Hamas ta saki ƙarin 'yan Isra'ila biyu da ta yi garkuwa da su

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya,

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Yusuf Mohammed, Haruna Kakangi and Umar Mikail

  1. Isra'ila ta ce ta tarwatsa maɓuyar 'ƴan ta'adda' a Lebanon

    Israeli soldiers

    Asalin hoton, Reuters

    Kakakin rundunar sojin Isra'ila Daniel Hagari ya bayyana cewa, a cikin sa'o'i 24 da suka wuce, dakarun Isra'ila sun kai hari kan maɓuyar 'ƴan ta'adda' takwas a ƙasar Lebanon.

    Bakwai daga ciki an auka musu ne kafin su yi nasarar harba makamai masu linzami da kuma rokoki, in ji shi.

    Har ila yau, Hagari ya ce an kai hare-hare kan gungun mayaƙan Hezbollah 20 tun bayan ɓarkewar faɗa a kan iyakar ƙasar a farkon wannan watan.

    Yanzu haka dai rundunar ta IDF ta ce ta harba makami mai linzami kan wani abu da ba ta yarda da shi ba da ya shiga sararin samaniyar Isra'ila daga Lebanon.

    • Ana kwashe 'yan Isra'ila a ƙauyukan iyaka da Lebanon saboda barazanar hari
    • Ko sauran ƙasashe za su iya shiga yaƙin Gaza da Isra'ila?
  2. Kamfanin Google ya karrama Rashidi Yekini

    Rashidi Yekini

    Asalin hoton, AFP

    Kamfanin Google ya karrama marigayi dan kwallon Najeriya, Rashidi Yekini ta hanyar sanya zanensa a shafin na google a daidai lokacin da dan wasan ke cika shekaru 60 da haihuwa.

    Yekini dai ya faɗa ƙangin talauci da rashin matsuguni bayan yin fice a matsayin ɗaya daga cikin manyan taurarin ƙwallon ƙafa na Najeriya.

    Zanen na Google ya kwatanta murnar da Yekini ya yi lokacin da ya ci wa Najeriya ƙwallonta ta farko a gasar cin kofin duniya a 1994.

    Hakan ya nuna lokacin da Yekini ya zura ƙwallo a ragar Bulgeriya, ya shige cikin ragar tare da kama ta da hannu bibbiyu yayin da hawayen murna ke kwararo masa.

    • Najeriya za ta kara da Afirka ta Kudu a wasan neman gurbin kofin duniya
    • Afcon 2024: Najeriya ta samu gurbin shiga gasar kofin Afirka
  3. Shirin da muke yi don bunƙasa kiwon lafiya a Najeriya - Pate

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
  4. Labarai da dumi-dumi, Ayari na uku ɗauke da agaji ya shiga Gaza daga Masar

    Rahotannin da muke samu na nuna cewa ayarin motoci na uku ɗauke da kayan agaji ya shiga Gaza daga Masar.

    Kamfanin dillancin labaran Reuters da AFP sun ce ƙarin motocin agaji sun shiga Gaza ta iyakar Rafah.

    Wannan ya biyo bayan shigar motocin agaji 34 a ranakun Asabar da Lahadi.

    Za mu ci gaba da kawo muku ƙarin bayani...

  5. Isra'ila na ruwan wuta har a kudancin Gaza

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare a Zirin Gaza, ciki har da kudancin yankin, inda ta ce Falasɗinawa su je domin tsira da rayukansu.

    Wakilin BBC a Khan Younis da ke kudancin Gaza ya ce Isra'ila ta yi ta kai hare-haren bama-bamai a cikin dare.

    Ya ce wasu daga cikin bama-baman na da kusan mita ɗari da wani asibiti.

    Hamas dai na ci gaba da harba rokoki cikin Isra'ila.

    Isra'ila shiada wa wa mutanen arewacin Gaza da su yi hijira zuwa kudancin yankin fiye da mako ɗaya da ya wuce gabanin yiwuwar kai farmaki ta ƙasa.

    Dubban Falasdinawa na kwana a kan tituna da kuma fakewa a asibitoci.

    Wasu mutane sun koma gidajensu a arewacin ƙasar saboda ƙarancin abinci da ruwan sha da kuma matsalolin rashin tsaro a kudancin ƙasar.

    Hamas ta ce hare-haren da Isra'ila ke kai wa a Gaza sun kashe sama da mutane 4,600.

    Harin da Hamas ta kai kan Isra'ila a farkon wannan watan ya yi sanadiyar mutuwar fiye da ƴan Isra'ila 1,400.

    • Shugabannin Saudiyya da Iran karon farko sun tattauna a kan rikicin Gaza
    • Rikicin Isra'ila da Gaza: Nawa Amurka ke kashewa wajen tallafa wa Isra'ila?
  6. Ƴan Gaza na komawa arewa duk da gargadin da Isra'ila ta yi - MDD

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Wasu mutanen da suka tsere daga arewacin Gaza bayan da sojojin Isra'ila suka ce su fice yanzu suna komawa, in ji shugaban hukumar kula da ƴan gudun hijira ta Falasɗinawa na Majalisar Dinkin Duniya.

    Thomas White na hukumar UNRWA ya shaida wa BBC 4 cewa: "Akwai matukar haɗari a arewa amma har a kudancin ƙasar mutane na rasa rayukansu."

    White ya ce mutane 8,000 ne ke samun matsuguni a rukunin gidajen ajiyar kaya na hukumarsa kuma suna rayuwa kan lita ɗaya na ruwa da buredi a rana.

    Sojojin Isra'ila sun ce sun kai hari kan wurare 320 a faɗin zirin Gaza cikin sa'o'i 24 da suka wuce.

    • Luguden wutar Isra'ila ya kashe mutum fiye da 900 a Gaza
    • Ko samame ta ƙasa da Isra’ila ke shirin kai wa Gaza zai yi nasara?
  7. Ba a yi yunkurin hallaka ni ba - Bello

    Yahaya Bello

    Asalin hoton, FACEBOOK/YAHAYA BELLO

    Gwamnan jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya, Yahaya Bello ya musanta cewa ya tsallake rijiya da baya yayin da aka kai masa hari a kan hanyar Lakwaja zuwa Abuja.

    Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ruwaito kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kogi, Kingsley Fanwo yana cewa ƴan bindiga sanye da kayan sojoji sun kai hari kan ayarin motocin Mista Bello a ranar Lahadi.

    Mista Fanwo ya ce maharan sun tare ayarin motocin gwamnan a inda suka buɗewa motarsa wuta.

    Sai dai a wata sanarwa da gwamnan ya fitar, ya ce labarin ba gaskiya ba ne, kuma ya kamata a yi watsi da ita.

    Ya ce 'yar matsala ce ta taso tsakanin jami’an tsaronsa da sojojin da ke aiki kan babbar hanyar.

    • Ra'ayi Riga Hira da Gwamnan Kogi Yahaya Bello 11/06/2022
    • Kungiyar IS ta yi ikirarin kai hari a wani Coci a Jihar Kogi
  8. Kotun ƙoli za ta saurari ƙarar da Atiku da Obi suka ɗaukaka kan nasarar Tinubu

    OBI,TINUBU da ATIKU

    Asalin hoton, OBI/ATIKU/TINUBU/FACEBOOK

    Kotun Kolin Najeriya za ta saurari ƙarar da Atiku Abubakar da Peter Obi suka ɗaukaka suna ƙalubakantar zaɓen shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2023.

    Kotun ƙolin ita ce dama ta ƙarshe da Atiku da Obi ke da ita kan batun zaben kuma a raran Litinin ɗin nan za ta zauna a Abuja, babban birnin Najeriya.

    A ranar 6 ga watan Satumba ne kotun sauraren ƙararrakin zabe ta yi watsi da ƙarar Atiku da Obi kan nasarar zaben Tinubu.

    Dukkan alƙalai biyar da ke gudanar da shari'ar sun ce ƴan takarar na adawa sun kasa nuna wata shaida cewa zaben bai inganta ba.

    Sun ce Jam'iyun PDP da LP sun kasa tabbatar da cewa an kaɗa kuri'u ba bisa ka'ida ba kuma da batun cewa an muzguna wa masu zaɓe, sun ƙara da cewa ƴan adawan sun kasa gabatar da sahihan shaidu domin tabbatar da karrarkin nasu.

    • Ko za a iya soke sakamakon zaɓen Najeriya?
    • 'Tinubu bai gana da alƙalin-alƙalan Najeriya ba a London'
  9. Barka

    Barkan ku da safiyar Litinin.