'Faɗa ya rincaɓe' a kusa da asibitin Al Quds a birnin Gaza

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Mukhtar Adamu Bawa, Ahmad Tijjani Bawage and Abdullahi Bello Diginza

  1. Manchester United za ta farfaɗo - Ten Hag

  2. An jibge jami’an tsaro a sassan jihar Kogi gabanin zaɓen gwamna

    A ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba, al'ummar jihar Kogi za su fita rumfunan zaɓe don zaɓar sabon gwamna.

    Gwamna Yahaya Bello na jihar na kammala wa'adin mulkinsa na shekara takwas, inda ƴan takara 18 ke ƙoƙarin gadarsa.

    Gabanin zaɓen, an jibge jami'an tsaro da dama don tabbatar da an gudanar da zaɓen lami lafiya.

    ...
    ...

    Asalin hoton, ...

    ...

    Asalin hoton, ...

    ...
    ..
  3. Ƴan Laberiya na shirin shiga zaɓe zagaye na biyu ranar Talata

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Al'ummar Laberiya za su kaɗa kuri'a a ranar Talata a zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasa tsakanin Shugaba George Weah da tsohon mataimakin shugaban ƙasar Joseph Boakai, sakamakon babu wanda ya samu kashi 50 na kuri'un da aka kaɗa a zagayen farko domin samun nasara.

    Tsohon ɗan wasan kwallon kafa Weah ya jagoranci zagayen farko, inda ya samu kashi 43.83 cikin 100 na kuri'u, sannan Boakai ya samu kashi 43.44 cikin 100.

    Tazarar da ke tsakaninsu, da rashin samun ɗan takara na uku mai karfi, na nufin zuwa zagaye na biyu na zaɓen wanda shima za a fafata sosai, in ji Maja Bovcon, babban manazarci a Afirka a kamfanin leken asiri na Verisk Maplecroft.

    "Nasarar karshe za ta kasance ga duk wanda ya samu ƙuri'u mafi yawa," in ji Bovcon.

    • George Weah na neman ƙarin lokaci duk da fitintinun da ke damun Liberia
    • Gasar Kofin Duniya : Shugaban Liberia ya harzuka 'yan kasarsa
  4. Macron ya yi kira da a dakatar da yaƙi don ayyukan jin ƙai a Gaza

    ...

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya yi kira da a dakatar da yaƙi don ayyukan jin ƙai ga yakin Gaza.

    Macro yayi wannan kira ne yayin wani taron ƙasashen duniya da aka shirya a birnin Paris

    Ƙasashen G7 wanda suka haɗa da Faransa su ma sun yi wannan kiran a jiya, a wani taron ministocin harkokin kasashe waje a Tokyo.

    Macron ya kuma ce taimakon da Faransa ke bai wa Falasɗinawa zai ƙaru sau biyar a shekara mai zuwa, daga Yuro miliyan 20 a bana zuwa Yuro miliyan 100 a shekarar 2024.

    • Tsagaita wuta zai ba Hamas damar sake shiri don kai hare-hare - Anthony Blinken
    • Ƴan Isra'ila na rige-rigen mallakar bindiga bayan harin Hamas
  5. Hungary za ta tura dakaru 200 zuwa Chadi

    Majalisar dokokin Hungary ta amince da tura sojoji 200 zuwa ƙasar Chadi, domin inganta zaman lafiya da tsaro, da kuma yaƙi da ta'addanci.

    Chadi, ƙasar da ke tsakiyar Afrika na fuskantar barazanar tsaro daga ƙungiyoyin masu aikata laifi.

    A cewar ma'aikatar tsaron kasar, tura dakaru daga farkon 2024 zuwa Disamban 2025, zai kuma rage matsin lamba na kwararar bakin haure zuwa Turai.

    A halin da ake ciki, majalisar ministocin kasar Chadi ranar Laraba, ta amince da wata doka da za ta yi afuwa ga mutanen da ke da hannu a zanga-zangar adawa da gwamnati ranar 20 ga Oktoban 2022.

    Mutane akalla 50 ne suka mutu lokacin da ɗaruruwan masu zanga-zangar nuna adawa da gwamnatin Chadi suka yi arangama da jami’an tsaro.

    Masu zanga-zangar dai na adawa ne da tsawaita wa'adin gwamnatin riƙon kwarya da shekaru biyu, inda suka zargi shugaban rikon kwaryar Janar Mahamat Idris Deby da neman ci gaba da zaman dafa'an a kan karagar mulki.

    • Kawuna sun rabu kan korar da sojojin Nijar ke wa ƙasashen duniya
    • An kashe mutum 50 a zanga-zangar Chadi
  6. Guinea ta sa tukwicin dubban daloli domin kama Kanal Pivi

    ...

    Asalin hoton, Président Mamadi Doumbouya/Facebook

    Gwamnatin ƙasar Guinea ta sanya tukwicin saifa miliyan 500 ta Guinea kwatankwacin dalar Amurka 57,340 ga duk wanda ya samar da bayanai da za su kai ga kama Kanal Claude Pivi, wanda ya tsere daga gidan yari ranar 4 ga watan Nuwamba.

    Pivi, tsohon shugaban tsaron fadar shugaban ƙasar, ya kasance jigo a shari’ar da ake ci gaba da yi dangane da kisan kiyashin da aka yi a filin wasa na watan Satumban 2009.

    Ministan shari'an kasar, Charles Wright ya jaddada bukatar gaggawa ta kama Pivi don ci gaba da shari'a da kuma tsaron rayukan waɗanda lamarin ya shafa.

    Wright ya tabbatar wa jama'a cewa za a kare waɗanda suka ba da bayanan da za su taimaka wajen kama shi.

    Wasu mutane ɗauke da makamai sun kai hari gidan yarin na Conakry, inda suka kubutar da Pivi da Claude Pivi da Blaise Goumou da kuma wani mutum daban.

    An dai sake kama mutanen uku da suka tsere, yayin da kuma ake ci gaba da neman Pivi.

    Tsohon shugaban mulkin sojan kasar Camara, Kanal Goumou da Kanal Pivi na cikin mutane fiye da 12 da ake tuhuma da laifin kisan gillar da aka yi a filin wasa cikin shekara ta 2009 wanda ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 150, tare da yi wa mata sama da 100 fyade.

    Kyaftin Camara ya musanta ba da umarnin kisan

    • Shugaban da ya fi kowa daɗewa a mulki na neman a sake zaɓen sa
    • Mamady Doumbouya: Tarihin sojan da ya jagoranci ƙwace mulki a Guinea
  7. Hotunan yadda jama'a daga arewacin Gaza ke ficewa zuwa kudu

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce a yau ta sake bude hanyar Salah al-Din Kreider na tsawon sa'o'i shida da zai bai wa Falasɗinawa a arewacin Gaza damar ficewa zuwa kudu.

    A jiya, kimanin mutum 50,000 ne suka yi nasarar ficewa daga arewa ta wannan hanya, in ji hukumar jin ƙai ta Majalisar Dinkin Duniya, adadi mafi yawa a cikin kwana guda.

    Ga hotunan yadda jama'a daga arewacin Gazan suke ficewa zuwa kudu.

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    ...

    Asalin hoton, Reuters

  8. Labarai da dumi-dumi, 'Yan kwadago sun rufe titin zuwa filin jirgin sama na Abuja

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni daga filin jirgin saman Abuja na cewa kungiyoyin kwadago sun rufe titin da ke zuwa filin jirgin saman da safiyar yau, Alhamis.

    Da safiyar nan ne, mutane suka rika wallafa bidiyo na yadda motoci da masu ababen hawa suka tsaya jingum-jingum a kan titin. A daya daga cikin bidiyon da aka wallafa a shafin X, ana iya ganin wata motar dakon kaya daga nesa an gindaya ta a tsakiyar titi.

    Haka zalika, an jiyo kade-kade na tashi, yayin da ake iya hango wasu mutane sanye da tufafi iri daya a kan motocin da ke nesa.

    Sakataren tsare-tsare na kungiyar NLC, Kwamared Nasir Kabir ya shaida wa BBC cewa mambobinsu sun rufe titin shiga filin jirgin saman na Abuja da kuma hana duk wani jirgin sama da ke da niyyar tashi zuwa jihar Imo.

    Haka kuma wata sanarwa da babban sakataren NLC, Kwamared Emmanuel Ugboaja ya fitar ta ce matakin ya hadar da filin jirgin sama na Lagos.

    Ta kuma ambaci matakin da 'yan kwadagon ke dauka a dambarwarsu da gwamnatin jihar Imo.

    A ranar Laraba dai 8 ga watan Nuwamban 2023, kungiyoyin kwadago na NLC da TUC suka fara wani yajin aiki, wanda suka sanar da rufe duk wasu harkokin samar da lantarki da na sufurin jiragen sama a jihar ta Imo.

    Matakin na zuwa ne kwanaki kalilan bayan zargin da kungiyar NLC ta yi wa gwamnan jihar Hope Uzodinma da hadin bakin 'yan sanda wajen kama shi tare da dukan sa. 'Yan kwadagon daga bisani sun nuna hoton shugaban kungiyar NLC, Joe Ajaero da idonsa na dama a kumbure.

    • Ƙarin ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya sun ci alwashi shiga yajin aiki
    • Abu bakwai da gwamnatin Najeriya ta cimma da 'yan ƙwadago
  9. Isra'ila ta ce sun fafata tsawon sa'a goma kafin kwace 'tungar' Hamas

    Israel Soldiers

    Asalin hoton, IDF

    Bayanan hoto, A still from footage of the battle, released by the IDF

    Dakarun tsaron Isra'ila sun sanar a shafin sada zumunta na X cewa sojojinta sun ƙwace wani tungar Hamas da ke Jabalia a arewacin Gaza.

    Sun ce sun kwashe sa’o’i 10 suna fafata wa, inda suka kakkabe ‘yan ta’addan Hamas da ƙwace makamai da dama da kuma lalata hanyoyin ƙarƙashin ƙasa na ‘yan ta’adda.

    Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da kamfanin dillancin labaran Falasɗinawa Wafa ya bayar da rahoton cewa, jiragen saman Isra'ila sun yi ruwan bama-bamai tare da lalata wani gida a sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia tare da wasu mutane da suka makale a karkashin ɓaraguzan ginin.

    Ya kuma ce mutane da dama sun jikkata a birnin Gaza.

    BBC ba ta iya tantance rahotannin ba.

    Sojojin Isra'ila a baya sun ce Hamas ta rasa iko da arewacin Gaza kuma dakarunta sun kutsa cikin birnin Gaza.

    • 'Ayyukan Isra'ila ka iya jefa Gabas ta Tsakiya cikin haɗari'
    • Abin da shugaban Hamas ya shaida wa BBC game da rikicin Gaza
  10. Tsohon gwamnan CBN, Emefiele ya koma gida bayan shafe kwana151 a tsare

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    A jiya ne tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele, ya isa gidansa da ke Abuja, bayan da wata babbar kotun Abuja ta bayar da belinsa.

    Ya shafe kwanaki 151 a hannun jami’an tsaro.

    Babbar kotun tarayyar da ke zamanta a Maitama ta bayar da umarnin a sake shi daga gidan yari, duk da rashin amincewar da babban lauyan gwamnatin tarayya, AGF, da hukumar yaki da cin-hanci da rashawa EFCC suka yi.

    Kotun, a hukuncin da mai shari’a Olukayode Adeniyi ya yanke, ta bayar da umarnin a saki tsohon gwamnan babban bankin ga lauyoyinsa, duk da cewa ta umarce shi da ya miƙa dukkan takardun tafiye-tafiyen sa na kasashen waje.

    • Tinubu ya dakatar da gwamnan CBN Emefiele
    • Zanga-zangar nuna adawa da gwamnan Babban Bankin Najeriya
  11. Kurman da ya ɓata ya haɗu da danginsa, bayan rahoton BBC

    ...

    Asalin hoton, ...

    Murna da sowa da dariya har kunne sun mamaye dangin wani kurma mai suna Adamu, wanda ya ɓata tsawon shekara ɗaya, amma aka gano shi kuma aka mayar da shi gida a kauyen Dan-Dausa, shiyyar Maturgi ta yankin karamar hukumar Talatar Mafara a jihar Zamfara.

    Ƴan'uwan kurman sun gano shi ne kwana guda bayan rahoton da BBC ta yi a kan ɓatansa.

    Kurman dai ya samu kansa ne ƙwatsam a garin Bida na jihar Neja da ke tsakiyar Najeriya, bayan motar da yake ciki tare da abokan tafiyarsa, ta yi gaba ta bar shi, kimanin shekara ɗaya da ta wuce.

    A dalilin neman 'yan'uwan wannan kurma kuma, an yi dacen gano iyayen wani kurman shi kuma daga jihar Kebbi, wanda ya kwashe shekara fiye da goma da ɓacewa.

    Ku saurari rahoton Abdulsalam Ibrahim Ahmed

    Bayanan sautiLatsa hoton sama don sauraron rahoton
  12. Sojojin Isra'ila sun ce sun lalata hanyoyin ƙarƙashin ƙasa na Hamas 130

    ...

    Asalin hoton, IDF

    Dakarun tsaron Isra'ila sun ce sun lalata hanyoyin ƙarƙashin ƙasa na Hamas 130 tun bayan fara kai farmakin ƙasa a Gaza.

    A cikin wata sanarwa da dakarun Isra'ilar suka fitar sun ce "A halin yanzu dakarun yaƙin ƙasar suna aiki don fallasa tare da lalata kayayyakin 'yan ta'adda na Hamas a Gaza, ciki har da hanyoyin ƙarƙashin ƙasa."

    "Ruwa da kuma ajiyar iskar oxygen da aka gano a cikin hanyoyin na nuni da shirye-shiryen Hamas na tsawaita zama a karkashin kasa." in ji sanarwar.

    A ranar Laraba ne rundunar sojin ta ce ta lalata wata hanyar ƙarƙashin ƙasa ta Hamas da ke kusa da wata makaranta da Hukumar Agaji ta Falasɗinu ke ɗaukar nauyinta a yankin Beit Hanoun da ke arewacin Gaza.

    Rundunar ta kuma wallafa wani bidiyo da ake zargin ya nuna ɓarnar da aka yi a hanyoyin ƙarƙashin ƙasa da ke kusa da makarantar.

    Isra'ila ta fara kai hare-hare a Gaza bayan harin Hamas a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutum 1,400 tare da yin garkuwa da sama da 200.

    Rundunar ta kuma tabbatar da mutuwar wani soja guda wanda ya kai adadin sojojin da aka kashe a harin ta ƙasa zuwa 31.

    Ma'aikatar lafiya ta Hamas ta ce adadin mutanen da aka kashe a Gaza ya karu zuwa 10,569 tun lokacin da Isra'ila ta fara kai hare-haren ramuwar gayya.

    • Mummunan harin ba-zata da Hamas ta kaddamar a kan Isra'ila
    • Rayuwa a Gaza: 'Babu wurin fakewa a ruwan makamai masu linzami'
  13. Sabbin hotuna daga Gaza bayan wasu ƙarin hare-hare cikin dare

    Ga wasu sabbin hotuna daga Gaza bayan wasu karin hare-hare cikin dare a birnin Gaza da kuma sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia da ke arewacin Gaza.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai farmaki kan wani sansanin sojin Hamas da ke arewacin kasar cikin dare.

    Ma'aikatar harkokin cikin gidan Falasɗianawa ta Hamas ta ce mutum 6 ne suka mutu cikin dare a lokacin da aka kai harin bam a wani gida a Khan Younis, wasu da dama kuma sun jikkata a hare-haren.

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

  14. Ƙasashen duniya za su yi taro a Faransa don kai kayan agaji Gaza

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wakilai daga ƙasashe 80 da kungiyoyin ƙasashen duniya za su gana a birnin Paris nan gaba a yau domin tattauna hanyoyin kai agajin jin kai ga mutanen Gaza.

    Taron wanda gwamnatin Faransa ta dauki nauyin shiryawa, ya mayar da hankali kan maido da muhimman kayayyaki kamar ruwa da man fetur da wutar lantarki tare da tabbatar da cewa agaji ya isa ga waɗanda ake so ba ƙungiyar Hamas ba.

    Tawagogin ƙasashen Larabawa, da hukumar Falasɗinawa da Masar da wasu shugabannin Tarayyar Turai za su halarci taron.

    Amma ba za a wakilta Isra'ila ba kuma Amurka tana tura tawagar masu ƙaramin karfi ne kawai.

    Jami'an Faransa sun ce za a sanar da Isra'ila abubuwan da ke faruwa.

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce a makon da ya gabata ana buƙatar wasu dala biliyan 1.2 don biyan buƙatun mutanen Gaza da gaɓar yamma da Kogin Jordan.

    • Za a shigar da kayan agaji zuwa Gaza
    • Yadda sabon yaƙi ya ɓarke tsakanin Isra’ila da Falasɗinawa
  15. Gwamnatin soji a Myanmar ta rasa iko da yankuna da ke kan iyakarta da China

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin soji a Myanmar ta rasa iko da yankuna da dama da ke kan iyakarta da China a cikin 'yan kwanaki, sakamakon hare-haren haɗin-gwiwa na kungiyoyin mayaƙan kabilun yankin da suka ci karfin sojojinta da hana tsallake iyaka.

    Gwamnati ta rinƙa mayar da martani ta hare-haren sama da harba makaman atilary, lamarin da ya tilastawa dubban mutane barin matsugunansu.

    Sai dai duk da hakan ta gaza wajen ƙwato yankunanta.

    Sojojin da ke mulki sun fuskanci babban koma-baya, irinsa mafi muni tun kwace mulki a watan Fabarairun 2021.

    Kuma wannan shi ne karo na farko da mayaƙan jihar Shan suka fito ƙarara suna nuna aniyarsu ta kifar da gwamnatin soji, domin dawo da ƙasar kan turbar dimokuraɗiyya.

    • Shin duniya ta manta da Musulman Rohingya ne?
    • BBC ta bankado yadda sojojin Myanmar suka azabtar tare da kashe mutane da dama
  16. Hukumar kare haƙƙin bil'adama ta MDD ya zargi Isra'ila da Hamas da laifukan yaƙi

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban hukumar kare haƙƙin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya, Volker Turk, ya ce Isra'ila da Hamas dukkaninsu sun aikata laifukan yaƙi a Gaza.

    A lokacin wata tattaunawa da shi daga iyakar Rafah da ta haɗa Masar da Gaza, Turk ya ce a cikin laifukan yaƙin da Hamas ta aikata harda cigaba da riƙe mutanen da tayi garkuwa dasu.

    Sai dai ya ce ita kuma laifukan yaƙin Isra'ila a kullum ƙaruwa suke ciki harda abin da ya kira hukunta dukkanin Falasdinawa fararan-hula, da tilastawa mutane gudun hijira ba bisa ƙa'ida ba.

    Ya ce a ziyarar da ya kai yankin mutane da dama sun nuna matuƙar damuwarsu kan yadda laifin wasu mutane ya shafi dukkanin al'ummarsu.

    • Tsagaita wuta zai ba Hamas damar sake shiri don kai hare-hare - Anthony Blinken
    • Rikicin Isra'ila da Gaza: Mene ne asalin sa?
  17. Assalamu alaikum

    Masu bin mu a wanna shafi muna muku maraba da shigowa shafin kai-tsaye na BBC Hausa.

    Aisha Babangida ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Sai ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.