Majalisar dattijan Najeriya na son a tsagaita wuta a Gaza
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Rahoto kai-tsaye
A'isha Babangida and Mukhtar Adamu Bawa
Amurka na adawa da ƙudurin Isra'ila na yin zaman dirshan a Gaza
Asalin hoton, Getty Images
Amurka ta ce tana adawa da "sake mamaye" Gaza da Isra'ila ke shirin yi, kuma dole ne yankin ya ci gaba da zama yanki na Falasɗinawa.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Vedant Patel ya ce dole ne Falasdinawa su kasance a sahun gaba wajen yanke shawara game da yankin.
Bayanin ya biyo bayan ikirarin da Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya yi cewa Isra'ila za ta dauki nauyin tsaro gaba kacokan a Gaza na "wani lokaci da ba a kayyade ba" bayan kawo karshen yakin.
Mista Netanyahu bai bayyana ko hakan zai kunshi sojojin Isra'ila su ci gaba da zama a cikin yankin ko kuma za su tabbatar tsaron ne daga waje ba.
Kotun ɗaukaka ƙara ta ce Lalong ne ya lashe zaɓen sanata a Filato
Asalin hoton, X/@SIMONLALONG
Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta soke cancantar jam'iyyar PDP da ɗan takararta na sanata a mazaɓar majalisar dattawa ta Filato ta kudu, Napoleon Bali bisa zargin su da ƙin bin umarnin kotu.
Sa'ilin da take karanta hukunci, mai shari'a Elfreda William-Dawodu ta bayyana ƙuri'un da aka kaɗa wa PDP zaɓen sanatan Filato ta kudu a matsayin wofi, sannan ta bayyana tsohon gwamnan jihar ta Filato, Simon Lalong a matsayin zaɓaɓɓen sanata daga yankin.
Lalong, wanda ya yi takarar sanata a ƙarƙashin jam'iyyar APC, shi ne ya zo na biyu kamar yadda hukumar zaɓe ta INEC ta bayyana a lokacin zaɓen na watan Fabarairun 2023.
Mai shari'ar ta ce PDP ba ta cancanci shiga zaɓen ba kasancewar ta ƙi yin biyayya ga umurnin Babbar Kotun Filato wadda ta buƙace ta da ta gudanar da zaɓen shugabannin jam'iyyar na mazaɓu da ƙananan hukumomi da kuma na jiha kamar yadda doka ta tsara.
A shekarar 2022 ne kotun ta umarci PDP da gudanar da zaɓen shugabanninta bisa doka, sai dai jam'iyyar ba ta yi hakan ba.
Yanzu haka da Simon Lalong shi ne ministan ƙwadago a ƙarƙashin gwamnatin shugaban ƙasar, Bola Ahmed Tinubu.
Labarai da dumi-dumi, Sojojin Isra'ila sun kutsa tsakiyar Birnin Gaza - Netanyahu
Asalin hoton, Getty Images
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya ce yanzu haka dakarun ƙasar suna a tsakiyar Birnin Gaza.
A tattaunawa da manema labaru, Netanyahu ya ce "Mun yi wa Birnin Gaza ƙawanya, muna gudanar da aiki a cikinsa."
Firaministan ya ce babu batun tsagaita wuta ko kai wa mutanen Gaza man fetur har sai an saki mutanen da Hamas ke garkuwa da su.
Ya kuma yi kira ga mazauna Gaza da su koma kudancin yankin.
Tun farko ministan tsaron Isra'ila, Yoav Gallant ya ce "Sojojin sun ɓullo ne ta arewa da kuma ta kudu, inda suka dira a cikin birnin ta ƙasa da ta sama da kuma ta ruwa," kamar yadda Gallant ya shaida wa manema labaru.
Ya ƙara da cewa "Suna kutsawa ne a cikin motocin sulke da tankokin yaƙi, bisa manufa ɗaya - wato gano mayaƙan Hamas, da maɓuyarsu, da kwamandojinsu, da kuma ɗakunansu na isar da saƙonni."
An kashe sama da mutum 10,300 a Gaza - Hamas
Ma'aikatar lafiya da ke ƙarƙashin ikon Hamas ta ce ya zuwa yanzu an kashe sama da mutum 10,328 a Gaza, ciki har da yara sama da 4,100, tun bayan da Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare a yankin.
An samu ɗoriyar mutum 300 da aka kashe a alƙaluman da hukumar ta fitar a jiya.
Wasu na ɗora ayar tambaya a kan alƙaluman na ma'aikatar lafiyar da ke Gaza, to amma Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce tana da yaƙinin cewa alƙaluman daidai ne.
Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare a Gaza ne bayan da Hamas ta kashe kimanin mutum 1,400 a wani hari da ta kai cikin Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoban da ya gabata.
Ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya za su tsunduma yajin aikin gama-gari
Asalin hoton, NLC
Jagorancin ƙungiyoyin ƴan ƙwadago a Najeriya, NLC da TUC sun bayyana aniyarsu ta tsunduma yajin aikin gama-gari a faɗin Najeriya daga ranar Talata 14, ga watan Nuwamban 2023.
Ƙungiyoyin sun cimma wannan matsaya ce a taron da suka gudanar yau Talata a Abuja bayan wata tattaunawa da suka gudanar.
Ƙungiyoyin sun bayyana cewa tuni suka fara tuntuɓar mambobinsu a faɗin ƙasar domin shirya wa yajin aikin na makon gobe.
A tattaunawarsa da BBC, sakatareen tsare-tsare na ƙungiyar ƙwadagon, kwamared Nasir Kabir ya ce za su shiga yajin aikin ne kasancewar gwamnatin tarayyara Najeriya ba ta nuna aniyar cika alƙawurran da ta ɗaukar wa ƙungiyar ba.
A farkon watan Oktoba ne ƙungiyoyin ƙwadagon da gwamnatin Najeriya suka tattauna tare da samun matsaya domin kauce wa yajin aikin da ƙungiyoyin suka ƙuduri aniyar shiga a wancan lokaci.
Sai dai daga baya ƙungiyar NLC ta nuna rashin jin daɗin ta kan abin da ta kira rashin wani yunƙuri daga gwamnati na cika alƙawurran da ta ɗauka.
Haka nan kamun da ƴan sanda suka yi wa shugaban na NLC, Joe Ajaero a makon da ya gabata ya haifar da ƙarin rashin jituwa tsakanin ɓangarorin biyu.
Tuni dai NLC ta gabatar da wasu buƙatun da ta buƙaci a cika mata matuƙar ana son hana ta shiga yajin aikin da ta ayyana.
Isra'ila na tunawa da mutanen da harin Hamas ya ritsa da su ranar 7 ga watan Oktoba
An gudanar da tarukan nuna juyayi a faɗin Isra'ila don tunawa da ranar da aka cika wata ɗaya tun bayan da Hamas ta kaddamar da hari daga Zirin Gaza.
Latsa wannan bidiyo don ganin yadda aka yi taron juyayin a Tel Aviv, babban birnin Isra'ila da kuma birnin Kudus.
Bayanan bidiyo, Latsa sama don kallon bidiyon
Aiki ya tsaya cak a gomman asibitocin Gaza - WHO
Aiki ya tsaya cak a sama da asibitoci goma da ke Gaza, a cewar wani likita daga Hukumar Lafiya ta Duniya.
Dr Ahmed Al-Mandhari, darektan WHO a gabashin tekun Bahar Rum, ya ce kusan asibitoci 15 cikin 35 a Gaza sun daina aiki.
Ya ce sun daina aiki ne saboda hare-hare daga Isra'ila da kuma rashin man fetur.
"Sauran asibitocin...suna aiki na ɗan wani lokaci," ya faɗa wa BBC.
Ya ce a cikin kwanaki biyu da suka gabata, asibitoci da yawa sun rufe sakamakon rashin man fetur.
Barayi sun ritsa minista da bindiga a Afirka ta Kudu
Asalin hoton, South Africa government
Ministar sufuri ta Afirka ta Kudu ta bayyana yadda aka ritsa ta da bakin bindiga, aka yi mata fashi bayan abin hawanta ya tsaya a babban titi lokacin da take canza fasasshiyar taya.
Sindisiwe Chikunga ta fada wa wani kwamitin majalisar dokoki cewa daya daga cikin mutanen da suka tare ta da ke sanye da fuskar bad-da-kama ya ritsa ta da bindiga a lokacin balahirar da safiyar Litinin..
Ta ce sace mata kwamfutocin tafi-da-gidanka da wayar salula da makaman masu tsaron lafiyarta.
Afirka ta Kudu tsawon lokaci tana fuskantar yawan laifuka ciki har da satar mota da satar mutane don neman fansa da fizge.
Sai dai ba abu ne da aka saba gani ba, a yi wa ministan gwamnati da ke tafiya da masu tsaron lafiya dauke da bindiga, fashi a ababen hawansu.
Sun "ritsa ni da bindiga a ka, kuma suka umarce ni da na fito", in ji Sindisiwe Chikunga.
Ta kara da cewa sun nemi ta ba su kudi, amma ta ce musu ba ta kudi a jikinta. Daga nan sai suka binciki motar, inda suka yi awon gaba da duk abin da suka samu.
Yayin da suke ci gaba da cinna mata bindigogi, 'yan fashin sun kuma yi kokarin karbe wa ministar zobenta amma sai ta fada musu shi ne kawai abin da ya rage mata a tsakaninta da mijinta da ya riga mu gidan gaskiya. "Kuma ina matukar ganin kimarsa".
Kididdigar baya-bayan nan ta shekara ta nuna cewa kusan mutum miliyan daya da dubu dari uku ne suka ce an raba su da dukiyarsu a kasar.
Majalisar dattijan Najeriya na son a tsagaita wuta a Gaza
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, ...
Majalisar dattijan Najerya ta buƙaci gwamnatin tarayyar ƙasar ta haɗa kai da wasu kasashe domin yin kira a tsagaita bude wuta a rikicin Isra’ila da Hamas.
Tun a ranar 7 ga watan Oktoba ne sojojin Isra'ila suke yin ruwan bama-bamai a Gaza, bayan mayaƙan Hamas sun ƙaddamar da harin da ya yi sanadin mutuwar mutum 1,400 a Isra'ila, waɗanda mafi yawansu fararen hula ne, a cewar hukumomin Isra'ila.
A cewar ma'aikatar lafiya ta Hamas, adadin waɗanda suka mutu a Gaza ya zarce mutum 10,000 ciki har da yara sama da 4,000.
A wani kudiri da Sanata Abdulrahman Kawu daga Kano ta Kudu ya gabatar a ranar Talata, Majalisar Dattawar bayan muhawara mai zurfi ta bayyana mace-mace da kuma adadin waɗanda suka rasa muhallansu sakamakon rikicin na Isra'ila da Hamas a matsayin abin tsoro.
Yayin da suke bayyana ra'ayinsu, ƴan majalisar sun yi Allah-wadai da kashe-kashen da aka yi a bangarorin biyu, sannan suka buƙaci a zauna lafiya domin kauce wa abin da zai kawwo yaɗuwar rikicin.
Wannan kiran na zuwa ne sa'o'i 24 bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta ƙara jaddada buƙatar tsagaita wuta cikin gaggawa, inda ta bayyana Gaza a matsayin makabarta ga kananan yara yayin da adadin wadanda suka mutu ya haura 10,000.
Iƙirarin aikata kisan ƙare dangi a Gaza ya janyo suka ga 'yar majalisar Amurka
Dangin mutanen da aka kashe na shirin yi wa Netanyahu zanga-zanga
Asalin hoton, AFP
Dangin ƴan Isra'ila da ke cikin makoki na mutuwar ƴan'uwansu da na waɗanda aka sace gami da waɗanda suka ɓata sun shirya gudanar da zanga-zanga a wajen ginin majalisar dokokin Isra'ila a yau, da yamma don nuna fushi ga firaminstan ƙasar Netanyahu da kuma gwamnatinsa.
Yau ne dai ya cika wata guda da hare-haren Hamas da suka kashe mutum 1,400 a Isra'ila tare da yin garkuwa da sama da 200.
An buga a zauren whatsApp na dangin da abin ya shafa cewa "Netanyahu bai halarci ko wanne jana'iza da makokin da aka gudanar ba kuma bai kira iyalan waɗanda suka mutu saboda haka, gobe za mu tuntuɓe shi."
Yadda Sarki Charles III ya gabatar da jawabinsa na farko ga Majalisa
Sarki Charles III ya gabatar da Jawabin Sarki na farko ga Majalisar dokoki, abin da ke alamta shiga farkon sabon zangon zaman majalisar.
Ya fara jawabin nasa ne da jinjinawa "mahaifiyarsa" Marigayiya Sarauniya Elizabeth.
Asalin hoton, PA Media
Asalin hoton, PA Media
Asalin hoton, PA Media
Asalin hoton, PA Media
Asalin hoton, PA Media
An ware kimanin naira miliyan 380 don yaƙi da kuɗin cizo a birnin Seoul
Asalin hoton, OTHER
Hukumomin Koriya ta Kudu suna aiki ba ji-ba gani don shawo kan ɓullar ƙwarin kuɗin cizo da ya janyo damuwa a faɗin ƙasar.
Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ce an samu ɓullar ƙwarin masu shan jini a sassa 17 na Seoul babban birnin ƙasar, da biranen Busan da Incheon zuwa ranar 5 ga wannan wata na Nuwamba.
Birnin Seoul ya ware kudin kasar won miliyan 500 kwatankwacin naira miliyan 380 a canjin hukuma tare da kafa kwamitin kai dauki ga annobar kudin cizo.
Waɗannan ƙwari sun zama wani batun fargaba a tsakanin jama'a cikin 'yan kwanakin baya-bayan nan a Faransa da kuma Birtaniya.
Tun cikin watan Satumba ne aka ba da rahoton ɓullar kuɗin cizo a Koriya ta Kudu, a wata jami'a da ke birnin Daegu na kudu maso yamma.
Daga bisani aka bayar da rahoton ganin kuɗin-cizon a ɗakunan masu yawon buɗe ido da gidajen wankan hutu.
Wasu 'yan Koriya ta Kudu sun riƙa gujevwa shiga silima da ababen hawa na jama'a saboda fargabar kuɗin cizo.
Ko ka san asalin kudin cizo?
Fargabar ɗiban kuɗin-cizo a birnin da zai yi baƙin fita kunya
Jama'ar birnin Ƙudus sun yin taron juyayi wata ɗaya bayan harin Hamas
Ga hotunan yadda ‘yan Isra’ila a birnin Ƙudus suka taru dauke da tutoci tare da kunnanan kyandira domin tunawa da waɗanda harin Hamas ya kashe a Isra’ila wata daya da ya wuce.
Aƙalla mutum 1,400 ne aka kashe a Isra'ila a ranar 7 ga Oktoba.
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Nijar ta nemi Togo ta shiga tsakani a rikicinsu da Ecowas
Asalin hoton, AFP
Gwamnatin sojan Nijar ta nemi shugaban ƙasar Togo, Faure Gnassingbe ya shiga tsakani a tattaunawa da ƙasashen duniya musamman ma ƙungiyar raya tattalin arzikin Afrika ta Yamma (Ecowas) wadda ta kakaɓa wa Nijar takunkumi tun bayan juyin mulki.
Ministan tsaron Nijar, Janar Salifou Mody ne ya bayyana haka lokacin da yake ganawa da Shugaba Gnassingbe a Lome babban birnin kasar ranar Litinin. Ya kuma nemi Togo ta tsayawa Nijar a yarjejeniyar janye sojojin Faransa daga kasar ta yankin Sahel.
"Yana da muhimmanci a koyaushe mu tunatar da abokan kawancenmu cewa, kofar Nijar a buɗe take, ko da an yi kulle-kullen da ba za mu iya magana da abokan hulɗarmu ba,” Mody ya shaida wa manema labarai bayan kammala taron.
Kungiyar Ecowas ta sanya wa Nijar takunkumin tattalin arziƙi da kuma rufe harkokin kasuwanci na kan iyaka da Nijar a yunƙurin matsa wa shugabannin kasar lamba har sai sun mayar da mulkin dimokradiyya.
Togo, duk da kasancewarta mamba a kungiyar Ecowas, ta dauki wasu matakai na hadin gwiwa da shugabannin sojojin Nijar tare da bayyana aniyar hawa teburin tattaunawa.
Tuni dai Faransa ta fara janye dakarunta 1,500 daga Jamhuriyar Nijar, bayan da gwamnatin mulkin sojan ƙasar ta buƙaci su fice jim kadan da hamɓarar da Shugaba Mohamed Bazoum a ranar 28 ga watan Yuli.
Ministan harkokin wajen Togo, Robert Dussey ya ce kasarsu a shirye take ta taimaka wajen tattaunawa.
"Togo na adawa da duk wani matakin juyin mulki" in ji shi. "Amma a yanayi na musamman na ƙasarku, Togo ta fahimta, kuma tana son taimaka muku." in ji ministan
Shugaban Najeriyar, Bola Tinubu, wanda kuma shi ne jagoran Ecowas, ya bayyana taka-tsantsan wajen mu'amala da Nijar saboda damuwar da ake da ita dangane da hamɓaras da Shugaba Bazoum daga kan mulki.
Gwamnatin mulkin soja a Nijar ta ce za ta miƙa mulki bayan shekara uku hannun farar hula, yayin da ƙungiyar Ecowas ta buƙaci a gaggauta mayar da aiki da tsarin mulki.
Duk da haka, ana ci gaba da ƙoƙarin diflomasiyya don ganin a shawo kan lamarin.
Ecowas ba ta yi mana adalci ba – Firaministan Nijar
'Mutane sun wahala a Nijar kuma suna neman wanda za su ɗora wa laifi'
An ƙwace kambun bajinta da Hilda Bassey ta kafa a fegen girki a duniya
Asalin hoton, Guinness World Records
Kundin Bajinta na Guinness World Records ya bayyana cewa wani mai gidan cin abinci ɗan ƙasar Ireland, Alan Fisher, ya karya tarihin girki mafi daɗewa a duniya, inda ya zarce tarihin da ƴar Najeriya Hilda Baci ta kafa a farkon shekarar nan da sama da sa’o’i 24.
Kundin Bajinta na Guinness World Records ya tabbatar da hakan ne a ranar Talata a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X, inda ya kuma ayyana Alan Fisher a matsayin sabon wanda ya ƙwace kambun bajintar.
"An tsige Hilda Bassey a matsayin wace ta lashe kambun bajinta na Guiness na tarihin girki mafi daɗewa a duniya." in ji kundin Bajintar
"Alan Fisher daga Ireland ya yi girki na tsawon sa'o'i 119 da mintuna 57 a gidan abincinsa da ke Japan,".
A watan Yuni ne aka ayyana Hilda a matsayin wacce ta lashe kambun bajinta na kafa tarihin girki mafi daɗewa a duniya.
Me ya sa ƴan Najeriya ke rige-rigen shiga Kundin Bajinta na Guiness?
Amfanin tumatir ga lafiyar jiki
An zaro mutane a cikin baraguzai bayan fashewar bama-bamai a Khan Younis
An ba da rahoton samun gomman mutanen da suka rasu bayan fashewar bama-bamai a kudancin Zirin Gaza.
Jami'an ma'aikatar lafiya da ke karkashin Hamas sun ce an kashe akalla mutum 23 a hare-haren sama na Isra'ila guda biyu da aka kai Rafa da Khan Younis.
Kamfanin dillancin labaran Falasdinawa mai suna Wafa ya ce an kashe akalla mutum 12 a Khan Younis, yayin 25 suka mutu a Rafah.
Rundunar sojojin Isra'ila ba ta ce uffan ba, amma ta sanar da cewa ayyukanta a Gaza sun ci gaba har cikin tsakiyar dare.
Bayanan bidiyo, Khan Younis: Ana zaro mutane a cikin baraguzai bayan munanan hare-haren bam
Ana juyayi kan mutanen da hare-haren Hamas suka ritsa da su a Tel Aviv
Tsawon wata daya kenan tun bayan hare-haren da Hamas ta kaddamar a Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba kuma 'yan Isra'ila na gudanar da juyayi a fadin kasar don tunawa da wadanda lamarin ya ritsa da su.
An yi tsit na tsawon minti daya daidai karfe 11.
Wadannan hotuna na nuna mutanen da suka taru a Dandalin Dizengoff da ke Tel Aviv, inda hotuna ke nuna fuskokin mutanen da ake ci gaba da garkuwa da su har yanzu a Gaza.
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Getty Images
Ka canza sana'a, siyasa ba ta karɓe ka ba - Tinubu ya faɗa wa Obi
Asalin hoton, TINUBU/TWITTER
Gwamnatin Najeriya ta kalubalanci dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP a zaben 2023 da ya wuce, ya rungumi salon yakin neman zabe na amfani da batutuwan kawo ci gaba, maimakon amfani da addini da kabilanci kamar yadda ya yi a zaben da ya wuce.
Ta ce ta rasa yadda Peter Obi wanda ta kira mai kwaikwayon abin da ya ga wani ya yi, da jam'iyyarsa ta LP suka hakikancewa kansu cewa su ne suka ci zaben da za a zahiri ya zo na uku.
Gwamnatin na mayar da martani ne ga wani taron manema labarai da Peter Obi ya gudanar ranar Litinin inda ta zarge shi da zubar da mutuncin bangaren shari'a.
Shi dai Obi ya ce kotun koli ta yi watsi da shaida ta yankan shakku, kamar kin amfani da dokokin zaɓe da ya ce INEC ta yi, kuma abu ne da ya ce bai kamata hukumar zaɓen ta yi wasa da shi ba.
Sai dai gwamnatin Najeriya ta ce dan takarar na jam'iyyar LP a zaben da ya wuce, yayin taron manema labaran da ya gudanar, tamkar Atiku Abubakar, ya yi kokarin zubar da mutuncin Kotun Koli da hukumar zabe ta INEC saboda a cewarta, don kawai ba su ayyana shi wanda ya ci zaben 25 ga watan Fabrairu ba.
Ta ce kamaya ya yi a zurfafa nazari kan babban mafarkin Peter Obi, wanda ya yi imanin cewa zai iya cin zabe ta hanyar gudanar da yakin neman zabe mafi haddasa gaba da janyo rarrabuwar kawuna da ya gwara kan Kiristoci da Musulmai da kuma wannan kabila da wata a kasa mai yawan kabilu da yawan addinai kamar Najeriya.
Sanarwar da Babban Mashawarcin Tinubu kan harkar yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, ta ce Peter Obi ya yi kokari ba tare da nasara ba wajen tunzura 'yan Najeriya da karairayi da gugar zana, sannan ta zarge shi da yin tufaka da warwara.
Gwamnatin Tinubu ta ce Obi ya amfana da hukunce-hukuncen kotuna a baya amma a yanzu yana bata suna kotun saboda hukuncinta bai yi masa dadi ba.
Hujjojin kotun ƙoli na yin watsi da ƙarar Atiku da Obi kan nasarar Tinubu
Kalaman Peter Obi sun yamutsa hazo a siyasar Najeriya
Isra'ila ta ce ƙarin motoci 70 ɗauke da kayan agaji sun shiga Gaza
Asalin hoton, cogat
Manyan motoci 70 dauke da kayan agaji na ƙasashen duniya da suka haɗa da magunguna da abinci da ruwa da sauransu, sun shiga Gaza ta kan iyakar Rafah a yau, Talata.
An gudanar da binciken waɗannan manyan motoci kafin su tsallaka zuwa Gaza daga Masar.
Kafin a fara rikicin, kusan manyan motoci 500 ne suke shiga Gaza a kowace rana.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce tuni mutane miliyan 1.2 a yankin Gaza sun dogara da tallafin abinci.