Hukuncin Kotun Koli ba shi ne karshen siyasata ba - Peter Obi

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Mukhtar Adamu Bawa, Haruna Kakangi and Ahmad Tijjani Bawage

  1. 'Yan a-ware sun kashe mutum 20 a Kamaru

    Kamaru

    Hukumomi a Kamaru sun ce ‘yan a-ware sun kashe akalla mutane 20 a hari cikin dare a wani kauye da ke kudu maso yammacin kasar.

    Haka kuma wadansu mutane 10 sun ji rauni sakamakon harin da aka kai a kauyen da ake kira Manyu.

    Wani babban jami’in dan sanda a kauyen Manyu ya bayyana lamarin a matsayin harin ta’addanci kuma wadanda suka ji rauni an garzaya da su zuwa asibiti.

    Mr Vianga Mekala ya kara da cewar har yanzu ba su gano dalilan da suka sa ‘yan a-ware na Ambazoniya suka kashe mutanen ba -- wadanda dukkansu farar hula ne.

    A cewarsa, an kona gidaje 10 a lokacin harin amma jami’an tsaro sun kai dauki daga baya.

    Yankunan da ke amfani da turanci Ingishi sun dade suna fama da tashin hankali tun daga shekara ta 2017, inda mayakan ‘yan aware ke yaki da dakarun gwamnati.

    Kungiyoyin agaji sun bayyana cewa bangarorin biyu sun aikata mummunar ta’asa a tsawon lokacin da aka soma yakin.

    Kawo yanzu dai mutane fiye da dubu shida ne suka mutu a yayin da wadansu kusan miliyan daya suka rasa muhallansu sakamakon yakin basasar.

    • Jami'an tsaro sun kama jagoran a-ware na Biafra a Finland
    • Bam ya hallaka mutum 9 a kan iyakar Kamaru da Najeriya
  2. Mutane sun koma amfani da jakuna wajen daukar gawawwaki a Gaza

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Daraktan asibitin Al Shifa da ke birnin Gaza ya bayyana cewa, mutane sun koma daukar gawarwakin mutanen da suka mutu da jakuna saboda an katse hanyar sadarwa kuma sun kasa kiran motocin ɗaukar marasa lafiya.

    Duk da cewa an dawo da sadarwar a safiyar yau, samun bayanai daga birnin Gaza na da matuƙar wahala.

    Tabbatar da bayanan da ake da su da kuma tabbatar da shaidu daga yankin shima yana ba da aiki.

    'Yan jarida suna kokawa wajen samun sahihan bayanai masu inganci.

    • Ana damuwa kan yawaitar kisan ƴan jarida a rikicin Isra'ila da Falasɗinawa
    • Mutumin da ya rasa duka ƴaƴansa huɗu a hari ɗaya da Isra'ila ta kai
  3. 'Yan ci-rani kusan 32,000 ne suka isa tsibirin Canary daga Afirka ta Yamma a bana

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, ...

    Hukumomin Sifaniya sun bayar da rahoton cewa, 'yan ci-rani kusan 32,000 ne suka isa tsibirin Canary ta teku daga Afirka ta Yamma a bana, wanda ya zarce adadi mafi yawa da aka taba samu a baya cikin shekara ta 2006.

    Tun a ranar Juma’ar da ta gabata ne, aka kuɓutar da sama da mutum 700 a tekun Atlantika da ke kusa da El Hierro, mafi ƙanƙanta da ke yammacin Canary.

    Tsibirin Canary ya zama wuri na farko da bakin haure daga ƙasashe kamar Senegal da sauran sassan Afirka ke amfani da shi wajen neman shiga kasar Sifaniya.

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla bakin haure 140 ne suka mutu a kokarin tsallakawa tun farkon wannan shekara.

    • 'An gano' jirgin da ya ɓata ɗauke da 'yan ci-rani 200 a cikin teku
    • MDD ta yi Allah-wadai da gano ƴan cirani 92 tsirara a iyakar Girka da Turkiyya
  4. Tauraron YouTube na kokarin gina rijiyoyi 100 a Afrika

    Mr Beast/Instagram

    Asalin hoton, Mr Beast/Instagram

    Wani tauraron YouTube ɗan Amurka kuma mai ba da agaji Mista Beast, wanda aka fi sani da Jimmy Donaldson, ya samu yabo da suka a wani bidiyo da ya wallafa a shafukan sada zumunta inda ya bayyana cewa zai gina rijiyoyi 100 a Afirka.

    Ya ce zai gina rijiyoyi 52 a cikin al'ummar Kenya da wasu 48 a ƙasashe da suka hada da Zimbabwe da Uganda da Somalia da kuma Kamaru.

    Mutane da yawa sun yabawa Mista Beast bisa ƙoƙarinsa na taimakawa al'ummomin karkara tare da nuna damuwarsu game da almubazzaranci da kuɗaɗen gwamnati da ake nufi da irin waɗannan ayyuka.

    Mista Beast yana da mabiya kusan miliyan 207 a shafin sada zumuntansa na YouTube.

    Yayin da wasu ke yaba wa abin da ya yi, wasu 'yan Afirka sun soki bidiyon da cewa ka iya ci gaba da tabarbarewar ra'ayi game da talaucin Afirka.

    Bugu da ƙari, wasu sun bayyana damuwarsu kan illar rijiyoyin ga muhalli, inda suka ce za su iya taimakawa wajen raguwar ruwan ƙasa.

    Mista Beast ya kare ƙoƙarin sa na taimakon jama’a, inda ya bayyana ƙudurinsa na yin amfani da dandalinsa wajen taimakawa mutane da zaburar da wasu su yi hakan.

    • Matar da ta gina rijiyoyin ruwa fiye da 1000 a karkara
    • Bidiyon matan da suka yi kasadar shiga rijiya don neman ruwa ya ja hankalin mutane a Indiya
  5. An kashe mutum tara bayan fasa gidan yarin Guinea

    Dadis Camara

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, An sake kama Kaftin Moussa Dadis Camara sannan aka mayar da shi gidan yari ranar Asabar

    Kasar Guinea ta ce mutum tara aka kashe a lokacin da aka fasa gidan yari ranar 4 ga watan Nuwamba yayin da kuma wasu shida suka ji raunukan bindiga, abin da ya kai ga sace tsohon shugaban mulkin sojan kasar Moussa Dadis Camara da karin mutum uku.

    Sama da sojoji da jami’an gidan yari 60, aka kora bayan faruwar lamarin.

    A rahoton tantance abin da ya faru na wucin gadi, mai gabatar da ƙara, Yamoussa Conte ya bayyana cewa an kai gawawwakin mutum tara zuwa dakin ajiye gawa uku.

    Huɗu daga cikin waɗanda suka mutu, jami'an tsaro ne, yayin da uku wadanda har yanzu ba a tantance ko su wane ne ba, ana kyautata zaton suna cikin maharan da aka kashe "a yayin musayar wuta" lokacin da suke gudu zuwa gundumar Samatran.

    Conte ya yi kiran a ci gaba da gudanar da bincike tare da daukar matakin hukunta tsohon shugaban mulkin sojan kasar Moussa Dadis Camara da Kanal Moussa Thiegboro Camara da Kanal Blaise Gomou da kuma Kanal Claude Pivi da sauransu.

    Zarge-zargen da ake tuhumarsu da su, sun hada da "aikata kisa" kan jami'an tsaro da kisan kai ba da gangan ba, da keta umarni, da kuma hada baki wajen aikata laifi."

    An sake kama tsohon shugaban kasar, Moussa Dadis Camara ne kuma an mayar da shi gidan yari sa'o'i kaɗan bayan tserewa daga kurkukun da wasu 'yan bindiga suka fasa a safiyar Asabar.

    Ana ci gaba da farautar Kanal Claude Pivi.

    • An bayar da umarnin harbe duk wanda ya yi yunkurin fasa gidan yari a Najeriya
    • Gwamnati ta fitar da sunayen mutanen da suka tsere daga gidan yarin Kuje
    Dadis Camara

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Musa Dadis Camara ya jagoranci Guinea daga karshen 2008 zuwa farkon shekara ta 2010

    Ministan shari'ar kasar, Alphonse Charles Wright ya yi alkawarin ci gaba da shari'a kan Camara bisa zarginsa da hannu wajen kashe masu zanga-zangar adawa da gwamnati a 2009, abin da ya yi sanadin mutuwar mutum 150 tare da yi wa mata sama da 100 fyade a Conakry.

  6. An caka wa wani sojan Isra'ila wuƙa a birnin Ƙudus

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, ...

    Wani sojan Isra'ila ya samu munanan raunuka a wani hari da aka kai da wuƙa a kusa da Ƙofar shiga tsohon birnin da ke Gabashin Ƙudus.

    Jami’an tsaro sun ce sun harbe wanda ake zargi da kai harin ɗan shekara 16 kuma ɗan asalin yankin Issawiya da ke birnin, bayan da ya daba wa mutane biyu wuƙa a kan titin Sultan Suleiman.

    Sun ƙara da cewa an kama mutum na biyu da ake zargi kuma ana ci gaba da bincike.

    Jami’in agajin gaggawa na Isra’ila, Magen David Adom,, ya tabbatar da cewa an kai wata mata ‘yar shekara 20 asibiti domin mata magani bayan ta samu munanan raunuka.

    • Kalaman ƙarshe na yaron da aka caka wa wuƙa saboda zargin ƙin jinin Musulmai
    • Rikicin Isra'ila da Gaza: Mene ne asalin sa?
  7. Abin da 'Yan Ghana ke cewa kan tsaida Mahmudu Bawumia dan takarar NPP

    Mahamudu Bawumia

    Asalin hoton, GE

    Bayanan hoto, Mahamudu Bawumia ya roki hadin kan jam'iyyarsa a lokacin da take neman wa'adi na uku jere a kan mulkin Ghana

    Al'ummar Ghana, musamman magoya jam'iyyar NPP mai mulki na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu, bayan tsayar da Mataimakin Shugaban Kasar, Alhaji Mahamudu Bawunia, a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar a zabe mai zuwa.

    A karshen mako ne dai, aka kammala zaben fid da gwani na jam'iyyar NPP tsakanin masu neman takara hudu, wadanda aka tantance daga cikin kusan mutum goma.

    Mataimakin Shugaban Kasa Mahamudu Bawumia, zai kasance dan arewa na farko kuma Musulmi da zai yi takarar shugaban kasa a karkashin tutar jam'iyyar NPP tun bayan komawar Ghana kan tafarkin dimokradiyyar jam'iyyu da dama a 1992.

    A jawabinsa bayan samun nasara, Mahamudu Bawumiya ya yi alkawarin jagorantar NPP "mai hadin kai da kuzari" zuwa nasara a zaben kasar na 2024.

    Ya lashe zaben fitar da gwani ne da gagarumin rinjaye, inda ya samu kuri'u kashi 61.47%. Babban abokin karawar Bawumia a zaben fid da gwanin na karshen mako, Kennedy Ohene Agyapong, wanda ya samu kashi 37.4 na kuri'u da aka kada, ya karbi sakamakon zaben.

    Shugaba Nana Akufo-Addo zai sauka daga kan mukamin shugaban kasa bayan zaben watan Disamban 2024, lokacin da zai kammala wa'adin mulkinsa na biyu.

    Ana sa ran zaben zai fi zafi tsakanin 'yan takarar shugaban kasa biyu, Mahamudu Bawumia na jam'iyyar NPP da tsohon shugaban Ghana John Dramani Mahama na babbar jam'iyyar adawa ta NDC.

    Tare da Mista Mahama wanda shi ma ya fito daga arewa, wannan ne karon farko da manyan jam'iyyun siyasar Ghana biyu suka tsayar da 'yan takarar shugaban kasarsu duka 'yan arewa.

    Ana kallon kudancin Ghana, a matsayin inda jam'iyyar NPP ta fi karfi, yayin da NDC ke da da dumbin magoya baya a arewaci.

    Dauko Mahamudu Bawumia, NPP na fatan cewa za ta samu karin karbuwa a yankin arewa, yayin da jam'iyyar ke sa ran ci gaba da rike martabarta a tsakanin magoya baya daga kudancin kasar.

    Wani dan kasar da muka zanta da shi, ya ce zaben mataimakin shugaban Ghana a matsayin dan takarar NPP, wani babban kalubale ne ga jam'iyyar NDC mai adawa da kuma dan takararta John Mahama.

    Ya ce tsohon shugaban kasar Mahama ya taba mulki, kuma sun ga kamun ludayinsa, ba sabon dan takara ba ne a wajensu.

    Shi ma wani wanda ga alama mai goyon bayan jam'iyyar NDC ne ya ce, Lashe zaben da Bawumia ya yi, bai ba su wani tsoro ba.

    Ya mayar da martani ga masu ikirarin za su rusa aniyar dan takarar NDC na cin zabe wa'adi na biyu.

    Mahamudu Bawumia shi ne shugaban kwamitin kula da tattalin arziki na gwamnatin Ghana don haka zai fuskanci gagarumin aiki wajen shawo kan masu zabe su amince su kada masa kuri'u, don bai wa NPP karin damar mulki a wa'adi na uku.

    • Jama'iyar NPP a Ghana na duba halin zuwa kotu
    • Yadda Babban Bankin Ghana ya yi asarar dala biliyan 5 a shekara ɗaya
  8. Sabbin hotuna daga Gaza

    Ga wasu sabbin hotuna da ke nuna yadda jama'a ke duba ɓaraguzan gine-gine a kudancin Gaza a safiyar yau, Litinin wajen neman ƴan uwansu, da kuma sauran hotunan da ke nuna halin da Falaɗinawa suke ciki.

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, A Khan Younis da ke kudancin Gaza, mutane na bincika ɓaraguzan gine-gine inda suke neman ƴan uwan su.
    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Wani mutum na kallon yadda gidansa ya lalace sakamakon rikicin Isra'ila da Hamas
    ...

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Wata mota da ta lalace a arewacin Gaza, inda Isra'ila ke mayar da hankali wajen kai hare-hare ta ƙasa
    ...

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Lokacin da mazauna yankin Gaza suke yin kaura bayan da Isra'ila ta sake gargadin cewa mutane su fice daga kudu
    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Falasɗinawa na ɗibar ruwa a Rafah da ke kudancin gabar teku sakamakon karancin ruwan sha da tsafta
    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Wasu iyali na jira su bar Gaza kan iyakar Rafah bayan an dakatar da kwashe 'yan kasashen waje zuwa Masar ranar Lahadi
    • Labarai masu sosa rai na mutanen da aka kashe a Gaza
    • Tawagar ƙwararru ta MDD ta buƙaci Isra’ila ta tsagaita buɗe wuta a Gaza
  9. Amurka na ci gaba da faɗaɗa kokarin diflomasiyya yayin da rikicin Gaza ke tsananta

    ...

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, ...

    Gwamnatin Amurka na ci gaba da faɗaɗa kokarin diflomasiyyarta a Gabas ta Tsakiya, yayin da Jami'anta ke fatan shawo kan rikicin Isra'ila da Hamas.

    A zantarwar da za ta yi da shugabannin duniya, mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris za ta bai wa batun ƙarin shigar da kayan jin-ƙai da neman ƙarin kariya ga fararen hula.

    Sakataren Wajen Amurka, Antony Blinken zai tattauna da takwaransa na Turkiyya a Ankara, kwana na hudu kenan da yake gudanar da rangadi a yankin Gabas ta Tsakiya a karo na biyu, tun bayan barkewar yaƙin Isra'ila da Hamas.

    A halin yanzu, Daraktan hukumar CIA, William Burns, yana Isra'ila don musayar bayanan sirri tsakanin kasashen biyu.

    Wakiliyar BBC ta ce zai kuma gana da shugabannin Gabas ta Tsakiya ciki har da Firaminsitan Isra'ila Benjamin Netanyahu.

    • Manyan jami’an Amurka na ƙoƙarin hana bazuwar rikici a Gabas ta Tsakiya
    • Burin China a yaƙin Isra'ila da Hamas
  10. Tinubu zai halarci taron ƙasashen Larabawa da Afirka

    ...

    Asalin hoton, FACEBOOK/BOLA AHMED TINUBU

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu zai halarci taron ƙasashen Larabawa da Afirka da za a yi a birnin Riyadh na ƙasar Saudiyya, a wani ɓangare na ƙoƙarin da gwamnatin kasar ke yi na jawo hannun jarin kasashen waje ga tattalin arzikin ƙasar.

    Mashawarcin shugaban ƙasa na musamman kan harkokin yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan a ranar Lahadin da ta gabata yayin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban ƙasa a Abuja.

    "Shugaban zai yi amfani da taron ne wajen jawo hannun jarin kasashen waje kai tsaye zuwa cikin kasar. Taron tabbas zai samar da fa'ida ta fuskar tattalin arzikin ƙasar da Afirka."

    Taron dai na ƙoƙarin zaƙulo fannonin haɗin gwiwa, da samar da ra'ayi bai daya ta fannin ilmi da gogewa, da zayyana ayyuka da tsare-tsare na kyautata alaƙa tsakanin kasashen Larabawa da Afirka.

    Taron kuma ya mayar da hankali ne kan tunkarar kalubalen da duniya ke fuskanta, kamar tashe-tashen hankula da yaƙi da ta'addanci da fatara da ilimi da kiwon lafiya da samar da abinci da bashi da kuma sauyin yanayi.

    An gudanar da taron na karshe ne a shekarar 2016. Ngelale ya ce, za a yi cikakken bayani kan tarurrukan da shugaban kasar zai yi da masu zuba jari, waɗanda suka shafi farfado da tattalin arzikin kasar.

    Shugaba Tinubu dai zai samu rakiyar ‘yan majalisar ministoci da shugabannin ‘yan kasuwa, inda ake sa ran yin cikakken bayani a yayin ganawarsa da masu son zuba jari.

    • Me Tinubu zai yi da bashin kusan dala biliyan takwas da zai karbo?
    • Waiwaye: Majalisa ta hana Tinubu sayen jirgin ruwa, ƴan kwadago za su koma yajin aiki
  11. Dubban mutane sun maƙale a ambaliyar ruwa a Somaliya - MDD

    ...

    Asalin hoton, UNFPA SOMALIA/X

    Hukumar jin ƙai ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce dubban mutane sun maƙale a yankunan da ambaliyar ruwa ta mamaye sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a jihar Jubbaland ta Somaliya.

    Ruwan saman mai ƙarfi da aka fara a watan da ya gabata ya ƙara kaimi a kogin Juba, lamarin da ya haddasa ambaliya a yankunan kogin na jihar, in ji ofishin kula da ayyukan jin kai na jihar Ocha.

    Sanarwar da hukumar ta fitar ya ce, "A gundumar Luuq, mutum 2,400 ne suka maƙale a yankin da ruwa ya kewaye."

    Ana ci gaba da ganin ƙoƙarin hukumomi da kuma jami'an agaji wajen kwashe mutanen yankin da suka makale.

    Akalla mutum 14 ne suka mutu yayin da wasu 47,000 suka rasa muhallansu sakamakon ambaliyar ruwan da ta afku a ƙasar tun watan jiya, in ji sanarwar.

    Ministan yaɗa labarai na Somaliya Daud Aweis ya ce ambaliyar ruwan da ta shafi jihohin Hirshabeelle da kuma Kudu maso Yamma ta yi barna sosai.

    Ƙasar dai na fama da ruwan sama mai karfi tun bayan bullar fari mafi muni cikin shekaru arba'in.

    Hukumar samar da abinci da noma ta yi gargaɗin cewa ana fuskantar ambaliyar ruwa musamman a yankin kudu maso yammacin Gedo.

    • An yi ruwan sama misalin na shekara 20 cikin kwana ɗaya a Libya
    • 'Tamkar ambaliyar tsunami ce ta auka wa birnin Libya'
  12. Hare-hare sun tsananta yayin da Isra'ila ta ce ta raba Gaza gida biyu

    ...

    Asalin hoton, MAHMUD HAMS/GETTY IMAGES

    An samu ƙarin hare-hare ta sama da fashewar bama-bamai a arewacin Gaza cikin dare.

    An ba da rahoton sake samun katsewar intanet da sadarwa a yankin amma a daren, wakilin BBC a Gaza, Rushdi Abualouf ya shaida cewa yana ganin an kai hare-hare ta sama mafi muni tun farkon yaƙin.

    Ya ce an kai hare-haren ne kan arewa maso yammacin Gaza, inda aka yi ruwan bama-bamai a sansanin 'yan gudun hijira na bakin teku wanda aka fi sani da sansanin Shati.

    Kuma a cikin sa'a da ta wuce, Isra'ila ta ce jiragen yakinta sun kai hari a wurare 450 a yankin.

    Isra'ila ta kuma ce dakarunta sun raba Gaza gida biyu bayan farmakin da suka kai ta ƙasa kan mayakan Hamas.

    Bisa sabon alƙalumman da jami'ai suka fitar, an kashe sama da mutum 9,700 a Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoba.

    A Isra'ila kuma, Hamas ta kashe mutane sama da 1,400 tare da yin garkuwa da wasu sama da 200.

    • Sabon harin Isra'ila ya kashe fararen hula fiye da 30 a Gaza
    • Sabbin bayanan gaskiya guda 5 bayan mako huɗu na yaƙin Gaza
  13. Majalisar Dinkin Duniya ta sake jaddada neman tsagaita buɗe wuta a Gaza

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Majalisar Dinkin Duniya ta sake jaddada kiranta na neman tsagaita bude wuta cikin gaggawa a Gaza.

    Wata Sanarwar a madadin shugabannin hukumomin Majalisar Dinkin Duniya goma sha daya, tare da ƙungiyoyin agaji guda shida, ta bukaci Isra'ila da ta kare fararen hula tare da ba da damar shigar da ƙarin abinci da ruwa da magunguna da kuma mai zuwa Gaza.

    Ta ce an yi wa jama'ar Gaza kawanya tare da hana su samun abubuwan da ake bukata na rayuwa.

    Ta ce salwantar rayukan ma'aikata 88 na hukumar kula da 'yan gudun hijirar Falasdinnawa ta Majalisar Dinkin Duniya shi ne mafi girman mace-macen da Majalisar Dinkin Duniya ta fuskanta a yaki daya.

    • Tsagaita wuta zai ba Hamas damar sake shiri don kai hare-hare - Anthony Blinken
    • Me ya sa ba za a buɗe mashigar Rafah ga kowa ba?
  14. Assalamu alaikum

    Masu bin mu a wanna shafi muna muku maraba da shigowa shafin kai-tsaye na BBC Hausa.

    Aisha Babangida ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Sai ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.