Sai da safenku
Nan za mu rufe wannan shafi a yau Litinin kafin mu kawo muku wasu sabbin rahotonnin gobe da safe.
Umar Mikail ne ke cewa sai da safenku.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
A'isha Babangida, Mukhtar Adamu Bawa and Umar Mikail
Nan za mu rufe wannan shafi a yau Litinin kafin mu kawo muku wasu sabbin rahotonnin gobe da safe.
Umar Mikail ne ke cewa sai da safenku.

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar kare haƙƙin yara ta Save the Children,reshen Falasɗinu ta ce ana kashe yaro ɗaya cikin kowane minti 10 sakamakon yaƙin da Isra'ila ke yi a Zirin Gaza.
Da yake magana da BBC daga birnin Ƙudus, shugaban ƙungiyar Jason Lee ya ce baya ga yara 20,000 da aka jikkata, ɗaya cikin duk mutum uku yaro ne.
Ya ce cutuka masu yaɗuwa na ƙaruwa saboda cunkokso da kuma ƙarancin kayan tsafta.
"Likitoci na yin tiyata ba tare da yi wa mutane allurar kashe zafin ciwo ba, mutane na amfani da wayoyinsu don ganin haske a asibitoci," in ji shi.

Asalin hoton, Getty Images
Fadar shugaban ƙasar Najeriya ta mayar wa da jagoran adawa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, martani tana mai ba shi shawarar ya "kawo ƙarshen" burinsa na zama shugaban ƙasa.
Martanin na zuwa ne bayan wani taron manema labarai da ya gudanar a yau Litinin, inda ya yi watsi da hukuncin kotun ƙolin da ya jaddada nasarar Shugaba Bola Tinubu na jam'iyyar APC a zaɓen 2023.
Kazalika, Atiku ya ba da shawarar sauya wa'adin mulki zuwa karo ɗaya kuma na shekara shida, da kuma mayar da zaɓe da tattara sakamako ta hanyar latironi su zama tilas a Najeriya.
"....[Atiku] ya mayar da kansa ɗan jagaliya ta hanyar ƙasƙantar da hukumomin ƙasa baki ɗaya don cimma abin da ba zai iya samu ba a akwatin zaɓe," a cewar martanin da Bayo Onanuga - mai taimaka wa shugaban ƙasa kan kafofin yaɗa labarai - ya wallafa a dandalin X.
Ya ƙara da cewa "muna so mu bai wa Atiku shawarar cewa dole ne yanzu ya katse burinsa kuma ya matsa gefe".

Asalin hoton, KNSG
Cibiyar tallafi ta Sarki Salman na Saudiyya ta ce za ta ɗauki nauyin raba tagwayen da aka haifa manne da juna a jihar Kano da ke arewacin Najeriya.
Tuni Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya raka Hassana da Hussaina zuwa filin jirgin sama na Aminu Kano, inda aka tafi da su Saudiyyar a yau Litinin.
Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito cewa jariran suna haɗe ne ta ƙirji kuma sun haɗa wasu gaɓoɓin masu muhimmanci.
"King Salman Humanitarian Aid and Relief Centre (KSARelief) da haɗin gwiwar wasu sanannun likitocin fiɗa na yunƙurin tallafa wa waɗannan yara don su yi rayuwa mai kyau a nan gaba," a cewar wata sanarwa daga ofishin jakadancin Saudiyya da ke Abuja.
Sanarwar ta ƙara da cewa za a gudanar da tiyatar ne a cibiyar King Abdulaziz Medical City da ke birnin Riyadh.

Gwamnatin Birtaniya ta kori wani mai taimaka mata bayan ya nemi a tsagaita wuta a yaƙin da Isra'ila take yi a Zirin Gaza.
Fadar Downing Street ta ce Paul Bristow ya yi kalaman da "suka saɓa da aƙidar al'umma".
Cikin wasiƙar da ya rubuta wa firaministan Birtaniya, Mista Bristow ya ce "tsagaita wuta mai ɗorewa" za ta ceto rayuka kuma ta ba da damar kai kayan agaji ga waɗanda suke buƙatarsa.
Gwamnatin ta Birtaniya na goyon "tsahirtawa saboda ayyukan jin-ƙai" amma ban da tsagaita wuta.
Yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a makon da ya gabata, Firaminista Rishi Sunak ya ce "tsahirtawa saboda ayyukan jin-ƙai" za ta ba da damar shigar da agaji Gaza amma ya yi watsi da tsagaita wuta, yana cewa Isra'ila na da 'yancin kare kanta.
Mista Bristow ɗan majalisar jam'iyyar Conservative ne daga mazaɓar Peterborough kuma mataimaki ne na musamman ga sakataren kimiyya da fasaha na Birtaniya.

Asalin hoton, X/Reuters
Sojojin Sudan sun tsare ƙananan yara da aka ce an tilasta musu yin faɗa tare da dakarun Rapid Support Forces (RSF) a lokacin rikicin da ake fama da shi.
Waɗannan yaran, da ba a ƙayyade yawan su ba, ana tsare da su ne a Wadi Saidna, arewacin Khartoum.
A cikin watan Satumba ne sojojin ƙasar Sudan (SAF) suka miƙa kananan yara 30 fursunonin yaki ga kungiyar agaji ta Red Cross (ICRC).
Ƙungiyar ta RSF ta sha fuskantar zarge-zargen ɗaukar ƙananan yara aiki, wanda ya saɓa wa dokokin ƙasashen duniya, a rikicin Sudan da ake ci gaba da yi.
Ana ci gaba da gwabza fada tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF a yankuna daban-daban, yayin da ake sabunta tattaunawa a Saudiyya da nufin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma bayar da tallafin jin-ƙai.

Asalin hoton, Reuters
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce ƙasarsa ba za ta taɓa yarda da maganar tsagaita wuta a yaƙi tsakaninta da Hamas ba.
"Kamar yadda Amurka ba ta yarda da tsagaita wuta ba bayan harin bam kan Pearl Harbour ko kuma harin 9 ga watan Nuwamba, Isra'ila ma ba za ta yarda da tsagaita wuta kan Hamas ba bayan harin ranar 7 ga watan Oktoba," in ji shi yayin jawabin da ya kammala ɗazun nan.
"Kiraye-kirayen tsagaita wuta na nufin Isra'ila ta miƙa wuya ga Hamas, ta miƙa wuya ga ta'addanci," a cewarsa.
"Littafin Injila ya ce akwai lokacin zaman lafiya, da kuma lokacin yaƙi. Wannan lokacin yaƙi ne.
"Yaƙi ne game da makomarmu. A yau muna yaƙi ne tsakanin dakarun al'umma da kuma dakarun rashin imani."

Asalin hoton, ISA
Rundunar sojin Isra'ila (IDF) da kuma ta leƙen asiri (ISA) sun ce sun ceto wata sojar ƙasar daga cikin mutanen da Hamas ke garkuwa da su.
Cikin wata sanarwar haɗin gwiwa, sun ce an kuɓutar da Ori Megidish ne bayan wani harin rundunar IDF cikin dare a Zirin Gaza.
"Likitoci sun duba sojar kuma lafiyarta ƙalau, har ma ta gana da danginta. IDF da ISA za su ci gaba da yin bakin ƙoƙarinsu wajen ƙwato mutanen da ake garkuwa da su," a cewar sanarwar.

Asalin hoton, Nema
Hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya, National Emergency Management Agency (Nema), ta ce an kwaso ƙarin 'yan ƙasar 99 da suka maƙale a Jamhuriyar Nijar.
Sanarwar da hukumar ta fitar ta ce mutanen sun sauka a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas da misalin ƙarfe 2:15 na ranar yau Litinin bayan ƙungiyar kula da 'yan gudun hijira ta ƙasashen duniya IOM ta ɗebo su.
Sai dai Nema ba ta yi ƙarin bayani kan abin da ya maƙalar da su ba. Amma 'yan Najeriya da sauran ƙasashen Afirka ta Yamma kan yi sansani a Nijar a yunƙurinsu na tsallakawa Turai ta ɓarauniyar hanya.
Cikin mutanen akwai maza manya 76, da mata manya 15, da yara mata bakwai, da yara maza 15, da jaririya ɗaya.

Asalin hoton, Nema

Asalin hoton, Reuters
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya siffanta bidiyon da Hamas ta fitar da ke nuna mutum uku da take garkuwa da su a matsayin "farfagandar rashin imani".
Cikin wata sanarwa, Netanyahu ya bayyana sunayen matan yana cewa: "Ina miƙa hannuna ga Elena Trupanov, da Daniel Aloni da Rimon Kirsht waɗanda Hamas ta yi garkuwa da su a matsayin laifin yaƙi. Ina mai rungumarku."
BBC ba za ta wallafa bidiyon ba mai tsawon minti ɗaya da kaɗan. Yana nuna mata ne uku a jikin bango, inda ɗaya daga cikinsu ta yi magana.
"Zuciyoyinmu na tare da ku da kuma sauran mutanen. Muna yin bakin ƙoƙarinmu wajen dawo da dukkansu da kuma waɗanda suka ɓata," in ji shi.

Asalin hoton, Al Qassam Brigade
Ƙungiyar Hamas ta fitar da wani bidiyo na mata uku da take garkuwa da su a Zirin Gaza.
BBC ba ta san a yanayin da aka ɗauki bidiyon ba, amma dai da alama matan uku na cikin ƙoshin lafiya kuma ba tare da wata alamar rauni ba.
Mace ɗaya ce ta yi ta magana a bidiyon gaba ɗaya cikin harshen Hiburu (hebrew), inda ta dinga sukar Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da kuma kiran a sake su.
Ba za mu iya wallafa bidiyon ba. Fursunonin yaƙi da kuma waɗanda ake garkuwa da su na da kariya a ƙarƙashin dokar ƙasashen duniya ta jin-ƙai, kuma BBC ba ta wallafa bidiyon da babu mamaki an ɗauke shi ne bisa tilstawa.

Asalin hoton, Reuters
Isra'ila ta nemi Rasha ta kare "'yan ƙasarta da kuma dukkan Yahudawa" bayan wani dandazon wasu mutane sun kutsa filin jirgin sama na Dagestan suna ta ihun ƙin jinin Yahudawa.
Wani bidiyo da aka wallafa a intanet ya nuna yadda mutanen cikin fushi suke shiga sassan filin jirgin da ke Makhachkala a Rasha suna neman matafiyan da suka sauka daga birnin Tel Aviv.
Wasu daga cikin mutanen sun shiga har kan titin tashin jirgin kuma suka zagaye shi.
Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Rasha, Rosaviatsia, ta ce ta shawo kan lamarin daga baya.
An rufe filin jirgin ranar Lahadi da dare. Rosaviatsia ta ce an sake buɗe shi a ranar Litinin, amma ta ce jiragen da suke zuwa daga Isra'ila "za a dinga sauya musu masauki zuwa wasu filayen jirgin na ɗan lokaci.".
Kamfanin dillancin labarai na Rasha ya ce an kama mutum 60 daga cikin fusatattun mutanen yana mai ambato ma'aikatar harkokin cikin gida.

Ma'aikatar tsaron ƙasar Ghana ta kare jami'anta da ake zargi da cin zalin fararen hula a wani samame da aka kai a arewacin ƙasar a karshen mako.
Ma'aikatar ta ce a ranar Talatar da ta gabata an tura wata tawaga ta farko ta jami'an leken asiri na yaki da ta'addanci a garin Garu domin gudanar da abin da ta kira "aiki na musamman", ba tare da yin wani karin bayani ba.
Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ya bayyana cewa daga nan ne wasu fusatattun matasa dauke da makamai suka kai wa tawagar jami’an hari a Garu.
Bayan haka ne aka tura sojoji don ƙwato makaman da aka yi amfani da su wajen kai harin.
Wasu ‘yan majalisar sun soki jami’an tsaro da zargin wuce gona da iri, sai dai ma’aikatar ta jaddada buƙatar kare jami’an tsaron jihar ba tare da yin tsokaci kan rahotannin raunukan da matasan suka samu ba.

Asalin hoton, Nigeria Police Force/Facebook
Gwamnatin jihar Abia ta ce ta gano gawawwakin wasu mutane sama da 50, ciki har da wadansu da ba su da kawuna guda 20, da kuma kwarangwal da dama a kusa da kasuwar shanu ta Lokpanta a garin Umunneochi.
Gwamnan jihar, Alex Otti ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da manema labarai ta wata-wata a gidan gwamnati, yau Litinin, inda ya jaddada ƙudurinsa na magance matsalolin rashin tsaro a jihar da ke kudancin Najeriya.
Ya alaƙanta kai hare-hare a kasuwar, da matsaloli kamar karuwanci da fataucin miyagun kwayoyi da sauran miyagun ayyuka a yankin.
A matsayin martani, gwamnan ya bayyana cewa kasuwar Lokpanta za ta fara aiki a kullum daga karfe 6 na safe zuwa 6 na yamma.

Asalin hoton, Reuters
Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane miliyan 6 da dubu 900 ne ke gudun hijira a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango sakamakon karuwar tashe-tashen hankula.
Hukumar kula da ƴan cirani ta Majalisar Dinkin Duniya ta tattara bayanan bin diddigi daga dukkan larduna 26 na kasar.
Ta ce akasarin waɗanda suka rasa matsugunansu na zaune ne a gabas inda aka ce rikici ne ya haddasa.
A arewacin Kivu kadai, mutane kusan miliyan daya ne suka tsere daga gidajensu, sakamakon faɗan da ake yi da 'yan tawayen M23.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa DR Congo na fuskantar daya daga cikin manyan matsalolin gudun hijira da kuma rikicin jin ƙai a duniya.

Asalin hoton, EPA
Afirka ta Kudu ta yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta aika da "dakarun kariya cikin gaggawa" don kare fararen hula daga hare-haren bama-bamai a yaƙin Isra'ila da Gaza.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ma'aikatar hulda da kasashen duniya ta bayyana damuwarta a cikin wata sanarwa kan yawan yaran da aka kashe a rikicin tare da zargin Isra'ila da keta dokokin ƙasashen duniya.
A daya bangaren kuma Isra’ila ta kare matakin da ta dauka na kai hare-hare a Gaza a matsayin kariyar kai biyo bayan kashe mutane 1,400 da Hamas ta yi a ranar 7 ga Oktoba yayin da kuma aka yi garkuwa da mutane 230.
Ma'aikatar lafiya ta Hamas a Gaza ta ce sama da mutane 8,000 ne aka kashe tun bayan fara harin ramuwar gayya na Isra'ila.

Asalin hoton, Sir Siminalayi Fubara/Facebook
Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya bayyana cewa bai yi wani abu da zai saka majalisar dokokin jihar ta tsige shi ba.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga magoya bayansa a harabar majalisar bayan da ‘yan majalisar ƙarƙashin jagorancin kakakin majalisar, Martin Amaewhule suka fara shirin tsige shi.
"Su fito wa da mutanen Ribas shaidar laifin da na aikata da har zai saka a tsige ni," in ji gwamnan yayin da yake jawabi ga magoya bayansa a harabar majalisar.
Gwamnan ya tabbatar wa al’ummar jihar Ribas cewa zai ci gaba da samar da ribar dimokuradiyya inda ya ce zai yi jawabi ga manema labarai a lokacin da ya dace.
Jaridar Punch ta ruwaito da farko cewa an yi harbe-harben bindiga da hayaki mai sa hawaye a harabar majalisar a yau, ranar Litinin lokacin da ƴan majalisar suka zauna domin fara shirin tsige gwamnan.
Lamarin dai ya kai ga dakatar da wasu ‘yan majalisar da ake kyautata zaton suna goyon bayan gwamnan.
Hakan ya biyo bayan wata gobara da ta tashi a harabar majalisar a daren jiya.