'Faɗa ya rincaɓe' a kusa da asibitin Al Quds a birnin Gaza
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Rahoto kai-tsaye
A'isha Babangida, Mukhtar Adamu Bawa, Ahmad Tijjani Bawage and Abdullahi Bello Diginza
Rufewa
Masu bin mu a wannan shafi nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonin abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabin labarai.
A madadin sauran abokan aiki Abdullahi bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.
Sojojin Isra'ila sun ce bidiyon 'yan ƙasarta da ake riƙe da su alamun suna raye ne
Asalin hoton, EPA
Dangane da bidiyon da muka ce ƙungiyar Falasdinawa ta Islamic Jihad ta fitar na 'yan Isra'ila da ke hannunta - wata uwa mai shekara 70 da ƙaramin yaro guda.
Mai magana da yawun sojin Isra'ila, Rear Admiral Daniel Hagari, ya ce bidiyon ya wata alama ce da ke nuna cewa mutanen na raye.
"Dole mu rungume su, tare da iyalansu," in ji shi, ya ƙara da cewa: "dama ba ta kuɓuce mana ba, kuma ba za ta kuɓuce mana ba dangane da kuɓutar da mutanen da aka yi garkuwa da su".
Bai dai yi karin bayani kan sakin mutanen ba, yana mai cewa masu garkuwar na amfani da "tunani na ta'addanci".
"Idan muka samu cikakken bayani, za mu sanar da danginsu," in ji shi.
Magoya bayan Man United za su yi zanga-zanga a Old Trafford
Ramaphosa ya umarci sojojin Afirka ta Kudu su hana haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba
Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa, ya ba sojoji sama da dubu uku umarnin yaƙi da haƙar ma'adinai ba bisa ka'ida ba.
Sojojin za su yi aiki kafaɗa da kafaɗa da yan sanda tsawon wata shida masu zuwa.
Haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba ta zamar wa Afirka ta Kudu babbar matsala.
Masu haƙar ma'adinai da dama sun mutu a ƙarƙashin ƙasa.
Ba kasafai ake sa Rundunar Tsaro ta (SANDF) aiki ba, amma a baya-baya nan an yi amfani da su wajen yaƙi da ƙungiyoyi 'yan daba.
'Yan tawayen Colombia sun sako mahaifin Luis Díaz
Majalisar Wakilan Madagascar ta buƙaci a dakatar da zaɓen shugaban ƙasar
Kakakin majalisar wakilan Madagascar ya buƙaci a dakatar da zaɓen shugaban ƙasa da za a gudanar a mako mai zuwa sakamakon zanga-zangar yan adawa.
Mai fafutikar ƙoƙarin warware rikicin siyasar ƙasar, Christine Razanamahasoa ta ce yanayin da ƙasar ta ke ciki ba zai bayar da damar gudanar da sahihin zaɓe a ranar 16 ga watan Nuwamba ba.
Madagascar ta faɗa yanayin rashin tabbas sakamakon rikicin siyasa tsakanin shugaba Andry Rajoelina da tsohon shugaban ƙasar Marc Ravalomanana
'Isra'ila za ta fara tsagaita wuta na sa'o'i huɗu a kowace rana a Gaza'
Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock
Fadar Gwamnatin Amurka ta ce Isra'ila za ta fara aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta na sa'o'i huɗu a kowace rana a yankunan arewacin Gaza, kamar yadda mai magana da yawun fadar White House, John Kirby ya shaida wa manema labarai.
Ya ce za a fitar da sanarwar sa'o'i uku kafin lokacin.
"Kuma dakarun Isra'ila sun shaida mana cewa ba za kai hare-hare a waɗanan yankuna ba a daidai lokacin tsagaita wutar, kuma matakin zai fara a yau," in ji shi.
Tun da farko sojojin Isra'ila sun ce ''suna ƙoƙarin tsagaita wuta domin bayar da dama shigar da kayan agaji ga fararen zuwa Gaza", tare da tabbatar da cewa "babu tsagaita wuta".
Ƙungiyar 'Islamic Jihad' ta saki bidiyon 'yan Isra'ila da take garkuwa da su
Ƙungiyar Falasɗinawa ta Islamic Jihad a Gaza, ta saki wani bidiyo na 'yan Isra'ila biyu - wata tsohuwa da ƙaramin yaro - da ke hannunta.
BBC ba za ta nuna bidiyon ba - wanda ya haura mintuna uku - to amma za mu iya bayyana abin da ke cikinsa.
Fursunonin yaƙi da waɗanda aka yi garkuwa da na da kariya ƙarƙashin dokokin jin-ƙai na duniya, don haka BBC ba za ta yaɗa wani abu da watakila aka naɗa bisa tursasawa.
Bidiyon ya fara nuna mata a kan keken marasa lafiya, inda aka boye abin da ke bayanta, sannan sai na ƙaramin yaron, wanda ke nuna alamar ba wuri ɗaya aka ɗauke shi ba.
Alamu sun nuna cewa duka bidiyoyin an yayyanka su.
Sun ce ana waɗanda ke tsare da su ɗin na kula da su, sannan sun soki firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.
Gwamnatin Najeriya ta soki zanga-zangar NLC da TUC a filin jirgin saman Abuja
Asalin hoton, Facebook/Festus Keyamo
Ministan harkokin sufurin jiragen sama a Najeriya Festus Keyamo ya soki zanga-zangar gamayyar ƙungiyoyin ƙwadagon Najeriya NLC ta TUC da suka gudanar a filin jirgin sama na Abuja.
Da safiyar ranar Alhamis ne, mutane suka riƙa wallafa bidiyo na yadda motoci da masu ababen hawa suka tsaya jingum-jingum a kan titin.
Matakin na zuwa ne kwanaki kalilan bayan zargin da kungiyar NLC ta yi wa gwamnan jihar Hope Uzodinma da hadin bakin 'yan sanda wajen kama shi tare da dukan sa. 'Yan kwadagon daga bisani sun nuna hoton shugaban kungiyar NLC, Joe Ajaero da idonsa na dama a kumbure.
Yayin da yake jawabi a wurin bitar ma'aikatan sufurin jiragen sama a birnin Warri na jihar Delta da ke kudu maso kudancin ƙasar, Mista Keyamo ya soki matakin ƙungoyin ƙwadogon, yana mai cewa me ya sa ƙungiyoyin suka zaɓi gudanar da zanga-zanga a sashen ma'aikatar sufurin jiragen saman.
An fara rarraba kayan aikin zaɓen gwamna a jihar Kogi
Hukumar Zaɓe Mai zaman kanta a Najeriya, INEC ta fara raba kayayyakin aikin zaɓe a jihar Kogi gabanin za ben gwamnan jihar da za a gudanar ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba.
Jihar Kogi - wadda ke tsakiyar Najeriya - na ɗaya daga cikin jihohi ukun da za a gudanar da zaɓen a cikin wannan makon.
Wakiliyar BBC da ke jihar ta ce tuni jami'an hukumar zaɓen suka fara rarraba kayyakin zuwa ƙananan hukumomi daban-daban da ke faɗin jihar.
Haka kuma ta ce an girke jami'an tsaro masu tarin yawa a sassan birnin Lokojo domin tabbatar da tsaro ga kayyakin zaɓen.
'Yan takara 18 ke takara a zaɓen kujerar gwamnan, sai dai ana ganin fafatawar za ta fi zafi ne tsakanin manyan 'yan takara uku, Ododo Ahmed Usman na jam'iyyar APC da Sanata Dino Melaye na jam'iyyar PDP, sai kuma Murtala Yakubu Ajaka na jam'iyyar SDP.
Dattawan Arewa sun ce za su sasanta Dangote da AbdusSamad BUA
'Faɗa ya rincaɓe' a kusa da asibitin Al Quds a birnin Gaza
Asalin hoton, Reuters
Faɗa na ci gaba da rincaɓewa a birnin Gaza, kuma kamar yadda muka ruwaito tun da farko, ɗafa na ci gaba da tsananta a kusa da asibitin Al Quds yayin tankokin yaƙi ke tunƙarar asibitin.
Hanyoyin sadarwa sun yi wahalar gaske, to amma na samu zantawa da wani mutum da safiyar nan, wanda ya ce faɗa ya tsananta a yankin.
Sojojin Isra'ila sun kai wa gine-gine da dama hari a yunƙurinsu na mayar da martani kan harin ranar 7 ga watan Oktoba da Hamas ta kai Isra'ila.
An kwashe kwanaki ana kai hare-hare ta sama a yankin. A yanzu ana kai hare-hare wurin daga cikin teku da ta ƙasa.
Hukumomi na neman mutanen da suka sare bishiya mai tsarki a Ghana
Asalin hoton, Ghana Police
Bayanan hoto, Ghana troopers
Hukumomi a Ghana suna neman mutanen da suka sare wata bishiya mai tsarki da ya shafe tsawon shekara 300.
Mazauna garin Feyiase a kudancin Ghana sun ce wasu mutane ne suka sare bishiyar da adduna cikin duhun daren Talata.
Bishiyar goron tana da dumbin tarihi da kuma muhimmancin bauta a Masarautar Ashanti.
Tarihihi ya ce bishiyar ta tsiro ne a wurin da bokan farko na Masarautar Ashanti Komfo Anokye ya tofar da tukar goro.
An kuma yi imani cewa goron bishiyar yana da dumbin daraja kuma har yana iya warkar da cutuka da tarwatsa mugun nufi.
Majalisar wakilan Najeriya ta yi ƙarin haske kan batun jirgin ruwan alfarma na shugaban ƙasa
Ƴan majalisar wakilan Najeriya sun yi ƙarin haske kan kwamitin da aka kafa domin gano ainihin bayani game da wani jirgin ruwa na alfarma na shugaban ƙasa da aka saka a cikin kwarya-kwaryan kasafin kudi.
Akwai bayanai masu cin karo da juna game da ko an riga an karɓo jirgin ruwan tun kafin a saka batun cikin kasafin kudin.
Honorabul Kabiru Alassan Rurum dan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Rano da Bunkure a jihar Kano ya yi wa BBC ƙarin bayani.
Bayanan sautiLatsa hoton sama don sauraron tattanawa
Dubban mutane na samun mafaka a asibitin Quds
Asalin hoton, EPA
Bayanan hoto, Falasɗinawa sun zauna mafaka a asibitin Al Quds lokacin da Isra'ila ke luguan wuta kan birnin Gaza - an ɗauki hoton a ranar 31 ga watan Oktoba
Sojojin Isra'ila sun kewaye wani ɓangare na birnin Gaza kuma suna ci gaba da dannawa zuwa yankin da asibitin Al Quds yake, inda mutane sama da 14,000 ke zaman mafaka.
Akwai kuma kusan mutum 100 da ake yi wa jinya a cikin asibitin.
A ranar Laraba asibitin ya ce ba zai iya matsar da mutanen ba, saboda babu hanyoyi masu kyau da za a iya bi.
Harin jirgi maras matuki ya faɗa kan birnin Eilat na Isra'ila - Sojoji
Dakarun tsaron Isra'ila sun ce wani harin jirgin maras matuki ya faɗa kan ginin fararen hula a birnin Eilat da ke kudancin ƙasar.
Sojojin sun ce suna bincike kan harin jirgin, da abin da ya faru.
Chadi ta amince da yin afuwa ga masu zanga-zangar kin jinin gwamnati a bara
Asalin hoton, AFP
Gwamnatin mulkin soji a Chadi ta amince da yin afuwa ga masu zanga-zangar kin jinin gwamnati a bara, wadda ta lakume gomman rayuka.
An kashe mutane akalla 50 da jikkata sama da 300 lokacin da ɗaruruwan masu kin jin gwamnati suka yi artabu da jami'an tsaro a ranar 20 ga watan Oktoban 2022, a cewar ma'aikatar shari'ar ƙasar.
Ƙungiyar kare hakkin ɗan adam ta Amnesty International ta kiyasta cewa alkaluman waɗanda suka mutu zai kai 100, tare da kama kusan 600.
Masu zanga-zangar sun nuna adawa ga ƙarin wa'adin shekara biyu kafin miƙa mulki, inda suka zargi shugaban gwamnatin mulkin sojin ƙasar Janar Mahamat Idriss Déby da son ci gaba da zama kan mulki.
Wasu sojoji 15 ne suka ɗora Janar Mahamatvkan karagar mulki a 2021, bayan mutuwar mahaifinsa Idriss Déby wanda ya mulki ƙasar ta Chadi tsawon shekara 30.
Kasafin kuɗin Tinubu da ya kunshi kuɗin sayen motocin alfarma
Asalin hoton, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu/Facebook
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya rattaɓa hannu kan wani ƙarin kasafin kuɗi dala biliyan 2.8 mai cike da ce-ce-ku-ce, da ya haɗa da kuɗaɗen sayen sabbin motocin da harbin bindiga ba ya ratsa su na shugaban da matarsa.
Kasafin kuɗin da ‘yan majalisar suka amince da shi, ya kuma ware kuɗaɗen sayen jirgin ruwa na shugaban ƙasa, da motocin aiki na matarsa, da kuma gyaran fadar shugaban.
Da farko dai, Tinubu ya gabatar da shirin kashe kuɗin a matsayin wata hanya ta magance “matsalolin gaggawa” kamar tsaro da halin matsin rayuwa da ƴan ƙasar ke ciki.
Masu suka dai na cewa kashe kuɗaɗen kan irin abubuwan da aka lissafo bai da ma'ana kuma bai zama dole ba idan aka yi la’akari da matsalolin tattalin arziki da ‘yan Najeriya ke fuskanta, da suka haɗa da hauhawar farashin kayayyaki, da matsalolin kuɗi, da rashin tsaro, da kuma satar ɗanyen mai da sauransu.
Shugaba Tinubu ya buƙaci a yi hakuri, bisa la’akari da sauye-sauyen da gwamnatinsa ke yi.
Labarai da dumi-dumi, 'Adadin waɗanda suka mutu a Gaza ya haura 10,812'
Ma’aikatar lafiya ta Hamas a Gaza ta ce adadin waɗanda suka mutu a Gaza ya haura 10,812 da suka hada da ƙananan yara 4,412 tun bayan harin da aka kai a Isra’ila a ranar 7 ga Oktoba.
Jimillar da ma’aikatar ta bayar a baya ya tsaya a 10,569
Isra'ila ta yi jayayya da daidaiton adadin, amma Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi imanin alƙaluman na da sahihanci.
Mayakan 'yan tawayen CAR biyar sun miƙa wuya ga dakarun MDD
Asalin hoton, United Nations
Bayanan hoto, ...
Mayakan 'yan tawaye 5 na ƙungiyar Coalition of Patriots for Change CPC sun miƙa wuya ga tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya, Minusca da ke lardin Haute-Kotto da ke gabashin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, a ranar 9 ga watan Nuwamba kamar yadda jaridar Le Democrate ta ruwaito.
Wannan ya nuna koma baya ga ƙungiyar CPC, bayan ficewar wata kungiya mai dauke da makamai ta fice daga kawancen 'yan tawayen tare da bayyana aniyar yin aiki da gwamnati.
"A cewar mai magana da yawun Minusca, wadannan mayaka sun gabatar da makamansu ga sojojin Majalisar Dinkin Duniya kafin a mika su ga tawagar DDR [Disarmament, Demobilization and Reintegration] a Bria," in ji Le Democrate.
Kakakin na Minusca ya bayyana fatansa na cewa ƙarin mayaƙan 'yan tawaye za su kwance ɗamara a cikin kwanaki masu zuwa a daidai lokacin da jam'iyyar CPC ke fama da matsalolin kudi.
A shekarar 2021 ne jam'iyyar CPC ta ƙaddamar da farmaki kan gwamnatin CAR, amma an tura ta zuwa arewa zuwa Chadi da gabas, kusa da kan iyakar Sudan ta Kudu.
Boko Haram: Me zai biyo bayan miƙa wuyan da ƴan ƙungiyar suke yi a Borno?
Ambazonia: Yadda 'yan tawayen Kamaru suka 'kashe sarki da kona ƙauyuka' a Najeriya