Ma'aikatar lafiya a Burkina Faso ta ayyana cutar zazzaɓin Dengue a matsayin 'annoba', bayan da ɓarkewar cutar a ƙasar ta ti sanadiyyar mutuwar fiye da mutum 200.
Cikin wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar, ta ce a wannan shekara kaɗai an samu mutum 50,478 da ake zargi sun kamu da cutar, tare da mutuwar mutum 214, inda kusan kashi 20 na adadin suka mutu a makon da ya gabata.
Mafiya yawan waɗanda suka mutu a manyan biranen ƙasar suke, Ouagadougou babban birnin ƙasar, da Bobo Dioulasso da ke kudu maso yammacin ƙasar.
Ma'aikatar lafiyar ƙasar na gudanar da gwajin cutar kyauta, inda take kira ga 'yan ƙasar da su yi riƙa yin gwajin cutar har zuwa lokacin da za a kawar da ita.
Zazzaɓin Dengue babbar barazana ce ga duniya, wadda lke kashe mutum 20,000 a kowace shekara.
Tun shekarar 2000, cutar ke ci gaba da ƙaruwa, musamman sakamakon sauyin yanayi, da yawan ƙaurar jama'a daga ƙauyuka zuwa manyan biranen ƙasar.
A farkon wannan watan ne, Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta yi gargaɗin cewa cutar ka iya zama babbar barazana ga yankunan Afirka.
Wannan ko ba ya rasa nasaba da ƙaruwar dumamar yanayi, wanda ke taimaka wa sauro -wanda shi ne ke yaɗa cutar - rayuwa.
An ɗaukar cutar ta hanyar cizon sauron da ke dauke da ƙwayar cutar.
WHO ta ce rabin al'ummar duniya a yanzu na cikin hatsarin kamuwa da zazzaɓin Dengue, inda aka yi kiyasin cewar mutum miliyan 100 zuwa 400 na kamuwa da cutar a kowace shekara.
Mafiya yawan masu ɗauke da cutar ba sa nuna wata alama, amma waɗanda ke nuna alamun, babbar alamar cutar da suke nuna wa ita ce zazzaɓi mai tsanani, da ciwon kai da ƙaiƙayin jiki, da tashin zuciya da ƙananan ƙuraje.