'Kasashen Yamma kan mance da doka idan jinin Musulmi ake zubarwa'

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Haruna Kakangi, Mukhtari Adamu Bawa and Abdullahi Bello Diginza

  1. Za a buga wasan Premier a jajiberin Kirsimeti karon farko tun 1995

  2. Afirka ta Kudu za ta samu rancen dala biliyan 1 daga Bankin Duniya

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Bankin Duniya za ta bai wa Afirka ta Kudu rancen dala biliyan 1 don taimakawa wajen yaƙi da matsalar makamashi mai tsanani, wanda ya kai ga katsewar wutar lantarki mafi muni a ƙasar.

    Katsewar wutar lantarki wanda ke gudana tun daga shekarar 2007, ya kawo cikas ga tattalin arzikin Afirka ta Kudu, tare da kawo cikas ga ci gaban kayayyakin da ake samarwa a cikin gida.

    Sama da kashi 80 cikin 100 na wutar lantarkin kasar ana samar da su ne daga kwal, wanda hakan ya sa ta zama kasa ta 14 mafi girma a duniya da ke fitar da iskar Carbon dioxide.

    Wannan rancen na da nufin taimaka wa Afirka ta Kudu wajen yin kwaskwarima ga kamfanin samar da wutar lantarki na gwamnati, Eskom, wanda ke da bashin sama da dala biliyan 26.

    • Najeriya: Yadda rashin lantarki ke kassara harkokin kasuwanci a fadin ƙasar
    • Ko Afirka ta Kudu za ta rungumi fasahar makamashin hasken rana?
  3. An harba ƙarin makaman roka a tsakiyar Isra'ila

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    A cikin sa'a da ta gabata an harba makaman roka da dama zuwa tsakiyar Isra'ila daga Gaza.

    Jiniyar ankararwa kan hare-hare ta sama ta ringa ƙara a fadin ƙasar inda aka ba da rahoton cewa an kakkaɓo wasu makamai da aka harbo ta sama

    An buga faifan bidiyon abin da ya biyo bayan harba makaman rokan da ya fada kan wani gini a Petah Tikva, kusa da Tel Aviv, a shafukan sada zumunta.

    Jim kaɗan bayan fitar da sanarwar, hukumar bayar da agajin gaggawa ta Isra'ila ta ce ba a samu rahoton waɗanda suka jikkata ba ya zuwa lokacin.

    Hamas, wadda ta harba dubban rokoki kan Isra'ila tun ranar 7 ga watan Oktoba, ta ce ita ce ke da alhakin kai sabbin hare-haren.

    • Ko samame ta ƙasa da Isra’ila ke shirin kai wa Gaza zai yi nasara?
    • Ana kwashe 'yan Isra'ila a ƙauyukan iyaka da Lebanon saboda barazanar hari
  4. Ƴan sanda sun ceto kyanwa 1,000 da aka yi yunƙurin yankawa a China

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƴan sandan ƙasar China sun ceto kyanwa sama da 1,000 da aka shirya yankawa da sayar da su a matsayin naman alade.

    An samu nasarar hakan ne ta hanyar taimakon wasu bayanai dsa aka tattara daga masu rajin kare hakkin dabbobi a birnin Zhangjiagang.

    A China, akan sayar da naman mage guda daya kimanin dalar Amurka uku.

    Babu tabbas ko magunan da aka so yankawar waɗanda ke gararamba ne a gari ko kuma waɗanda ake ajiyewa a gida.

    A cewar jaridar 'The Paper', masu fafutuka a birnin Zhangjiagang sun lura da yawan magunan da ake tsare da su a cikin akwatunan katako a wata makabarta inda aka sa musu ido har tsawon kwanaki shida.

    Lokacin da aka loda magunan a kan babbar mota a ranar 12 ga Oktoba, sai suka tsayar da motar inda nan take suka kira 'yan sanda.

    • Me ya sa muke tunanin cewa mage ba ta son mutane?
    • An nemi ɗauki bayan ƙudajen zuma miliyan biyar sun faɗo daga mota
  5. Labarai da dumi-dumi, Adadin waɗanda suka mutu a Gaza ya haura 7,000 - Hamas

    Ma'aikatar lafiya ta Hamas ta ce aƙalla mutum 7,000 ne aka kashe a Gaza tun lokacin da aka fara yaƙin a ranar 7 ga watan Oktoba - wanda ya yi sanadiyar mutuwar sama da 500 tun daga ranar Laraba.

    Adadin ya hada da yara sama da 2,900, a cewar ma’aikatar.

    A cikin sa'o'i 24 da suka gabata, Isra'ila ta ce ta kai hari ta sama kan wasu wurare 250 na Hamas.

    • Bayani kan hanya ɗaya tilo da Falasɗinawa za su iya fita daga Gaza
    • Musulmai da Yahudawan Birtaniya na fargabar alaƙarsu saboda yaƙin Gaza
  6. Isra'ila ta ce Hamas tayi garkuwa da ƴan Afirika uku

    ...

    Asalin hoton, EPA

    Gwamnatin Isra'ila ta ce ƴan Tanzaniya biyu da ɗan Afirka ta Kudu na daga cikin mutane 224 da kungiyar Hamas ta yi garkuwa da su bayan harin ranar 7 ga Oktoba.

    Babu sunan ko ɗaya daga cikin ukun da aka ambata.

    Hukumomin Tanzaniya a baya sun tabbatar da cewa wasu ƴan ƙasarta biyu sun bata.

    BBC ta tattauna da dangin ɗaya daga cikinsu, Joshua Mollel, wanda ɗalibi ne a fannin aikin gona a wani kibbutz da aka kai masa hari.

    Ƴan ƙasashen waje daga ƙasashe 25 gaba ɗaya na hannun Hamas, in ji Isra'ila.

    Tuni dai Isra'ila ta mayar da martani da hare-hare ta sama kan Gaza, wanda ma'aikatar lafiya ta Hamas ta ce ta kashe kusan mutum 6,500.

    • Mutanen da ƙungiyar Hamas ke garkuwa da su tsawon shekaru
    • Me ya sa alaƙar Iran da Hamas ke da ƙarfi?
  7. Hujjojin kotun ƙoli na yin watsi da ƙarar Atiku da Obi kan nasarar Tinubu

  8. Za a dauki shekaru kafin a maido da tsaro – Ministan Isra’ila

    ...

    Asalin hoton, EPA

    Ministan yakin Isra'ila, Benny Gantz, ya ce maido da tsaro a kudancin Isra'ila zai dauki shekaru bayan harin Hamas a ranar 7 ga watan Oktoba.

    Yace hakan zai haɗa da matakan soji da sauran su.

    "Ba za a halaka mu ba, amma maƙiyanmu na iya fuskantar hallaka," in ji shi.

    • Abin da Isra'ila take lissafawa kafin ta auka wa Gaza
    • Rikicin Gaza na rura wutar tunzuri a manyan makarantun Amurka
  9. Mutanen da suka mutu a hatsarin kwale-kwale a DR Congo sun kai 54

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Hukumomi a Lardin Demokradiyyar Kongo sun ce adadin wadanda suka mutu sakamakon hatsarin kwale-kwale a ranar Lahadi ya kai 54, yayin da aka gano wasu gawarwaki 10.

    Ministan lafiya da harkokin jin kai na lardin ya ba da rahoton cewa an ceto mutum 267, kuma kusan 50 ne har yanzu ba a gansu ba, duk da cewa ba a iya dawo da bayanan fasinja ba yayin da mai jirgin shi ma ya nutse.

    Lamarin dai ya faru ne a lokacin da wani jirgin ruwan ya nutse a kogin Lulanga da ke yammacin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo,wanda ya zama hatsarin kwale-kwale mafi muni na biyu a wannan watan.

    Ministan Sufuri, Mark Ekila, ya ce an samu haɗurran jiragen ruwa guda 88 a bana.

    A ranar 13 ga Oktoba, wani jirgin ruwa ya nutse a tashar jiragen ruwa na Mbandaka a babban birnin Equateur, inda ya kashe mutane 63 tare da barin wasu fiye da 100 da har yanzu ba a san su ba.

    Gwamnati na shirin ɗaukar tsauraran matakai, da suka hada da haramta safarar jiragen ruwa da kuma raba fasinjoji da kaya da dabbobi.

    Matsakaicin hanyoyin sufuri na DR Congo yakan tilastawa mutane yin amfani da tsofaffin kwale-kwale a karkashin yanayi mara kyau.

    • Daliban Islamiyya da dama sun mutu a hatsarin kwale-kwale a jihar Kano
    • Ƙasar da yara suka fi shan uƙuba a duniya
  10. Kotun ƙoli ta yi watsi da buƙatar Atiku ta gabatar da sabbin hujjoji

    ...

    Asalin hoton, ATIKU ABUBAKAR

    Kotun kolin Najeriya ta yi watsi da buƙatar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ta gabatar da sabbin hujjoji kan zargin da yake yi wa shugaban ƙasar, Bola Tinubu.

    Mai shari’a Inyang Okoro ya yanke hukuncin ne a zaman da kotun ke yi yau Alhamis domin sauraron ƙorafin da jam'iyyun adawa suka ɗaukaka kan kalubalantar nasarar Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa.

    Atiku ya nemi a ba shi damar gabatar da ƙarin hujjojin da za su tabbatar da iƙirarinsa na cewa Tinubu ya miƙa takardar shaidar jabu ga hukumar zabe ta kasa INEC.

    Lauyan Atiku Chris Uche (SAN), ya ce takardar mai shafi 32 da aka miƙa wa wanda yake karewa ya kamata a shigar da ita domin a yi adalci.

    Sai dai kotun ta yanke hukuncin cewa lokacin shigar da irin waɗannan shaidun ya wuce, saboda tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasar.

    Wa'adin kwanaki 180 ya kare ne a ranar 17 ga Satumba, wanda hakan ya sa Kotun Koli ba ta da hurumin karbar takardar.

    • Babu hujjar da ke nuna cewa takardun digirin Tinubu na bogi ne
    • Ranar da Tinubu zai san matsayin zaɓensa a Kotun Ƙoli
  11. Rasha ta yi atisayen harba makamin nukiliya

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Kasar Rasha ta gudanar da atisayen soji domin tabbatar da cewa tana cikin shirin iya kai gagarumin farmakin nukiliya a cewar ministan tsaron kasar, Sergei Shoigu.

    Atisayen ya haɗa da "martani kan harin makamin nukiliya daga maƙiya", in ji ministan tsaron.

    Kafar talabijin ta ƙasar ta nuno ministan yana yi wa shugaba Putin bayani kan atisayen.

    Lamarin ya zo ne daidai lokacin da majalisar dokokin ƙasar Rasha ta goyi bayan janyewar da ƙasar ta yi daga yarjejeniyar ƙasa da ƙasa kan haramta gwajin makaman nukiliya.

    Rasha da Amurka sukan yi atisayin gwajin makamin nukiliya a kai-a kai, inda Rasha ta saba yin nata a karshen watan Oktoba.

    Sanarwar da Kremlin ta fitar ta ce atisayen na baya-bayan nan sun haɗa da harba nau'uka daban-daban na muggan makamai masu linzami, waɗanda suka hada da makami mai linzami da ake iya amfani da shi wajen kai hari tsakanin nahiyoyi da makami mai linzami da aka harba daga wani jirgin ruwa mai karfin nukiliya.

    • Makaman nukiliya nawa Rasha ta mallaka?
    • MDD ta yi gargadi mai tsanani kan yuwuwar bala'in nukiliya a Ukraine
  12. Ecowas ba ta yi mana adalci ba – Firaministan Nijar

  13. Sojojin Sudan da RSF za su ci gaba da tattaunawar zaman lafiya a Jeddah

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Amurka da Saudiyya sun ce za su ci gaba da tattaunawa a Jeddah, da nufin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Sudan.

    Rahotanni sun ce wakilan sojojin ƙasar Sudan da dakarun kar ta kwana na RSF sun isa birnin tashar jiragen ruwa na Saudiyya domin tattaunawa.

    Tattaunawar zaman lafiya da ta gabata a birnin Jeddah ta ruguje a cikin watan Yuni bayan ƙeta yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta da dama.

    A wannan karon an fahimci cewa, yunkurin shiga tsakani zai hada da mai gudanarwa na Afirka, daga ƙungiyar raya yankin Igad.

    Rikicin watanni shida tsakanin sojojin Sudan da RSF ya haifar da bala'in jin kai.

    Sama da mutum 9,000 ne aka kashe sannan wasu kimanin miliyan shida suka rasa muhallansu.

    • Zaɓi mai tsauri da masu shiga tsakani ke da shi a rikicin Sudan
    • Ricikin Sudan: Fararen hula 56 sun mutu a faɗa tsakanin sojoji da dakarun RSF
  14. Hotunan makoki a Gaza bayan wasu ƙarin hare-hare ta sama da Isra'ila ta kai

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Wata mata a Khan Younis tana kuka ka rashin da tayi sakamakon hare-haren Isra'ila
    ...

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Wasu yara ’yan’uwa sun jikkata bayan harin Isra'ila a birnin Gaza
    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Mohammed al-Akhras yana makoki a Gaza bayan an kashe 'yarsa da matarsa
    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Wasu maza suna zaune a cikin ɓaraguzan gine-gine a Gaza inda Isra'ila ta ce ta kai hari kan cibiyoyin Hamas 250 cikin dare.
  15. Za a fara sauraren bahasi kan gobarar da ta tashi a birnin Johannesburg

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Za a fara sauraren bahasi kan mummunar gobarar da ta tashi a rukunin gidajen wajen birnin Johannesburg in da mutum 77 suka mutu.

    Kwamitin sauraren bahasin ƙarƙashin jagorancin tsohon alƙalin kotun tsarin mulki Sisi Khampepe, zai ji ta bakin mazauna gidan don samun labari kan ainahin abin da ya faru lokacin gobarar a Watan Agusta, a lamari mafi muni da Afirka ta Kudu ta fuskanta.

    Za kuma su yi bincike kan gidaje masu cunkoson jama’a da yawanci ake bai wa ‘yan cirani haya a Johannesburg.

    Ginin gidan da gobarar ta tashi dai ɗaya ne daga cikin gwamman gidaje masu cinkoso, waɗanda gungun masu aikata laifi, da ‘yan daba ke iko da su da bai wa mutane haya ba bisa ka’ida ba, ga marasa karfi ko ‘yan cirani.

    • Gobara ta ƙona kimanin shaguna 50 a kasuwar Singa
    • Wace nasara shugabannin Afirka suka cimma a ziyarar sasanta Ukraine da Rasha?
  16. An kai hari kan cibiyoyin Hamas 250 a kwana guda

    ...

    Asalin hoton, Rex Features

    Dakarun tsaron Isra'ila sun ce jiragen yaƙi sun kai hari kan cibiyoyin Hamas 250 a zirin Gaza a kwana guda.

    Sojojin ruwan Isra'ila sun lalata wani makami mai linzami na Hamas daga sama a yankin Khan Younis na Gaza, in ji dakarun.

    A 'yan sa'o'i da suka gabata, wata tashar Telegram ta Hamas ta ce ta harbo wani jirgin saman Isra'ila da makami mai linzami da ke kusa da sansanin 'yan gudun hijira na Bureij a Gaza.

    Bai bayar da shaida ko lokaci ba.

    • Takaddamar Isra'ila da shugaban MDD saboda kalamansa kan harin Hamas
    • Kalli jariran Falasɗinawa da ake fargabar za su rasu idan lantarki ta katse a Gaza
  17. ECOWAS ba ta yi wa Jamhuriyar Nijar adalci ba - Lamine

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo

    Wannan ce tattaunawa ta farko da BBC Hausa ta yi da Firaministan Jamhuriyar Nijar Ali Lamine tun bayan hawa mukamin.

    A cikin tattaunawar, shugaban sashen Hausa na BBC, Aliyu Tanko ya yi masa tambayoyi kan halin da kasar ke ciki da kuma yadda jagororin sojin kasar ke kallon matakan da kasashen duniya suka dauka kansu tun bayan juyin mulkin da suka yi wa Mohammed Bazoum.

    • Ecowas ta ce hafsoshin sojinta sun sa ranar shiga Nijar
    • Ci gaba da tsare Mohamed Bazoum na jawo ƙarin barazana
  18. DSS ta saki tsohon shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa

    ...

    Asalin hoton, EFCC

    Hukumar tsaro ta DSS ta saki tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC bayan shafe sama da kwana ɗari a hannun hukumar.

    A cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X a daren ranar Alhamis, DSS ta tabbatar da sakin tsohon jami'in na EFCC.

    DSS dai ta kama Abdulrasheed Bawa ne a ranar 14 ga watan Yunin bana, kuma tun daga lokacin take tsare da shi a hedikwatarta da ke birnin Abuja.

    A jiya Laraba da dare ne hukumar ta saki Bawa, wanda rahotanni ke cewa ana binciken shi da aikata ba daidai ba a aikin sa.

    An dai riƙa yaɗa wani bidiyo da ke nuna shigar Abdulrasheed Bawa gida, inda iyalai da ƴan uwa ke taya shi murna da farin ciki.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  19. Sojojin Isra’ila sun kai mamaya ta ƙasa da tsakar dare a Zirin Gaza

    ...

    Asalin hoton, X: @IDF

    Sojojin Isra’ila sun ce sun kai mamaya ta ƙasa da tsakar dare a Zirin Gaza, a wuraren da Hamas ke iko da su.

    Mai magana da yawun sojin Laftanal Kanal Jonathan Concirus ya shaidawa BBC cewa dakarun sun kai harin share fage gabannin kai hari ta kasa da suke shirin yi.

    Ya ce sun yi abin da ake kira share fage, inda sojoji suka shiga da daddare kuma suka fito, domin shirya fagen daga, da shirya kan su kan aikin da ke tafe inda ya ce a yanzu dakarun sun koma Isra'ila.

    Ya ƙara da cewa sun yi aikin cikin nasara ba tare da wata tangarɗa ba.

    • Ta waɗanne hanyoyi Iran za ta iya shiga yaƙin Isra'ila da Gaza?
    • Yadda gawawwaki suka mamaye asibitocin Gaza
  20. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar mu, barkan mu da safiyar Alhamis.

    Aisha Babangida ke fatan kasancewa da ku a wannan shafi na kai tsaye, BBC Hausa domin kawo muku irin wainar da ake toyawa Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntarmu domin yin muhawara kan labaran da muka wallafa

    Ku biyo ni.