ya je ya yi ciki da wata mota da take wucewa a kan wani titi da ke kusa.
Bidiyon da wani mutum da ke tsaye a gefe Jack Schneider ya ɗauka, ya nuna lokacin da jirgin ya yi karo da shingen filin jirgin a lokacin da ya yi saukar gaggawa.
"Lokacin da na ga yadda jirgin saman ya sauko da gudu, na san ba zai samu lokacin da zai tsaya ba," Schneider ya faɗa wa wata tashar labarai a yankin WFAA-TV ranar Asabar.
"A bayyane take karara yana gudu sosai, tayoyinsa suna hayaki."
An kai direban motar asibiti bayan ya ji 'yan raunuka, amma mutum biyu da ke cikin jirgin ba su ji ko kwarzane ba.
Hukumar kula da Sufurin Jiragen Sama ta Tarayya a Amurka na gudanar da bincike don gano sanadin wannan hatsari.

Asalin hoton, Kukoyi Busola/X
Uwargidan Shugaban Najeriya Remi Tinubu ta bayar da tallafin naira 250,000 ga kowacce daga cikin mata da marayun da sojoji suka mutu suka bari su 1,709.
Wata sanarwa mai taimakawa uwargidan shugaban ƙasar ta harkar yaɗa labarai Busola Kukoyi ta fitar, ta ce tallafin yana cikin ajandar gwamnatinsu ta sabunta kyakkyawan fata.
"Karkashin tsarinmu na sabunta kyakkyawan fata ga ƴan Najeriya, mun zo nan ne don tallafawa matan da suka rasa mazajensu 1,709, za mu bai wa kowacce naira 250,000," in ji Remi.
"Wannan zai ba ku damar ƙara jari ko kuma fara sana'o'in da kuke so domin kula da iyalanku".
Waɗanda suka ci gajiyar tallafin sun fito ne daga sassa daban-daban na ƙasar.
Uwargidan shugaban ƙasar ta ce bai kamata sadaukarwa da sojojin suka yi wajen tsaron ƙasar ya tafi a banza ba, ba tare da an samarwa iyalansu walwalar da ta kamata ba.

Asalin hoton, Kukoyi Busola/X

Asalin hoton, Getty Images
Fitaccen mawakin Najeriya Mr Eazi ya shaida wa wani gidan rediyon ƙasar cewa bai ɓoye bikin aurensa ba saɓanin maganganun da jama'a ke yi.
"Wa ya gaya maka cewa an yi bikin aurena a asirce? Je ka kalli bidiyon wakata za ka sami amsar tambayarka. Mun naɗi bidiyon a birnin Venice," kamar yadda ya shaida wa Naija FM a Legas.
Mista Eazi ya auri Temi Otedola, ɗiyar hamshakin attajiri ɗan kasuwa Femi Otedola.
Ma'auratan sun yi soyayya na wasu shekaru kafin a yi baikon aurensu a shekarar 2022, inda suka yi aure bayan watanni.
Tun da farko mun ba da rahoton cewa an binne mutane 179 a wani babban rami a cikin asibitin birnin Gaza mafi girma Al-Shifa, a cewar daraktan asibitin.
Yanzu mun tattauna da Dr Adnan al-Bursh daga asibitin, wanda ya ce an binne gawawwaki 200 a harabar asibitin.
Aikin binne mutanen ya ɗauki tawagar likitocin asibitin kusan 100 sa'o'i shida kafin binne gawawwaki 200.
"Mun fara aikin da karfe 08:30 na safe kuma mun gama da misalin karfe 3;00 na rana," in ji shi.
Shugaban sashen tiyatar kashi, Al-Bursh, ya ce “an bar gawawwaki tsawon kwanaki har suka fara zagwanyewa” don haka likitocin ba su da wani zaɓi illa tona babban rami.
Ya ce "ba su iya buɗe tagogin gine-ginen ba saboda warin da ke fitowa daga bayan asibitin" - ya ƙara da cewa kusan gawawwaki 120 ne a wajen, kafin a binne su.
Wasu 80 kuma suna cikin dakin ajiyar gawawwaki, in ji shi.
Mata da ƙananan yara ne suka fi yawa cikin waɗanda suka mutu.
Ƙungiyar agaji ta Red Cross ta gargaɗi likitocin da su bar su saboda fargabar ci gaba da ruwan makamai da ake yi, "amma mun ɗauki alhakin [binne su]," in ji Al-Bursh.

Asalin hoton, ATIKU ABUBAKAR/FACEBOOK
Jagoran adawa a Najeriya ya yi kira ga jam'iyyun adawa a ƙasar su haɗa karfi da karfe, don tsamo dimokraɗiyyar ƙasar daga komawa zuwa mai bin tsarin jam'iyya ɗaya.
Ya kuma ja hankali a kan buƙatar yin hattara game da tsunduma Najeriya, cikin tsarin mulkin kama-karya na jam'iyya ɗaya.
Wata sanarwa da Paul Ibe, mashawarcin ɗan takarar shugaban ƙasar a zaɓen watan Fabrairun 2023 kan harkar yada labarai ya fitar ranar Talata, ta ce Atiku ya yi kiran ne lokacin da ya karɓi bakuncin shugabannin majalisar tuntuɓa tsakanin jam'iyyu ta Najeriya (IPAC).
Tsohon mataimakin shugaban Najeriyar, shi ne ya zo na biyu a zaɓen shugaban ƙasa da aka yi a farkon wannan shekara, wanda Bola Tinubu ya kayar da shi.
A cewarsa, aikin kare mutuncin dimokraɗiyya a ƙasar, ba kawai na mutum ɗaya ba ne.
Ya nunar da cewa hakikanin gaskiya tsarin dimokraɗiyyarmu cikin sauri na komawa zuwa tsarin jam'iyya ɗaya, "kuma tabbas kun sani cewa idan tsarin jam'iyya ɗaya ne da mu, to kawai mu mance da maganar dimokraɗiyya".
Atiku ya ƙara da cewa “Dukkanmu mun ga yadda jam'iyyar APC ke daɗa mayar da Najeriya zuwa ƙasar mulkin kama-karya mai jam'iyya ɗaya. Idan ba mu zo mun haɗu don kalubalantar abin da jam'iyya mai mulki take ƙoƙarin kafawa ba, dimokraɗiyyarmu za ta sha wahala, kuma sakamakon haka zai shafi hatta zuri'ar da ba a ma haifa ba”.

Asalin hoton, ATIKU ABUBAKAR
Atiku Abubakar ya kuma soki lamirin hukumar zabe ta INEC saboda abin da ya kira gudanar da "zabe mafi lalacewa a kasar".
“Kwanan nan ma a zaben da aka gudanar cikin jihohin kasar uku, INEC ta sake nuna rashin mutunta tsare-tsaren dimokradiyyarmu da ta saba.
“Duk muna iya ganin yadda INEC ta ayyana wani sakamako a jihar Kogi, inda jimillar adadin kuri'un aka kada suka zarce yawan kuri'un aka tantance a wata karamar hukuma.
“Ba za mu samu ingantacciyar dimokradiyya a yanayin da abin da INEC kawai ta sani shi ne tabbatar da nasarar jam'iyya mai mulki ta kowanne hali."
Birtaniya da Amurka sun sanar da sake kakaba wa Hamas jerin takunkumai zagaye na uku tun bayan harin da ƙungiyar ta kai wa Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba.
Baitulmalin Amurka wanda shi ne ma'aikatar harkokin kuɗin ƙasar na cewa takunkuman za su shafi "manyan kusoshin Hamas da kuma tsare-tsaren da Iran ke samar da tallafi ga Hamas da kuma ƙungiyar Islamic Jihad ta Falasɗinawa" - wadda ita ma wata ƙungiya ce mai gwagwarmaya da makamai a Zirin Gaza.
Kusoshin na fuskantar haramcin tafiye-tafiye da rufe kadarorinsu da kuma hana cinikayyar makamai.
Wasu daga cikin mutanen da takunkuman suka shafa akwai wakilin Islamic Jihad a ƙasar Iran, Naseer Abu Sharif da wani ɗan canji mazaunin Lebanon, wanda ake zargi da gudanar da harkokin tura kuɗi tsakanin Hamas da ƙasar Iran.

Asalin hoton, Nigeria Presidency
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi alhinin mutuwar fitaccen ɗan wasan kwaikwayo Usman Baba Pategi wanda aka fi sani da 'Samanja Mazan Fama'.
Ya rasu ne a daren Asabar bayan fama da jinya mai tsawo.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce Shugaban ya kwatanta mutuwar da abu mai ciwo, inda ya ce Samanja ya ba da gudummawa a ƙasar ta hanyoyi daban-daban a tsawon rayuwarsa.
Ya ce faɗakarwa da marigayin ya riƙa yi ta hanyar wasannin kwaikwayo, sun koyar da matasan ƙasar da dama abubuwa masu kyau.
Shugaba Tinubu ya buƙaci iyalan Pategi, da al'ummar jihohin Niger da Kwara, da masarautar Pategi, da masana'antar harkar nishaɗi da su ɗauki dangana.

Asalin hoton, Al-Mansur Gusau
'Ya'yan kungiyar kwadago ta NLC da takwararta ta TUC sun yi wa ginin majalisun dokokin na tarayya tsinke da tsakar ranar Talata, inda suka garkame kofar shiga ginin, a wani yunkuri na tursasa yajin aikin da suka kira a fadin Najeriya.
'Yan kwadagon sun tafi yajin aikin ne daga daren Talata sanadin wata takaddama tsakaninsu da gwamnatin Najeriya.
Rahotanni sun ce tun daga misalin karfe 11:45 ne, masu yajin aikin suka hana ma'aikatan majalisa da baki masu zuwa, shiga ko fita daga harabar ginin.
Sai dai jaridar Vanguard ta ruwaito cewa 'yan majalisar da suka riga suka shiga zaurukan majalisar biyu sun ci gaba da gudanar da ayyukansu, kamar yadda suka saba.

Asalin hoton, Getty Images
Dangin mutanen da Hamas ke garkuwa da su, sun fara wata zanga-zanga ta hanyar gudanar da maci na tsawon kwana biyar, inda suke kiran a kubutar da makusantan nasu.
Isra'ila ta ce 'yan bindigan Hamas sun sace fiye da mutum 240 a lokacin harin 7 ga watan Oktoba, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 1,200.
Bayan tsawon sama da wata daya, dangi da magoya bayan mutanen da ake garkuwa da su a yau Talata sun fara maci na tsawon kilomita 70 daga birnin Tel Aviv zuwa ofishin Firaminista da ke birnin Kudus.
"Muna maci ne don zuwa ga firaminista mu fada masa cikin murya mai amo cewa muna bukatar a kubutar da su, su dawo gida yanzu," daya daga cikin mutanen da ke tattakin ya fada wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Jim kadan fara macin, rundunar sojin Isra'ila ta tabbatar cewa an kashe daya daga cikin mutanen da ake garkuwa da su - wadda sojar Isra'ila ce 'yar shekara 19.

Asalin hoton, Reuters
Ambaliyar ruwa a Somaliya ta bar mazauna yankin ba su da gidaje da kuma karancin abinci.
Kimanin mutane miliyan 1.6 ne ake tunanin ambaliyar ruwan ya shafa a Somaliya.
Shugaban Somaliya, Hassan Sheikh Mohamud, ya ce: "ambaliyar ruwan ya tilastawa mutane da dama barin muhallansu kuma gidaje da dukiyoyi sun lalace kuma jama'a na fama da yunwa, wannan ita ce matsalarmu a yanzu, abin da muke mai da hankali a kai."
Shugaban ya kuma nuna damuwarsa kan yadda ake ƙara samun barkewar cututtuka kamar zazzabin cizon sauro da kwalara.