Hukuncin Kotun Koli ba shi ne karshen siyasata ba - Peter Obi

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Mukhtar Adamu Bawa, Haruna Kakangi and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Rufewa

    Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na kai-tsaye.

    Mu tara gobe da safe don kawo muku wasu sababbi.

    Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

  2. An kama fitacciyar ƴar gwagwarmayar Falasɗinawa

    Tamimi

    Asalin hoton, Getty Images

    Sojojin Isra'ila sun kama fitacciyar ƴar gwagwarmayar Falasɗinawa Ahad Tamimi a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka yi wa ƙawanya.

    An tsare Tamimi, mai shekara 22, a cikin dare a ƙauyen Nabi Saleh, a cewar ƙungiyar fursunoni ta Falasɗinawa.

    Sojojin Isra'ila sun faɗa wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa ana zarginta ne da "tunzura tashin hankali da ta'addanci".

    Sai dai kafofin yaɗa labaran Isra'ila sun ruwaito cewa an kama Tamimi ne bayan da ta wallafa wani sako a shafin Instagram da ke barazanar "yi wa Yahudawa ƴan kama wuri zauna yankan rago.

  3. Sojojin Najeriya sun ce sun kubutar da matar da ta yi yunkurin kashe kanta a teku

    NIGERIAN ARMY

    Asalin hoton, NIGERIAN ARMY/X

    Rundunar Sojan Najeriya ta 81, sun dakile wani yunkurin kashe kanta da wata Misis Francesca Spark ta yi, wadda ta fada cikin tafkin Legas da ke kusa da 81 Division Officers’ Mess, Marina Lagos.

    Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sashen, Lt.-Col. Olabisi Ayeni, a ranar Litinin. Ayeni ta ce Spark ta yi yunkurin kashe kanta; amma sojojin Bataliya ta 65 da ke wurin sun hango ta kuma cikin hanzari suka yi amfani da dabarar sojan su wajen ceto ta.

    Likitocin bataliyan sun ba ta agajin gaggawa . "Bayan an natsar da ita, mun tuntubi danginta kuma aka mika ta ga mijinta, wani Mista Ovie Spark, wanda ke zaune a Awoyaya Legas," in ji shi.

    Ayeni ya ce babban kwamandan rundunar (GOC) 81 Division NA, Maj.-Gen. Muhammed Usman, ya yabawa sojojin bisa yadda suka kasance a cikin lura da hazaka da jajircewa.

    “GOC ya ce ya ji dadin yadda sojoji suka yi amfani da horo kan yadda za a shawo kan bala’o’i don jure wa irin wannan mawuyacin hali da ka iya janyo asarar rayukan dan kasa.

    "GOC ya tabbatar wa mazauna yankin kudurin rundunar na kare su da dukiyoyinsu ko da a lokutan gaggawa," in ji Ayeni.

  4. Afirka ta Kudu ta janye jakadanta daga Isra'ila

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Afirka ta Kudu ta ce za ta janye dukkan jami'an diflomasiyyarta daga Tel Aviv bayan kazamin harin da Isra'ila ta kai a Gaza a daren Lahadi.

    Harin bama-bamai dai na daya daga cikin mafi muni da Isra'ila ta yi tun bayan yakin da aka fara wata guda da ta wuce. A cewar asibitin Al-Shifa na birnin Gaza, kimanin mutane 200 ne suka mutu.

    Gwamnatin Afirka ta Kudu, wadda ta dade tana goyon bayan Falasdinawa, ta yi kakkausar suka ga Isra'ila a ranar Litinin

    Ministan harkokin wajen kasar Naledi Pandor ya shaidawa taron manema labarai cewa, Afirka ta Kudu na janye jami'an diflomasiyyarta, yana mai cewa: "Muna matukar damuwa da yadda ake ci gaba da kashe kananan yara da fararen hular da ba su ji ba ba su gani ba a yankunan Falasdinawa, kuma mun yi imanin ramuwar gayyar da Isra'ila ke yi ya zama abin damuwa. daya daga cikin hukuncin gamayya.

    Har yanzu dai Isra'ila ba ta ce uffan ba game da wannan furuci na Afirka ta Kudu ba amma ta dage cewa tana kokarin ganin ta rage asarar rayukan fararen hula tare da zargin Hamas da ke iko da zirin Gaza da yin amfani dda fararen hula a matsayin garkuwa.

    A ranar 7 ga Oktoba, mayakan Hamas - wadanda Birtaniya da Amurka da sauran kasashen yammacin duniya suka ayyana a matsayin kungiyar ta'addanci - sun kashe mutane fiye da 1,400 a Isra'ila. Haka kuma sun yi garkuwa da mutane sama da 230 ciki har da wani dan kasar Afirka ta Kudu daya wanda har yanzu ba a tabbatar da sunansa ba.

  5. Gobara ta kashe mutane a ofishin jakadancin Canada da ke Abuja

    Gobara

    Asalin hoton, FCT EMERGENCY MANAGEMENT AGENCY

    Rahotanni na bayyana cewa wasu mutum biyu sun mutu yayin da wasu suka jikkata a wata gobara da ta tashi a ofishin jakadancin Canada a Abuja, babban birnin Najeriya.

    Gobarar ta ƙona wani sashe na ofishin jakadancin. Sai dai ba a san abin da ya haddasa gobarar ba zuwa yanzu.

    An ga hayaki na tashi sama daga ginin ofishin wanda ke tsakiyar Abuja, kuma kusa da ma'aikatar tsaro ta ƙasa da ofisoshin jakadancin Birtaniya da Ghana.

    Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriya, Ajuri Ngelale ya fitar, ta ambato shugaba Bola Tinubu na jajantawa gwamnatin Canada, da al'ummomin diflomasiyya, da kuma dukkan mutanen da wutar ta shafa.

    "Shugaba Tinubu na tabbatarwa hukumomin Canada cewa gwamnatin Najeriya za ta su ba su dukkan goyon baya a ɓangaren diflomasiyya da taimakawa ma'aikatan ofishin jakadancin da gobarar ta shafa," in ji sanarwar.

    Tinubu yayi addu'ar Allah ya ji kan waɗanda suka mutu tare da yi wa waɗanda suka jikkata fatan samu lafiya.

  6. Kotu ta buƙaci EFCC ta saki Emefiele

    Godwin Emefiele

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata kotu a Najeriya ta bayar da umarnin cewa a saki tsohon gwamnan babban bankin Njaeriya Godwin Emefiele ba tare da an gindaya wani sharadi ba ko kuma a kai shi kotu a ranar Laraba domin sauraron bukatarsa ta neman beli.

    Tsohon gwamnan CBN din bai bayyana a gaban kotu ba a yau Litinin lokacin zaman sauraron bukatarsa ta neman beli wanda hakan ya sanya alkalin kotun Olukayode Adeniyi, ya bukaci hukumar EFCC da lauyoyin gwamnati da cewa su sake shi ko kuma su kawo shi kotu cikin kwana biyu.

    An tsare Emefele mai shekaru 61 da haihuwa a ranar 10 ga wayan Yuni, bayan zarginsa da almundahana wajen siyo wadansu kayayyaki.

    Tun da farko hkukmar DSS ne suka tsare shi bisa zargin mallakar bindiga ba bisa ka'ida ba ind adaga baya suka jefar da wannan zargin.

    A ranar Litinin hkumar EFCC ta bayyana cewa ya kwashe mako guda a hannunta.Shugaban Najeriya Bola Tinubu ne ya sauke shi daga mukaminsa a ranar 9 ga watan Yuni inda daga baya hukumar DSS ta kama shi.

  7. Gaza na zama makabartar yara - MDD

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya António Guterres, ya ce ana cikin yanayi maras kyau a Gaza - kuma yankin Falasɗinawa na saurin zama "makabartar yara".

    "Ana kashe ɗaruruwan yara maza da mata ko kuma jikkata su a kowace rana,"in ji Guterres - wanda yake jagorantar MDD tun 2017, a wani taron manema labarai.

    Ya ce rikicin "yana girgiza duniya" da "salwantar da rayuka da dama".

    Guterres ya ƙara yin Alla-wadai kan harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba", inda ya ce mayakanta sun yi amfani da fararen hula a matsayin mafaka wajen ci gaba da far wa Isra'ila.

  8. Motoci 30 ɗauke da kayan agaji sun shiga Gaza a yau Litinin

    Aƙalla motocin agaji 30 ne suka shiga Gaza a yau Litinin, a cewar mai magana da yawun Hukumar Tsaron Amurka, John Kirby.

    Hukumomin bayar da agaji sun ce ana buƙatar ɗaruruwan motocin kayan agaji a kowace rana a Gaza.

    Amurka za ta ci gaba da tattaunawa da Isra'ila kan tsagaita wuta na wucin gadi, in ji Kirby.

    Sai dai ya ce Amurkar ba ta amince cewa tsagaita wuta baki-ɗaya shi ne ake buƙata ba a wannan lokaci.

  9. Hukuncin Kotun Koli ba shi ne karshen siyasa ta ba - Peter Obi

    Peter Obi

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗan takarar shugaban ƙasa a Najeriya na jam'iyyar Labour a zaɓukan 2023, Peter Obi, ya ce hukuncin Kotun Koli ba shi ne karshen siyasarsa ba.

    Obi ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ya kira a yau Litinin a Abuja, inda ya ce shi da magoya bayansa waɗanda ake kira "Obedient Movement" sun zama ƴan adawa a siyasar Najeriya.

    "Muradina shi ne samar da sabuwar Najeriya kuma hakan ba zai sauya ba duk da hukuncin da Kotun Koli ta yanke a ranar 26 ga watan Oktoba," in ji shi.

    Ya ce "yadda abubuwa ke tafiya a ƙasar nan, su suka saka muka fito domin zama ƴan adawa a ɓangaren siyasar ƙasar, saboda tana son samun ƴan adawa masu karfi.

    Obi ya ce Kotun ta yi watsi da shaida ta yankan shakku, kamar kin amfani da dokokin zaɓe da ya ce INEC ba ta yi ba, abu kuma da ya ce bai kamata hukumar zaɓen tayi wasa da shi ba.

  10. An yanke ƙafar ɗan wasan fim na Najeriya, Mista Ibu

    MR IBU

    Asalin hoton, @REALMRIBU/INSTAGRAM

    An yi wa fitaccen ɗan wasan 'Nigerian film' John Okafor, wanda aka fi sani da Mista Ibu tiyata don cire ɗaya daga cikin kafafunsa.

    Hakan na ƙunshe ne a wani bayani da aka wallafa a shafin instagram na ɗan wasan kwaikwayon, a yau Litinin.

    Sanarwar ta ce, "Da misalin karfe ɗaya na rana, aka samu nasarar yi wa mahaifinmu tiyata sau bakwai don yanke kafarsa ɗaya."

    Iyalan ɗan wasan fim ɗin sun yi kira ga ‘yan Najeriya da su saka Mista Ibu cikin addu'a da kuma taimaka musu.

    A watan da ya gabata, wani bidiyo da Mista Ibu ya wallafa a shafinsa na Instagram ya karaɗe shafukan sada zumunta, inda aka ga yana neman taimako da kuma addu'a wajen magoya bayansa.

  11. Babu rikici tsakanin ƙabilu a Kagarko - Uba Sani

    Gwanman jihar Kaduna, Uba Sani

    Asalin hoton, UBA SANI

    Bayanan hoto, Gwanman jihar Kaduna, Uba Sani

    Gwamnatin jihar Kaduna ta musanta bayanan da ke cewa an yi sulhu tsakanin al'ummar Hausa da Fulani da kuma Koro a ƙaramar hukumar Kagarko sanadiyyar rashin jituwa da ke tsakanin su.

    Gwamnatin ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwar da ta fitar yau Litinin, wadda ta samu sa hannun Muhammad Lawal Shehu, mai magana da yawun gwamnan jihar, Sanata Uba Sani.

    Sanarwar ta ce tana jan hankalin al'umma daga wasu rahotannin da babu gaskiya a cikin su, waɗanda ke bayyana cewa ministar mata ta Najeriya, Uju Kennedy-Ohanenye ta yi wani zaman shiga-tsakani da manyan ƙabilun, a wani yunƙuri na kawo ƙarshen rikicin da aka kwashe shekara 20 ana fama da shi a yankin.

    Sai dai sanarwar ta bayyana cewa "Kagarko na daga cikin ƙananan hukumomi mafiya kwanciyar zaman lafiya da lumana a jihar, kuma an kwashe shekaru ba tare da wani rahoton na rikici a ƙaramar hukumar ba."

    Sanarwar ta ce wasu tsirarun mutane ne suka tunkari ministar da batun, kawai domin cimma wasu muradu na ƙashin kansu.

  12. Lauyoyin Bazoum sun nemi kotu ta bayar da umarnin mayar da shi kan mulki

    Mohammed Bazoum
    Bayanan hoto, Mohammed Bazoum

    Lauyoyin hamɓararren shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohammed Bazoum sun buƙaci kotun Ecowas da ta umurci a mayar da shi kan mulki kasancewar hamɓarar da shi da aka yi da kuma tsare shi sun saɓa wa doka.

    Ana tsare da Bazoum ne tun bayan da sojoji masu gadin fadar shugaban ƙasar suka hamɓarar da shi daga mulki ranar 26 ga watan Yulin 2023.

    Sojojin sun zargi gwamnatin Bazoum da gaza magance matsalar tsaron ƙasar.

    Sai dai ɗaya daga cikin lauyoyinsa waɗanda suka garzaya kotun Ecowas, Seydou Diagne, a bayanin da ya yi, ya buƙaci kotun, wadda ke zaman ta a Najeriya ta yanke hukunci cewar "hamɓarar da shi da aka yi ƙarfi da yaji take hakkinsa ne na shiga harkokin siyasa."

    Kotun Ecowas, kotu ce wadda kan yanke hukunci kan ƙararraki daga ƙasashen yammacin nahiyar Afirka, sai dai ba wajibi ne ga ƙasashe su yi amfani da hukuncin kotun ba kasancewar babu takamaiman tsarin tabbatar da hukuncin.

  13. Rashford ya bukaci masu gulmar makomarsa a United su bari

  14. Labarai da dumi-dumi, Ma'aikatar lafiyar Gaza ta ce mutanen da aka kashe a Gaza sun zarce 10,000

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Adadin mutanen da aka kashe a Gaza tun lokacin da Isra'ila ta fara kai hare-hare a yankin ya kai 10,022 a cewar ma'aikatar lafiya ta Hamas a Gaza.

    Wannan adadi ya zo ne bayan wani kazamin harin da Isra'ila ta kai cikin dare, inda sojojin Isra'ila suka ce sun kai hari kan daruruwan wurare da suka hada da wani sansanin sojin Hamas.

    Daraktan asibiti mafi girma a birnin Gaza ya shaida wa BBC tun da farko cewa an kashe mutane kusan 200.

    Dubban yara ne ake kyautata zaton na cikin waɗanda suka mutu.

    Wasu 'yan siyasa, ciki har da shugaban Amurka Joe Biden, sun nuna shakku kan sahihancin alƙaluman ma'aikatar lafiya ta Gaza.

    Da aka tambaye ta game da wannan, Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce sun yi imanin adadin na da sahihanci.

    Kamar sauran hukumomin gwamnati a Gaza, ma'aikatar lafiya na karkashin ikon Hamas, haramtacciyar kungiyar ta'addanci a Burtaniya da Amurka da Tarayyar Turai.

    Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare a Gaza bayan Hamas ta kashe mutane sama da 1,400 a Isra'ila tare da yin garkuwa da wasu fiye da 200 a ranar 7 ga Oktoba.

    Sojojin Isra'ila sun ce farmakin na su na da nufin rusa kungiyar Hamas gaba daya.

  15. An hana zirga-zirgar jiragen ruwa da daddare a jihar Taraba

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Mataimakin gwamnan Taraba a Najeriya, Alhaji Aminu Alkali, ya sanar da matakin hana zirga-zirgar jiragen ruwa da dare a kogunan jihar.

    Bugu da ƙari, sabbin ƙa'idoji suna buƙatar masunta su cire shinge da kuma ma'aikatan jirgin ruwa su daina lodin fasinjoji.

    Hakan ya biyo bayan kwato gawarwaki 20 bayan wani mummunan hatsarin kwale-kwale a watan da ya gabata a kan kogin Benue, daya daga cikin manyan kogunan Najeriya.

    Aƙalla mutum 14 ne suka tsira amma sama da mutum 70 aka yi imanin sun bace.

    Yunkurin ceto ya samu cikas sakamakon yadda ruwan kogin ya yi kamari, in ji kakakin rundunar ‘yan sandan Taraba Usman Abdullahi a makon da ya gabata.

    Hukumomin kasar dai na danganta wadannan hadurran jiragen ruwa da ake yawan samu a yankunan kogunan Najeriya da dalilai da suka hada da yawan lodin kwale-kwale da rashin amfani da rigar ceto.

  16. "Ban yi tunanin za a iya sace tsohuwa mai shekara 85 ba"

    Israel

    Asalin hoton, Courtesy of Elinor Shahar

    Bayanan hoto, Adva Adar with her grandmother Yafa, 85, who is being held hostage by Hamas

    A ranar 7 ga Oktoba ne, kungiyar Hamas ta yi garkuwa da kakar Adva Adar mai shekara 85 tare da kai ta Gaza, haɗe da wasu mutane sama da 200 daga Isra'ila.

    Bayan wata guda, yayin da sojojin Isra'ila ke kai hare-hare ta sama a kewayen birnin Gaza, Adva na fatan cewa waɗannan ayyuka za su kai ga kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su.

    Ta ƙara da cewa ba ta taɓa tunanin za a iya sace tsohuwa kamar kakarta ba, mai shekaru 85.

    Tun farko tana shirin ziyartar kakarta a wannan ranar, cikin yankin kibbutz Nir Oz, tare da danginta don bikin Yahudawa na Sukkot, amma da karfe 6:30 na safe kakarta, Yafa Adar, ta tura musu takaitaccen sakon waya, inda ta ce an harbo makamin roka kuma ta nemi mafaka.

    Bayan haka, Adva ta rasa hanyar sadarwa da kakarta, daga baya kuma ta ga bidiyon da ƙungiyar Hamas ke ɗaukan kakar tata,

  17. Ina son ran dan wasa ya baci don ba a saka shi a wasa ba - Guardiola

  18. Boko Haram ta kashe manoma a Borno

    ...

    Asalin hoton, ...

    Mayaƙan Boko Haram sun kai hari kan manoman shinkafa a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, inda suka kashe manoma da dama da yammacin ranar Lahadi, a lokacin da suke aiki a gonakinsu.

    Wasu manoman uku da suka tsira daga harin sun samu kulawa a asibiti.

    Bayanan da BBC ta tattara sun nuna cewa manoman sun tashi ne daga garuruwan Zabarmari zuwa Mafa inda lamarin ya faru.

    Wani mutum da BBC ta tattauna da shi, Lawal Wakili ya ce ya ce an daɗe rabon da Boko Haram su kai irin wannan hari.

    Wani manomimin mai suna Bello Zabarmari ya ce ƴan bindigar sun yi amfani da wuƙa ne suka yi wa manoman yankar rago "sun yayyanka su ne da wuƙa."

    A halin yanzu kwamishinan ƴan sanda, CP Yusufu Lawal da sauran manyan jami'an tsaro na cikin garin Zabarmari inda suke yin bincike kan lamarin.

    Har yanzu dai ba a tantance ainihin adadin manoman da abin ya shafa ba, kuma hukumomi na kokarin tattara karin bayanai.

  19. An harba makaman roka a kasuwa mai cunkoson jama'a a Sudan

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Sama da mutum 20 ne suka rasa rayukansu, kuma wasu da dama suka jikkata, yayin da wasu makaman roka suka afkawa wata kasuwa mai cike da cunkoson jama'a a Omdurman, da ke wajen birnin Khartoum, babban birnin Sudan.

    Lamarin ya faru ne biyo bayan wata mummunar musayar wuta da aka yi tsakanin sojojin Sudan da dakarun Rapid Support Forces (RSF), a cewar wani rukunin lauyoyin gaggawa na Sudan, mai zaman kanta.

    Wata majiyar lafiya ta tabbatar da cewa harin da aka kai a ranar Asabar ya kasshe rayuka 15 a unguwar Al-Thawra da ke Omdurman.

    Lauyoyin sun yi Allah-wadai da kakkausar murya ga ɓangarorin biyu saboda ci gaba da rikicin da ke faruwa a yankunan da ke da yawan jama'a tare da yin kira da a tsagaita bude wuta cikin gaggawa.

    Ana ci gaba da gwabza faɗa a babban birnin ƙasar da wasu biranen Darfur da yankin Kordofan a daidai lokacin da ake tattaunawa tsakanin dakarun da ke gaba da juna a Jeddah na ƙasar Saudiyya.

    Tun lokacin da rikicin ya fara a tsakiyar watan Afrilu, ya yi sanadin asarar rayuka sama da 9,000 tare da raba kusan mutane miliyan shida da muhallansu.

  20. Birtaniya ta janye ma'aikatan ofishin jakadancinta daga Lebanon

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, ...

    Birtaniya ta janye wasu daga cikin ma'aikatan ofishin jakadancinta da ke Lebanon na wani ɗan lokaci da 'yan uwansu sakamakon tashe-tashen hankula a yankin.

    Ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta yi nuni da halin da ake ciki a yanzu a matsayin dalilin da ya sa aka dauki matakin.

    Matakin na zuwa ne a dai dai lokacin da rikicin kan iyaka ya barke tsakanin kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon da sojojin Isra'ila a cikin 'yan makonnin nan.

    Kafofin yaɗa labaran kasar Labanon sun rawaito cewa wani harin da Isra'ila ta kai a kudancin kasar ya yi sanadin mutuwar yara uku da kakarsu.

    A martanin da kakakin sojin Isra'ila Daniel Hagari ya mayar, ya bayyana cewa an ɗauki wannan matakin ne biyo bayan harba makami mai linzami wanda ya yi sanadin mutuwar wani dan kasar Isra'ila.

    • Isra'ila ta kai hari Lebanon da Gaza da ta ce na ramuwar gayya ne
    • Malaman cocin da suka ce yaƙi ba zai sanya su guje wa Gaza ba