Majalisar dattijan Najeriya na son a tsagaita wuta a Gaza

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida and Mukhtar Adamu Bawa

  1. Wata ɗaya bayan harin Hamas, har yanzu 'yan Isra'ila na jin tsananin raɗaɗi, Daga Yolande Knell wakiliyar BBC a birnin Kudus

    Israel

    Asalin hoton, Reuters

    Rana ce da ta ruguza jin da Isra'ila take yi, cewa ba za a iya yin galaba a kanta ba, da kuma karfin sojinta. Rana ce da ta yi zagon kasa ga tsaron Isra'ila, ta yadda duk wnai dan kasar sai da ya ji a jikinsa.

    Sai dai da farko, ba haka aka yi zaton lamarin zai kasance ba.

    Lokacin da na ga "fargarwar zuwa mugun abu" da sanyin safiya a kan wayata, inda ake gargadi game da wata roka da aka harbo daga Gaza, ba mu dauka girman harin ya kai haka ba.

    Na aikawa abokan aikina sakonni - wasunsu suna can sun halartar bukukuwan karshe na ranakun hutun Yahudawa - don fada musu cewa ni na nufi ofis.

    Jim kadan kuma, sai na samu kaina ina fadi-tashin yadda zan fahimci girman abin da nake fada lokacin da nake bayar da rahoto, hatta a lokacin da kalmomi suke fita daga bakina.

    Matsananciyar gobarar da makami mai linzami ya haddasa, wadda ta sanya ni rugawa ciki da wajen ofis don neman mafaka, sai ga shi ashe wani abu ne kawai na labewa da sabara don wasu jerin hare-hare da ba a taba ganin irinsu ba masu sarkakiya da aka shafe tsawon lokaci ana shiryawa.

    Mun ga hotunan mayakan Hamas masu tayar da hankali a kan babura suna shigowa ta kafar da suka ruguza a jikin katangar Gaza, da kuma masu saukar laima a kudancin Isra'ila, inda suka far wa sansanonin sojoji masu tsananin kariya, a lokacin da suke daukan kansu bidiyo a lambunan Kibbutz da suka aukawa.

    Bayan tsawon sa'o'i ne kuma sai masu zuwa taron shagali suka rika kiran gidajen talbijin na Isra'ila suna bayyana irin kisan kiyashin da aka tafka a lokacin da suka buya daga 'yan bindigan a bikin raye-raye na Nova da ya yi kaurin suna. Mazaunan yankin cikin firgici sun rika yada bidiyo na zugar Falasdinawa dauke da makamai a kan titunan Sderot.

    An tabbatar cewa ita ce rana mafi muni a tarihin shekara 75 na Isra'ila, inda cikin wani tsararren shiri aka rika yi wa mutane kisan gilla na rashin imani. Daga wasu da ke yankin Kibbutz a kusa da Gaza, hotuna daga bisani sun bayyana inda suka nuna kisan kiyashi na rashin imani da aka yi daukacin iyalai. Duka-duka, an kiyasta cewa mutum 1,400 ne aka kashe a wannan al'amari.

    Israel

    Asalin hoton, Reuters

    Muhimmancin lokacin da aka kai harin yana da tasiri, don kuwa ya zo ne daidai kusan lokacin da aka cika shekara 50 bayan wani harin shammata da Masar da Siriya suka kai a rana mafi tsarki ta shekarar Yahudawa, Yom Kippur, lamarin da ya haddasa wani gagarumin yaki a yankin.

    Tsananin radadi da razanar da 'yan Isra'ila suka shiga, har yanzu shaidar na nan, kuma na ga cikakken wannan al'amari ranar 8 ga watan Oktoba da na je Ashkelon.

    • Tawagar ƙwararru ta MDD ta buƙaci Isra’ila ta tsagaita buɗe wuta a Gaza
    • Mutumin da ya rasa duka ƴaƴansa huɗu a hari ɗaya da Isra'ila ta kai
  2. Ƙarin ƴan ƙasashen waje masu fasfo za su bar Gaza a yau

    ...

    Asalin hoton, ...

    A yau ne dai wasu ƴan kasashen ketare da suka haɗa da wasu mutane biyu daga Birtaniya za su tashi daga Gaza ta hanyar Rafah zuwa Masar.

    Kimanin masu riƙe da fasfo na kasashen waje 600 ciki har da Jamus da Romania da Faransa da Philippines da Ukraine da Kanada da kuma Moldova ne ke cikin sabon jerin sunayen da hukumomin da ke da alhakin tsallakawa ta buga na waɗanda za su fice daga Gaza.

    Tun da farko dai an sake buɗe mashigar Rafah ga wasu masu fasfo na kasashen waje tare da Falasɗinawan da suka jikkata a ranar 1 ga Nuwamba, bayan rufeta sama da makonni uku.

    An sake rufe mashigar na ɗan gajeren lokaci a ranar Asabar amma kuma aka sake buɗe ta a ranar Litinin.

    • Bayani kan hanya ɗaya tilo da Falasɗinawa za su iya fita daga Gaza
    • Me ya sa mashigar Rafah a Gaza ke da muhimmanci
  3. Japan ta ce ƙasashen G7 za su ci gaba da taimakawa Ukraine a yaƙinta da Rasha

    ...

    Asalin hoton, iStock

    Bayanan hoto, ...

    Japan ta ce taimakon da ƙasashen G7 ke bai wa Ukraine a yaƙinta da Rasha ba zai fuskanci nakasu ba, sakamakon mummunan rikici a yankin gabas ta tsakiya.

    Ministocin ƙasashen bakwai mafiya karfin tattalin arzki a duniya, da Tarayyar Turai za su yi taro a birnin Tokyo wanda zai ƙunshi tattaunawa da takwaransu na Ukraine ta Intanet.

    Ministan harkokin ƙasashen ƙetare a Japan, Yoko Kamikawa, kafin taron ya shaidawa BBC cewa manufar G7 na cigaba da kakaɓawa Rasha takunkumi bata sauya ba ko kaɗan.

    Tun soma rikicin Isra'ila da Hamas sau guda G7 ta fitar da sanarwa a kan yaƙin.

    • Me ke faruwa tsakanin Ukraine da Rasha bayan ɓarkewar faɗa a Gaza?
    • Taron G7: Mene ne taron, kuma me ya sa ake yin sa a Cornwall?
  4. Gwanan Oyo ya yi wa ma'aikata ƙarin naira 25,000 a kan albashinsu

    ...

    Asalin hoton, @SEYIAMAKINDE TWITTER

    Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya bayyana cewa ma’aikatan jihar da ‘yan fansho za su rika karbar tallafin kudi na naira 25,000 da kuma N15,000 duk wata na tsawon watanni shida har sai an cimma matsaya kan sabon mafi ƙarancin albashi

    Ya kuma jaddada muhimmancin ma’aikata da al’ummar jihar wajen haɗa hannu da gwamnatin jihar domin bunƙasa tattalin arzikin jihar na tsawon lokaci.

    Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga ma’aikatan a ofishin gwamna, Sakatariya, Agodi a Ibadan.

    Ya yi nuni da cewa duk da cewa gwamnatinsa za ta so ta yi aikin da za a riƙa tunawa da su shekaru da dama bayan ya bar mulki, za ta ci gaba da kula da jin daɗin ma’aikatanta.

    Za a biya kudaden tallafin ne na tsawon watanni shida masu zuwa, wanda hakan zai sa a samu karin Naira biliyan 2.2 a kan lissafin albashin ma’aikata na wata-wata.

    Gwamnan ya cimma yarjejeniya da shugabannin ƙwadago domin aiwatar da wannan shiri.

    • Ma'aikatan ƙananan hukumomi a Najeriya na neman a ƙara musu albashi da kashi 300
    • A kwana uku kacal albashina ke karewa - Ma'aikacin gwamnati a Abuja
  5. Isra'ila ta ce ta ƙwace tungar Hamas da ke arewacin Zirin Gaza

    Dakarun tsaron Isra'ila sun ba da sabbin bayanai suna me cewa;

    • Dakarun sun ƙwace iko da tungar kungiyar Hamas da ke arewacin zirin Gaza, sun kuma gano makamai masu linzami, da kayan leƙen asiri.
    • Dakarun sojin ruwan Isra'ila sun kai hari kan mayaƙan Hamas da suka haɗa da "wurare ɗauke da kadarori na fasaha"
    • Sojojin Isra'ila sun gano mayaƙan Hamas a wani gini da ke kusa da asibitin Al-Quds a birnin Gaza a wani harin da suka kai ta sama da ke nuni da kasancewar wani ma'ajiyar makaman Hamas a wani yanki na farar hula", in ji Isra'ila.

    A matsayi tunatarwa, ma;aikatar lafiya ta Hamas a Gaza ta ce sama da mutum 10,000 ne aka kashe tun lokacin da Isra'ila ta fara ƙaddamar da hari a ranar 7 ga watan Oktoba, bayan hare-haren Hamas.

    • Takaddamar Isra'ila da shugaban MDD saboda kalamansa kan harin Hamas
    • Mutanen da ƙungiyar Hamas ke garkuwa da su tsawon shekaru
  6. 'Za mu samar da sansanin ba da kulawar lafiya ta gaggawa a Gaza'

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Hukumomin Haɗaddiyar Daular Larabawa sun ce za su samar da sansanin bada kulawar lafiya ta gaggawa a Gaza.

    Babu dai wasu bayanai masu karfi da ke nuna ko shirin na hadin gwiwa ne da Isra'ila.

    Jakadiyar Daular a Majalisar dinkin duniya, Lana Nusseibeh ta ce an soma kai kayayyakin da ake buƙata daga birnin Abu Dhabi zuwa Al Arish na Masar, daga nan kuma a aika su cikin Gaza.

    Ta ƙara da cewa a yanzu Hadaddiyar Daular Larabawa za ta bai wa yara Falasɗinawa dubu daya da ke buƙatar kulawar gaggawa tare da iyayensu mafaka.

    • Sabon harin Isra'ila ya kashe fararen hula fiye da 30 a Gaza
    • Hanyoyin sadarwa sun katse a Gaza yayin da Isra'ila ta tsananta luguden wuta
  7. Netanyahu ya ce Isra'ila za ta karɓe ikon tsaro a Gaza bayan yaƙi

    ...

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, ...

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce yana sa ran za su karɓe ikon tsaro a Gaza da zaran sun kammala kakaɓe Hamas.

    A wani jawabi da ya gabatar ta talabiji, Netanyahu ya ce matakin zai kasance na dindindin.

    Sanan Ya ce da Isra'ila ke kula da harkokin tsaro a Gaza, da yanzu ba a samu yaɗuwar ta'addanci ba.

    Netanyahu ya ƙara da cewa za a cigaba da ɗan tsahirtawa kamar na sa'a guda zuwa ɗan lokaci domin bada damar shigar da kayan agaji Gaza.

    Netanyahu ya kuma jadadda cewa babu wani batun tsagaita wuta har sai Hamas ta saki mutanensu da take rike da su, yana mai cewa batun ya dakatar ganganci ne da ka iya lalata kokarinsu.

    • Rikicin Isra'ila da Gaza: Mene ne asalin sa?
    • Tsagaita wuta zai ba Hamas damar sake shiri don kai hare-hare - Anthony Blinken
  8. Assalamu alaikum

    Masu bin mu a wanna shafi muna muku maraba da shigowa shafin kai-tsaye na BBC Hausa.

    Aisha Babangida ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Sai ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.