An jikkata mutum biyu a wani harbi a asibiti a Toda, Japan

Asalin hoton, Getty Images
An jikkata wasu mutane biyu sakamakon harbin bindiga a wani asibit da ke birnin Toda da ke tsakiyar kasar Japan, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka rawaito.
Wanda ake zargi yana da shekaru tsakanin 50 zuwa 70, ya gudu ne a kan babur, kuma a halin yanzu ana neman sa.
A lokaci guda kuma rahotanni sun nuna cewa an yi garkuwa da mutum biyu a cikin wani gidan waya da ke garin Warabi da ke kusa.
Babu tabbas idan waɗannan al'amuran biyu suna da alaƙa.
Kafofin yaɗa labaran ƙasar Japan sun yaɗa hotunan wani mutum dauke da bindiga a ƙofar ofishin gidan waya da ke kusa da babban asibitin Toda Chuo, inda aka yi harbin.
An bayyana waɗanda suka jikkata a matsayin likita da tsoffi majinyaci, yayin da kuma waɗanda akayi garkuwa da su wasu mata biyu ‘yan shekara 20 zuwa 30 ne.
Ofishin gidan waya a Warabi yana da tazarar kilomita 2.5 daga asibitin.
Jami’an tsaro sun kewaye yankin, kuma an aika da tawagogin bincike na musamman.
Hukumomi sun shawarci mazauna yankin da ke da nisan mita 300 daga ofishin gidan waya na Warabi da su fice, tare da rufe gine-ginen da ke kusa da su.
- An tsare dan shekara shida da zargin harbin malamarsa da bindiga a Amurka
- 'Ba mu hana likitoci duba masu harbin bindiga ko hatsarin mota ba'












