Isra'ila ta shafe shekara 56 tana gallaza wa Falasɗinawa - Antonio Guterres

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Yusuf Mohammed, Haruna Kakangi and Umar Mikail

  1. Ƙarshen rahotonni

    A nan za mu rufe wannan shafi da ya kawo rahotonni kai-tsaye.

    Idan kuka duba ƙasa za ku ga labaran da muka wallafa a yau Talata musamman game da halin da ake ciki a Gaza da kuma Isra'ila.

    Ku kasance da mu gobe da safe, inda za mu kawo wasu rahotonnin.

    Umar Mikail ne ke muku fatan alheri.

  2. Sojojin Najeriya sun kashe 'yan fashi da dama a jihar Sokoto

    Rundunar sojin Najeriya ta ce ta halaka ‘yan bindiga da dama a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin ƙasar.

    Lamarin ya faru ne a ƙauyen Tukandu bayan harin da dakarun runduna ta takwas suka kai a yau Talata.

    Wata sanarwa daga rundunar ta ce dakarun sun kuma ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 tare da babura daga hannun ‘yan bindigar.

    Latsa hoton ƙasa ku saurari rahoton da Zubairu Ahmad Kasarawa ya haɗa mana:

    Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari rahoton da Zubairu Ahmad Kasarawa ya haɗa mana:
  3. Za a je zagaye na biyu a zaɓen shugaban ƙasar Liberiya

    Gaza

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban Liberiya George Weah da babban ɗan takarar adawa Joseph Boakai za su shiga zagaye na biyu bayan kowannensu ya gaza samun kashi 50 na ƙuri'un da aka kaɗa a zaɓen shugaban ƙasa.

    Shugaba Weah da ke neman tazarce a jam'iyyar Congress for Democratic Change (CDC), ya samu kashi 43.83 cikin 100 na ƙuri'un, yayin da Mista Boakai na Unity Party (UP) ya samu 43.44.

    A cewar shugabar hukumar zaɓen ƙasar, Davidetta Lansanah, za a gudanar da zagaye na biyun a ranar 14 ga watan Nuwamba.

    Ta kara da cewa an buɗe yaƙin neman zaɓe da yau Talata har zuwa 12 ga watan Nuwamba.

  4. Kayan agaji ba su shiga Gaza cikin sauri yadda ya kamata ba - Biden

    Joe Biden

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban Amurka Joe Biden ya ce kayan agaji ba su shiga Zirin Gaza cikin sauri kamar yadda ake buƙata.

    "Ba kamar yadda ake buƙata ba," kamar yadda ya amsa bayan wani ɗan jarida ya tambaye shi kan ko agajin na shiga zirin.

    Kalaman nasa na zuwa ne yayin da hukumar MDD a Gaza ta ce dole za ta tsayar da ayyukan agaji cikin awa 24 idan ba a bari man fetur ya shiga zirin ba.

    Tun da farko, wata mai magana da yawun MDD ta ce manyan motoci 20 da ke kan layi ba su samu damar shiga Gaza ba, amma tana fatan za su samu shiga ranar Laraba.

  5. Isra'ila ta nemi sakataren MDD Antonio Guterres ya sauka daga muƙaminsa

    Antonio Guterres

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan harkokin wajen Isra'ila ya soki Sakataren MDD Antonio Guterres game da kalaman da ya yi cewa "ba haka kawai Hamas ta kai hari Isra'ila ba".

    Cikin fushi Eli Cohen ya mayar wa da Mista Guterres martani cewa "sakatare a wace duniyar kake zaune ne?"

    Sakataren ya bayyana haka ne hakan yayin da yake yi wa Zauren TSaro na MDD jawabi, kamar yadda muka bayyana a nan.

    Daga baya ministan ya ce ya fasa ganawa da Mista Guterres da aka tsara tun farko - wanda shi kuma kakakinsa ya ce sakataren zai gana da iyalan waɗanda Hamas ke garkuwa da su tare da jami'an Isra'ila.

    "Babban sakataren MDD ɗin da ya nuna sassauci game da kashe-kashen yara da mata da tsofaffi, bai cancanci ya shugabanci MDD ba," in ji wakilin Isra'ila a MDD Gilad Erdan cikin wani saƙo a dandalin X.

  6. Isra'ila ta shafe shekara 56 tana gallaza wa Falasɗinawa - Antonio Guterres

    Guterres

    Asalin hoton, EPA

    Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) Antonio Antonio Guterres ya ce "ba haka kawai Hamas ta kai hare-hare" cikin Isra'ila ba, inda ta kashe mutum 1,400 a farkon watan nan.

    Da yake yi wa taron Zauren Tsaro (UNSC) jawabi a yau, Mista Guterres ya ce an shafe tsawon shekaru ana gallaza wa Falasɗinawa.

    "An tsare Falasɗinawa cikin ƙunci tsawon shekara 56," in ji shi.

    "An gina gidaje a kan ƙasarsu suna gani, an tashi hankalinsu, an lalata tattalin arzikinsu, an kori mutanensu, an rushe gidajensu. Fatan da suke da shi na zaman lafiya na ƙarewa."

    Sai dai kuma sakataren ya ce waɗannan matsaloli da Falasɗinawa ke ciki ba za su sa "a goyi bayan harin da Hamas ta kai ba, wanda shi ma ba zai sa a ce abin da Isra'ila ta yi na hukunta dukkan Falasɗinawa ya yi daidai ba".

    "A irin wannan lokaci mai haɗari, yana da kyau a fayyace abubuwa ƙarara, farawa da ɗabi'un mutuntawa da kuma kare rayukan fararen hula."

  7. Hare-haren Isra'ila sun raba mutum miliyan 1.4 da muhallansu a Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, EPA

    Mutum kusan miliyan 1.4 daga miliyan 2.2 na Zirin Gaza ne aka raba da muhallansu - kuma adadin na ƙaruwa cikin sauri tun bayan da Isra'ila ta umarci mazauna arewaci su koma kudancin birnin a ranar 13 ga watan Oktoba.

    Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta ce idan ba a bari an shigar da man fetur cikin Gaza ba za ta dakatar da aikin agajin da take yi a gobe Laraba.

    Akwai mutum kusan 590,000 da ke samun mafaka a sansanoni 150 da aka bayyana a matsayin na 'yan gudun hijira a hukumance - akasarinsu ginin makarantu ne da MDD ke kula da su.

    An yi ta nuna fargabar cunkoso, yayin da MDD ke cewa adadin ya ninka fiye da sau biyu na mutanen da ya kamata su zauna a wuraren.

  8. Ƴan bindiga sun yi garkuwa da kusan mutum 40 a Kamaru

    ...

    Asalin hoton, AP

    Kimanin ‘yan kasar Chadi da Kamaru 40 ne aka yi garkuwa da su a garin Touboro da ke arewacin Kamaru, kamar yadda wani magajin garin ya bayyana.

    Celestin Yandal ya shaida wa BBC cewa wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai hari inda suka yi wa 'yan kasuwa na Chadi kwanton ɓauna a ranar Lahadin da ta gabata, yayin da suke komawa gida daga kasuwar Touboro inda suke cinikin shanu.

    Ya ce an kuma yi garkuwa da wasu mutanen "da suke barin Chadi zuwa Kamaru, ciki har da dalibai, da wadanda ke komawa kan iyakar Chadi".

    Ma'aikatar tsaron ƙasar Chadi ta ce kawo yanzu dakarunta sun kuɓutar da mutane takwas daga cikin wadanɗa aka yi garkuwa da su.

    Har yanzu ma'aikatar tsaron Kamaru ba ta amsa bukatar BBC na jin ta bakinta ba, amma wani jami'in tsaro ya ce sojoji na kokarin kubutar da sauran waɗanda aka yi garkuwa da su.

    Ƙasashen Kamaru da Chadi dai na da iyaka mai tsawon kilomita 1,100 (kilomita 680), inda ake fuskantar yawancin laifukan yin garkuwa da mutane da sata da sauran munanan ayyuka.

    A baya-bayan nan ne ƙasashen biyu suka ƙuduri aniyar ƙarfafa haɗin gwiwa domin kare 'yan ƙasarsu da albarkatunsu.

    • Kamaru: Sabuwar ƙungiyar ‘yan tawaye ta ɓulla a ƙasar
    • Yadda ƙudajen zuma suka yi kane-kane a unguwannin Kamaru
  9. Majalisa ta kafa kwamitin bincke kan gyaran matatun fetur na Najeriya

    Man fetur

    Asalin hoton, Getty Images

    A Najeriya, majalisar dattawa ta kafa wani kwamiti da zai gudanar da bincike don sanin inda aka kwana a aikin gyara matatun man fetur na ƙasar.

    Binciken zai haɗa da ɗimbin kudin da aka kashe da sunan gyaran tun daga shekara ta 2010 zuwa 2023, wanda ake zargin ya kai fiye da naira tiriliyan 11.

    'Yan majalisar sun ce ba daidai ba ne a ce gwamnati ta kashe irin wannan kuɗi mai yawa ba tare da samun biyan bukata ba.

    Sanata Kawu Sumaila ya halarci zaman majalisar, kuma ya yi wa Ibrahim Isa ƙarin bayani kan muhawarar da suka yi a zaman.

    Latsa hoton da ke ƙasa don sauraron hirar:

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama don sauraron hirar:
  10. Macron ya gana da jagoran Falasɗinawa a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan

    Macron da Mahmoud Abbas

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban Faransa Emmanuel Macron, wanda ya tattauna da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ɗazu, ya fara ganawa da Shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas a Ramallah.

    Macron ne shugaba na farko daga ƙasashen Yamma da ya gana da Abbas a yankin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan (West Bank) da Isra'ila ta mamaye tun daga ranar 7 ga watan Oktoba. Firaministan Birtaniya ya gana da shi a makon da ya gabata amma a Masar.

    Abin da ya kamata a sani shi ne, yayin da gwamnatin Palestinian Authority ta Abbas ke iko da West Bank, ba ta da iko da Gaza - Hamas ce ke iko da shi tun 2007.

    Da yake magana yayin taron manema labarai da Netanyahu a Tel Aviv, macron ya nemi ƙasashen duniya su haɗa kai wajen daƙile Hamas kamar yadda suka yi wajen kawo ƙarshen ƙungiyar Islamic State.

  11. Labarai da dumi-dumi, Hamas ta harba rokoki kan birnin Tel Aviv

    Jiniyar da ke alamta kai hari ta yi kuka a tsakiyar Isra'ila bayan Hamas ta kaddamar da hare-haren roka kan birnin Tel Aviv cikin mintuna kalilan da suka wuce.

    Hukumomin ba da agajin gaggawa na Isra'ila sun ce ba a samu rahoton wanda ya ko jikkata ba zuwa lokacin kawo wannan rahoto daga birni na biyu mafi girma a Isra'ila da kuma wasu wuraren, sai dai wasu da suka ji raunuka a lokacin da suke kokarin neman mafaka.

  12. "Yara sama da 2,300 ne aka kashe a hare-haren da Isra'ila ta kaddamar a Gaza"

    Jakadan Falasdinawa a Najeriya ya yi ikirarin cewa hare-haren da Isra'ila ta kaddamar a kan Zirin Gaza tun bayan harin da Hamas ta kai wa kasar, sun yi sanadin mutuwar kananan yara fiye 2,300.

    A cewar Abdullah Abu Shawesh, hare-haren sun kuma yi sanadin hallaka mata kusan 1,500.

    Isra'ila dai ta lashi takobin wargaza kungiyar Hamas, wadda ta kai mummunan harin bazata, da ya yi sanadin kashe mutuwar mutum 1,400 tare da sace fiye da wasu 200.

    Jakadan al'ummar Falasdinawan na wannan bayani ne yayin wani taron manema labarai da ya kira don sanar da duniya halin da ake ciki game da rikicin Isra'ila da Gaza da kuma yadda lamarin ya ranar Talata a Abuja, babban birnin Najeriya.

    Abu Shawesh ya ce jimillar Falasdinawan da aka kashe tun daga ranar 7 ga watan Oktoba, sun kai 5791.

    Jakadan ya kuma zargi kasashen Turai da mara baya ga Isra'ila kan abin da ya kira kisan kiyashin da take yi a yankunan Falasdin ba.

    A cewarsa bai kamata a rika zaben dokokin kasashen duniya da za a yi aiki da su ba, sannan a yi watsi da wasu.

    Abdullah Abu Shawesh ya ce matakin soja, bai taba yin aiki ba a lokutan baya, don haka ba zai yi aiki ba ma a wannan lokaci.

  13. Gwamnatin Najeriya za ta fito da wani tsarin don farfaɗo da darajar naira, Daga Zubairu Ahmad Kasarawa

    Gwamnatin Najeriya ta ce nan da ‘yan makonni kaɗan masu zuwa za ta fito da wani tsarin da zai samar da kimanin dala biliyan goma, da za a yi amfani da shi wajen farfaɗo da darajar naira da kuma sauke farashin kaya.

    Gwamnatin ta ce za ta samar da kuɗin ne ta hanyoyin shigo da masu saka jari daga ketare da kuma samarwa kamfanin mai na NNPCL wadatattun kuɗaɗen ketare.

    Ku latsa ƙasa don sauraron rahoton Zubairu Ahmad Kasarawa.

    Bayanan sautiLatsa hoton sama domin sauraron rahoton
  14. Najeriya ta ƙaddamar da riga-kafin HPV mai haddasa kansar bakin mahaifa

    ..

    Najeriya ta kaddamar da shirin allurar riga-kafin cutar Human papillomavirus (HPV) wadda ke haifar da cutar kansar bakin mahaifa kashi na farko.

    Hakan na nufin za a sanya allurar a cikin jadawalin rigakafin yau da kullum na ƙasa.

    Babban maƙasudin wannan yunƙurin shi ne haɓaka karɓar allurar riga-kafin da nufin yaƙar cutar kansar bakin mahaifa wadda za a iya guje ma wa ta hanyar rigakafin.

    Cutar kansar bakin mahaifa ita ce ta biyu da ta fi kamari a tsakanin mata a Najeriya, kuma ita ce ta hudu da ta fi kama mata a duniya.

    Ministan lafiya na Najeriya, Muhammad Pate, ya bayyana wa BBC halin da ake ciki game da cutar kansar bakin mahaifa a ƙasar.

    Ya ce, “Aƙalla mata 12,000 ke fama da ciwon kansar bakin mahaifa [a Najeriya] duk shekara, kusan kashi 90% ne ke rasa rayukansu saboda hakan. Dakile shi [Human papillomavirus] a tsakanin ƴan mata masu tasowa, kafin su kamu da kwayar cutar da ke haifar da kansar shi ya sa muka bullo da riga-kafin cutar papillomavirus".

    Yunƙurin tabbatar da wannan rigakafin ya sa an tattaro ƴan sa kai da ma’aikatan lafiya sun ziyarci makarantu a faɗin ƙasar ta yammacin Afirka domin wayar da kan yara mata kan muhimmancin riga-kafin.

    • Riga-kafin kansar mahaifa na rage kamuwa da cutar da kaso 90 cikin 100
    • Ranar Kansa Ta Duniya: Cutukan kansa mafiya haɗari shida da suka kamata ku sani
  15. Amurka ta kawo ƙarshen agaji a Gabon sakamakon juyin mulki

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Amurka ta dakatar da yawancin tallafin da take bai wa ƙasar Gabon a matsayin martani kan juyin mulkin da sojoji suka yi watanni biyu da suka gabata.

    Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce a hukumance ta tabbatar da cewa an yi juyin mulki a ƙasar da ke yammacin Afirka, wanda a ƙarƙashin dokokin Amurka na buƙatar kawo ƙarshen taimakon da ba na jin-kai ba.

    Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta ce, za a ci gaba da bai wa Gabon taimakon jin-kai, da lafiya da ilimi.

    A watan da ya gabata, Amurka ta ce ta dakatar da wasu shirye-shiryen taimakon ƙasashen waje da gwamnatin sojan Gabon ke amfana da su.

    Sojoji ƙarƙashin jagorancin Janar Brice Oligui Nguema sun hamɓarar da gwamnatin Ali Bongo Ondimba a watan Agusta, a daidai lokacin da aka ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen da aka yi ta ce-ce-ku-ce a kai.

    Gwamnatin mulkin sojan ta nada Raymond Ndong Sima, wanda ya kasance madugun 'yan adawa, a matsayin Firaministan Gabon.

    • Wasu abubuwan da ƙila ba ku sani ba game da ƙasar Gabon
    • Ali Bongo da shugabannin Afirka da suka kafe a kan mulki
  16. An kashe sama da mutane 700 a Gaza cikin kwana ɗaya

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikatar lafiya a Gaza ta fitar da wani bayani, inda ta ce akalla mutane 5,791 aka kashe a Gaza tun daga ranar 7 ga Oktoba.

    Hakan ya nuna ƙarin mutane fiye da 700 kan adadin da aka sanar jiya.

    Isra'ila ta ce ta kai hari kan wurare sama da 400 a Gaza a ranar da ta gabata - ta ce tana kai hari ne kan kayayyakin aiki na Hamas.

    • Yadda kan ƙasashen Afirka ya rabu game da rikicin Isra'ila da Gaza
    • Yadda gawawwaki suka mamaye asibitocin Gaza
  17. Kotu ta yanke wa wani likita ɗaurin rai-da-rai a kan fyade

    ..

    Kotun laifukan lalata da cin zarafin cikin gida a jihar Legas da ke zamanta a Ikeja a ranar Talata ta yanke hukuncin ɗaurin rai-da-rai kan daraktan kula da lafiya na gidauniyar kula da cutar daji, Dakta Olufemi Olaleye, bisa laifin lalata da ‘yar uwar matarsa.

    Mai shari’a Rahman Oshodi ya yanke masa hukuncin ne bayan ya same shi da laifin lalata da yarinyar ‘yar shekara 15.

    Alƙalin kotun ya ce masu gabatar da ƙara sun iya tabbatar da ƙarar ba tare da wata shakka ba, kuma dukkan shaidun da ke gaban kotun sun daidaita da na wanda aka azabtar.

    An gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban kotu a ranar 30 ga Nuwamba, 2022, kuma ya musanta aikata laifin.

    Daraktan ƙararrakin jama’a Dr Babajide Martins ya shaidawa kotun cewa Olaleye ya aikata laifukan ne a tsakanin watan Fabrairun 2020 zuwa Nuwamba 2021.

  18. Mun fuskanci bala'i a hannun Hamas - Tsohuwar da aka saki

    Yocheved Lifschitz

    Yocheved Lifschitz, mai shekaru 85, ta ce ta shiga mawuyacin hali, inda ta bayyana yadda ƴan bindigar Hamas suka yi garkuwa da ita a kan babura daga ƙauyen kibbutz.

    Ta ce sun shigo da ita Gaza ta wata ƙofa, inda ta ji raunuka. Ta ƙara da cewa ta fuskanci matsala wurin numfashi.

    Ta kuma bayyana cewa sun rinƙa kwana kan katifu a cikin ramukan da Hamas ta gina na ƙarƙashin ƙasa a Gaza, inda likita ya riƙa kai mata ziyara bayan kwana uku-uku.

    Lifschitz ta ce gwamnatin Isra'ila ta kashe biliyoyin kuɗi a shingen kan iyaka - amma hakan bai hana Hamas shiga ba.

    Lifschitz na ɗaya daga cikin mata biyu da Hamas ta saki ranar Litinin - ta uku da huɗu da aka yi garkuwa da su tun bayan da ƙungiyar Hamas ta yi awon gaba da mutane sama da 200 daga Isra'ila aka kai su Gaza.

    • Wace ce Hamas, mene ne ke faruwa a Isra'ila, da sauran tambayoyi
    • 'Yadda Putin ke son ya ci gajiyar yaƙin Isra'ila da Gaza'
  19. An ci tarar Pillars Naira miliyan ɗaya

    ...

    Asalin hoton, TWITTER/KANO PILLERS

    A ranar Litinin ne aka ci tarar Kano Pillars kuɗi har Naira miliyan ɗaya, sakamakon kutsen da magoya bayanta suka yi a filin wasa, lokacin da suka fafata da Rivers United.

    An tabbatar da cewa magoya bayan ƙungiyar Kano Pillars sun ketara shingen filin wasa domin murnar cin ƙwallon da suka yi a minti na 92 ​​a karawar da suka yi a filin wasa na Sani Abacha.

    Bayan nazarin rahotanni daga jami'an wasan, hukumar kula da gasar Firimiya ta Najeriya, NPFL ta tuhumi kulob din da laifin karya doka mai lamba B13.18.

    Don haka an umurci kulob din da ya biya tarar cikin kwana 14 kuma ya ja kunne kan hakan, wanda gaza yin hakan zai zamo tamkar ci gaba da saɓa wa dokokin hukumar ta NPFL.

    • Kano Pillars ta naɗa Abdu Maikaba sabon kocinta
    • Wanne sauyi sabbin shugabannin riƙo 13 za su kawo wa Kano Pillars?
  20. Ana kula da tsofaffin mata biyu da Hamas ta sako

    Yocheved Lifschitz

    Asalin hoton, Jenny Yerushalmi, Ichilov Hospital

    Mutanen biyu da aka yi garkuwa da su a Gaza waɗanda aka saki a yammacin ranar Litinin - Nurit Cooper da Yocheved Lifshitz - suna jinya a asibiti a Tel Aviv.

    Ɗiyar ɗaya daga cikinsu, Sharone Lifschitz, ta shaida wa BBC cewa da alamu mahaifiyarta na cikin ƙoshin lafiya.

    ...

    Asalin hoton, Jenny Yerushalmi, Ichilov Hospital

    Da take magana daga asibitin, ta ce ma’aikatan jinya sun shaida mata cewa mahaifiyarta na cikin natsuwa kuma akwai bayanan da take son isarwa ga iyalan sauran waɗanda aka yi garkuwa da su.

    Ta ce har yanzu akwai sama da mutane dari biyu da ake tsare da su - ciki har da mahaifinta.