Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Netanyahu ya yi watsi da kiraye-kirayen tsagaita wuta

Wannan shafi ne da ke kawo mu ku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Mukhtar Adamu Bawa, A'isha Babangida, Haruna Kakangi and Ahmad Tijjani Bawage

  1. 'Sai da muka gargaɗi mazauna Gaza da miliyoyin saƙonni kafin fara kai musu hari'

    Shugaban ƙasar Isra'ila, Isaac Herzog ya ce sun gargaɗi fararen hular Gaza da miliyoyin rubuce-rubuce kafin kai musu hari.

    Ya ƙara da cewa sojojin Isra'ila sun aika da sakonnin tes ga mutanen Gaza miliyan shida, sun yi kira ta tarho ga mutane miliyan hudu, sun kuma watsar da takardu masu dauke da saƙonni miliyan 1.2.

    Herzog ya jaddada bin dokokin ƙasashen duniya gami da samar da fadakarwa da gargaɗi kafin kai wani hari.

  2. Arsenal na zawarcin ɗan wasan tsakiyan Royal Antwerp

  3. Rwanda ta ɓullo da shirin shiga ƙasar ba tare da biza ba ga duk 'yan Afirka

    Shugaban Rwanda Paul Kagame ya ɓullo da tsarin shiga ƙasarsa ba tare da biza ba ga daukacin 'yan Afirka, lamarin da ya sa ƙasar ta kasance ta hudu a Afirka da ke yin hakan.

    Shugaban ya jaddada cewa, duk wani dan Afirka a yanzu zai iya kai ziyara Rwanda kyauta, ba tare da biyan kudin biza ba.

    Ya kara da cewa, an dauki wannan mataki ne da nufin cin gajiyar harkokin yawon bude ido a nahiyar Afirka.

    Rwanda na ci gaba da wani gangami na bunkasa fannin yawon bude ido, inda ta hada gwiwa da kungiyoyin kwallon kafa irinsu Arsenal da Bayern Munich domin tallata kasar a matsayin wurin yawon bude ido.

    Yanzu Rwanda ta shiga sahun Seychelle da Gambia da Benin, a matsayin kasashen Afirka daya tilo da ke ba da izinin shiga ba tare da biza ga dukkan 'yan Afirka ba.

    Hakazalika, shugaban kasar Kenya William Ruto ya bayyana shirin kawo karshen bukatuwar biza ga dukkan masu ziyara a Afirka nan da shekara ta 2024.

    Bugu da kari, kasashen Afirka daban-daban sun ƙulla yarjejeniyoyin kasashen biyu na tafiye-tafiye ba tare da biza ba, kamar Ghana da Afirka ta Kudu, da Uganda da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo. Kongo.

  4. Surukan shugaban gwamnatin Scotland Humza Yousaf sun baro Gaza

    Yanzu muke samun labarin cewa surukan shugaban gwamnatin Scotland Humza Yousaf sun fita daga Gaza inda suka nufi kasar Masar, bayan an ritsa da su a yankin tun 7 ga watan Oktoba ranar da Hamas ta kai hare-hare kan Isra'ila.

    Suna cikin mutane sama da 100 da ke cikin wadanda aka dauki sunayensu a sashen kula da 'yan Birtaniyan da aka yarda su fita daga Gaza a yau.

    Wata sanarwa daga Humza Yousaf da matarsa Nadia El-Nakla ta ce: "Muna matukar farin cikin tabbatar da cewa mahaifan Nadia sun samu damar barin Gaza ta iyakar Rafah da safiyar yau.

  5. Muna iyakar ƙoƙari wajen dawo da waɗanda aka yi garkuwa da su - Blinken

    A cikin jawabinsa na baya-bayan nan, Blinken ya bayyana ci gaba da nuna damuwarsa ga dimbin mutanen da aka yi garkuwa da su, wadanda suka hada da Isra'ilawa da Amurkawa da daidaikun mutane daga wasu kasashe a rikicin Israi'ila da Gaza.

    Ya kuma jaddada kudurinsu na yin duk mai yiwuwa don ganin an dawo da wadannan mutane lafiya zuwa ga iyalansu da kuma ‘yan uwansu.

    An kammala taron manema labarai jim kadan bayan haka.

  6. Ambaliyar ruwa ta yi barna a wasu sassan Kenya

    Mummunar ambaliyar ruwa a Kenya ta shafe wasu tituna a wasu garuruwan ƙasar, tare da yin awon gaba da ababen hawa.

    A Mombasa, ambaliyar ruwan ta tilasta wa matafiya barin ababen hawansu, inda suka yi amfani da babura wajen isa tashar jirgin sama da tashar jirgin ƙasa.

    A garin Isiolo, ambaliyar ruwa ta yi awon gaba da wani matashi a kan babur, kuma ƙungiyar 'Save the Elephants' ta ceto mutum takwas da suka maƙale a cikin wata babbar mota da ta nutse.

    Ma'aikatar hasashen yanayi ta yi gargaɗi game da ruwan sama mai ƙarfi da ake kira El Niño da zai haifar da ambaliya, da lalata kayayyakin more rayuwa, da kuma yiyuwar asarar rayuka a Kenya da sauran ƙasashen gabashin Afirka.

    Duk da haka, shugaban ƙasar Kenya William Ruto ya yi ta ce-ce-ku-ce cewa ƙasar ba za ta fuskanci irin wannan ruwan sama mai suna El Niño ba, da ma'aikatar hasashen yanayi suka yi gargaɗin cewa ana raina yanayin da ake yi hasashe.

    • NEMA ta yi Gargadin fuskantar ambaliyar ruwa a Najeriya
    • 'Tamkar ambaliyar tsunami ce ta auka wa birnin Libya'
  7. Shin me jagoran Hezbollah mai yiwuwa zai ce?, Daga Jeremy Bowen

    Akwai mabambantan abubuwan da ke hange masu yawa game da abin da jagoran Hezbollah mai yiwuwa zai ce a jawabinsa na yammacin yau Juma'a.

    Zai iya fadar abubuwan da za su iza wuta, ko kuma ya gindaya jan layi ga Isra'ila, tare da gargadin cewa su yi hankali da kansu.

    Amma abin da 'yan Isra'ila suka fi tsoro shi ne yana iya cewa “mun hahharbo muku makamai masu linzami don haka ku yi ta kanku.”

    Hezbollah dai tana da matukar karfi fiye da na Hamas. Wani fitaccen abu da ake kiyasi shi ne suna da makamai masu linzami da rokoki iri daban-daban kimanin 150,000, wadanda akasari Iran ta samar mata, don kai wa Isra'ila hari.

    An dan yi nunin jawabin Hassan Nasrallah a tashoshin shafukan sada zumunta da wani talla mai kayatarwa, inda aka ga mai yiwuwa wani mai kamar jagoran da gemu, ya yi rawani da kuma wani katon zobe.

    Zoben yana matukar kama da zoben Qassem Soleimani, jagoran rundunar juyin-juya-hali ta Iran, ya saba sanyawa, kuma lokacin da Amurkawa suka hallaka shi a 2020, da zoben hannunsa ne kawai aka iya shaida shi.

    Don haka, kowa a yankin zai kalli wannan alamar a matsayin wani haske, da gaske kuma Isra'ila za ta yi matukar damuwa kan abin da Hezbollah za ta iya yi.

    • Mun samu rokokin zamani duk da kokarin Isra'ila na hana mu - Hezbollah
    • Rayuwa a Gaza: 'Babu wurin fakewa a ruwan makamai masu linzami'
  8. Rasha ta kai hare-hare ta sama a arewa maso gabashin Ukraine

    Rasha ta kai hare-hare ta sama da tsakar dare a arewa maso gabashin yankin Kharkiv da ke Ukraine.

    Magajin birnin ya ce an lalata ababen more rayuwa a wata gunduma, sannan gobara ta ɓarke a wurin.

    Shi ma gwamnan yankin ya ce, Rasha na kai hare-haren ne da jirage marasa matuƙa, sun kuma faɗa kan wani matsugunin farar hula.

    Kawo yanzu babu wani rahoto kan waɗanda harin ya shafa ko dai jikkata ko asarar rai.

    • Jirgin Ukraine ya kai wa jirgin ruwan Rasha hari a Bahar Aswad
    • Me ya sa alaƙar Rasha da Kim Jong Un ke neman rikita duniya?
  9. Isra'ila ta saka jami'anta cikin 'shirin ko-ta-kwana' a kan iyakarta da Lebanon

    Kakakin rundunar sojin Isra'ila Daniel Hagari ya bayar da rahoton cewa suna cikin shirin ko-ta-kwana a kan iyakar arewacin Isra'ila.

    A makonnin baya-bayan nan, an yi ta arangama a kan iyakar arewacin Isra'ila da Lebanon, wanda ya haɗa da kungiyar Hezbollah da sojojin Isra'ila.

    A yau ne ake sa ran shugaban kungiyar Hezbollah da aka ayyana a matsayin ƙungiyar ta’addanci a Birtaniya da Amurka da sauran ƙasashe, zai yi jawabi kan yaƙin Isra'ila da Gaza.

    Hagari ya kara da cewa, a jiya, sun gudanar da wani gagarumin farmaki kan wasu gungun 'yan ta'addar Hezbollah, a matsayin mayar da martani ga wani babban harin da ƙungiyar ta kai wanda ya yi sanadin jikkata fararen hula kamar yadda kamfanin dalancin labarai na reuters ya ruwaito.

    Ya jaddada cewa Isra'ila za ta mayar da martani mai karfi kan duk wani harin da aka kai wa fararen hula, kuma tana ci gaba da kasancewa cikin shiri ko ta kwana a kan iyakar arewacin kasar domin tunkarar duk wani abu da ke faruwa a cikin kwanaki masu zuwa.

    • Ko samame ta ƙasa da Isra’ila ke shirin kai wa Gaza zai yi nasara?
    • Babban asibitin Gaza na cikin mayuwacin hali sakamakon katsewar lantarki
  10. Hotunan yadda ƴan ƙasashen waje ke shirin ficewa daga Gaza

    Masu riƙe da fasfo na ƙasashen waje a Gaza na tafiya zuwa kudancin yankin, yayin da suke jiran gano sunayensu a jerin sunayen mutanen da aka bai wa damar barin Gaza ta kan iyakar Rafah.

  11. Kotu ta umarci EFCC ta saki Emefiele ko ta gurfanar da shi

    Mai shari’a Adegbola Adeniyi na babbar kotun birnin tarayya, ya bayar da umarnin a gaggauta sakin tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele ba tare da wani sharaɗi ba.

    Wannan umarni ya zo ne a matsayin martani ga wata buƙatar gaggawa da Emefiele ya shigar, inda ya buƙaci a sake shi daga hannun Hukumar Yaƙi da cin Hanci da Rashawa Ta Najeriya (EFCC).

    Kotun ta umurci hukumar EFCC ta gurfanar da Emefiele a gaban kotu a ranar Litinin 6 ga watan Nuwamba, 2023, wadda ita ce ranar da aka sanya da za a ci gaba da sauraron ƙarar da aka shigar, tare da yiwuwar kotu ta bayar da belinsa.

    Emefiele dai ya shigar da buƙatar gaggawar ne a gaban kotu, inda ya buƙaci a tilasta wa hukumar EFCC ta sake shi daga gidan yari, har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci kan shari’ar da ya dace.

    A ranar 9 ga watan Yuni ne dai shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Emefiele daga mukaminsa na shugaban babban bankin ƙasar.

    • Abin da ya kamata ku sani game da kama gwamnan CBN Emefiele
    • Tinubu ya dakatar da gwamnan CBN Emefiele
  12. Blinken ya gana da Netanyahu a Tel Aviv

    Ofishin firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya wallafa hotunan ganawarsa da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken.

    A cikin wani rubutu a kan shafin sada zumunta na X, an ambaci cewa a halin yanzu suna ganawar sirri a Kirya da ke Tel Aviv kuma ana shirin ganawa da mambobin majalisar ministocin yaƙi.

    Wannan ita ce ziyara ta uku da Blinken ya kai ƙasar tun bayan harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba.

  13. An gano gawar wata 'yar Kenya da ta bace a filin jirgin sama na Boston

    Hukumomi a Amurka da Kenya na neman wanda ya kashe wata Ba'armukiya ƴar asalin Kenya, Margaret Mbitu.

    Ƴan sanda suka ce sun gano gawarta da mugun rauni a cikin wata mota da aka ajiye a filin jirgin sama na Boston Logan dake Massachusetts.

    Babban wanda ake zargi da aikata laifin shine abokin aikin Mbitu, Kevin Kangethe, wanda ake kyautata zaton ya gudu zuwa Kenya bayan ya bar gawarta a filin jirgin sama.

    A cewar mahaifiyar Mbitu, diyarta ta dade tana kokarin kawo karshen alakarta da Kangethe.

    An ga Mbitu a raye a lokacin da ta bar wurin aiki a daren Litinin.

    • Ƴan sandan Kenya sun tono gawar mutum 21 da ake zargin Fasto ya sa su azumin mutuwa
    • Ana tuhumar mutum takwas da laifin tayar da gobarar da ta kashe 'yan ci-rani a Mexico
  14. Putin ya nuna sha'awar shiga harkar albarkatun ma'adinai a Equatorial Guinea

    Shugaba Vladimir Putin ya ce kamfanonin Rasha na da matukar sha'awar shiga harkar albarkatun ma'adinai a Equatorial Guinea.

    Shugaban ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da shugaban ƙasarEquatorial Guinea, Teodoro Obiang Nguema a birnin Moscow, inda shugabannin biyu suka amince da karfafa huldar dake tsakaninsu.

    Putin ya jaddada gagarumin damar zuba jari, musamman wajen haƙo albarkatun ma'adinai.

    Equatorial Guinea, karamar kasa ce mai arzikin man fetur a tsakiyar Afirka, tana da albarkatun ma'adinai da yawa kamar zinari da diamond da uranium da iskar gas.

    Shugaba Nguema ya yi maraba da kamfanonin ƙasar Rasha don zuba jari a ƙasarsa. Ya kuma godewa ƙasar Rasha kan sake buɗe ofishin jakadancinta a Equatorial Guinea.

    • Me ya sa Amurka ta damu da ƙawancen Putin da Kim Jong Un
    • Ukraine ba ta shirya wa zaman lafiya ba - Putin
  15. Masu masana'antu sun nuna damuwa yayin da farashin dizal ke ƙara hauhawa

    Masu masana’antun na nuna matukar damuwa yayin da farashin man dizal ke ci gaba da hauhawa, inda ya kai Naira 1,275 a kowace lita a Legas, sannan ya haura Naira 1,300 a yankunan da ke wajen jihar.

    Jaridar Daily trust ta ruwaito cewa wannan ƙarin farashin man dizal ya yi kamari a wasu yankuna, inda farashin litar ya kai Naira 1,270 a jihar Kano, wanda ya ma fi girma a wajen birnin.

    Tabarbarewar farashin man dizal na haifar da fargaba a tsakanin masu ruwa da tsaki domin ya zama babbar barazana ga al'ummar kasar da tuni ke kokawa da hauhawar farashin kayayyaki.

    • Tashin farashin Gas ɗin girki na ƙara damun magidanta a Najeriya
    • Farashin man fetur zai iya ƙaruwa saboda tashin dala
  16. Blinken ya isa Isra'ila don ganawa da Netanyahu

    Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken na ganawa da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, bayan ya isa ƙasar a wata ziyara da ya kai ƙasashen Isra'ila da Jordan.

    Wannan ce ziyara karo na biyu tun bayan ɓarkewar yaki tsakanin Hamas da Isra'ila.

    Zai tattauna da jami'an Isra'ila kan yadda za a dakatar da hare-haren soji da fafatawa ta ƙasa.

    Ya kuma ce zai ci gaba da matsa lambar ganin an ci gaba da shigar da agaji zuwa Gaza da kuma kwashe Amurkawan da suka maƙale a can.

    A gobe Asabar ake sa ran, ministan harkokin Jordan, Ayman Safadi, zai gana da Mista Blinken.

    Inda za su tattauna kan halin da Falasdinawa ke ciki a Gaza, da buƙatar daukr matakin gaggawa na dakatar da yaƙin, da bai wa farar hula kariya, yayin da ita kuma Isra'ila ya zama wajibi ta mutunta yarjejeniyar ƙasa da ƙasa.

    • Rikicin Isra'ila da Gaza: Mene ne asalin sa?
    • Shugabannin Saudiyya da Iran karon farko sun tattauna a kan rikicin Gaza
  17. Shugaban Hezbollah zai yi jawabi kan yaƙin Isra'ila da Gaza

    Nan gaba a yau ake sa ran shugaban ƙungiyar, Hezbollah ta Lebanon,zai gabatar da jawabi na farko tun bayan ɓarkewar yaki tsakanin ƙungiyar Hamas da Isra'ila.

    Za dai a sanya ido da kaffa-kaffa kan jawabin na Hassan Nasrallah, inda ake bayyana damuwa kan watakil zai iya yin hannun ka mai sanda kan shigar Hezbollah yakin ake yi a Gaza.

    Tuni mayakan Hezbollah suka fara taho mu gama da sojojin Isra'ila a iyakar kasasashen biyu, ana kuma fargaba kan kungiyar ka iya zama wata jagaba a yakin.

    A bangare guda Isra'ila ta gargadi Hezbolla, kan matukar bata janye daga tsoma baki a yakin ba za ta mai da kakkausan martani idan har ta dauki matakin shiga yakin.

    • Mutanen da ƙungiyar Hamas ke garkuwa da su tsawon shekaru
    • Yadda gawawwaki suka mamaye asibitocin Gaza
  18. Isra'ila ta ce sojojinta sun yi wa Gaza ƙawanya

    Isra'ila ta ce sojojinta sun kewaye birnin Gaza, tare da fara fafatawa ta ƙasa da mayaƙan Hamas.

    Ta ce ana fafatawar a wuraren wasu gine-gine, da ta yi amanna na daga cikin ababen more rayuwa da Hamas ta gina da ta yi ikirarin tana gab da lalata su baki daya.

    Wakilin BBC ya ce ana ci gaba da fafatawa ta ƙasa, kuma an kashe sojojin Isra'ila 19, akwai ƙananan ƙauyuka akan hanyar shiga birnin Gaza, amma da zarar an nausa ciki lamarin zai ɗauki sabon salo.

    A bangare guda 'yan majalisar Isra'ila sun sanar da mayar da 'yan Gaza da ke aiki a Isra'ila zuwa inda sukai wa ƙawanya.

    • Tawagar ƙwararru ta MDD ta buƙaci Isra’ila ta tsagaita buɗe wuta a Gaza
    • Halin da aka shiga a Gaza ranar da aka katse hanyoyin sadarwa
  19. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkan mu da safiyar wannan rana ta Juma'a.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a wannan lokaci, don kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a fadin duniya.