Rufewa
Mun zo ƙarshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Kada ku manta za ku iya duba ƙasa don ci gaba da karanta labaran da muka wallafa muku.
Ahmad Tijjani Bawage ke cewa mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo mu ku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Mukhtar Adamu Bawa, A'isha Babangida, Haruna Kakangi and Ahmad Tijjani Bawage
Mun zo ƙarshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Kada ku manta za ku iya duba ƙasa don ci gaba da karanta labaran da muka wallafa muku.
Ahmad Tijjani Bawage ke cewa mu kwana lafiya.
Fadar shugaban Najeriya ta ce Faransa za ta dawo wa ƙasar dala miliyan 150 na kuɗin da tsohon Shugaban mulkin sojin Najeriya, Janar Sani Abacha ya sata.
Fadar shugaban ƙasar ta bayyana haka ne a yau Juma'a lokacin da shugaba Tinubu ya karɓi bakuncin ministar Turai da harkokin wajen Faransa, Catherine Colonna, a fadarsa da ke Abuja.
Tinubu ya ce ya ji daɗin labarin dawowa Najeriya kuɗin Abacha da Faransa ke shirin yi, inda ya ce za a yi amfani da kuɗin wajen samar da ci gaba a ƙasar.
Shugaban ya kuma yi farin ciki da irin ƙaruwar hulɗar dangantaka tsakanin ƙasashen biyu, musamman ma a ɓangaren sauyin yanayi, ci gaban tattalin arziki, ilimi da kuma raya al'adu.
Tinubu ya kuma yaba da rattaɓa hannu kan yarjejeniyar Yuro miliyan 100 tsakanin Najeriya da Faransa don tallafawa shirin i-DICE - wani shiri na Gwamnatin Tarayya na inganta zuba jari a Fasahar Sadarwa da kuma Masana'antu na Fasaha.
Ministan sadarwa da kirkire-kirkire, Dr Bosun Tijani, da ministan harkokin kasashen waje na kasar Faransa ne suka rattaƁa hannu kan yarjejeniyar a wani taro da aka yi a gidan Tafawa Ɓalewa, a hedkwatar ma’aikatar harkokin wajen.
A nata jawabin, ministar ta ƙasar Faransa ta miƙa sakon fatan alheri na shugaba Emmanuel Macron tare da bayyana shirin Faransa na faɗaɗa haɗin gwiwa da Najeriya a ɓangarori da dama.
Ma'aikatar lafiya ta Hamas ta ce sojojin Isra'ila sun kai hari ta sama kan motocin ɗaukar marasa lafiya a Gaza, inda gwamman mutane suka mutu tare da jikkata wasu da dama.
An ga hotunan Falasɗinawa kwance cikin jini.
Hakan na zuwa ne sa'o'i bayan ziyarar sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken, inda ya roki Isra'ilar da ta daina kai hare-hare kan fafaren hula.
Sojojin Isra'ila sun tabbatar da kai harin, suna masu cewa akwai Hamas cikin masu amfani da motocin.
Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kashe ƴan bindiga huɗu a ƙauyen Kampanin Doka a karamar hukumar birnin Gwari na jihar Kaduna.
Wata sanarwa da sojojin suka fitar, ta ce sun samu nasarar kashe ƴan bindigar ne a ranar 1 ga watan Nuwamba a wani samame da suka kai ƙauyen.
Sojojin sun ce sun kwato bindigar AK 47, da harsasai, da adda guda ɗaya, wayar tarho, da kuma babura 14 daga hannun ɓata-garin.
A wani samame na daban da sojojin suka yi ranar 2 ga watan Nuwamba a ƙauyen Sabon Sara, sun ce sun kashe wani ɗan bindiga ɗaya, wasu kuma suka tsere da raunukan bindiga, bayan da wasu manoma suka kai musu rahoton ganin ƴan bindigar.
"Mun ƙwato bindigar AK 47 guda biyu, yayin da ɗaya daga cikin manoman da ya samu rauni muka ɗauke shi zuwa wani asibitin sojoji da ke kusa don yi masa magani," in ji sanarwar sojojin.
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya yi watsi da kiraye-kirayen tsagaita wuta a yaƙi da Hamas.
Da yake magana a wani jawabi da aka watsa a gidan talabijin, Netanyahu ya ce ba zai amince da yunkurin ba har sai Hamas ta saki ƴan ƙasar da tayi garkuwa da su a harin da ta kai ranar 7 ga watan Oktoba.
Yana jawabi ne jim kaɗan bayan Sakataren harkokin tsaron Amurka Antony Blinken ya ƙara yin kira na tsagaita wuta na wucin gadi don bai wa ƙarin kayan agaji damar shiga Gaza,
Blinken ya kuma ce hakan zai samar da yanayin muhalli mai kyau ta yadda za a saki waɗanda aka yi garkuwa da su.
Sai dai Netanyahu ya ce: "Isra'ila ta ki amincewa da buƙatar tsagaita wuta na wucin gadi ba tare da saka batun sako waɗanda aka yi garkuwa da su ba."
Jami'in bayar da agaji a Falasɗinu na hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya, ya ce an kashe jami'an MDD 72 tun bayan soma yaƙin Isra'ila da Gaza.
Ɗaya daga cikinsu mai buƙata ta musamman ce mai sama da shekaru ashirin wadda aka kashe a arewacin Gaza tare da iyalanta, kamar yadda mai magana da yawun hukumar, Juliette Touma ta shaida wa BBC.
MDD ta tsugunar da mutane 700,000 a sansanoni daban-daban - inda sama da 100 ke amfani da bayan gida guda ɗaya a wasu sansanonin, a cewar Touma.
Ta ƙara nanata kiran da MDD tayi na tsagaita wuta, inda ta ce abu ne da ake buƙata.
Isra'ila ta yi watsi da buƙatar tsagaita wuta, kuma ƙasashe da dama, ciki har da Birtaniya da Amurka - waɗanda sakataren tsaronsu Antony Blinken ke Isra'ila a halin yanzu -ba su shiga cikin kiran tsagaita wuta da MDD tayi ba, maimakon haka ma kira suke yi na dakatar da faɗan na wani lokaci domin ba da damar kai kayan agaji.
Gamayyar ƙungiyoyin ƴan ƙwadago a Najeriya na NLC da TUC sun bayyana aniyarsu ta shiga yajin aikin gama-gari sanadiyyar kamawa da kuma dukan da aka yi wa shugaban ƙungiyar NLC, Joe Ajaero.
Ƙungiyar ta sanar da batun yajin aikin, wanda zai gudana a ranar Laraba ne a wata tattaunawa da manema labaru ranar Juma'a, a Abuja.
Shugabannin ƙungiyoyin sun bayyana cewa sun kuma bai wa Gwamnatin Tarayya sharuɗɗa shida da suke so a cika, ciki akwai sauke kwamishinan ƴan sanda na jihar Imo, da babban jami'in ƴan sanda na yankin da lamarin ya faru bisa zargin su da hannu a 'cin zarafi da kuma wulaƙanta Mista Ajaero da sauran ƴaƴan ƙungiyar."
Hukumar samar da abinci da bunkasa noma ta duniya ta ce 'yan Najeriya akalla miliyan biyu da dubu 600, a jihohin Borno da Sokoto da Zamfara da kuma babban birnin kasar Abuja, na iya fuskantar matsalar rashin abinci a tsakanin watan Yuni da Agustan 2024.
Wakilin hukumar, Dr. Abubakar Suleiman ne, ya bayyana haka yayin gabatar da bayani na gargadin wurwuri ranar Juma'a a Abuja.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa bayanin, wani bangare ne na rahoto a kan tabbacin halin wadata al'umma da abinci, da kuma hasashe game da halin da za a shiga nan gaba.
A cewarsa, halin da ake ciki yanzu ya faru ne bayan wata damuna da ba a saba da ganin irin ta ba, wadda aka samu matsaloli da dama, wanda suka haɗa da ta'azzarar halin rashin tsaro kamar rikicin ƴan tayar-da-ƙayar-baya da na ƴan fashin daji.
Shugaban kungiyar Hizbullah, mafi karfi a fagen siyasa da na soji a kasar Lebanon, Hassan Nasrallah,, ya yaba da hare-haren da Hamas ta kai a Isra'ila a ranar 7 ga Oktoba wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutum 1,400
Ya faɗi hakan ne a jawabinsa na farko kan yaƙin Gaza.
Ya ce ayyukan Hamas - wadda ƙasashen yamma ke kallo a matsayin ƙungiyar ta'addanci kamar Hezbollah - daidai ne amma kuma ya ce zallar Falasɗinawa ne suka tsara hare-haren.
A cikin jawabin nasa, ya caccaki Amurka, yana mai cewa ita ce ke da alhakin yaƙin Gaza.
Nasrallah ya kuma godewa sojojin da Iran ke marawa baya a kasashen Yaman da Iraki.
'Yan tawayen Houthi a Yaman dai na ci gaba da harba jiragen sama marasa matuka kan Isra'ila, yayin da mayakan Shi'a na Iraƙi ke kai wa sojojin Amurka hari a Iraki da Siriya."
Rundunar hadin gwiwa ta Operation Delta Safe (OPDS) ta kama wani jirgin ruwa tare da ma’aikatansa biyu a jihar Ribas, ɗauke da lita 300,000 na gas da aka tace ba bisa ƙa’ida ba.
An kama jirgin ne a tashar jirgin ruwa da ke Onne, a jihar Ribas cikin kogin Bonny.
Commodore John Siyanbade, wanda ke wakiltar kwamandan OPDS, Olusegun Ferreira ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Fatakwal.
An kama jirgin ruwan ne a ranar 29 ga Oktoba, 2023.
Jirgin yana jigilar gas ne ba bisa ƙa'ida ba, kuma ana amfani da shi a zaman wurin ajiyar wannan haramtaccen kayan.
An tsare mutane biyu da ake zargi da ke cikin jirgin kuma za a miƙa su ga hukumomin da suka dace domin gurfanar da su a gaban kuliya.
Kwamanda Siyanbade ya kuma yi gargaɗi ga duk masu hannu a irin wannan ayyukan da su daina ayyukansu cikin gaggawa domin gujewa fuskantar shari’a.
A yau ne shugaban ƙungiyar Hezbolla, Hassan Nasrallah ya gabatar da jawabi. Kuma jawabin nasa ya mayar da hankali ne kacokan kan rikicin da ke wakana a Gaza, tsakanin Isra'ila da Hams.
To amma me ya sa jawabin na shugaban Hezbollah ya zamo abin ce-ce-ku-ce a wannan lokaci?
Ƙarfin soji da na siyasa
Hezbollah ƙungiya ce da mabiya aƙidar Shi'a suka kafa wadda ke da gagarumin tasiri a ɓangaren siyasa kuma ita ce ke iko da dakarun soji mafi ƙarfi a Lebanon.
Ƙasar Iran ce ta kafa ƙungiyar a farkon shekarun 1980 don ƙalubalantar Isra'ila, wadda dakarunta suka mamaye kudancin Isra'ila a lokacin yaƙin basasar ƙasar.
Hezbollah ta shiga zaɓukan ƙasar tun shekarar 1992 kuma ta kasance tana taka rawa sosai a harkar siyasar ƙasar.
Munanan hare-hare
Mayaƙan Hezbollah sun ƙaddamar da munanan hare-hare kan Isra'ila da kuma dakarun Amurka da ke Lebanon, sannan a lokacin da Isra'ila ta janye daga Lebanon a 2020, Hezbollah ta ce ita ce ta kore ta.
Tun daga wancan lokacin ne Hezbollah ke da dubban mayaƙa da gagarumin rumbun miyagun makamai a kudancin Lebanon, kuma ƙungiyar ta ci gaba da adawa da kasancewar Isra'ila a wasu wurare na kan iyaka da ake taƙaddama a kai.
Ƙasashen Yamma da Isra'ila da kuma ƙasashen yankin Gulf da Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa duk sun ayyana Hezbollah a matsayin ƙungiyar ƴan ta'adda.
Tarihin adawarta da Isra'ila
A shekarar 2006 ne yaƙi ya ɓarke tsakanin Hezbollah da Isra'ila bayan da mayaƙan Hezbollah suka kai wani mummunan samame a yankin Isra'ila.
Sojojin Isra'ila sun yi yunƙurin ganin sun kawar da duk wata barazana daga Hezbollah, sai dai ba su yi nasara ba.
Kuma tun daga wancan lokacin Hezbollah ta ci gaba da ƙara yawan dakarunta tare da tara muyagun makamai.
Jagoran Hezbollah Hassan Nasrallah yana gabatar da jawabi tsawon 'yan mintuna kalilan yanzu.
Yana yabawa hare-haren da Hamas ta kai na ranar 7 ga watan Oktoba a kan Isra'ila, wanda ya yi sanadin kashe fiye da mutum 1,400.
Wakilin BBC a yankin Gabas ta Tsakiya na kallon jawabin kuma za mu kawo muku sharhi kan abin da ya ce da kuma abin da hakan ke nufi kan yakin da ake ci gaba da gwabzawa.
A yanzu kuma, ga bayani game da jagoran wanda ba a cika gani a bainar jama'a ba, na kungiyar da Birtaniya da Amurka da Isra'ila da kuma karin wasu kasashe, suka ayyana a matsayin ta 'yan ta'adda.
Malamin mai bin mazhabar Shi'a, shi ne ke jagorantar Hezbollah tun daga 1992, kuma Nasrallah ya ba da gagarumar gudunmawa wajen mayar da ita kungiyar siyasa da runduna mai karfin soja.
Yana da alaka ta kukut da kasar Iran da kuma jagoran addininta, Ayatollah Ali Khamenei, tun daga 1981, lokacin da jagoran addinin Iran na farko, Ayatollah Ruhollah Khomeini, ya nada shi wakilinsa na musamman a Lebanon.
Tsawon shekaru kenan, ba a ga Nasrallah a bainar jama'a ba, kamar yadda ake zargi saboda tsoron kada Isra'ila ta hallaka shi.
Sai dai ya kasance abin matukar martabawa daga Hezbolla kuma yana gabatar da jawabansa ta talbijin a duk mako.
Dakarun haɗin gwiwar sojojin Najeriya da na jami'an DSS sun ce sun yi nasarar daƙile wani hari da wasu 'yan tayar da ƙayar bayan Boko Haram suka shirya kai wa a Kano da ke arewacin ƙasar.
Cikin wata sanarwa da rundunar sojin ƙasar ta wallafa a shafinta an X ta ce, hadin gwiwar jami'an tsaron kai wani ƙaramar hukumar Gezawa da ke jihar Kano, da nufin ganowa tare da kama wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne da ake kyautata zaton suna shirin wani gagarumin farmaki a Kano.
Sanarwar ta ce a lokacin samamen, jami'an tsaron sun kama mutum biyu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne, kuma an ƙwato manyan makamai da ababen fashewa.
"Wannan farmakin ya nuna kyakkyawan hadin gwiwa da ke tsakanin jami’an tsaron da kuma jajircewar sojojin Najeriya da sauran jami’an tsaro na dakile ta’addanci da kuma inganta tsaro a faɗin ƙasar", kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Rundunar Sojin ƙasar ta ƙarfafa wa jama’a gwiwa don bayar da muhimman bayanan da za su taimaka wa ƙoƙarin suke yi yi na magance matsalar tsaro a ƙasar.
Shugaban ƙungiyar Hizbullah, Hassan Nasrallah ya fara gabatar da jawabinsa karon farko tun bayan ɓarkewar rikicin baya-bayan nan na Isra'ila da Gaza.
Har yanzu dai ba a bayyana daga inda yake jawabin nasa ba.
Dubban mutane ne ke kallon jawabjin nasa a akwatunan talbijin, ciki har da dimbin magoya bayansa da suka taru a Beirut, babban birnin ƙasar Lebanon.
Ƙasashen Birtaniya da Amurka da sauran ƙasashen Yamma na kallon Hezbollah a matsayin ƙungiyar ta'addanci.
Ƙungiyar dai na da gagarumin tasiri a fagen siyasa da na soja a ƙasar Lebanon.