Wannan rana ce ta makoki.
A gefen wasu bishiyoyin ruman cikin wani lungu mai shiru wanda ya saba da yanayin makokin rasuwarsu, an haka kaburbura guda uku na mahaifiya Lianne da 'ya'yanta mata biyu: Noiya and Yahel Sharabi.
Dangin da Hamas ta yi kokarin shafe su daga doron duniya.
Sabani tsakanin wannan muhalli da wani hoto na mahaifiya Lianne da ke murmushi lokacin da ta sa hannuwa ta dafa kafadun 'ya'yanta 'yan mata biyu, wanda aka dauke watanni kalilan da suka wuce lokacin da suke murnar bikin Kibbutz Be'eri, a kudancin Isra'ila, ba a rufe yake ba.
Hatta gawawwakinsu, ba su iya komawa gida ba. An daidaita Be'eri - wurin da aka yi kisan kiyashi. An kashe dumbin mutane, duk da haka wadanda ke raye ba za su iya binne makusantansu a can ba.
Don haka ake binne wadannan dangi, 'Yan Isra'ila daga asalin Birtaniya a wata makabarta da ke da nisan kimanin kilomita 40 daga iyaka da Gaza.
Ahalin Sharabin, ba su iya samun kwanciyar hankali ba. Mahaifin 'yan matan Eli har yanzu ba a gan shi ba. An kuma sace kawunsu, Yosi. A nan yara ba za su iya kukan rashin mahaifansu ba. Iyaye ba za su iya makokin 'ya'yansu ba.
A Isra'ila, daruruwan mutane ne suka taru don jana'izarsu inda masu makokin da yawa suka sanya riga mai tambarin: "An yi wa Lianne, Noiya da Yahel kisan gilla. A dawo mana da Eli da Yosi yanzu."
'Yan mata suna kukan rashin kawayensu Yahel da Noiya, sun ma kasa fahimtar abin da ya faru da dangin nan.
Mutuwa da bata da kuma sacewa. Mugun al'amari a wannan rana, ga wannan kasa, da kuma wannan dangi.
Lianne ta je Isra'ila ne daga Bristol tun tana 'yar shekara 19 don aiki a kibbutz. Daga nan ta gina rayuwarta a can kafin Hamas ta yanke shawarar kwace hakan daga gare ta da kuma 'ya'yanta.