Boko Haram ta kashe aƙalla mutum 40 a Yobe - Ƴan sanda

Wannan shafi ne da ke kawo mu ku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida and Umar Mikail

  1. Motocin ɗaukar marasa lafiya sun isa Masar daga Gaza

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Motocin ɗaukar marasa lafiya na farko dauke da Falasɗinawan da suka jikkata daga Gaza sun tsallaka zuwa Masar ta kan iyakar Rafah, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta tabbatar.

    Tawagar BBC a birnin Alkahira ta ce aƙalla mutane bakwai ne suka tsallaka zuwa Masar ya zuwa yanzu kuma ana sa ran dayawa za su biyo baya.

    Mun ji cewa a yau za a bar Falasdinawa 88 da suka jikkata zuwa Masar don yi musu magani, sannan kuma za a bar wasu ‘yan kasashen waje 500 su fita zuwa Masar su ma.

    • Ƙungiyar Red Cross ta yi kiran a gagguta tsagaita wuta a Gaza
    • Halin da aka shiga a Gaza ranar da aka katse hanyoyin sadarwa
  2. Ba zan yarda na rasa tasirina na siyasa ba - Nyesom Wike

    Ministan Abuja ya yi karin haske a kan rikicin siyasar da ya dabaibaye siyasar jiharsa ta Ribas, kan yunkurin tsige Gwamna Siminalayi Fubara na jihar mai arzikin man fetur.

    Da yake karbar shugabannin yankin Kudu maso Kudu a ofishinsa ranar Talata, Nyesom Wike, wanda ya kammala wa'adi biyu na mulkin jihar a matsayin gwamna, ya jaddada muhimmancin rike jihar da yake da karfi don ci gaba da samun tasiri a siyasance.

    Ya nanata cewa da zarar ya rasa makarfafarsa a matsayinsa na dan siyasa, shi kenan ya rasa tasirinsa na siyasa.

    Wike ya bayyana cewa babu wani kazafi da za a yi masa, wanda zai hana shi barci da minshari. A cewarsa, dole ne sai an yi abin da ya dace.

    “Dukkanmu muna son kasancewa masu tasiri a fagen siyasa; dukkanmu muna son ci gaba da rike tsarinmu na siyasa,” ministan ya ce.

    “Idan martabar siyasarka ce? Shin za ka bari kawai, wani ya zo ya yi jifa da kai waje? Kowa yana da makarfafarsa.

    Idan ka kwace min makarfafata, ina da sauran tasiri kenan a siyasance?” Tashar talbijin ta Channels ta ruwaito cewa dangantaka tsakanin Wike da Fubara ta yi tsami sanadin barazanar da majalisar dokokin jihar suke yi ta tsige gwamnan.

    Wasu sun zargi Wike da hannu a makarkashiyar tsige gwamnan. Ginin Majalisar dokokin jihar Ribas ya hargitse zuwa wani fagen dambe bayan gobara ta tashi a wani bangaren ginin a daren Lahadi.

    • Ƙuri'un da ba za a iya bayaninsu ba a zaɓen Najeriya mai cike da taƙaddama
    • Yadda Wike ya tayar da ƙura bayan naɗa shi ministan Abuja
  3. Ƴan gudun hijirar Afganistan na barin Pakistan ba tare da komai ba

    ...
    Bayanan hoto, ...

    Pakistan ta fara kamen 'yan ƙasar Afganistan a daidai lokacin da ƙasar ta fara aikin korar ƴan gudun hijira da ba su ta takardar izinin zama.

    Duk da cewa dubban 'yan Afghanistan da suka koma gida a cikin watanni biyun da suka gabata, da dama sun ce ba sa son barin Pakistan saboda tsoron gwamnatin Taliban.

    Mutane da dama masu shekaru daban-daban na zaune a iyakar Pakistan da Afganistan a kan tarin kayayyaki da suka hada da kayan ɗaki da itacen wuta da injin dafa abinci da sauransu.

    Abdullah, wanda tawagar BBC ta haɗu da shi a wani gidan mai da ke lardin Punjab, ya ɗauki hayar motar ɗaukar kaya domin ya kwashe iyalansa 22, inda 20 daga cikinsu haifaffun Pakistan ne.

    Ya ce ya zo Pakistan ne a lokacin yaƙin Rasha kuma ya yi aiki a matsayin lebura.

    Yana nuna baƙin cikin barin gidansa da ya gina da kanshi da laka.

    Ya danganta tafiyar tasu da ''muguwar manufar gwamnati''.

    • Afghanistan: Ina duka 'yan gudun hijira za su tafi bayan Taliban ta karbe iko?
    • Fargaba ta ƙaru kan yiwuwar ɓallewar yaƙin basasa a wata jihar Indiya
  4. Labarai da dumi-dumi, 'An kashe mutum 8,796 a Gaza tun daga ranar 7 ga Oktoba'

    Ma'aikatar lafiya ta Hamas a Gaza ta ce mutum 8,796 ne aka kashe a can tun bayan fara yaƙin Isra'ila da Hamas.

    Hakan ya nuna ƙaruwar 271 daga adadin na ranar Talata wanda ya tsaya kan 8,525.

    Ma'aikatar ta ce 3,648 daga cikin waɗanda aka kashe a Zirin Gaza ƙananan yara ne.

    Isra'ila dai ta fara kai hare-hare ta sama a Gaza bayan Hamas ta ƙaddamar da munanan hare-hare a ranar 7 ga Oktoba.

    • Mummunan harin ba-zata da Hamas ta kaddamar a kan Isra'ila
    • Dalilai huɗu da suka sa Hamas ta kai wa Isra'ila hari
  5. WHO ta yi maraba da matakin Masar na karɓar marasa lafiya daga Gaza

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya yi maraba da yarjejeniyar jigilar mutanen da suka samu munanan raunuka daga Gaza zuwa Masar.

    A cikin wani sakon da ya wallafa a shafukan sada zumunta, ya ambato ci gaba da hadin gwiwa da ma'aikatar lafiya ta Masar da kuma ci gaba da ba da taimako tare da jaddada bukatar gaggauta ƙaruwar agajin jinya zuwa Gaza.

    Tedros ya kuma jaddada muhimmancin kare asibitoci daga harin bama-bamai da kuma amfani da sojoji."

    • Bayani kan hanya ɗaya tilo da Falasɗinawa za su iya fita daga Gaza
    • Rikicin Isra'ila da Gaza: Mene ne asalin sa?
  6. Tabbas Bazoum ya so tserewa daga Nijar - Babban mai shigar da ƙara

    ...

    Asalin hoton, ORTN

    Babban mai shigar da ƙara a jamhuriyar Nijar ya bayyana cewa hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum tabbas ya yi yunkurin tserewa daga ƙasar, duk da musantawar da lauyoyinsa suka yi da farko.

    Shugaba Bazoum, wanda sojoji suka yi wa juyin mulki a ranar 26 ga watan Yuli, ya kasance tsare a gidansa da ke cikin fadar shugaban ƙasa, tare da iyalansa, tun bayan juyin mulkin.

    Makarkashiyar tserewar da ake zargi, ta haɗa da fara zuwa wajen wata maboyar da ke wajen babban birnin ƙasar Yamai, kafin a yi amfani da jirgin helikwafta "na wasu kasashen waje" domin daukarsa zuwa Najeriya, kamar yadda mai magana da yawun gwamnatin ta gidan talbijin din kasar ya bayyana.

    Babban mai gabatar da ƙara, Salissou Chaibou, ya tabbatar da cikakkun bayanai kan "shirin tserewar" da gwamnatin soja ta zayyana.

    Chaibou ya bayyana cewa jami'an tsaron fadar shugaban kasar sun kama Bazoum, tare da iyalansa, da jami'an tsaro, da ma'aikatansa dauke da kaya iri-iri,a daren ranar 18 ga watan Oktoba lokacin da suke yunkurin fita.

    Binciken da aka yi na jakar Bazoum ya kai ga gano wasu makudan kuɗade na gida da na kasashen waje, da kuma kayayyaki masu daraja iri-iri.

    • Bazoum ya musanta zargin tserewa daga Nijar
    • Ci gaba da tsare Mohamed Bazoum na jawo ƙarin barazana
  7. 'Motocin daukar marasa lafiya na farko sun shiga Masar'

    Kamfanonin dillancin labarai na Reuters da AFP sun ruwaito cewa motocin daukar marasa lafiya na farko dauke da mutane daga Gaza sun shiga Masar ta mashigar Rafah.

    Hukumomin sun ambaci jami'ai a Masar.

    • Ana damuwa kan yawaitar kisan ƴan jarida a rikicin Isra'ila da Falasɗinawa
    • Halin da aka shiga a Gaza ranar da aka katse hanyoyin sadarwa
  8. Hotunan Falasɗinawan da suka jikkata suna jiran barin Gaza

    Ga wasu hotuna daga yankin Gaza da ke kan iyakar Rafah inda Falasɗinawan da suka jikkata ke jiran a kai su Masar domin yi musu magani.

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    ...

    Asalin hoton, Reuters

  9. Al'ummar Kenya sun fusata kan sabon harajin kaya ga matafiya

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, ...

    Al’ummar Kenya na zanga-zangar nuna rashin amincewa da umarnin da Hukumar Tara Haraji ta Kenya (KRA) ta bayar na biyan harajin kaya ko kayan gida da kimarsu ta kai dala 500, ko sama da haka ga masu yawon bude ido da kuma ƴan ƙasar da ke komawa daga kasashen waje.

    Hukumar ta bayyana cewa duk wani kaya, sababbi ko tsofaffi, wadanda suka wuce wannan adadin sai an biya musu haraji.

    Wannan matakin ya tayar da hankulan jama'a, tare da fargabar cewa hakan na iya hana masu yawon bude ido shiga ƙasar.

    Wasu 'yan majalisar sun yi ikirarin cewa hukumar haraji ta KRA na amfani da wannan umarni wajen musgunawa 'yan yawon bude ido, abin da zai iya bata martabar ƙasar.

    Wannan umarni na cikin jerin sabbin haraje-haraje da gwamnatin Shugaba William Ruto ta bullo da su, da ke yin tasiri ga halin tsadar rayuwa.

    Hakan dai na zuwa ne duk da alƙawarin da Ruto ya yi a zaɓen ƙasar na rage matsalolin kudi da iyalai ke fuskanta.

    • Shugaban Kenya ya nemi afuwar al'ummar ƙasar kan mace-macen masu azumi
    • Yadda kantin sauƙi na 'yan China ke barazana ga 'yan kasuwar Kenya
  10. Gwamnonin PDP za su gana da Wike a yau

    ...

    Gwamnonin jam’iyyar PDP a yau, Laraba za su gana da ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, kan halin da ake ciki a siyasar jihar Ribas, yayin da ake neman tsige gwamnan jihar, Siminalayi Fubara.

    Babban daraktan kungiyar gwamnonin PDP, CID Maduabum, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar bayan wani taro ranar Talata.

    Shugaban ƙungiyar, Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ne, zai jagoranci gwamnoni kusan 10 na jam’iyyar zuwa ofishin ministan babban birnin tarayya Abuja domin gudanar da tattaunawa.

    • Yadda Wike ya tayar da ƙura bayan naɗa shi ministan Abuja
    • Me zai faru a jihar Ribas bayan soke ‘yan takara ta APC
  11. Ƴan tawayen Mali sun yi iƙirarin ƙwace sansanin Kidal bayan ficewar MDD

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Ƴan tawayen Abzinawa a Ƙasar Mali sun sun ce sun karɓe iko da wani sansani a Kidal da ke arewacin kasar, wanda dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya suka fice.

    Tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Mali (Minusma) ta yi gaggawar barin Kidal bayan ta sha fama da hare-haren bama-bamai guda biyu a kan hanyarta ta zuwa Gao, wani garin arewacin kasar.

    Haɗaddiyar ƙungiyar Abzinawa ta bayyana nasarar da ta samu a shafukan sada zumunta tare da mamaye sansanin Kidal nan da nan bayan tafiyar tawagar MDD.

    Wannan dai shi ne zango na uku kuma na karshe da tawagar Majalisar Dinkin Duniya ta kwashe a yankin Kidal da ke fuskantar tashin hankali daga masu iƙirarin jihadi da kungiyoyin 'yan aware.

    A baya-bayan nan ne dai waɗannan kungiyoyin ‘yan awaren da ke karkashin yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta da mahukuntan ƙasar, sun sake ci gaba da gwabza fada, musamman na adawa da mika sansanonin su ga sojojin Mali.

    Gwamnatin mulkin sojan Mali ta buƙaci dakarun Majalisar Dinkin Duniya da su fice daga ƙasar nan da karshen wannan shekara, saboda aikin da aka kwashe shekaru 10 ana yi na yaƙi da masu iƙirarin jihadi wanda bai cimma manufarta ba.

    • Rayuwa a biranen Mali da ƴan bindiga suka yi wa ƙawanya
    • Mali: Kasashen Yamma sun soki kasar Rasha kan ‘aikewa’ da sojojin haya
  12. An ɗaure wanda ya kitsa juyin mulkin Gambia shekaru 12 a gidan yari

    ...

    Asalin hoton, Alia Fadera

    Wani ƙaramin jami’in sojan ruwa da gwamnatin Gambia ta bayyana a matsayin wanda ya kitsa yunƙurin juyin mulki a watan Disambar bara, an same shi da laifin cin amanar ƙasa tare da yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 12 a gidan yari.

    Wata babbar kotu a ranar Talata ta yanke hukuncin cewa Lans Kofur Sanna Fadera ya shirya tare da yunƙurin hamɓarar da zaɓaɓɓiyar gwamnatin shugaba Adama Barrow ba bisa ka'ida ba.

    Hukumomin ƙasar dai sun tuhumi Fadera da wasu sojoji bakwai da laifin cin amanar ƙasa, da haɗa baki da kuma tayar da ƙayar baya, bisa zarginsu da hannu a yunƙurin juyin mulkin shekarar 2022.

    Kotun ta sallami wasu jami’an soji uku a ranar Talata.

    Kotun ta kuma wanke wani ɗan sanda da wasu fararen hula biyu da ake tuhuma da laifin ɓoye cin amanar ƙasa da kuma haɗa baki wajen aikata manyan laifuka.

    • Wani sojan ruwa ne ya jagoranci yunkurin juyin mulki a Gambia - Gwamnati
    • Tarihin mai gadin da ya zama shugaban kasar Gambia
  13. Hotunan asibitin wucin gadi na Masar da aka gina a kusa da Gaza

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ga hotunan farko na asibitin filin Masar da aka gina a Sheikh Zuweid kusa da kan iyakar Rafah a Masar.

    An gina asibitin ne don kula da mutanen da suka jikkata da ke tsallakawa daga Gaza.

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

  14. Motocin ɗaukar marasa lafiya a kofar Rafah na shirin tashi zuwa Masar

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Ga wasu hotuna kai tsaye na jerin motocin daukar marasa lafiya da suka isa kan iyakar Rafah - amma babu tabbas ko har yanzu ba su sami damar tsallakawa zuwa Masar ba.

    Tun da farko dai motocin daukar marasa lafiya sun tsallaka zuwa Gaza daga bangaren Masar don tattara mutanen da suka samu raunuka domin kawo musu magani a Masar.

    Wakilin BBC, Rushdi Abu Alouf a Gaza ya ce Masar na gina wani asibiti mai nisan kilomita 10 daga kan iyaka.

    ...

    Asalin hoton, Reuters

  15. Falasɗinawa 88 da aka ji wa raunuka ne za su bar Gaza

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Ɗaruruwan mutane ciki har da iyalai masu yara suna jira dauke da jakunkuna a wajen tashar iyakar Rafah zaune a ƙasa yayin da suke sa ran za a bar su su tsallaka zuwa Masar nan ba da jimawa ba.

    Babu alamun motocin ɗaukar marasa lafiya ko waɗanda suka jikkata sun shiga Masar, kodayake ana iya samun shirye-shirye na musamman ga waɗanda ke bukatar magani.

    A cewar hukumomin yankin, ana sa ran za a ba da izini ga mutane 88 da suka jikkata zuwa cikin Masar.

    An yi imanin cewa Masar na shirin kafa wani asibiti mai nisan kilomita 10 daga kan iyakar.

    ...

    Asalin hoton, Reuters

  16. An buɗe iyakar Rafah ga wasu 'yan ƙasashen waje a karon farko

    Rafah Crossing

    Asalin hoton, Reuters

    Dubban jama'a na jira a iyakar Rafah bayan da aka buɗe ƙofofin shiga cikin Masar.

    Akwai hotuna kai tsaye na ɗimbin jama'a da ke jira don wucewa ta kan iyakar.

    Tun da farko, motocin ɗaukar marasa lafiya sun tsallaka daga Masar zuwa yankin Gaza don tattara mutanen da suka jikkata .

    Ya zuwa yanzu mutanen da Hamas ta kama ta sake su ne kaɗai fararen hulan da suka bar Gaza tun daga ranar 7 ga Oktoba - kasancewar duka hanyoyin a rufe.

    An sami rahoton cewa Qatar ta ƙulla yarjejeniya don bai wa wasu mutane daman ficewa daga Gaza, tare da haɗin gwiwar Amurka.

    ...

    Asalin hoton, EBU

    ...

    Asalin hoton, Reuters

  17. Isra'ila ta tura jiragen ruwan yaƙi a tekun Maliya

    ..

    Asalin hoton, IDF

    A jiya, ƙungiyar 'yan tawayen Houthi a ƙasar Yemen - mai nisan mil dari kudu da Isra'ila - ta ce ta kai hari kan Isra'ila har sau uku da makamai masu linzami da jirage marasa matuka, kuma za su sake kai wasu hare-haren.

    Yanzu haka dai rundunar sojin Isra'ila ta ce ta girke jiragen ruwanta na yaƙi a tekun Maliya domin ƙarfafa matakan tsaro a yankin.

    Da sanyin safiyar Larabar, rundunar IDF ta ce ta dakile wani hari ta sama daga tekun Bahar Maliya a kudancin birnin Eilat da ke kudancin Isra'ila.

    • Rikicin Isra'ila da Gaza: Mene ne asalin sa?
    • Yaya mamayen ƙasa na sojojin Isra'ila zai kasance a Gaza?
  18. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da safiyar Laraba tare da fatan kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa lafiya.

    Aisha Babangida da Ibrahim Yusuf ne za su kawo muku rahotanni daga sassan duniya, musamman game da halin da ake ciki a hare-haren da Isra'la ke kai wa Zirin Gaza da kuma martanin mayaƙan Hamas a kan ƙasar.