Isra'ila ta kai wa sojin Masar hari 'cikin kuskure', ta tsananta hari kan Gaza

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Umar Mikail

  1. MDD ta buƙaci a bar motocin agaji su shiga Gaza yau Lahadi

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Hukumar Agaji ta Majalisar Dinkin Duniya ya ce yana fatan za a ƙyale motocin kayan agaji kashi na biyu shiga Gaza a yau Lahadi.

    Martin Griffiths, ya ce an cimma yarjejeniya da Masar kan ƙyale manyan motocin kayan agaji tsallakawa ta iyakar Rafah.

    A jiya Asabar manyan motoci 20 ɗauke da magunguna da abinci suka wuce ta mashigar.

    Mista Griffiths, ya yi kiran da a sanya man fetur a cikin kayan da za a kai Gaza.

    Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya sun bayyana halin da ake ciki a Gaza a matsayin mai tayar da hankali, sannan sun ci gaba da nanata kiran a tsagaita wuta.

  2. Marabanku

    Masu bin mu a shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da hutun ƙarshen mako.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a sassa daban-daban na duniya.

    Kuna kuma iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta da muhawara.