Isra'ila ta shafe shekara 56 tana gallaza wa Falasɗinawa - Antonio Guterres

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Yusuf Mohammed, Haruna Kakangi and Umar Mikail

  1. An kashe ƙarin ma'aikatan jin-ƙai shida a Gaza

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    An kashe ƙarin ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya shida a Gaza, a cewar hukumar kula da ƴan gudun hijira ta Falasdinawa UNRWA.

    Ya kawo adadin ma'aikatan UNRWA da aka kashe a Gaza tun lokacin da aka fara rikicin zuwa 35.

    "Muna jimamin rashin abokan aikinmu yayin da suke yin duk abin da za su iya don taimakawa mabuƙata," Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya wallafa a shafinsa na X a daren Litinin.

    • Yaya mamayen ƙasa na sojojin Isra'ila zai kasance a Gaza?
    • Rayuwa a Gaza: 'Babu wurin fakewa a ruwan makamai masu linzami'
  2. 'Ƴan Birtaniya shida ne Hamas ke garkuwa da su'

    ..
    Bayanan hoto, Ministar gwamnatin Birtaniya Victoria Atkins

    Ministar gwamnatin Birtaniya, Victoria Atkins ta ce adadin ƴan ƙasar Birtaniya da aka kashe a yaƙin da aka yi tsakanin Isra’ila da Hamas ya kai 10.

    Ta ce wasu mutanen Birtaniyya guda shida kuma sun ɓace, waɗanda ake kyautata zaton ana garkuwa da su a Gaza.

    "Mun fahimta - kuma ina yin taka tsan-tsan saboda mun san muhimmancin daidaiton alƙaluma a cikin wannan yanayin - amma mun fahimci cewa garkuwa ne aka yi da su," kamar yadda ta faɗa wa kafar yaɗa labaru ta Sky News.

    ''Su ne muka fi bai wa fifiko''

    • Musulmai da Yahudawan Birtaniya na fargabar alaƙarsu saboda yaƙin Gaza
    • Rikicin Isra'ila da Gaza: Mene ne asalin sa?
  3. Mutane da dama sun mutu a hatsarin kwale-kwale a DR Congo

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Akalla mutane 40 ne suka nutse bayan da wani kwale-kwale ɗauke da fasinjoji ya kife a wani kogi da ke yammacin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo, mako ɗaya bayan wasu 47 sun mutu a wani hatsarin makamancin haka.

    Kwale-kwalen na dauke da fasinjoji da kayayyaki, a lokacin da ya kife a kogin Lulonga.

    Lamarin ya faru ne a kusa da ƙauyen Boyeka da ke lardin Equateur.

    Fasinjojin wadanda akasari 'yan kasuwa ne, suna dawowa ne daga wata kasuwar yankin zuwa Mbandaka, babban birnin lardin.

    Adadin waɗanda suka mutu na iya ƙaruwa yayin da wasu fasinjojin suka bace. Fiye da mutum 200 sun tsira, kamar yadda kafafen yaɗa labarai na cikin gida suka ruwaito.

    Hatsarin dai ya faru ne kwanaki goma bayan da wani kwale-kwalen ya kife a wannan lardin, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama, da kuma bacewar wasu da ba a san adadinsu ba.

    • Adadin wadanda suka rasu sakamakon arangama a sansanonin MDD a Dimokraɗiyar Congo ya kai 19
    • 'Ambaliyar ruwa ta tafi da matata da ƴaƴana 13'
  4. Isra'ila ta harba makamai masu linzami 400 a Gaza cikin kwana ɗaya

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Dakarun tsaron Isra'ila (IDF) sun ce sun kai hari sama da 400 a Gaza a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, saɓanin 320 da ta sanar a daidai wannan lokaci a jiya.

    A wata sanarwa da aka buga a shafin X, IDF ta ce makaman da ta harba sun hari 'yan bindigar Hamas ne waanda da suka harba rokoki zuwa Isra'ila, da kuma ramukan da ke bai wa Hamas damar kutsawa cikin Isra'ila ta cikin teku.

    Har ila yau, ta ce an kai hari kan cibiyoyin bayar da umarni da mayaƙa ke amfani da su da kuma inda ake shirya makamai a masallatai.

    IDF ta kara da cewa "za a ci gaba da aiki domin tabbatar da tsaron fararen hula marasa laifi".

    • Luguden wutar Isra'ila ya kashe mutum fiye da 900 a Gaza
    • Ba za mu gushe ba har sai mun shafe Hamas daga doron kasa - Netanyahu