Isra'ila ta amince a kai kayan gaji Gaza amma ta Masar

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Haruna Kakangi and Umar Mikail

  1. Biden ya goyi bayan bayanin Isra'ila kan mummunan harin asibiti a Gaza, Daga Gareth Evans

    Biden and Netanyahu

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Shugaba Joe Biden ya samu tarba daga Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu

    Shugaban Amurka Joe Biden ya ce mummunar fashewar wani abu a asibitin Gaza, ga alama aikin Falasdinawa 'yan ta-da-kayar-baya ne, inda ya goyi bayan bahasin Isra'ila game da aukuwar lamarin, daidai lokacin da yake ziyara a kasar.

    Mista Biden wanda ya sauka a Tel Aviv yau Laraba, ya ce ya yi "matukar takaici da bacin rai" dalilin abin fashewar.

    Rundunar sojojin Isra'ila ta ce lamarin ya faru ne sakamakon wata roka da Falasdinawa suka harba amma ta kuskure.

    Sai dai jami'an Falasdinawa sun ce wani harin Isra'ila ta sama ne ya fada kan asibitin.

    Jami'an lafiya a Gaza sun ce kusan mutum 500 ne suka mutu sanadin abin fashewar, sai dai ba a tabbatar da wani hakikanin adadi na wadanda suka mutu ba.

    Tashin abin fashewar a asibitin Al-Ahli Arab da maryacen Talata, ya dusashe ziyarar Joe Biden mai cike da dumbin kasada, lamarin da ya kara janyo tunzuri da haddasa zanga-zanga a fadin yankin.

    Ya sauka a birnin Tel Aviv ranar Laraba, inda ya samu kyakkyawar tarba daga Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, kafin shugabannin biyu su gudanar da taron manema labarai na hadin gwiwa.

    "Na yi matukar takaici da bacin rai kan fashewar wani abu da aka samu a asibitin Gaza jiya," Mista Biden ya ce.

    "Bisa la'akari da abin da na gani, ga alama kamar daya bangaren ne ya haddasa lamarin, ba ku ba" ya fada wa Shugaba Netanyahu. "Sai dai akwai dumbin mutane a can waje da ba su tabbatar ba don haka akwai bukatar mu shawo kan dumbin abubuwa."

    Shugaban na Amurka ya jaddada goyon bayansa ga Isra'ila kuma ya yi alla-wadai da kungiyar Hamas ta Falasdinawa 'yan ta-da-kayar-baya, wadda ta kaddamar da wani hari da ba a taba ganin irinsa ba kan Isra'ila daga Gaza a ranar 7 ga watan Oktoba.

    Harin dai ya yi sanadin mutuwar mutum 1,400.

    Akalla mutum 3,000 ne aka kashe a hare-haren ramuwar gayya da Isra'ila ta kai a Gaza, a cewar jami'an lafiya na Falasdinawa.

    Shugaba Joe Biden ya shirya tafiya zuwa Jordan daga Isra'ila don ganawa da Sarki Abdullah da jagoran Falasdinawa Shugaba Mahmoud Abbas da kuma Shugaban Masar Abdul Fattah al-Sisi, amma an soke wannan bangare na ziyarar bayan tashin abin fashewa a asibiti ranar Talata.

    Jordan ta soke ganawar kuma ta yi alla-wadai da abin da ta kira "wani babban bala'i kuma mummunan laifin yaki". Fadar White House, a lokaci guda, ta ce an cimma shawarar ne "bisa amincewar juna" kuma Shugaba Biden zai kira Mahmoud Abbas da Shugaba Sisi a lokacin da yake komawa gida Amurka.

    Ana sa ran Shugaban Amurka zai gana da majalisar tsare-tsaren yaki ta Isra'ila nan gaba a ranar Laraba.

    • Isra'ila da Falasɗinawa na zargin juna da kai hari kan asibitin Gaza
    • Rikicin Isra'ila da Gaza: Mene ne asalin sa?

    Zai yi "tsauraran tambayoyi" don samun kyakkyawar fahimta kan manufofi da bukatun yakin Isra'ila a Gaza, kamar yadda mai magana da yawun Majalisar Tsaron Kasa ta Amurka, John Kirby ya ce.

    "Zai yi tambayoyi masu tsauri amma zai yi tambayoyin ne a matsayinsa na aboki," Kirby ya fada wa manema labarai, ya kara da cewa Amurka za ta jaddada bukatar kai kayan agajin jin kai zuwa Gaza, kuma akwai wajabcin a kaucewa kai hari kan fararen hula.

    Mista Biden ya kuma gana da ma'aikatan ba da agajin gaggawa wadanda suka kai dauki bayan harin Hamas da kuma wasu da suka rasa makusantansu ko kuma wadanda ake garkuwa da danginsu, a cewar jami'ai.

    Isra'ila ta nemi taimakon kayan aikin sojoji cikin gaggawa na dala biliyan goma daga Amurka bayan harin da Hamas ta kai, CBS News, abokiyar kawancen BBC a Amurka ta ruwaito daga abin da ta kira wasu majiyoyi masu alaka da rokon.

    Hukumomi a Gaza, wanda Hamas ke karkashin ikon Hamas sun ce mutum 500 ne suka mutu a fashewar da aka samu a asibiti, wanda wani likita ya kira "kisan kiyashi".

  2. Majalisar dattawa ta tabbatar da Olukoyede a matsayin shugaban EFCC

    ...

    Asalin hoton, EFCC/Facebook

    Majalisar Dattawa ta tabbatar da Ola Olukoyede a matsayin Shugaban Hukumar Yaki da cin hanci da rashawa (EFCC).

    Hakazalika majalisar ta tabbatar da nadin Muhammad Hammajoda a matsayin sakataren hukumar.

    Tabbatar da mutanen biyu ya biyo bayan tantance su ne da babban zauren majalisar ya yi a yau ranar Laraba kimanin mako guda bayan da shugaba Bola Tinubu ya nada su.

  3. Kenya na neman mutum 35 ruwa a jallo game da hare-haren 'yan bindiga

    ...

    Asalin hoton, Ministry of Interior/X

    Bayanan hoto, ...

    Gwamnatin Kenya ta fitar da sunaye da hotunan wasu mutum 35 da ake zargi da hannu wajen kai hare-haren ‘yan bindiga a jihar Lamu da ke gaɓar tekun ƙasar.

    Daga cikinsu akwai 'yan Tanzaniya da Somaliya da Bajamushe da ɗan Birtaniya da kuma ɗan kasar Bangaladash, wanda akasarin kuma ƴan Kenya ne.

    Waɗanda ake zargin dai suna da alaƙa da dasa bama-bamai a kan tituna da kuma kashe fararen hula a kan hanyar Lamu zuwa Witu zuwa Garsen.

    Ana kuma alaƙanta su da harin da aka kai sansanin sojin Amurka a Manda Bay, a Lamu, a shekarar 2020.

    Ma'aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar ta ce waɗanda ake zargi na cikin ƙungiyar ta'addanci ta al-Shabab da ke da alhakin shiryawa da kuma kitsa munanan hare-hare a gundumar Lamu da kuma babban yankin Boni Enclave.

    Hukumomin ƙasar sun ce za a bayar da " lada" ga duk wanda ya samu bayanai dangane da inda waɗanda ake zargin suke.

    Al-Shabab ta zafafa kai hare-hare a yankunan arewa maso gabashin Kenya da kuma bakin teku a cikin 'yan watannin nan.

    Kungiyar da ke da alaƙa da al-Qaeda na fuskantar wani gagarumin farmakin soji a Somaliya da ke neman fatattakar mayaƙan masu iƙirarin jihadi.

    • ' Muna fama da karuwar hare-haren 'yan bindiga a yankinmu'
    • 'Yan bindiga sun kai hari a Nairobi
  4. Majalisar dattawa na tantance shugaban EFCC

    ...

    Asalin hoton, Ajuri Ngelale/Facebook

    Majalisar dattawa na tantance waɗanda shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya naɗa a matsayin Shugaban Hukumar Yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Ola Olukoyede; da Sakataren Hukumar, Muhammad Hammajoda.

    A ranar 12 ga watan Oktoban 2023 ne shugaban ƙasar ya naɗa Ola Olukoyede a matsayin shugaban hukumar kuma Muhammad Hammajoda a matsayin sakataren hukumar har sai majalisar dattawa ta tabbatar da su.

    A ranar 14 ga watan Yunin 2023, Tinubu ya dakatar da Abdulrasheed Bawa a matsayin shugaban hukumar don ba da damar gudanar da bincike mai kyau a kan yadda ya ke aiki a lokacin da yake shugabancin hukumar.

    • Ya kamata a binciki shugaban EFCC — Matawalle
    • Ministocin a Najeriya: Su wane ne ƙusoshin gwamnatin Tinubu?
  5. Faransa ta shawarci ‘yan kasarta kada su yi tafiya zuwa Labanon

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Faransa ta shawarci ‘yan kasarta da kada su yi tafiya zuwa kasar Labanon, ganin yadda ake fama da tashe-tashen hankula a yankin, musamman ma kan iyakar kudancin kasar da Isra’ila.

    Tun da farko, Amurka ta shawarci ƴan ƙasarta da ke Lebanon da su fice daga kasar yayin da akwai sauran zaɓuɓɓukan kasuwanci.

    Har ila yau, Ofishin Harkokin Wajen Birtaniya yana ba da shawara game da duk wani balaguron tafiya zuwa Lebanon.

    "Ya kamata 'yan Burtaniya da ke Lebanon su yi la'akari da ko suna bukatar ci gaba da zama a Lebanon, idan kuma ba haka ba, su fice ta hanyar kasuwanci yayin da suke nan," in ji sanarwar a ranar Talata.

    • Kasashen Canada da Spain da Jamus da kuma Ostiraliya su ma sun bayar da gargaɗi.
    • Mummunan harin ba-zata da Hamas ta kaddamar a kan Isra'ila
  6. China ta yi Allah-wadai da hari kan asibitin Gaza amma ba ta ɗora alhaki ba

    Ma'aikatar harkokin wajen kasar China ta ce ta yi Allah-wadai da harin da aka kai kan asibitin Gaza ko da yake ba ta fito fili ta zargi Isra'ila, ko kuma 'yan gwagwarmayar Falasɗinawa ba.

    Kakakin ya ce, China ta yi kakkausar suka kan harin da aka kai a asibitin Gaza, wanda ya yi sanadin jikkatar mutane masu yawa.

    “Muna jimamin waɗanda suka mutu sakamakon harin, kuma muna jajantawa waɗanda suka jikkata.

    China ta yi kira da a tsagaita buɗe wuta cikin gaggawa, da dakatar da tashin hankali, da duk wani ƙoƙari na kare fararen hula, da kaucewa wani bala'in jin ƙai mafi muni."

  7. Labarai da dumi-dumi, Mutum 471 ne suka mutu a hari kan asibitin Gaza - ma'aikatar lafiyar yankin

    Ma'aikatar lafiya ta Falasɗinawa ta ce mutum 471 ne suka mutu a harin da aka kai a asibitin Gaza ranar Talata, yayin da mutum 314 suka jikkata.

    Za mu kawo muku karin bayani nan ba da jimawa ba.

    • Babban asibitin Gaza na cikin mayuwacin hali sakamakon katsewar lantarki
    • Rayuwa a Gaza: 'Babu wurin fakewa a ruwan makamai masu linzami'
  8. Yaƙin Isra'ila da Gaza: masu zanga-zanga sun yi arangama da jami'an tsaro a Ramallah

    An harba hayaƙi mai sa hawaye kan masu zanga-zanga a birnin Ramallah da ke gaɓar yamma da kogin Jordan da aka mamaye, bayan mummunan harin makamai da aka yi a wani asibiti a Gaza ya yi da ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane.

    Masu zanga-zangar adawa da mulkin gwamnatin Falasdinawa karkashin jagorancin Fatah sun yi arangama da jami'an tsaron Falasdinawa.

    Kamfanin dillancin labaran AFP ya ce mutanen da ke zanga-zangar sun yi kira ga shugaban Falasɗinawa, Mahmoud Abbas da ya yi murabus saboda martanin da ya mayar kan rikicin da ke tsakanin Isra'ila da 'yan adawar siyasarsa na Hamas a Zirin Gaza.

  9. Ƙungiyar ƙwadago ta ba gwamnoni wa'adin mako biyu kan mafi ƙarancin albashi

    ...

    Asalin hoton, Nigeria Labour Congress HQ/Facebook

    Ƙungiyar kwadago ta bai wa gwamnonin jihohi wa’adin mako biyu su fara tattaunawa kan batun biyan ƙarancin albashin N35,000 ga ma’aikata a jihohinsu.

    Jaridar Punch ta ruwaito cewa wannan wa’adin ya yi daidai da sharuddan yarjejeniyar fahimtar juna da gwamnatin tarayya, da ƙungiyoyin kwadago ta Najeriya suka sanya wa hannu.

    Sassan Jihohin ƙungiyoyin ƙwadagon sun ba da wa'adin makonni biyu inda suka tuntubi gwamnonin da su hanzarta aiwatar da shirin biyan ƙarancin albashin.

    A wani labarin kuma, shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ƙaddamar da shirin bada tallafin kudi naira tiriliyan 1 da nufin taimakawa gidaje miliyan 15 domin rage raɗaɗin tattalin arzikin da ake samu na cire tallafin man fetur.

    A ƙarkashin wannan shirin, kowane magidanci zai karbi Naira 25,000 na tsawon watanni uku, wanda ya kai kusan naira tiriliyan 1.13.

    Ministar ma'aikatar jin ƙai, Dr. Betta Edu, ta bayyana cewa kimanin ‘yan Najeriya miliyan 61 ne za su ci gajiyar wannan tallafin kudi.

    A baya dai shugabannin ƙungiyar ƙwadago sun cimma matsaya da gwamnatin tarayya a ranar 1 ga watan Oktoba, inda ta tanadi cewa duk ma’aikatan tarayya za su karbi ƙarancin albashin naira 35,000 daga watan Satumba, har sai an kammala sabon mafi karancin albashi na kasa.

    • Abubuwan da aka cimma a tattaunawar ‘yan kwadago da gwamnatin Najeriya
    • Ko yaya yajin aikin ƙungiyar ƙwadago ya kasance a jihohin Najeriya?
  10. An kashe ƴan yawon bude ido a wani hari a Uganda

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƴan sandan Uganda na farautar ƙungiyar mayaƙan Allied Defence Force (ADF), waɗanda ake kyautata zaton sun kashe 'yan yawon bude ido biyu da mai masu jagora a dajin Sarauniya Elizabeth.

    Waɗanda harin ya rutsa da su sun hada da wani dan kasar Birtaniya, da ɗan Afirka ta Kudu, da kuma wani jagora ɗan kasar Uganda. An ƙona motarsu ta safari.

    Mayakan na ADF dai suna kan iyaka ne a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, kusa da tafkin Edward a yammacin kasar.

    Hukumomin Uganda na ci gaba da zaƙulo waɗanda ake zargin 'yan tawayen ADF ne, kuma sun yi ta'aziyya ga iyalan waɗanda abin ya shafa, rundunar ‘yan sandan ta ce a cikin wata sanarwa.

    Kungiyar ADF ce ke da alhakin kai munanan hare-hare a baya a Uganda, ciki har da harin da aka kai kan ɗalibai a watan Yuni.

    Harin na baya-bayan nan ya zo ne kwanaki bayan da shugaba Yoweri Museveni ya ce sun dakile wani hari da kungiyar ta kai majami'u ranar Lahadi.

    A baya dai ya ce sojojin Uganda sun kai hare-hare ta sama a kan wasu wurare hudu na ƙungiyar ADF a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.

    • Iyayen da suka kai ƴaƴansu yawon ganin duniya kafin su makance
    • Hare-haren Uganda: Sirrin ƙungiyar ƴan tawayen ADF mai alaƙa da IS
  11. Shugaba Biden ya gana da Netanyahu

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaba Amurka, Joe Biden a lokacin da yake ganawa da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya danganta harin makamai da aka kai a wani asibitin gaza ranar Talata ga Falasɗinawa, ba Isra'ila ba, bisa bayanan da ya samu in da Biden ya ce a cikin kalamansa - 'ɗayan ɓangaren ne'.

    Wannan lamari dai ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin jama'a a yankin tare da soke taron da aka shirya yi tsakanin shugaba Biden da shugabannin ƙasashen Larabawa.

    Shugaban ya jajanta wa Isra'ila game da harin da Hamas ta kai amma ya jaddada mahimmancin rage asarar fararen hula.

    • Isra'ila da Falasɗinawa na zargin juna da kai hari kan asibitin Gaza
    • Shin kun san asalin rikicin Isra'ila da Falasɗinu?
  12. Mata a Nijar na zaman dirshen a gaban ofishin ECOWAS

    ...

    Mata a jamhuriyar Nijar sun yi zaman dirshen a gaban ofishin kungiyar ECOWAS ko CEDEAO domin tillasta wa kungiyar ta cire takunkumin da ta kakaba wa kasar tun bayan juyin milkin 26 ga watan Yulin wannan shekara.

    Tattalin arziƙin ƙasar da rayuwar al'umma sun shiga wani mawuyacin halin tun bayan da ƙungiyar ta ECOWAS ta dauki wasu matakai a kan Nijar bayan hamɓarar da shugaban ƙasar Mohammed Bazoum.

    Farashin kayan abinci da na masarufi ya yi tashin gwaron zabi.

    Tun farko dai ECOWAS ta bai wa jagororin mulkin soji na ƙasar wa'adin mayar da mulki ga fararen hula sai dai har yanzu abin ya ci tura.

    ...
    ...
    ...
    • 'Mutane sun wahala a Nijar kuma suna neman wanda za su ɗora wa laifi'
    • Ƙasashen da Ecowas ta yi nasarar mai da mulkin dimokraɗiyya
  13. Abin da ya sa na fice daga majalisa ana tsaka da muhawara - Ndume

  14. Adadin Falasdinawan da suka mutu ya haura 3,300 - minista

    Ministan lafiya na Falasdinawa Mai al-Kaila ya ce adadin da aka kashe a Gaza tun bayan da Isra'ila ta fara kai hare-hare ta sama kwanaki 11 da suka gabata ya kai 3,300.

    Ya ƙara da cewa an kuma jikkata wasu mutum 13,000.

    Aƙalla ‘yan Isra’ila 1,300 ne aka kashe a hare-haren Hamas da suka fara sabon rikici, inda ake tunanin an yi garkuwa da aƙalla mutane 199.

    • Kalaman ƙarshe na yaron da aka caka wa wuƙa saboda zargin ƙin jinin Musulmai
    • Abin da ke faruwa a Gaza daga bakin mazauna yankin
  15. Babban birnin Guinea-Bissau a cikin duhu bayan katsewar wutar lantarki

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, ...

    Bissau babban birnin kasar Guinea Bissau na cikin duhu sakamakon rashin biyan kudin wutar lantarki.

    Kamfanin samar da wutar lantarki na Turkiyya Karpowership ya katse wutar lantarkin ne saboda gwamnatin Afirka ta Yamma na bin su dala miliyan 17.

    Ministan tattalin arziki Suleimane Seidi ya yi alkawarin warware mafi yawan basukan nan da makonni biyu.

    Karpowership, babban mai gudanar da ayyukan samar da wutar lantarki, yana da kwangilar shekaru biyar don samar da kusan dukkanin wutar lantarkin Guinea-Bissau.

    A watan da ya gabata, wannan kamfani na Turkiyya ya dakatar da wutar lantarki a babban birnin kasar Saliyo saboda wasu basussuka da ba a biya ba.

    • Najeriya: Yadda rashin lantarki ke kassara harkokin kasuwanci a fadin ƙasar
    • Nijar ta shiga matsalar lantarki bayan katsewa daga Najeriya
  16. Na yi takaicin harin da aka kai kan asibitin Gaza - Biden

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka, Joe Biden ya ce ya yi matuƙar bacin rai da baƙin ciki da harin da aka yi a asibitin Al Ahli Arab da ke Gaza, da kuma mummunan asarar rayuka da aka yi.

    Shgaban ya ce da jin wannan labari, ya yi magana da Sarki Abdullah na biyu na Jordan, da Firayim Minista Netanyahu na Isra'ila kuma ya ce ya umarci jami'an tsaron kasar da su ci gaba da tattara bayanai kan hakikanin abin da ya faru.

    Ya ƙara da cewa Amurka tana tsaye ba tare da shakka ba don kare rayuwar farar hula a lokacin rikici.

    Biden ya kuma ce Amurka na jimamin marasa lafiya da ma'aikatan kiwon lafiya da sauran waɗanda ba su ji ba ba su gani ba da aka kashe ko suka jikkata a wannan bala'in.

    • Musulmai da Yahudawan Birtaniya na fargabar alaƙarsu saboda yaƙin Gaza
    • Ko samame ta ƙasa da Isra’ila ke shirin kai wa Gaza zai yi nasara?
  17. Yara biyar sun mutu sakamakon ruwan sama mai ƙarfi a Zimbabwe

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Ƙananan yara biyar da suka hada da ‘yan’uwa hudu sun mutu a ƙasar Zimbabwe sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da ambaliyar ruwa da ta lalata gidaje da muhimman ababen more rayuwa, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito.

    Hudu daga cikinsu sun mutu ne bayan da wata tsawa ta faɗo kansu a daren ranar Litinin a lokacin da suke bacci da mahaifiyarsu a cikin wata bukka a lardin Manicaland na gabashin kasar. Mahaifiyar ba ta ji rauni ba.

    Dayan yaron ya mutu ne da rauni da ya samu a kai sakamakon ambaliyar ruwa da ta lalata gidaje sama da 17 a wani kauye da ke Gokwe North, a tsakiyar lardin Midlands.

    An ce an kai wasu yara biyu daga kauye daya zuwa asibiti.

    Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake tafka ruwan sama mai karfi tare da tsawa, da iska mai karfi da ƙanƙara a wurare tsakanin Litinin da Talata, a cewar hukumar hasashen yanayi.

    • Ambaliyar Libya: Gawawwakin da ba a iya gane su ba saboda bala'i
    • 'Za a fuskanci babban bala'i idan ba a kawo karshen dauke wuta ba'
  18. Shugaban Amurka Joe Biden ya isa Isra'ila

    Shugaban Amurka, Joe Biden tare da Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Shugaban Amurka, Joe Biden tare da Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu

    Shugaban Amurka Joe Biden ya isa Isra'ila a daidai lokacin da ƙasashen duniya ke nuna ɓacin ransu kan kisan daruruwan mutane a wani mummunan harin makami da aka kai a wani asibiti da ke Gaza.

    Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya jagoranci yin Allah wadai da harin da ya shafi mata da ƙananan yara.

    Hamas ta ɗora alhakin harin da ya kashe mutane da dama kan Isra'ila amma Isra'ila ta ce makamin rokan da aka harba na wata ƙungiyar masu iƙirarin jihadi ta Falasɗinawa ne.

    Akwai kiraye-kirayen da shugabannin kasashen duniya suka yi na a gudanar da bincike na gaggawa tare da yin cikakken bincike kan mutanen da suka mutu.

    Wannan lamarin dai ya kawo cikas ga ƙoƙarin shugaba Biden na nuna goyon baya ga Israila bayan harin da Hamas ta kai a cikin Isra'ila.

    Tuni dai aka soke taron da aka shirya yi tsakanin Biden da shugabannin ƙasashen Larabawa a kasar Jordan.

    • Yadda kan ƙasashen Afirka ya rabu game da rikicin Isra'ila da Gaza
    • Sahihan bidiyon harin da Hamas ta ƙaddamar kan Isra'ila
  19. An soke taron Biden da shugabannin Larabawa bayan harin asibitin Gaza

    ...

    Asalin hoton, EPA

    Harin da aka kai a wani asibitin Gaza ya janyo ce-ce-ku-ce a duniya inda aka soke wani muhimmin taron da shugaban Amurka Joe Biden zai ya shirya yi da shugabannin Larabawa ciki har da Mahmud Abbas na Falasɗinawa.

    An shirya Biden ya nufi Jordan ne bayan ya gana da firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu inda zai gana da Sarki Abdallah na Jordan da Shugaba Abdul Fattah al-Sisi na Masar da Abbas.

    Da yawa daga cikin shugabannin kasashen Larabawa na zargin Isra'ila da aikata laifin yaki.

    Shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas, ya bayyana hakan a matsayin kisan kiyashi, yana mai cewa Isra’ila ta ketare iyaka.

    • Amurka ta fara matsar da jiragen yaki kusa da Isra'ila bayan harin Hamas
    • Yadda kan ƙasashen Afirka ya rabu game da rikicin Isra'ila da Gaza
  20. Hotunan yadda harin da aka kai ya lalata asibitin Gaza

    Ɗaruruwan Falasɗinawa ne ake fargabar sun mutu bayan da wata fashewa da aka samu a wani asibiti a Gaza a daren Talata.

    Hamas ta dora alhakin harin kan Isra'ila amma Isra'ila ta ce harin rokokin daga kungiyar masu iƙirarin jihadi ta Falasdinawa ne.

    Ga hotunan irin ɓarnar da harin ya yi a wajen asibitin na Al Ahli.

    ...

    Asalin hoton, EPA

    ...

    Asalin hoton, EPA

    ...

    Asalin hoton, EPA

    ...

    Asalin hoton, EPA

    • Bayani kan hanya ɗaya tilo da Falasɗinawa za su iya fita daga Gaza
    • Ana kwashe 'yan Isra'ila a ƙauyukan iyaka da Lebanon saboda barazanar hari