Ana kiran kai wa Gaza kayan agaji yayin da Isra'ila ke ci gaba da luguden wuta

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Umar Mikail

  1. Biden ya tattauna da Netanyahu da Mahmoud Abbas

    Biden Netanyahu

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Joe Biden ya tattauna ta wayar tarho tare da firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, da kuma shugaban Falasdinawa, Mahmoud Abbas.

    Mista Biden ya bukaci Isra'ila da ta samar da kariya ga Falasdinawa fararen hula.

    shugaban na Amurka ya kuma bukaci Mista Abbas da ya fito ya yi Alla-wadai da abin da Hamas ke yi.

    Nan gaba a yau ne kuma sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, zai kai ziyara Masar, a wani ɓangare na rangadin da yake yi a ƙasashen Larabawa da nufin kare bazuwar rikicin.

    Mista Blinken ya mayar da hankali sosai da sosai a kan halin da jama'a ke ciki a Gaza a yayin da ya nuna damuwa a kan yadda rikicin ya rincaɓe.

  2. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa Kai-tsaye, barkanmu da hutun ƙashen mako.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya, musamman kan rikicin Isra'ila da Falasɗinu.

    Kuna iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta da muhawara.

    Ku biyo mu ...