Ƙarshen rahotonnin ke nan
Mun zo ƙarshen rahotonni a wannan shafi.
Mu haɗu da ku gobe domin samun wasu daga sassan duniya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Abdullahi Bello Diginza and Umar Mikail
Mun zo ƙarshen rahotonni a wannan shafi.
Mu haɗu da ku gobe domin samun wasu daga sassan duniya.
Sojojin Isra'ila sun kashe ƙarin Falasɗinawa biyu a Zawaita, wani gari da ke arewa maso yammacin Nablus a yankin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, kamar yadda ma'aikatar lafiya ta Falasɗinawa ta bayyana.
An kashe Jihad Saleh mai shekara 29 da Mohammed Abu Zer mai 17 ne tare da jikkata wasu biyu a harin da aka kai kan garin.
Zuwa yanzu, Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 93 a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da ta mamaye tun daga ranar 7 ga watan Oktoba, in ji hukumomin yankin.

Asalin hoton, Kogi State Government
Gwamnan jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya, Yahaya Bello, ya tsallake rijiya da baya bayan wasu 'yan bindiga sun buɗe wa ayarin motocinsa wuta a kan hanyarsa ta zuwa Abuja, a cewar gwamnatin jihar.
Wata sanarwa da kafofin yaɗa labarai suka ruwaito a ƙasar ta ce lamarin ya faru a yammacin yau Lahadi yayin da gwamnan ke kan hanyarsa ta zuwa ziyarar aiki daga Lokoja babban birnin jihar.
Sanarwar da kwamishinan yaɗa labarai, Kingsley Fanwo, ya fitar ta ce maharan sun kai masa harin ne sanye da kakin sojojin Najeriya a wurare uku da ke kan hanyar zuwa Abuja.
"An kai harin ne a wurare uku, na ukun shi ne a kusa da Ƙaramar Hukumar Kwali ta Abuja da misalin ƙarfe 4:00 na yamma," in ji sanarwar da Daily Trust ta ruwaito.
A cewar Fanwo, dakarun tsaron da ke tare da gwamnan ne suka daƙile harin.
A ranar 11 ga watan Nuwamba ne za a gudanar da zaɓen gwamna a Kogi, amma Yahaya Bello ba ya cikin 'yan takarar sakamakon shafe shekara takwas da ya yi yana jagorantar jihar a ƙarƙashin jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.
Mun kawo rahoto cewa rundunar sojin Isr'aila ta ce ta kai wa tashar sinitiri ta sojin Masar hari cikin kuskure a kusa da iyakarta da Gaza.
Rundar sojin Masar ta ce wasu daga cikin masu gadinta sun ji "ƙananan raunuka" a harin ba tare da bayar da ƙarin bayani ba.
Sojin Isra'ila sun fitar da sanarwa cewa suna gudanar da bincike kan faruwar lamarin.

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock
"Ba mu taɓa cewa za mu kai hari ta ƙasa ba," kamar yadda mai magana da yawun rundunar sojin Isra'ila, Laftanar Kanar Peter Lerner, ya faɗa wa BBC.
Game da dubban sojojin da ke kusa da Gaza kuwa, Lerner cewa "yanzu horo ake ba su, da kayan aiki, sannan kuma an faɗa musu za a iya tura su yaƙi don kawo ƙarshen Hamas".
A kwanan nan, kakakin rundunar sojan ta IDF ya nanata cewa abin da suka saka a gaba shi ne tsananta hare-hare ta sama kafin "mataki na gaba a yaƙin".
Da alama ita ce alama mafi ƙarara da muka samu zuwa yanzu, inda shugaban IDF Herzi Halevi ya ce: "Za mu shiga Gaza, za mu shiga aiki na musaman."
Masu sharhi na cewa za a iya farawa da ƙananan hare-hare.
Ƙawayen Isra'ilar da wasu 'yan ƙasar na matsa mata don ta jinkirta kai hari ta ƙasa har sai an kuɓutar da mutanen da Hamas ke garkuwa da su, ciki har da 'yan ƙasar waje.
Da alama tana duba hakan, duk da cewa ta zargi Hamas da ƙoƙarin ɓata lokaci don ta sake shiryawa.
Dangin wata matashiya a Birtaniya da ta ɓata tun bayan harin Hamas a garin Kibbutz Be’eri da ke kudancin Isra'ila sun ce an kashe ta.
Iyalin Noiya Sharabi mai shekara 16 sun faɗa wa BBC cewa an gano gawarta.
'Yar uwar Noiya mai shekara 13, Yahel, da kuma mahaifiyarsu Lianne, su ma duk an kashe su a harin na ranar 7 ga watan Oktoba.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce ɗaya daga cikin tankokin yaƙinta ta harba makami cikin kuskure kan wata tashar sintiri ta sojin Masar a kan iyakar Gaza da ke Kerem Shalom.
Kerem Shalom mahaɗar kasuwanci ce da ke rufe a yanzu a kudancin Gaza. Ita ce ta haɗa Masar da Isra'ila da kuma Zirin Gaza.
Rundunar sojin Isra'ilar ta bayyana "rashin jin daɗinta" bayan faruwar lamarin kuma ta ce tana bincike kan faruwarsa.
Za mu kawo ƙarin bayani da zarar mun samu.
Yayin da manyan tankokin mai ke tunkarar kan iyakar Masar da Gaza, Majalisar Dinkin Duniya ta ce har yanzu ba a shigar da mai cikin Gaza ba.
Yayin da tankokin ke ci gaba da jiran izinin shiga Gaza bari mu duba dalilan da ya sa ake buƙatar man a Gaza, da wuraren da ke buƙatarsa.
Rahoton MDD ya ce ya zama wajibi a buƙaci man, kuma rashinsa ka iya kawo rashin tsaftataccen ruwan sha a Gaza, saboda cibiyoyin bayar da ruwan sha da famfuna ba za su yi aiki ba idan babu man fetur.
Haka kuma ana buƙatar man domin kunna injunan bayar da wutar lantarki a asibitocin yankin.
A makon da ya gabata ne ƙungiyar agaji ta Red Cross ta yi gargaɗin cewa asibitocin Gaza na cikin hatsarin komawa 'mutuware' (Dakin ajiye gawarwaki) idan ba su samu wutar lantarki ba.
Cibiyoyin lafiya na cikin mawuyacin halin tun bayan ta Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare kan Gaza, yayin da take yi wa yankin luguden wuta ta sama da makaman atilare.
A wani mataki na mayar da martani kan mayaƙan Hamas waɗanda suka kai hari Isra'ila mako biyu da suka gabata tare da kashe mutum 1,400.
Isra'ila ta ce ba za ta mayar da wutar lantarki zuwa Gaza ba, har sai Hamas ta sako mutanenta fiye da 200 da tayi garkuwa da su a lokacin harin.
To amma a jiya Isra'ila ta amince da barin manyan motoci 20 ɗauke da kayan agaji sun shiga Gaza bayan shafe kwanaki ana tattaunawa.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ayarin motocin kayan agaji 17 ɗauke da abinci da ruwan sha da magunguna, sun isa kan iyakar Rafah, inda ake ci gaba da tantance su, sai dai har yanzu ba su shiga Gaza ba.
Hotunan da ake aikowa daga wurin sun nuna tankokin man fetur a cikin motocin da ke tunkarar mashigar.
To sai dai Majalisar Dinkin Duniya na cewa har yanzu ba a shigar da man fetur Gaza ba.
Jami'an hukumar MDD da ke kula da 'yan gudun hijirar Falasdinawa ta UNRWA, sun ce tsawon mako biyu kenan ba a shigar da fetur zuwa Gaza ba, inda asibitoci da dama ke cikin mawuyacin hali sakamakon rashin man.
"Idan babu man fetur, ba za a samu ruwan sha ba, asibitoci ba za su yi aiki kamar yadda ya kamata ba, gidajen biredi ba za su yi aiki ba, tallafi ba zai isa inda ya kamata ba, raba kayan agaji ga fararen hula ba zai yiwuwa," kamar yadda mai magana da yawun UNRWA ya bayyana.

Rahotonni da ke fitowa daga mashigar Rafah na cewa ayari na biyu na manyan motoci 17 da ke ɗauke da kayan agaji ya isa mashigar Rafah da ke tsakanin Masar da kudancin Zirin Gaza.
Hotunan da aka ɗauka daga kan iyakar sun nuna manyan motocin, da motocin Majalisar Dinkin Duniya sun yi layi, to sai dai ba a tabbatar ko sun sallaka ba zuwa yanzu.

Asalin hoton, Getty Images
A jiya ne rukunin farko na motocin agajin 20 ɗauke da magunguna da abinci da ruwan sha suka isa Gaza ta kan iyakar ta Rafah.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce agajin ya yi kaɗan, ta kuma ce ana buƙatar aƙalla motoci 100 a kowace rana domin raba wa fararen hula a yankin.

Asalin hoton, Reuters
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya gargadin ƙungiyar Hezbollah mai ƙarfin soji a Lebanon, game da ƙaddamar da hari kan Isra'ila a karo na biyu.
"Zai zama babban kuskure da ƙungiyar za ta yi a rayuwarta, idan ta kawo mana hari", kamar yadda Netanyahu ya shaida wa dakarun Isra'ila da ke kusa da kan iyakar Lebanon.
Ya ce hakan zai sa Isra'ila ta ƙaddamar da munanan hare-hare da za su "wargaza" Lebanon.
Isra'ila da Amurka sun gargaɗi ƙasar Iran - da ke goyon bayan Hezbollah, wadda Amurka da Birtaniya da wasu ƙasashen yamma suka ayyana a matsayin 'ƙungiyar ta'adanci' - kan buɗe wani sabon yaƙi a kan iyakar arewacin Isra'ila.
Ibrahim Yusuf Muhammad ne ya gabatar da shirin na wannan makon
Ma'aikatar lafiyar Gaza da ke ƙarƙashin ikon Hamas ta ce aƙalla mutum 4,651 aka kashe a yankin Zirin Gaza tun ranar 7 ga watan Oktoba.
Ta ƙara da cewa kimanin mutum 14,245 ne kuma suka jikkata.
Cikin wata sanarwa da ma'aikatar lafiyar ta fitar, ta ce Falsɗinawa 266 ne aka kashe cikin sa'a 24 da suka wuce, ciki har da ƙananan yara 117.

Asalin hoton, Senator Uba Sani/X
Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta rufe makarantar 'Al-Azhar Academy Zaria' kan zargin mutuwar wani ɗalibi mai suna Marwan Nuhu Sambo, bayan yi masa hukunci sakamakon fashin zuwa makaranta da ya yi.
Cikin wata sanarwa da shugaban sashen lura da makarantu na jihar Dakta Usman Abubakar Zaria, ya fitar, a madadin kwamishinan ilimi na jihar, ya ce an ɗauki matakin ne har zuwa lokacin da za a kammala binciken ainihin abin da ya faru.
Sanarwar ta ce ma'aikatar ilimin jihar a madadin gwamnatin jihar Kaduna ta kafa wani kwamiti na musamman da zai bi diddigi domin gano haƙiƙanin abin da ya faru.
Tuni dai kwamitin ya ziyarci makarantar, da kuma gidan mahaifin ɗalibin domin yi danginsa ta'aziyya tare da ziyartar gidajen wasu abokan ɗalibin, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Haka kuma tawagar ta ziyarci asibitin da ya tabbatar da mutuwar ɗalibin a hukumance, da ofishin 'yan sandan Zariya, inda ake tsare da shugaban makarantar da mataimakinsa, da kuma maƙabartar da aka binne shi.
Sanarwar ta kuma yi kira ga al'umma da su kwantar da hankulansu, tare da bin doka da oda, yayin da ta ce ma'aikatar ilimin jihar na ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, domin tabbatar da gaskiya da adalci.

Asalin hoton, Nig. Army/X
Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kashe dan fashi guda a wani ƙwanton-ɓauna da sojojin suka yi wa tawagar 'yan fashin a yankin Bura na ƙaramar hukumar Ningi da ke jihar Bauchi.
Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar Asabar, mai ɗauke da sa hannun jami'in hulɗa da jama'a na rundunar, Burgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya ce sojojin sun amfani da bayanan sirri da suka samu game da 'yan fashin.
"Sojojin sun yi wa 'yan fashin kwanton-ɓauna tare da buɗe musu wuta, lamarin da ya yi sanadin mutuwar guda daga cikinsu, yayin da sauran suka tsere da raunukan harbin bingiga a jikinsu", kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Sojojin sun kuma ce sun samu nasarar ƙwato bindiga guda ƙirar Ak-47 da alburusai 14, da wayar hannu da kuma guru da layu daga ɗan fashin da suka kashe.
Sanarwar ta kuma ce sojojin na ci gaba da sintiri a yankin domin gano sauran 'yan fashin da suka tsere.
Yankin arewa maso yammacin Najeriya ne dai ya fi fama da matsalar 'yan fashin daji da masu garkuwa da mutane, to sai dai a baya-bayan matsalar ta fara ɓulla a wasu yankunan jihar Bauchi da ke kudu maso gabashin ƙasar.
Hotunan da ke fitowa daga Gaza na nuna irin ɓarnar da rikicin da ake tafka a a yankin ya haifar.
Gine-gine da dama ne suka rushe, inda mutane ke neman 'yan uwansu a karƙashin ɓaraguzan gine-ginen, yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare ta sama.
Akwai dogayen layuka a gidajen biredi yayin da mutane ke jiran sayen biredin sakamakon fargabar ƙarancin abinci da man fetur.
Kalli hotunan baya-bayan nan na wasu wurare a Gaza

Asalin hoton, EPA

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Reuters
Kafofin yaɗa labaran Siriya sun ce Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare kan manyan filayen jiragen samanta biyu.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar ya ce an kai wa filayen jiragen saman Damascus da na Aleppo hare-hare.
Aƙalla fararen hula biyu da ke aiki a filin jirgin saman Damascu aka kashe, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato hukumomin ƙasar na bayyanawa.
Ba jigilar fasinjojin kaɗai filayen jiragen Damascus da na Aleppo ke yi ba, har da zamansu sansanin sojin ƙasar.
Inda wasu rahotonni ke zargin filayen jiragen biyu da zama cibiyar jigilar makaman da Iran ke aike wa Hezbollah, ƙungiyar mayaƙan da ke da ƙarfi a ƙasashen Siriya da Lebanon.

Kungiyar Bayar da Agaji ta Duniya ta Red Cros (ICRC), ta ce yayin da aka shigar da kayan agajin da ake buƙata zuwa Gaza, ankwai buƙatar shigar da likitoci domin rage ƙarancin jami'an lafiya da asibitocin yankin ke fuskanta.
"Babban abin da ake buƙata a yanzu shi ne ci gaba da shigar da kayan agaji zuwa Gaza," kamar yadda Sarah Davies ta ICRC ta shaida wa BBC.
Ta ƙara da cewa ba kayan agajin kaɗai ake buƙata ba, "har da jami'an lafiya da tawagar likitoci waɗanda za su rage wahalhalun da ake fuskanta a asibitocin yankin".
A jiya ne aka buɗe mashigar Rafah da ke kan iyakar Masar da Gaza domin bayar da dama ga manyan motoci 20 maƙare da kayan agaji suka shiga Gaza, ƙarƙashin wata yarjejeniyar da aka cimma da Isra'ila.
To amma Misis Davies ta ce akwai buƙatar ci gaba da shigar da kayan agajin.
"Akwai buƙatar ci gaba da shigar da agajin, mota 20 ba za ta wadaci mutanen da ke buƙatar tallafi ba, haƙiƙa ana cikin wani mawuyacin hali," In ji ta.
"Muna yawan zantawa da tawagarmu da ke wurin, kuma yadda suke bayyana mana yanayin wurin yana da matuƙar tayar da hankali."
Yayin da Irsa'ila ta sha alwashin ci gaba da luguden wuta ta sama a Gaza, dubban mutane ne suka taru a biranen Amurka a jiya Asabar domin nuna goyon bayansu ga Falasɗinawan da rikicin ya rutsa da su.

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images
Hamas ta ce aƙalla mutum 55 ne suka mutu sakamakon hare-hare ta sama da Isra'ila ta ƙaddamar zuwa Gaza cikin dare, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.
Ƙungiyar Ta ce fiye da gidaje 30 ne suka rushe a lokacin hare-haren.
Hakan na zuwa ne bayan da mai magana da yawun sojojin Isra'ila ya ce hare-hare ta sama a Zirin Gaza za su taimaka wa dakarunta da ke ƙasa, wajen tsara ƙaddamar da hare-hare.
Daniel Hagari, ya ce hare-haren za su taimaka wa Isra'ila rage wa dakarunta da ke ƙasa hatsari, wadanda ke jibge a kusa da kan iyaka.
Ya kuma yi kira ga fararen hular Falasdinawa da ke Gaza su ci gaba da ƙaura zuwa kudancin yankin, musamman waɗande ke zaune a birnin Gaza, domin kare lafiyarsu.
Isara'ila ta kuma kai wasu ƙarin munanan hare-hare ta sama zuwa Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da ta mamaye.
Inda hari na baya-bayan nan ya faɗa kan wani masallaci a Jenin, wanda sojoin Isra'ila suka zarga da zama 'cibiyar 'yan ta'adda".