Isra'ila ba za ta taɓa yarda da tsagaita wuta kan Hamas ba - Netanyahu

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Mukhtar Adamu Bawa and Umar Mikail

  1. 'An kashe mutum 4 a rikicin da ya ɓarke a Gabar Yamma da Kogin Jordan'

    ...

    Dangane da halin da ake ciki a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da ke fuskantar mamaya, rahotanni na nuni da cewa aƙalla mutane hudu sun mutu sakamakon arangamar da aka yi tsakanin Falasɗinawa da sojojin Isra'ila a Jenin.

    Kamfanin dillancin labaran Wafa na ƙasar Falasɗinawa ya bayar da rahoton cewa, motocin sojin Isra'ila sun kai wani samame a garin Jenin, lamarin da ya yi sanadin lalata katangar da ke wajen asibitin Ibn Sina.

    An kuma ce an harba makamai masu linzami a cikin wani gida da kuma sansanin ƴan gudun hijira na Jenin.

    A martanin da kakakin sojin Isra'ila Daniel Hagari ya mayar, ya tabbatar da harin da aka kai ta sama a Jenin, inda ya ce sun kai hari tare da kawar da wasu mutane dauke da makamai.

    • Isra'ila ta rushe gidajen Falasɗinawa a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan
    • Mamayar Isra'ila: Abin da kuke buƙatar sani kan mamayar Isra'ila a Gabar Yamma da Kogin Jordan
  2. Sarki Charles III na cikin matsin lamba kan musgunawar zamanin mulkin mallaka

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar kare haƙƙin dan'adam ta Kenya, ta yi kira ga Sarki Charles III ya ba da haƙuri kan cin zarafin da Birtaniya ta yi a zamanin mulkin mallaka.

    Sarkin dai ya fara ziyarar kwana hudu a ƙasar Kenya da nufin samun ƙarin haske a kan kura-kuran da aka aikata wa jama'a a baya.

    Wannan ya haɗa da murƙushe wani yunkuri na neman yancin kai a cikin 1950, wanda ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 10,000 da shari'ar da babu adalci da kuma rataye mutum 1,000.

    Hukumar a ranar Lahadi ta ce "tana fatan sarkin zai nemi afuwa a bainar jama'a ba tare da wani kumbiya-kumbiya ba".

    Shekara goma da suka gabata, gwamnatin Birtaniya a hukumance ta amince da faruwar azabtarwa a karkashin mulkin mallaka, tare da nuna matuƙar nadama da bayar da diyya ga dubban tsoffin ƴan gwagwarmaya.

    Wasu al'ummomin Kenya da suka hada da Nandi da Kipsigis da kuma Pokot, su ma suna neman gwamnatin Birtaniya ta nemi afuwarsu da kuma biyansu diyya kan rashin adalcin da aka yi musu a tarihi lokacin mulkin mallaka.

    Har ila yau, sun buƙaci ƙasar Birtaniya ta maido da kayan tarihi na gargajiya da kuma filayen kakanni da gwamnatin mulkin mallakar ta ƙwace wadanda har yanzu ke hannun hukumomin Birtaniya.

    • Abin da ya sa wasu kasashen da Faransa ta yi wa mulkin-mallaka ke shiga kungiyar kasashe renon Ingila
    • Mene ne aikin Sarkin Ingila kuma su wane ne 'ya'yan sarautar?
  3. Isra'ila ta bayyana sunayen ƴan Tanzaniya biyu da Hamas ke riƙe da su

    ...

    Asalin hoton, MASHAV Israel

    Gwamnatin Isra'ila ta bayyana sunayen ƴan ƙasar Tanzaniya biyu waɗanda ake kyautata zaton ƙungiyar Hamas ta yi garkuwa da su tun bayan harin ranar 7 ga watan Oktoba.

    Sunan su Joshua Loitu Mollel da Clemence Felix Mtenga

    Joshua da Clemence sun kasance sun je wani shirin samar da horo kan aikin gona a Isra'ila, in ji ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi inda ta buƙaci a yi musu addu'a Allah ya dawo da su lafiya.

    Mahaifin Joshua ya samu tabbaci daga jakadan Isra'ila a Tanzaniya cewa gwamnatin na ci gaba da bibiyar lamarin.

    Iyalan Clemence dai har yanzu ba su ce komai ba kan batun.

    Bugu da kari, wani ɗan kasar Afirka ta Kudu da ba a tantance ba yana cikin mutum 224 da ƙungiyar Hamas ke garkuwa da su, kamar yadda gwamnatin Isra'ila ta bayyana.

    • Mutanen da ƙungiyar Hamas ke garkuwa da su tsawon shekaru
    • Kalli jariran Falasɗinawa da ake fargabar za su rasu idan lantarki ta katse a Gaza
  4. Ƴan Afrika za su fara zuwa Kenya ba tare da biza ba

    Passport

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Kenya William Ruto ya bayyana shirin kawar da buƙatar samun biza ga dukkan masu ziyara daga Afirka, nan da karshen wannan shekara.

    Ya jaddada buƙatar kawar da wannan shamaki da ke kawo cikas ga ci gaban nahiyar.

    Tafiye-tafiye ba tare da biza ba a Afirka sun kasance wani muhimmin buri ga Tarayyar Afirka tsawon shekara goma, tare da takaitaccen ci gaban da aka samu, da farko ana ganin shi a matsayin wani tsare-tsare kasashen yanki da na kasashe biyu.

    Ya zuwa 2022, Seychelles da Gambiya da Benin ne kawai suka bai wa dukkan 'yan Afirka damar shiga ƙasarsu ba tare da biza ba, bisa ga rahoton 2022 na goyon bayan Tarayyar Afirka

    Sai dai kuma, galibin ƙasashen Afirka na samun ci gaba wajen sauƙaka hanyoyin shiga ƙasashensu da kuma rage takunkumin da aka sanya wa masu ziyara daga wasu kasashen Afirka, kamar yadda wata kididdiga ta cibiyar 'Africa's Visa Openness' ta nuna.

    Kasar Kenya ta kasance ta 31 a cikin kasashen nahiyar 54 da ke cikin wannan kididdigar ta 2022.

    Shugaba Ruto ya bayyana illar da ke tattare da takunkumin hana biza ga harkokin kasuwanci.

    • Abin da ya sa Amurka za ta daina bai wa ɗaliban ƙasashen waje biza
    • Shugaban Najeriya ya yi alkawarin samar da biza ga 'yan Afirka
  5. Ɗaruruwan majinyata sun makale a asibitocin Gaza - MDD

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban hukumar Falasdinawa 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, Tom White ya ce daruruwan mutane a halin yanzu ke makale a asibitocin da ke arewacin Gaza, lamarin da ya sa ba za a iya mayar da su kudancin zirin ba.

    Wannan dai ya zo daidai da bayanan likitoci da kungiyoyin agaji daban-daban, waɗanda suka jaddada kalubalen da ke tattare da kwashe marasa lafiya daga asibitoci irin su Quds da ke arewacin Gaza.

    Isra'ila ta shawarci ƙungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasɗinawa, ta fice daga asibitin yayin da ake ci gaba da kai hare-hare a kusa.

    White ya ƙara da cewa mutane da dama a yankin arewancin Gaza na neman mafaka a makarantun hukumar kula da Falasɗinawa ƴan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) da asibitoci.

    A ziyarar da ya kai daya daga cikin asibitocin a wannan makon, ya lura cewa ba za a iya kwashe ɗaruruwan marasa lafiya ba.

    Ya kuma yi nuni da cewa, jama’a da dama a arewa da ba majinyata ba ne ba sa iya kaura saboda rashin sufuri da ababen hawa.

    Ya ce waɗannan mutane na fuskantar yunwa da ƙishirwa da tsoro kuma suna rayuwa a kan abinci kaɗan kamar guntun burodi.

    • Yadda gawawwaki suka mamaye asibitocin Gaza
    • Wanne irin taimako mutanen Gaza ke buƙata?
  6. Isra'ila ta ce ta kashe jami'an Hamas da dama cikin dare

    Sojojin Isra'ila sun ba da cikakken bayani kan ayyukansu na ƙasa a Gaza, inda suka bayyana cewa hare-haren nasu sun faɗaɗa cikin dare.

    Sun bayar da rahoton cewa dakarunsu sun yi artabu da 'yan ta'adda a Gaza, lamarin da ya yi sanadin mutuwar 'yan ta'adda da dama da suka fake a gine-gine da ramuka da kuma yunƙurin kai wa sojojin hari.

    Wata sanarwar da suka fitar ya ce wani jirgin sama da sojojin ƙasa ke jagoranta, ya kai hari kan wani gini da ke dauke da 'yan ta'addar Hamas sama da 20.

    Bugu da kari, wani jirgin yaƙi ya kai hari a wani sansanin soji da ake amfani da shi wajen harba makamai masu linzami da ke kusa da jami'ar Al-Azhar da ke arewacin Gaza a cikin dare.

    • Rikicin Isra'ila da Gaza: Mene ne asalin sa?
    • Mene ne hatsarin shiga yaƙi ta kasa a Zirin Gaza?
  7. Rikici ya barke a zauren majalisar dokokin jihar Ribas

    RIVERS STATE GOVERNMENT HOUSE MEDIA

    Asalin hoton, RIVERS STATE GOVERNMENT HOUSE MEDIA

    Sabon rikici ya barke a zauren majalisar dokokin jihar Ribas mai arzikin man fetur, sakamakon jita-jitar kokarin tsige gwamnan jihar Sim Fubara.

    Rikici ya kara muni ne bayan da wasu 'yan majalisar suka cire shugaban masu rinjaye, Edison Ehie daga kan kujerarsa.

    A daren ranar Lahadi kuma, wasu bata-gari sun cinnawa ginin majalisar dokokin jihar wuta.

    Gidan Talbajin na Channels ya bayyana cewa magoya bayan Gwamna Fubara sun gudanar da zanga-zanga a harabar majalisar domin nuna adawa da yunkurin tsige shi.

    Rahotanni sun nuna cewa, an soma takun-saka ne tsakanin Gwamna Fubara da kuma ministan Abuja, Nyesom Wike wanda shi ne ya yi uwa ya yi makarbiya domin ganin Mista Fubara ya gaje shi a matsayin gwamna.

    • Sabuwar ƙungiya ta ɓulla a Majalisar Dokokin Najeriya
    • Zaɓen Najeriya a Jihar Rivers: Jiha mai arzikin man fetur maras lantarki
  8. Jamus na neman zuba jari cikin harkar iskar gas a Najeriya

    ...

    Asalin hoton, Nigeria presidency/X

    Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya ce ƙasarsa na son zuba jari cikin harkar iskar gas a Najeriya da ma'adanai masu mahimmanci, yayin da ya fara ziyarar kwana biyu a ƙasar da ke Afirka ta Yamma.

    Wannan mataki dai wani bangare ne na ƙoƙarin da Jamus ke yi na fadada harkokin tattalin arziki a tsakanin abokan huldarta da kuma inganta dangantakar tattalin arziki a yankin Afirka ta Yamma mai arzikin makamashi, da nufin rage dogaro da makamashin Rasha.

    Najeriya ita ce ƙasa mafi yawan arzikin man fetur a nahiyar Afirka kuma ta biyu a matsayin babbar abokiyar cinikayyar Jamus a yankin kudu da hamadar Sahara.

    Adadin cinikin da ake yi tsakanin kasashen biyu a cikin shekara guda ya kai kimanin dala biliyan uku.

    Scholz ya kuma buƙaci yin haɗin gwiwa da Najeriya don taimaka wa kasarsa wajen magance kwararar bakin haure daga Afirka ta Yamma zuwa Turai.

    A nasa bangaren, shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya nemi goyon bayan Jamus wajen tunkarar matsalolin tsaro da habaka tattalin arzikin kasar.

    • Me Najeriya za ta samu a shigarta ƙungiyar G20?
    • Abin da ya sa Rasha ta dakatar da bai wa Turai iskar gas
  9. Kwamitin Sulhu na MDD zai yi taron gaggawa a kan rikicin Gaza

    Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar da taron gaggawa a yau Litinnin a kan matsalolin agaji da ake fuskanta a Gaza.

    Hadaddiyar Daular Larabawa ce ta bukaci a gudanar da taron bayan Isra'ila ta faɗaɗa hare-hare a yankin Falasɗinawa.

    Wakiliyar BBC ta ce a lokacin tattaunawar, ana sa ran a sanar da kwamitin halin da ake ciki kan ayyukan agaji a Gaza.

    A ranar Asabar ne, Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya nuna takaicinsa kan matsanancin yanayi kuma mafi muni da ya tilasta dakatar da ayyukan hukumomin ba da agaji, yayin da Isra'ila ke zafafa luguden wuta.

    Sau hudu dai Kwamitin Sulhun yana gazawa wajen ganin an amince da kudurin tsagaita wuta, saboda karfin ikon Rasha ko Amurka.

    • Bayani game da abubuwan da ba ku sani ba kan rikicin Isra’ila da Gaza
    • Hanyoyin sadarwa sun katse a Gaza yayin da Isra'ila ta tsananta luguden wuta
  10. Isra'ila ta ci gaba da luguden wuta a arewacin Gaza

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Isra'ila ta ci gaba da luguden wuta babu sararawa a arewacin Gaza, inda bama-bamanta ke dira a kusa da wani babban asibiti da ke birnin.

    Kungiyar agajin Red Cresent ta Falasɗinawa ta shaidawa BBC cewa an kai hari babu adadi a kewayen asibitin Al-Quds, wanda Isra'ila ta fadawa likitoci su fice.

    Daruruwan marasa lafiya, ciki har da jarirai na samun kulawa a asibitin, sannan akwai fararen-hula kusan dubu 14 da ke samun mafaka.

    Wakilin BBC ya ruwaito cewa Isra'ila so take ta ga Gaza ta ɗaɗe baki ɗaya kafin dakarunta su shiga ta ƙasa domin ganin sun yi nasara kan Hamas, sai dai ma'aikata lafiya sun yi gargadin cewa babu mafita ko hanyar kwashe marasa lafiya daga asibitin da ake kai wa hari.

    • Halin da aka shiga a Gaza ranar da aka katse hanyoyin sadarwa
    • Ƙungiyar Red Cross ta yi kiran a gagguta tsagaita wuta a Gaza
  11. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da hantsin Litinin tare da fatan kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa lafiya.

    Aisha Babangida ce za ta kawo muku rahotanni daga sassan duniya, musamman game da halin da ake ciki a hare-haren da Isra'la ke kai wa Zirin Gaza da kuma martanin mayaƙan Hamas a kan ƙasar.