'Kasashen Yamma kan mance da doka idan jinin Musulmi ake zubarwa'
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
A'isha Babangida, Haruna Kakangi, Mukhtari Adamu Bawa and Abdullahi Bello Diginza
Rufewa
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye, nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a faɗin duniya, musamman kan yaƙin Isra'ila da Hamas.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.
Amma yanzu a madadin sauran Abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.
Labarai da dumi-dumi, Shugabannin Turai sun yi kira a dakatar da faɗa don kai kayan agaji Gaza
Shugabannin Tarayyar Turai sun yi kiran a samar da "hanyoyin jin ƙai kuma a tsahirta" don ba da damar kai kayan agaji ga fararen hula a Gaza.
A cikin wani ƙuduri da suka ayyana yayin wani taro a Brussels, shugabannin ƙasashen Tarayyar Turai 27 sun bayyana "matuƙar damuwa saboda ƙazancewar al'amura a Gaza".
Sun yi kira a "ci gaba kuma cikin hanzari a samar da amintacciyar hanyar jin kan ɗan'adam don kai kayan agaji ga waɗanda ke cikin tsananin buƙata ta hanyar ɗaukar dukkan matakan da suka wajaba ciki har da kafofin jin kai sannan a dakata don buƙatun ayyukan jin kai".
Kudurin ya kuma ce Majalisar Turai "ta jaddada yin alla-wadai cikin murya mafi kaushi ga Hamas saboda hare-harenta na mugunta da ta'addanci a kan Isra'ila".
Ta kuma kara da cewa: "Amfani da fararen hula a matsayin garkuwa da Hamas ke yi shi ma musamman aika-aika ne da ake yin tur da ita."
Jami'in Hamas ya katse hira da BBC bayan yi masa tambaya kan kisan fararen hula, Daga Hugo Bachega a Beirut, Lebanon
A yau na yi hira da Ghazi Hamad, mamban Hamas, kuma mai magana da yawun ƙungiyar, da ke zaune a birnin Beirut.
Zama da wakilin wata ƙungiya da gwamnatocin duniya da dama ke kallo a matsayin ƙungiyar ta'addanci ba mataki ne da aka ɗauka cikin sauki ba.
To amma dama ce ta yi masatambayoyin ƙeƙe-da ƙeƙe kan hare-haren da Hamas ta ƙaddamar ranar 7 ga watan Oktoba, da suka yi sanadiyyar kashe fiye da mutum 1,400, mafi yawancinsu fararen hula, tare da yin garkuwa da fiye da mutum 200.
Hamad ya ƙi yadda cewa ƙungiyarsa ta kai hari kan fararen hula da gangan, duk kuwa da hujjojin da ake da su, ciki har da bidiyoyin da kyamarorin da mayaƙan ƙungiyar suka maƙala a jikinsu.
Ya ce harin, "atisayen soji" ne da aka shirya da nufin kai wa sojojin Isra'ila hari.
Na sake tambayarsa cewa ta yaya wannan hari zai kasance kan soji, bayan kashe ɗaruruwan fararen hula, ciki har da mutanen da suka halarci bikin shagalin kiɗe-kiɗe da waɗanda aka kai wa hari a gidajensu, suna tare da iyalansu.
Daga nan sai ya katse tattaunawar, ya kuma fice daga ɗakin.
Kafin nan, Hamad ya nuna cewa Hamas ta fara tattaunawar sulhu don sakin fararen hular da take tsare da sua Gaza.
To amma ya ce akwai buƙatar yin abubuwa masu yawa kafin hakan ya kasancewa, ba tare da fayyacewa ba.
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
A wajen wani gidan burodi da ke Rafa, mazaunan Gaza na jira a kan dogayen layuka don samun burodi yayin da ƙarancin man fetur ke tilasta rufe gidajen burodi.
Ƙungiyar bayar da agaji ta Red Cross ta bayyana halin da ake ciki a Gaza a matsayin wata "matsalar jin ƙan ɗan'adam da ba a taɓa gani ba" yayin da muhimman kayan buƙatun rayuwa a Gaza ke isar jama'a.
Jakadun Isra'ila da Falasɗinawa sun gabatar da jawabai a taron MDD
Jakadun Isra'ila da Falasdinawa sun yi jawabai a taron gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya kan halin da mutanen su ke ciki tun farkon fara yaƙin kasashen biyu.
Jakadan Falasdinawa a Majalisar, Riyad Mansour, ya buƙaci shugbannin su da su zabi adalci sama da ɗaukar fansa, ta hanyar dakatar da kashe-kashen da ake a Gaza.
A nasa ɓangaren Jakadan Isra'ial, Gilad Erdan, ya yi magana kan hare-haren da Hamas ke shirin kai wa Isra'ila, ya kuma ce wannan zaman na musamman bai da alaƙa da samar da zaman lafiya.
Iyalan 'yan Isra'ila da Hamas ta kama sun yi zanga-zangar neman sakinsu
Asalin hoton, EPA
Iyalan mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su, sun gudanar da wata zanga-zanga don neman sakin 'yan uwan nasu.
Sun gudanar da zanga-zangar ne a wajen ma'aikatar tsaron ƙasar da ke birnin Tel Aviv, inda suka riƙa rera waƙoƙin "A maido mana da 'yan uwanmu, a maido mana da 'ya'yanmu".
'Yan uwan mutanen sun buƙaci gwamnatin ƙasarsu, ta yi abin da ya kamata domin maido da mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su.
Mutanen na riƙe da takardun da ke ɗauke da hotuna da sunayen mutanen da Hamas din ta yi garkuwa da su.
Sojojin Isra'ila sun ce mutum 224 ne Hamas ke garkuwa da su.
MDD ta ce ''da kyar'' kayan agaji ke isar al'ummar Gaza
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Manyan motocin kayan agaji 74 ne suka tsallaka Gaza tun ranar 7 ga watan Oktoba
Shugaban Hukumar bayar da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya, Martin Griffiths, ya yi gargaɗin cewa 'dakyar' kayan agaji ke shiga Gaza a yayin da duniya ta ''kasa samar da abin da ake buƙata don ayyukan jin ƙai".
Mista Griffiths ya ce ''luguden wuta da ake ci gaba da yi wa Gaza na ƙara munana, har ma a wuraren da ya kamata a ce suna cikin lafiya".
Cikin wani saƙon X da ya wallafa, Mista Griffiths, ya ce "dokokin yaƙi a bayyane suke'' cewa dole a kare fararen hula, sannan su samu muhimman abubuwan buƙata domin su rayu.
Hakan na zuwa ne bayan da Hukumar Kula da 'yan Gudun Hijirar Falasɗinawa ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce ta samu man fetur mai yawa, sai dai ta yi gargaɗin cewa ana samun ƙarancinsa a faɗin Gaza.
Faransa ta ce yawan 'yan kasarta da aka kashe a harin Hamas sun kai 35
Ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta ce yawan 'yan kasar Faransa da aka kashe a hare-haren Hamas a kan Isra'ila ya karu zuwa 35, daga mutum 31.
Ma'aikatar ta ce 'yan kasar tara ne har yanzu ba a san inda suke ba, baya ga wadanda Hamas take ci gaba da yin garkuwa da su.
"Muna yin duk abin da za mu iya yi don ganin an sake su," a cewar wata sanarwar ma'aikatar harkokin waje.
Ta ce suna tuntubar dukkan iyalai Faransawa da "suka bace ko kuma wadanda ake garkuwa da su".
Iran na neman ƙulla alaƙa da shugabannin mulkin sojin Nijar
Asalin hoton, President of the Islamic Republic of Iran
Bayanan hoto, Nijar ce ƙasar Afirka ta baya-bayan nan da Iran ke neman ƙulla ƙawance da ita
Shugaban ƙasar Iran Ebrahim Raisi ya ce a shirye ƙasarsa take ta ƙulla alaƙa da Jamhuriyar Nijar, a ɓangarorin tattalin arziki".
Shugaba Raisi ya bayyana hakan ne ranar Laraba, bayan ganawa da sabon ministan harkokin wajen Nijar, Bakary Yaou Sangaré.
Cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin intanet na shugaban na Iran, Mista Raisi ya yaba wa burin Nijar na ''tsayawa da ƙafafunta'' da kuma ''jurje wa tsare-tsaren Turawa'' da ya ce alama ce da ke nuna shirin Afirka na "ƙwatar kai daga mulkin mallaka".
Nijar ce ƙasar Afirka ta baya-bayan nan da Iran ke shirin ƙulla ƙawance da ita, a ƙoƙarin da take na kawo ƙarshen wariyar da duniya ke nuna mata.
A watan Satumba ne, shugaba Raisi ya gana da ministan harkokin wajen Burkina Faso Olivia Rouomba, inda shugaban ya yaba da ƙasashen Afirka bisa "turjiyar da suke yi wajen fuskantar matsalar mulkin mallaka da ta'addanci."
A watan Yuli ne, ya ziyarci ƙasashen Kenya da Uganda da Zimbabwe, wata ziyara ta farko da wani shugaban Iran ya kai nahiyar Afirka a cikin fiye da shekara 10.
Saudiyya ta gayyaci shugaban ƙasar Iran zuwa Riyadh domin tattaunawa
Ecowas ba ta yi mana adalci ba – Firaministan Nijar
'Adadin Faransawan da suka mutu a harin Hamas ya kai 35'
Ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta ce adadin - Faransawan da suka mutu a harin da Hamas ta kai Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba - ya kai 35.
Cikin wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar, ta ce har yanzu ba a san inda Faransawa tara suke ba, yayin da wasu ke cikin mutanen da Hamas ke garkuwa da su.
"Muna yin duk abin da ya kamata domin samun kuɓutar da su." kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Ma'aikatar ta ce suna tattaunawa da iyalan Faransawan "waɗanda suka ɓace ko suke hannun Hamas".
Gakpo zai iya buga wasan Liverpool da Toulouse
Kotu ta samu wata da laifin kai yarinya Kenya don yi mata kaciya, Daga wakilin BBC Jeremy Britton
Bayanan hoto, Amina Noor ta fada wa babbar kotun hukunta laifuka ta Old Bailey cewa an yi wa yarinyar kaciyar ne saboda dalilai na al'ada
An samu wata mace da laifin kai wata yarinya 'yar Birtaniya zuwa Kenya don yi mata kaciya.
Amina Noor, mai shekara 39 ce, mutum na farko da aka samu da laifin taimaka wa wani wanda ba dan Birtaniya ba, don a yi wa mace kaciya.
Noor, daga yankin Harrow a arewa maso yammacin London, ta dauki yarinyar ne inda ta kai ta wani gida don yi mata irin wannan aiki na kaciya a 2006.
Ta fada wa babbar kotun hukunta manyan laifuka ta Old Bailey cewa, ana yin kaciyar ne saboda dalilai na al'ada kuma ita ma an yi mata kaciya lokacin da take karama.
Sai ranar 20 ga watan Disamba za a yanke wa Noor hukunci, wadda haifaffiyar Somaliya ce amma tana da shaidar zama 'yar Birtaniya.
Sai a shekara ta 2015 ne yarinyar - wadda a yanzu ta kai shekara 21 kuma ba za a iya fadar ko wace ce - ta shaida wa malamar makarantarsu cikin sirri cewa an yi mata kaciya, abin da ya sa aka sanar da 'yan sanda.
Bayan gudanar da gwaje-gwaje ne a asibitin koyarwa na University College a 2019, aka gano cewa gaba daya an cire wa yarinyar dan tsaka.
'Babu barazana'
Da take bayar da shaida a zaman sauraron shari'ar, Noor ta yi ikirarin cewa ta fuskanci matsin lamba ne na ganin an yi yarinyar kaciya saboda al'ada.
Ta ce ita da wata matar ne suka dauki yarinyar a babur mai kafa uku, kuma aka ce mata ta tsaya a kofar wani gida.
Ta yi ikirarin cewa tsammaninta kawai shi ne za a dan rede gaban yarinyar ta yadda za ta dan zubar da jini.
Sai dai, masu shigar da kara sun ce masu taya alkali hukunci na iya tabbatar da cewa wadda aka yi karar ta kwan da sanin cewa kaciya za a yi - kuma ko dai hakan ya kunsa ko bai kunshi cire wa yarinyar dan tsaka ba ko haddasa mata wani nau'in rauni, wanda ba shi da wata manufa a likitance.
Mai shigar da kara Deanna Heer KC ta ce Noor ta sha musanta cewa barazana aka yi mata don lallai ta amince da yi wa yarinyar kaciya.
Mece ce kaciyar mata, a ina ake yi kuma me ya sa?
Wata likita na son a halatta kaciyar Mata
Hamas ta ce an kashe waɗanda ake garkuwa da su 50 da fara luguden wutar Isra'ila
Mai magana da yawun rundunar sojin Hamas ya ce kimanin 'yan Isra'ila 50 da mayaƙanta ke garkuwa dasu a Gaza, aka kashe sakamakon hare-harenda Isra'ila ke kai wa Zirin Gaza, bayan mummunan harin da Hamas ta kai ranar 7 aga watan Oktoba.
Abu Obeida bai yi cikakken ƙarin bayani kan mutanen da aka kashen ba. Haka kuma BBC ba ta iya tabbatar da wannan adadi ko wani bayani da ta fitar ba.
Sojojin Isra'ila sun bayyana sunayen mutum 224 da Hamas ke garkuwa da su a Gaza.
'Idan jinin Musulmi ake zubarwa Kasashen Yamma sukan mance da doka'
Asalin hoton, EPA
Bayanan hoto, ...
Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi kakkausar suka kan matakin da gwamnatocin Kasashen Yamma suka ɗauka a kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza,
Mista Erdogan ya ce Kasashen Yamma sun kasa ɗaukar matakan da suka dace don magance rikicin saboda jinin Musulmai ake zubarwa.
Shugaban na Turkiya ya nuna shakku kan yadda ake aiwatar da yarjejeniyar kare hakkin dan'adam ta duniya, yana mai cewa da alama ƙasashen yammacin duniya sukan yi watsi da ita, idan ba ta dace da muradunsu ba, musamman idan ya shafi asarar rayukan Musulmai.
A wani muhimmin mataki, Erdogan ya soke ziyarar da ya shirya kai wa Isra'ila tare da nuna nadamar yin musabaha da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a taron Majalisar Dinkin Duniya da aka yi a birnin New York cikin watan jiya.
Wannan yana nuna gagarumin sauyi a dangantakar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.
A halin da ake ciki kuma, ministan harkokin wajen gwamnatin Falasɗinawa, Riyad al-Maliki, da ke kula da Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, ba Gaza ba, ya bayyana hare-haren da Isra'ila ta kai a matsayin "yakin ɗaukar fansa."
Da yake jawabi a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da ke kasar Netherlands, al-Maliki ya jaddada cewa harin bama-bamai a Gaza na baya-bayan nan ya fi tsanani fiye da hare-haren da Isra'ila ta kai a baya.
An dakatar da ɗan wasan Newcastle Tonali na tsawon wata goma
Hukuncin kotun koli abin takaici ne - PDP
Asalin hoton, Getty Images
Babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya, ta ce hukuncin Kotun Koli a kan korafin da ta shigar tare da dan takararta Atiku Abubakar, a kan nasarar zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu, babban abin tayar da hankali ne.
Ta ce 'yan Najeriya har yanzu sun kasa fahimtar yadda kotun koli ta lamunci manyan batutuwan yin jabun takardu da tafka karya da shaidar zur, bisa hujjar rashin cika ka'idojin shigar da kara.
Kotun dai ta yanke hukuncin da ya tabbatar da nasarar zaben Tinubu a zaben ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.
PDP ta ce ita, da mafi yawan al'ummar Najeriya sun kadu kuma sun ji takaici tare da nuna damuwa a kan tunanin Kotun Kolin, wanda jam'iyyar adawar ta ce ta yi imani ya saba da tanade-tanaden tsarin mulkin Najeriya da kundin dokokin zaben kasar.
Sanarwar da sakataren yada labaran PDP na kasa, Onarabul Debo Ologunagba ya fitar, babbar jam'iyyar adawar ta jaddada cewa wani abin takaici ne a ce kotun koli ta gaza dabbaka tanade-tanaden doka.
A maimakon haka, sai ta yi watsi da kyakkyawan zaton mafi yawan al'ummar Najeriya wadanda ke kallonta a matsayin gidan samun adalci ta hanyar yanke hukunci a kan batun da ya yi la'akari da dokoki da al'amura na gaskiya a cikin wannan shari'a.
Ta ce da gaske 'yan Najeriya sun yi tsammanin kotun koli za ta tabbatar kuma ta kare tanade-tanaden tsarin mulkin 1999 wadanda suka fayyace karara batun cancantar dan takara da sharadi mafi karanci da ake bukatar cikawa kafin a ayyana mutum a matsayin wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasar Najeriya.
"Musamman la'akari da bukatar doka ta cin kashi 25 na kuri'un da aka kada a birnin Abuja da kuma batutuwan da suka keta dokoki da tsare-tsaren zabe."
PDP dai ta ci gaba da zargin jam'iyyar APC mai mulki da tafka almundahana da jirkita sakamakon zabe.
Ta kuma yi ikirarin cewa hukuncin kamar yadda shaida ta bayyana, ya sanyaya kwarin gwiwar da 'yan Najeriya ke da shi ga bangaren
shari'a, musamman a matsayinta kotun koli na madafar karshe ga talaka.
Za mu ƙalubalanci zaɓen shugaban ƙasa - Atiku Abubakar
Kotu ta kori ɗaya daga cikin ƙorafe-ƙorafen jam'iyyar APM a kan Tinubu
Motocin agaji 12 sun tsallaka zuwa Gaza a ranar Alhamis
Asalin hoton, PRCS
Ƙungiyar bayar da agaji ta Red Crescent ta ce motocin daukar kayan agaji 12 sun tsallaka zuwa Gaza daga Masar ta kan iyakar Rafah a yau Alhamis.
Motocin sun kai ruwa da abinci da magunguna zuwa Gaza, amma babu man fetur, wanda Isra'ila ta hana ƙungiyoyin agaji shiga da shi.
Kungiyar ta ce, an bayar da izinin shigar da manyan motocin agaji 74 zuwa Zirin Gaza tun daga ranar 21 ga watan Oktoba.
A farkon makon nan, daraktan Hukumar kai agaji ta Majalisar Dinkin Duniya, Thomas White, ya shaida wa BBC cewa, kafin ɓarkewar rikici na baya-bayan nan, sama da manyan motoci 450 ne za su rika shiga da kaya zuwa Gaza a kowace rana.
Wanne irin taimako mutanen Gaza ke buƙata?
Ko sauran ƙasashe za su iya shiga yaƙin Gaza da Isra'ila?
An janye ƙarar da aka shigar kan shugaban Fifa
Nasarar da na samu a kotu ta kara min karfin gwiwar yi wa 'yan Najeriya aiki - Tinubu
Asalin hoton, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu/Facebook
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yaba da hukuncin da kotun koli wanda ya tabbatar da nasarar da ya samu a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu.
Kotun kolin a hukuncin da ta yanke ta yi watsi da karar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar da takwaransa na LP, Peter Obi suka shigar.
Hukuncin na zuwa ne ranar Alhamis, bayan manyan shugabannin adawar na Najeriya sun daukaka kara a kan hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa na watan Satumba.
A wata sanarwa da ya fitar jim kadan bayan hukuncin rukunin alkalan kotun bakwai, Shugaba Tinubu ya bayyana jin dadinsa da matsayar kotun kolin a karkashin jagorancin Mai shari’a John I. Okoro, kuma ya yi maraba da hukuncin.
Tinubu ya kuma yaba wa kotun bisa nuna rashin son kai da kuma sadaukarwar da ta nuna wajen tabbatar da bin doka da oda.
Wannan hukunci, a cewar Shugaba Tinubu, ya tabbatar da
hukunce-hukuncen zabe na Najeriya da kuma tsarin mulkin dimokradiyya, wanda ya
ba da gudunmawa ga martabar al’ummar kasar.
Ya ƙara
jaddada aniyarsa ta yiwa dukkan ‘yan Najeriya hidima, ba tare da la’akari da
bangaren siyasa ko kabila, ko kuma addini ba.
Tinubu ya kuma yi kira ga
daukacin ‘yan Najeriya, su hada kai domin gina kasa mai karfi da wadata.
Kotu ta tabbatar da nasarar zaɓen Shugaba Tinubu
Babu hujjar da ke nuna cewa takardun digirin Tinubu na bogi ne
Shekara daya bayan mummunan turmutsutsin Koriya ta Kudu
Bayanan hoto, Lee Ju-hyun tana komawa lungun da ta kusa mutuwa, saboda ba ta so ta manta da abin da ya faru
Shekara daya bayan mummunan turmutsutsin da ya yi sanadin mutuwar matasa kusan 160, Lee Ju-hyun ta sake komawa lungun da aka makure ta, har ta kusa mutuwa
Tana ziyartar wurin ne a kai-a kai, a kokarinta na ganin ba ta mance da miyagun abubuwan da suka faru ba har sai an yi adalci.
Biki ne na karshen mako, inda mutane sama da 100,000 suka sauka a unguwar Itaewon ta birnin Seoul, wadda fitacciyar unguwa ce ta masu zuwa yawon dare don liyafa da shagulgula.
Sun kwarara zuwa wani tsukakkiyar hanya daga fuskoki guda uku, har sai da ta kasance babu masaka tsinke, mutum ba zai iya matsawa gaba ba. Wasu ma ba za su iya ko numfashi ba. Da yawa a nan suka mutu.
Duk da dumbin gazawar hukumomi da bincike ya tabbatar, shekara guda bayan faruwar lamarin, babu wanda aka kama da alhaki, abin da ya bar wadanda suka tsallake rijiya da baya da kuma dangin wadanda suka mutu suna fama da alhini.