Girgizar ƙasa ta ɗaiɗaita dubban mutane a Nepal
Sama da kwana guda kenan da girgizar kasa ta fadawa yammacin yankin Nepal, dubban wadanda abin ya shafa na ci gaba da zama a sararin Allah alhalin ana fama da muku-mukun sanyi.
Girgizar ƙasar ta faro a daren juma'a, kuma ta fi muni a gundumar Jajakot, da yammacin Rukum.
Sama da mutum 150 ne suka mutu wasu sama da 300 suka jikkata, amma an fara sallamar masu ƙaramin rauni daga asibiti.
Jami'ai sun ce ana ci gaba da aikin ceto, sai dai yankin mai cunkson jama'a ne, yayin da dubban gidajen ƙasa suka baje a wurin.

