Isra'ila na shirin kai hare-hare a Gaza 'ta ruwa, sama da ƙasa'

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Umar Mikail

  1. Labarai da dumi-dumi, An gano gawarwakin wasu 'yan Isra'ila da Hamas ta yi garkuwa da su

    Sojojin Isra'ila sun gano gawarwakin wasu 'yan Isra'ila da ƙungiyar Hamas ta yi garkuwa da su lokacin harin da ta kai makon da ya gabata.

    Kafofin yaɗa labaran Isra'ila sun ce an gano gawarwakin ne a lokacin wani samame ta ƙasa da sojojin Isra'ila suka kai birnin Gaza ranar Juma'a.

    Rahotonni sun ce sojojin Isra'ila sun gano gawarwakin 'yan ƙasar da ba afayyace adadinsu ba, inda aka mayar da su Isra'ila.

    Haka kuma a lokacin samamen an gano wasu kayayyakin mutanen da Hamas din ta yi garkuwa da su.

  2. MDD na tattauna yadda za a tsagaita wuta a Gaza

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya na tattaunawa a kan kiraye-kirayen yadda za a tsagaita wuta a Gaza a yayin wani taron sirri da yake gudanarwa.

    Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya yi gargaɗin cewa yanayin da ake ciki ya kai wani sabon mataki mai haɗari.

    Ya ce kwashe mutane fiye da miliyan guda daga fagen daga zuwa wurin da babu abinci ba ruwa ko wajen zama babban haɗari ne.

    Rasha ta bayar da shawarar yadda za a shawo kan matsalar tare da kiran a tsagaita wuta da samar da kayan agaji tare da Alla-wadai da duk wani abu na tashin hankali da ta'addanci.

  3. Blinken na ziyara a Saudiyya kan rikicin Isra'ila da Hamas

    s

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken na wata ziyara a Saudiyya karo na biyar da yake yi a kasashe shida na Larabawa

    Mista Blinken na ziyarar ne domin ganin rikicin Hamas da Isra'ila bai bazu a yankin ba.

    Jami'in na Amurka na son asashen Larabawan su fito fili su soki Hamas tare da jure wa irin martanin da Isra'ila ke mayarwa.

    Ziyarar tasa na zuwa ne a daidai lokacin da ma'aikatar harkokin wajen Saudiyya ta fitar da kakkausar suka ta yin alla-wadai da Isra'ila da kuma Alla-wadai da hare haren da ta ce ana kai wa fararen hular da ba su da kariya.

  4. Sojojin Isra'ila sun ƙaddamar da hare-hare cikin Gaza

    w

    Asalin hoton, Reuters

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce tuni ta kaddamar da hare hare a cikin Gaza, kafin daga bisani ta fara kai hare hare ta kasa.

    Mai magana da yawun rundunar ya ce manufar hakan ita ce a kawar da 'yan ta'adda da kuma neman mutanen da aka yi garkuwa da su a lokacin da Hamas ta kai hari mako guda da ya gabata.

    Sojojin Isra'ila sun ce sun tare wasu hare hare ta sama da aka kai musu a kusa da birnin Haifa a ranar Juma'a.

    Da ya ke jawabi a wajen taron, jakadan Falasdinawa a Majalisar Dinkin Duniya Riyad Mansour ya yi kiran da a tsagaita wuta.

    Ya ce, ''akwai abubuwa uku da muke so a cimma, na farko tsagaita wuta, kanmu a haɗe yake a matsayinmu na ƙungiyar Larabawa ga waɗanda ke tunanin cewa ba haka bane''.

  5. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa Kai-tsaye, barkanmu da safiyar wannan rana ta Asabar.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya, musamman kan rikicin Isra'ila da Falasɗinu.

    Kuna iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta da muhawara.

    Ku biyo mu ...