Mu kwana lafiya
Ƙarshen rahotannin ke nan a wannan shafi.
Mu haɗu da ku gobe da safe don kawo muku wasu sababbi da suka shafi rayuwarku.
Umar Mikail ke muku fatan alheri.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Abdullahi Bello Diginza and Umar Mikail
Ƙarshen rahotannin ke nan a wannan shafi.
Mu haɗu da ku gobe da safe don kawo muku wasu sababbi da suka shafi rayuwarku.
Umar Mikail ke muku fatan alheri.
'Yan gwagwarmayar Faladinawa na Hamas da Islamic Jihad kan yi amfani da hanyoyin ƙarƙashin ƙasa wajen ɓuya da kuma kai wa Isra'ila hare-hare.
Yanzu haka, ana tsammanin ƙungiyar ta Hamas na riƙe da 'yan Isra'ila kusan 150 da ta kama a harin da ta kai a cikin irin waɗannan gidajen ƙarƙashin ƙasa.
Isra'ila ta ci alwashin sai ta kawar da Hamas daga ban-ƙasa, amma hakan ba zai yiwu ba har sai ta gano tare da lalata hanyoyin da aka ce tsayinsu yakan kai kilomita 500 kuma har zuwa cikin Isra'ila daga Gaza.
Kalli bidiyon sama ku sha labari.

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock
Rundunar sojin Isra'ila ta baje wasu daga cikin makaman da ta gano na mayaƙan Hamas da suka kai hare-hare a makon da ya gabata.
Ta ce holen makaman da ta yi a wani sansanin soja da ke kudancin ƙasar kashi 20 ne cikin 100 kacal na makaman da maharan suka yi amfani da su, lokacin da mutum kusan 1,000 suka tsallaka cikin ƙasar daga Gaza.
Wani sojan Isra'ila da ya rufe fuskarsa ya ce alamu sun nuna akasarin makaman an ƙera su ne a cikin Gaza, yana mai cewa babu wata hujja da ke nuna cewa Iran ce ta ba su makaman.
Sojan wanda ya ce sunansa Manjo G, ya ce akasarin makaman na Hamas "ƙananana ne".
Akwai 'yan kaɗan daga cikin makaman da aka ƙera tun lokacin Tarayyar Soviet waɗanda ake harbawa a kafaɗa, da ma rokokin harbawa a kafaɗa da ke da lambar gamayyar tsaro ta Nato a jikinsu.

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock
Dakarun Isra'ila da Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna sun kashe Falasɗinawa 56 a yankin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan tun bayan fara yaƙi tsakanin Hamas da ƙasar makon da ya gabata.
Ma'aikatar Lafiya ta Gaza ce ta ba da alƙaluman yayin da dakaru ke ci gaba da yi wa Zirin Gaza ruwan wuta.
Wani bidiyo ƙungiyar kare haƙƙi ta B'Tselem a Isra'ila ta wallafa ya nuna yadda wani ɗan kama-wuri-zauna ya harbe wani Bafalasɗine yayin da wani sojan ƙasar yake kallo.
Nebal Farukh na ƙungiyar agaji ta Red Crescent ya faɗa wa BBC cewa ƙungiyar tasu ta tattara rahoton Falasɗinawa fiye da 1,250 da aka raunata a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan cikin mako ɗaya.
Haka nan, an ci zarafin ma'aikatanta 34, ciki har da hanawa ko kuma jinkirta likitocinta wajen kula da mutanen da aka raunata yayin zanga-zangar goyon bayan Hamas.
Zuwa yanzu, hare-haren Isra'ila a kan Zirin Gaza ya kashe aƙalla mutum 2,450 tare da raunata 9,200, in ji Ma'aikatar Lafiya ta Falasɗinu.

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock
Tun a safiyar yau Lahadi Fafaroma Francis, shugaban jagoran ɗariƙar Katolika na duniya, ya yi kira ga Isra'ila ta bari a kai kayan agaji birnin Gaza.
"Wajibi ne a mutunta dokokin bayar da agaji, musamman a Gaza,inda ya zama dole a tabbatar da tsaron masu kai agaji don isar da kaya masu muhimmanci ga mazauna birnin," a cewar Fafaroman bayan kammala ibadar Angelus.
Ya ƙara da cewa: "Ina mai ba da shawara ƙarara cewa bai kamata a kai wa yara da mata da tsofaffi da sauran fararen hula hari ba a wannan rikici."

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock
Rundunar sojan Isra'ila ta ce jiragenta na helikwafta na kai hare-hare kan kayayyakin soja a Lebanon, yayin da take ci gaba da fafatawa da 'yan gwagwarmayar Lebanon.
Haka nan, an ce dakarun nata na fafatawa da wasu 'yan bindiga a kan iyakarta.
An kwashe kwana biyar ana musayar wuta tsakanin dakarun Isra'ila da na Hezbollah a Lebanon.
Wani wakilin BBC a kan iyakar ya ce makaman da aka harba ranar Asabar su ne mafiya yawa tun daga fara yaƙin.
A ranar Asabar, sojin Isra'ilar suka kashe mayaƙan Hamas uku da suka yi yunƙurin tsallakawa ƙasar daga Lebanon.
'Yan mintuna da suka wuce, gwamnatin Isra'ila ta fitar da bayanin cewa 'yan ƙasarta da suka mutu sakamakon harin da Hamas ta kai sun zama 1,400.
Ita kuma ma'aikatar lafiya ta birnin Gaza cewa ta yi waɗanda Isra'ila ta kashe a hare-haren ramuwar gayya sun kai 2,450.
Jiragen sama na Isra'ilar sun fara luguden wuta a kan Gaza ne jim kaɗan bayan hare-haren da Hamas ɗin ta kai ranar Asabar, 7 ga watan Oktoba, inda mayaƙanta suka tsallaka katangar tsaro tsakanin Gaza da ƙasar.

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock
Jagoran siyasar Hamas, Isma'il Haniyeh, ya tattauna da Ministan Harkokin Wajen Iran Hossein Amirabdollahian a Ƙatar, inda suka tattauna a kan mummunan harin da Hamas ta kai Isra'ila.
Cikin wani bidiyo da kafar yaɗa labaran Iran ta wallafa, an nuna mutanen biyu na rungume juna tare da sumbata a yayin da suke gaisawa.
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana harin a matsayin "babbar nasara a tarihi da za ta kawo koma-baya a mamayar da Isra'ila ta yi wa yankin Falasdinawa".
Cikin wata sanarwa, Hamas ta ce dukkan bangarorin biyu sun amince da ci gaba da haɗa kai domin cimma muradin ƙungiyar.

Asalin hoton, Reuters
Sojojin Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare ta sama zuwa arewacin Gaza, gabanin samamen soji ta ƙasa da take shirin ƙaddamarwa.
Ana sa ran Israila ta ƙaddamar da hare-hare da sama da ruwa da ta ƙasa a wani mataki na ramuwar gayya kan harin da ƙungiyar Hamas ta kai isra'ila a karshen makon da ya gabata, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum 1,300.
Fiye da Falasɗinawa 2,000 ne aka kashe sakamko hare-hare ta sama da isara'ila ta ƙaddamar cikin makon da ya gabata.

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon firaministan Isra'ila Ehud Barak ya ce a matakin da ake ciki yanzu ƙasar ba ta da sauran zaɓi da ya wuce matakin da gwamnatin Benjamin Netanyahu ke ɗauka a Gaza.
Yayin da yake zantawa da BBC mista Barak ya ce manufar wannan mataki shi ne tabbatar da murƙushe ƙarfin sojin ƙungiyar Hamas, tare da miƙa yankin Zirin Gaza hannun hukumomin Falasɗinu ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar Fatah.
Ya ƙara da cewa Isra'ila na mutunta dokokin ƙasa-da-ƙasa, amma dole ta kwace kan iyakarta daga hannun ƙungiyar Hamas da ya kira mai 'ayyuka irin na Al=Qaeda".
Shin kun san cewa tumatir, da ake girki da shi yau da kullum na iya rage wa ɗan'adam hatsarin kamuwa da hawan jini?
Saurara ƙarin bayani daga bakin Dakta Salihu Ibrahim Kwaifa

Asalin hoton, NAF
Rundunar sojin saman Najeriya ta ce ta kashe 'an bindiga masu yawa a yayin wasu hare-hare ta sama da ta ƙaddamar kan maɓoyar 'yan ta'adda a wasu sassan ƙasar.
Cikin wata sanarwar da rundunar ta fitar ranar Lahadi, mai ɗauke da sa hannun daraktan hulɗa da jama'a na rundunar, Air Commodore Edward Gabkwet, ta ce dakarun sojin ƙarƙashin haɗin gwiwar rundunonin Hadin Kai da ta Hadarin Daji sun kai hare-hare kan 'yan ta'adda a Bukar Meram, kusa da Tafkin Chadi a jihar Borno da kuma yankin Sangeko a jihar Zamfara.
Air Commodore Edward Gabkwet, ya ce rundunar ta ƙaddamar da hare-haren ne bayan da ta samu bayanai game da sauya matsuguni da 'yan bindigar ke yi.
Harin farko an kai shi a lokacin da 'yan bindigar ke ƙaura daga Suwa zuwa yankin Bukar Meram, domin shirya kai hare-hare kan fararen hula da sojoji, kamar yadda sanarawar ta bayyana.
Sanarwar ta ƙara da cewa harin ya samu nasarar halaka 'yan ta'addan masu yawan gaske tare da lalata babura fiye da 40 da motocin da ke dakon makamai ga 'yan bindigar.
Haka kuma Gabkwet ya ce sojojin ƙarƙashin rundunar Hadarin Daji, sun ƙaddamar da makamancin irin wannan hari ranar 11 ga watan Oktaba a yankin Sangeko da ke ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara.
Ya ƙara da cewa dakarun sun kai hari kan 'yan ta'addan waɗanda ke tafiya cikin jerin gwanon babura kimanin 70 a kan hanya daga Kabaro zuwa Sangeko, inda aka kashe da dama da jikkata wasu,tare da lalata babura masu yawa.
Editan BBC Jeremy Bowen na kudancin Isra'ila kusa da kan iyakar Gaza, inda ya ɗauki hotunan sojojin Isra'ila tare da tankokin yaƙinsu, yayin da suke wucewa ta kusa da Nahal Oz kibbutz.



Ƙungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci da tabbatar da dimokradiyya a Najeriya ta buƙaci shugabannin majalisun dokokin ƙasar biyu su yi watsi da kudirin lura da shafukan sada zumunta a ƙasar.
Cikin wata sanarwar da ƙungiyar ta fitar , a ce kudurin idan ya zaman doka, zai taƙaita 'yancin faɗar albarkacin baki da ɓoye sirri.
SERAP ta buƙaci gwamnatin ƙasar ƙarƙashin jagorancin shugaba Tinubu ta daina yunƙurin tilasta wa manyan kamfanonin fasaha na Google da Youtube taƙaita wannan 'yanci na ɗan'adam.
Rahotonni sun ambato babban mataimakin daraktan ƙungiyar, Kolawole Oluwadare, na cewa ƙudurin zai mayar da ''halastaccen 'yancin ɗan'adam zuwa laifi"
Ya ƙara da cewa "duk wani yunƙuri na sanya idanu domin lura da shafukan sada zumunta, za mu ɗauke shi a matsayin abin da ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Najeriya da dokokin 'yancin ɗan'adam na ƙasa-da-ƙasa."
An dai daɗe ana ta kiraye-kiraye ga hukumomin ƙasar da su yi wata doka da za ta riƙa lura da abubuwan da ake wallafawa a shafukan sada zumunta, sakamakon yawaitar yaduwar labaran ƙarya da na cin zarafi a shafukan.
Shirin Amsoshin Takardunku na wannan makon - wanda Badariyya Tijjani Kalarawi ta gabatar - ya yi duba kan asalin rikicin da ke tsakanin Isra'ila da Falasɗinawa.

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/SHUTTERSTOCK
Wata sabuar girgizar ƙasa ta afka wa yammacin Afghanistan - kwanaki bayan manyan girgizar ƙasa biyu da suka faru yankin da suka yi sanadin mutuwar mutum 1,000.
Hukumar binciken ƙarƙashin ƙasa ta Amurka ta ce girgizar ƙasar mai ƙarfin maki 6.3 ta auka kusa da birnin Herat.
Hukumomin lafiyar yankin sun ce aƙalla mutum guda ya rasa ransa.
Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ce kimanin mutum 100 aka kwantar a asibiti domin yi musu magani.
Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Dinkin Duniya Unicef, ya ce fiye da kashi 90 na waɗanda suka mutu a girgizar ƙasar farko mata ne da ƙananna yara
A ranar Lahadin ta da gabata ne wata mummunar girgizar ƙasa ta auka wa ƙauyen Zindajan mai nisan kilomita 40 daga birnin Herat.
Rundunar sojin isar'ila ta ce aƙalla sojojinta 279 aka kashe tun ranar 7 ga watan Octoba, lokacin da ƙungiyar Hamas ta ƙaddamar da harin da rundunar ta kira 'na ba-zata'.
Sojojin sun ce mutanen Isra'ila, sojoji da fararen hula da suka mutu, tun bayan ɓarkewar rikicin ya zarta 1,300.
Cikin bayanan da rundunar ke fitarwa ta ce adadin 'yan ƙasar da ake riƙe da su a Gaza ya kai 126.
A baya dai Isar'ila ta ce mutum 150 ne ake riƙe da su a Gaza.

Asalin hoton, Defence HQ
Sojojin Najeriya ƙarƙashin rundunar Hadarin Daji mai yaƙi da 'yan fashin daji a arewacin Najeriya ta ce ta samu nasarar kuɓutar da wasu ɗaliban Jami'ar Tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara, da 'yan bindiga suka sace da da tsakar daren ranar Asabar 14 ga watan Octoba.
'Yan bindigar sun far wa ɗakunan kwanan ɗaliban da ke unguwar Sabon Gida, da ke yankin Damba a karamar hukumar Gusau, cikin dare a lokacin da daliban suka fara bacci.
Inda suka fara harbin kan mai tsautsayi, lamarin da ya sa suka yi garkuwa da ɗaliban.
Cikin wata sanarwar da Rundunar hadarin Daji ta fitar - mai ɗauke da sa hannun jami'in hulda da jama'a na rundunar, Kaftin Ibrahim Yahaya - ta ce rundunar ta samu nasarar kuɓutar da ɗaliban ne bayan da suka mayar da martani a kan lokaci yayin da aka sanar da su halin da ake ciki game da satar ɗaliban.
Sanarwar ta ce nan take rundunar haɗa kan dakarunta, inda suka datse hanyar da suke tunanin 'yan bindigar za su ɓullo, inda suka yi musayar wuta da 'yan bindigar.
"Matsin da 'yan bindigar suka sha ya tilasta musu tserewa tare da barin ɗaliban", in ji sanarwar.
A lokacin musayar wutar- wadda aka yi da misalin ƙarfe12 na dare, dalibai biyu sun samu guduwa da kansu, yayin da jami'an tsaro suka ceto biyu.
A baya- bayan nan 'yan bindiga sun ɓullo da salon kai wa ɗaliban jami'o'i hari tare da sace su a ɗakunan kwanansu.
Ko a watan Satumba ma sai da 'yan bindigar suka kai wa ɗaliban na FUGUS hari a ɗakunan kwanansu inda suka sace ɗalibai masu yawa, wani lamari da ya tayar da ƙura a ƙasar.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar Lafiya ta Duniya, ta ce umarnin da Isra'ila ta bayar na kwashe marasa lafiya a asibitoci fiye da 20 a arewacin Gaza daidai yake da hukuncin kisa ga mutanen da ke kwance asibitin suna jinya.
Hukumar ta yi nuni da mutanen da ke cikin halin rai kwakwai-mutu-kwakwai ko kuma jariran da ke cikin kwalba.
Tuni asibitocin Gaza suka shiga cikin wani yanayi na tashin hankali da rudani.
Wata jami'ar WHO ta ce halin da Gaza ke ciki na da matuƙar tayar da hankali, dangane da ko mutum ya tsaya ko kuma ya fice, abin da muke gani shi ne yadda aka lalata yankin.
Likitoci sun shaida wa BBC cewa, ana ƙarancin magunguna a asibitocin sannan kuma man da ya rage musu da ake amfani da shi a injinansu bai taka kara ya karya ba.