Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Sunak ya goyi bayan kiran a dakatar da rikicin Gaza don nuna jin ƙai

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Yusuf Mohammed, Haruna Kakangi, Mukhtari Adamu Bawa and Abdullahi Bello Diginza

  1. Hukumar Alhazai ta bai wa jihohi wa'adin biyan kuɗin Hajji

    Hukumar alhazai ta ƙasa NAHCON ta yi kira ga jihohi da su hanzarta biyan wani ɓangare na kuɗaɗen hajjin maniyatan jihohinsu kafin watan Disamban bana domin tabbatar da kujerun da aka keɓe musu.

    A wata wasika da aka aika wa shugabannin hukumoin alhazai na jihohi, darektan harkar kudi na hukumar, Dr Salihu Usman ya bayyana cewa kiran ya zame dole bisa la'akari da wa'adin biyan kuɗi da ma'aikatar hajji ta saudiyya ta bayar.

    A cewarsa rashin biyan kudaden kafin cikar wa'adin zai sanya hukumar ta ɗauki matakin rage yawan kujerun da aka bai wa jihohin.

    NAHCON ta yi kira ga hukumonin jihohin da su bayar da cikakken goyon baya don tabbatar da nasarar aikin Hajjin 2024.

    • Gane Mini Hanya: Kan ƙarin kuɗin aikin Hajji
    • 'Tsadar rayuwa ta sa kuɗina ba za su kai ni Hajji ba a yanzu'
  2. Kotun ƙoli ta ajiye ranar yanke hukunci kan ƙarar da Atiku da Obi suka ɗaukaka

    Kotun ƙolin Najeriya ta tsayar da ranar Alhamis domin yanke hukunci kan ƙarar da ƴan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, da na jam’iyyar Labour (LP), Peter Obi suka ɗaukaka, suna ƙalubalantar hukuncin kotun ƙorafin zaɓen shugaban ƙasa na 25 ga watan Fabrairu.

    Daraktan yaɗa labarai na kotun ƙolin, Dr Festus Akande, ya tabbatar da hakan ranar Laraba.

    A ranar Litinin din da ta gabata ne dai jam’iyyun PDP da LP suka gabatar da ƙararrakinsu a gaban kotun yayin da aka kori ƙarar da jam’iyyar APM da ƴar takararta na shugaban ƙasa, Chichi Ojei suka shigar bayan sun janye ta.

    A ranar 6 ga watan Satumba ne kotun sauraron ƙararrakin zaben shugaban ƙasa ta yi watsi da ƙarar da bangarorin biyu suka shigar kan rashin isassun shaidu, amma Obi da Atiku sun ɗaukaka ƙara.

  3. Wazirin Fika Dr Adamu Fika ya rasu

    Allah ya yi wa wazirin Fika, Dr Adamu Fika rasuwa a ranar Talata 24 ga watan Oktoba 2023 bayan rashin lafiya da ya yi fama da ita.

    Wata sanarwa da ta fito daga majalisar masarautar Fika ta bayyana cewa za a yi jana'izar mamamcin a masallacin Sultan Bello da ke kaduna, a ranar laraba 25 ga watan Oktoba da ƙarfe huɗu na yamma.

    Ya rasu yana da shekara 90 bayan ya dawo daga ƙasar Ingila inda ya yi jinya.

    Marigayi Adamu Fika ya kasance ƙwararre a harkokin gudanarwa kuma ya rike mukamin uban Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, shi ne kuma shugaban kwamitin Amintattu (BOT) na ƙungiyar tuntuba ta arewa (ACF).

  4. Yau man fetur zai ƙare a Gaza - MDD

    A yayin da ƙasashe da dama na duniya ke kira da a tsagaita wuta domin a samu shigar da kayan agajin da ake bukata a Gaza, jami'an agaji na Majalisar Dinkin Duniya a yankin sun yi gargaɗin cewa a yau Laraba ne man fetur zai kare a yankin.

    Sai dai rundunar sojin Isra'ila ta zargi Hamas da ɓoye man, inda ta wallafa hoton tankokin mai guda goma sha biyu a yankin Zirin Gaza da ta ce suna ɗauke da lita 500,000 na man fetur.

    "Tambayi Hamas ko za ta iya sam muku," in ji rundunar yayin da ta ke mayar da martani ga UNRWA.

  5. Syria ta ce Isra'ila ta kashe sojojinta takwas

    Sojojin Siriya 8 ne suka mutu sannan bakwai suka jikkata sakamakon harin da Isra'ila ta kai kan sansanonin soji a lardin Daraa da ke kudancin ƙasar, kamar yadda kafafen yaɗa labaran ƙasar suka ruwaito.

    Kamfanin dillancin labaran Syria SANA ya ce harin ya faru ne da misalin karfe 01:45 agogon kasar a ranar Laraba.

    Rundunar sojin Isra'ila ta tabbatar da kai hari kan yankunan Siriya - inda ta ce jiragen yaƙinta sun kai hari kan kayayyakin aikin soji da na harba rokoki bayan da aka harba rokoki daga bakin iyakar ƙasar zuwa Isra'ila.

    • Mulkin mallakan da ya hargitsa rayuwa a Gabas ta Tsakiya
    • Gwamnatin Syria ta bayar da damar kai agaji yankin 'yan tawaye
  6. Za a fafata a zagaye na biyu a zaɓen shugaban Liberia

    A wata mai zuwa ne za a gudanar da zagaye na biyu a kasar Laberiya bayan an yi canjaras a zagayen farko tsakanin shugaba George Weah da babban abokin hamayyarsa Joseph Boakai.

    Mista Weah ya samu kashi 43.83% na ƙuri'un da aka kaɗa sannan Mista Boakai, wanda tsohon mataimakin shugaban ƙasa ne ya samu kashi 43.44%.

    Zaben na ranar 10 ga watan Oktoba shi ne zaben shugaban ƙasa wanda ya fi zafi a Laberiya tun bayan yaƙin basasa kimanin shekaru ashirin da suka gabata.

    Za a je zagaye na biyu ne yayin da babu ɗan takarar da ya samu fiye da kashi 50% na ƙuri'un da aka kaɗa a zagayen farko.

    A ranar 14 ga watan Nuwamba ne dai shugabar hukumar zaben, Davidetta Browne ta bayyana cewa za a gudanar da zagaye na biyu na zaɓen.

  7. An kashe ƙarin mutane 80 a Gaza cikin dare

    Gwamnatin Hamas da ke Zirin Gaza ta ce akalla mutane 80 ne suka mutu sakamakon harin da Isra'ila ta kai cikin dare.

    Sanarwar da ofishin yaɗa labaran gwamnatin ƙasar ya fitar ta ce sama da mutane 80 ne aka kashe tare da jikkata wasu ɗaruruwa bayan farmakin da Isra'ila ta kai, a cewar kamfanin dillancin labaran AFP.

    Isra'ila ta fara kai hari kan Hamas a Gaza tun bayan da wasu 'yan bindiga suka ƙaddamar da farmaki kan Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba, inda suka kashe mutane fiye da 1,400.

    Ma'aikatar lafiyar Gaza ta ce sama da mutane 5,800 aka kashe a Gaza tun daga lokacin.

    • Yadda gawawwaki suka mamaye asibitocin Gaza
    • Yaya mamayen ƙasa na sojojin Isra'ila zai kasance a Gaza?
  8. Barka da warahaka!

    Masu bibiyar mu a wannan shafi barkan mu da safiyar Laraba.